Back to Languages

Hausa - Chapter 37 - As-Saffat

Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink

Verse 1 — Surah As-Saffat 37:1

Inã rantsuwa da mãsu yin sahu-sahu (a cikin salla kõ yãƙi)

Verse 2 — Surah As-Saffat 37:2

Sa'an nan mãsu yin tsãwa* dõmin gargaɗi

Verse 3 — Surah As-Saffat 37:3

Sa'an nan da mãsu karãtun abin tunãtarwa

Verse 4 — Surah As-Saffat 37:4

Lalle Abin bautawarku haƙĩƙa ¦aya ne

Verse 5 — Surah As-Saffat 37:5

Ubangijin sammai da ƙasã da abin da ke tsakãninsu, kuma Ubangijin wurãren fitar rãnã

Verse 6 — Surah As-Saffat 37:6

Lalle Mũ, Mun ƙãwatãr da sama ta kusa da wata ƙawa, watau taurãri

Verse 7 — Surah As-Saffat 37:7

Kuma sunã tsari daga dukan Shaiɗan mai tsaurin kai

Verse 8 — Surah As-Saffat 37:8

Bã zã su iya saurãre zuwa ga jama'a mafi ɗaukaka (Malã'iku) ba, kuma anã jĩfar su daga kõwane gẽfe

Verse 9 — Surah As-Saffat 37:9

Dõmin tunkuɗẽwa kuma sunã da wata azãba tabbatacciya

Verse 10 — Surah As-Saffat 37:10

Fãce wanda ya fizgi wata kalma, sai yũla mai haske ta bĩ shi

Verse 11 — Surah As-Saffat 37:11

Ka tambaye su: "Shin sũ ne mafi wuya ga halittawa, kõ, kuwa waɗanda Muka halitta?" Lalle Mũ, Mun halitta su daga lãkã mai ɗauri

Verse 12 — Surah As-Saffat 37:12

Ã'a, kã yi mãmãki, alhãli kuwa sunã ta yin izgili

Verse 13 — Surah As-Saffat 37:13

Kuma idan aka tunãtar da su, bã su tunãwa

Verse 14 — Surah As-Saffat 37:14

Idan suka ga wata ãyã, sai su dinga yin izgili

Verse 15 — Surah As-Saffat 37:15

Kuma su ce, "Wannnan bã kõme ba, fãce sihiri, ne bayyananne

Verse 16 — Surah As-Saffat 37:16

Shin, idan mun mutu, kuma muka kasance turɓaya da kasũsuwa, ashe, lalle mũ tabbas waɗandaake tãyarwa ne

Verse 17 — Surah As-Saffat 37:17

Ashe kõ da ubanninmu na farko

Verse 18 — Surah As-Saffat 37:18

Ka ce: "Na'am alhãli kuwa kunã ƙasƙantattu

Verse 19 — Surah As-Saffat 37:19

Tsãwa guda kawai ce, sai gã su, sunã dũbi

Verse 20 — Surah As-Saffat 37:20

Kuma su ce: "Yã bonenmu! Wannan ita ce rãnar sakamako

Verse 21 — Surah As-Saffat 37:21

Wannan ita ce rãnar rarrabẽwa wadda kuka kasance kuna ƙaryatãwa

Verse 22 — Surah As-Saffat 37:22

Ku tãra waɗanda suka yi zãlunci, da abõkan haɗinsu, da abin da suka kasance sunã bautãwa

Verse 23 — Surah As-Saffat 37:23

Wanin Allah, sabõda haka ku shiryar da su zuwa ga hanyar Jahĩm

Verse 24 — Surah As-Saffat 37:24

Kuma ku tsayar da su, lalle su, waɗanda ake yi wa tambaya ne

Verse 25 — Surah As-Saffat 37:25

Me ya sãme ku, bã ku taimakon jũna

Verse 26 — Surah As-Saffat 37:26

Ã'a, sũ a yau, mãsu sallamãwa ne

Verse 27 — Surah As-Saffat 37:27

Kuma sãshensu ya fuskanta ga sãshe, sunã tambayar jũna

Verse 28 — Surah As-Saffat 37:28

Suka ce: "Lalle kũ, kun kasance kunã jẽ mana daga wajen dãma (inda muka amince)

Verse 29 — Surah As-Saffat 37:29

Suka ce: "Ã'a, ba ku kasance mũminai ba

Verse 30 — Surah As-Saffat 37:30

Kuma wani dalĩli bai kasance ba gare mu a kanku. Ã'a, kun kasance mutãne ne mãsu kẽtare iyãka

Verse 31 — Surah As-Saffat 37:31

Sabõda haka maganar Ubangijinmu ta wajaba a kanmu. Lalle mũ, mãsu ɗanɗanãwa ne

Verse 32 — Surah As-Saffat 37:32

Sabõda haka muka ɓatar da ku. Lalle mũ, mun kasance ɓatattu

Verse 33 — Surah As-Saffat 37:33

To lalle sũ a rãnar nan, mãsu tãrayya ne a cikin azãbar

Verse 34 — Surah As-Saffat 37:34

Lalle Mũ, kamar haka Muke aikatãwa game, da mãsu laifi

Verse 35 — Surah As-Saffat 37:35

Lalle sũ, sun kasance idan an ce musu: "Bãbu abin bautãwa, fãce Allah," sai su dõra girman kai

Verse 36 — Surah As-Saffat 37:36

Kuma sunã cẽwa, "Shin, mũ lalle mãsu barin gumãkanmu ne, sabõda maganar wani mawãƙi mahaukaci

Verse 37 — Surah As-Saffat 37:37

Ã'a, yã zo da gaskiya kuma ya gaskata Manzanni

Verse 38 — Surah As-Saffat 37:38

Lalle kũ, haƙĩƙa mãsu ɗanɗana azãba mai raɗaɗi ne

Verse 39 — Surah As-Saffat 37:39

Kuma bã zã a sãka muku ba fãce da abin da kuka kasance kunã aikatãwa

Verse 40 — Surah As-Saffat 37:40

Fãce bãyin Allah waɗanda aka tsarkake

Verse 41 — Surah As-Saffat 37:41

Waɗannan sunã da abinci sananne

Verse 42 — Surah As-Saffat 37:42

Ya'yan itãcen marmari, kuma sunã waɗanda ake girmamãwa

Verse 43 — Surah As-Saffat 37:43

A cikin gidãjen Aljannar ni'ima

Verse 44 — Surah As-Saffat 37:44

A kan karagu, sunã mãsu fuskantar jũna

Verse 45 — Surah As-Saffat 37:45

Anã kẽwayãwa a kansu da hinjãlan giya, ta daga waɗansu marẽmari

Verse 46 — Surah As-Saffat 37:46

Farã mai dãɗi ga mashãyan

Verse 47 — Surah As-Saffat 37:47

A cikinta bãbu jirĩ kuma ba su zama mãsu mãye daga gare ta ba

Verse 48 — Surah As-Saffat 37:48

Kuma a wurinsu, akwai mãtan aure mãsu taƙaita kallonsu, mãsu manyan idãnu

Verse 49 — Surah As-Saffat 37:49

Kamar dai su ƙwai ne ɓõyayye

Verse 50 — Surah As-Saffat 37:50

Sai sãshensu ya fuskanta a kan sãshe, sunã tambayar jũna

Verse 51 — Surah As-Saffat 37:51

Wani mai magana daga cikinsu ya ce: "Lalle ni wani abõki ya kasance a gare ni (a dũniya)

Verse 52 — Surah As-Saffat 37:52

Yanã cewa, "Shin, kai lalle, kanã daga mãsu gaskatãwa ne

Verse 53 — Surah As-Saffat 37:53

Ashe, idan muka mutu, kuma muka, kasance turɓaya da kasũsuwa, ashe, lalle, mũ tabbas waɗanda ake sãka wa ne

Verse 54 — Surah As-Saffat 37:54

(Mai maganar) ya ce: "Shin, kõ ku, mãsu tsinkãya ne (mu gan shi)

Verse 55 — Surah As-Saffat 37:55

Sai ya tsinkãya, sai ya gan shi a cikin tsakar Jahim

Verse 56 — Surah As-Saffat 37:56

Ya ce (masa), "Wallahi, lalle, kã yi kusa, haƙĩƙã, ka halakãni

Verse 57 — Surah As-Saffat 37:57

Kuma bã dõmin ni'imar Ubangijĩna ba, lalle, dã na kasance daga waɗanda ake halartarwa (tãre da kai a cikin wutã)

Verse 58 — Surah As-Saffat 37:58

Shin fa, ba mu zama mãsu mutuwa ba

Verse 59 — Surah As-Saffat 37:59

Sai mutuwarmu ta farko, kuma ba mu zama waɗanda ake azabtarwa ba

Verse 60 — Surah As-Saffat 37:60

Lalle, wannan shĩ ne babban rabo mai girma

Verse 61 — Surah As-Saffat 37:61

Sabõda irin wannan, sai mãsu aiki su yi ta aikatãwa

Verse 62 — Surah As-Saffat 37:62

Shin wancan shĩ ne mafi zama alhẽri ga liyafa kõ itãciyar zaƙƙũm

Verse 63 — Surah As-Saffat 37:63

Lalle, Mũ, Mun sanya ta fitina ga. azzãlumai

Verse 64 — Surah As-Saffat 37:64

Lalle ita wata itãciya ce wadda take fita daga asalin Jahĩm

Verse 65 — Surah As-Saffat 37:65

Gundarta, kamar dai shi kãnun Shaiɗan ne

Verse 66 — Surah As-Saffat 37:66

To, lalle sũ haƙĩƙa mãsu ci ne daga gare ta. Sa'an nan mãsu cika cikuna ne daga gare ta

Verse 67 — Surah As-Saffat 37:67

Sa'an nan lalle sunã da wani garwaye a kanta, daga ruwan zãfi

Verse 68 — Surah As-Saffat 37:68

Sa'an nan lalle makomarsu, haƙĩƙa, zuwa ga Jãhĩm take

Verse 69 — Surah As-Saffat 37:69

Lalle sũ, sun iske ubanninsu batattu

Verse 70 — Surah As-Saffat 37:70

Sabõda haka sũ, a kan gurãbunsu, suke gaggãwa

Verse 71 — Surah As-Saffat 37:71

Kuma tabbas haƙĩƙa mafi yawan mutãnen farko sun ɓace a gabãninsu

Verse 72 — Surah As-Saffat 37:72

Kuma tabbas haƙĩƙa, Mun aika mãsu gargaɗi a cikinsu

Verse 73 — Surah As-Saffat 37:73

Sai ka dũba yadda ãƙibar waɗanda aka yi wa gargaɗi ta kasance

Verse 74 — Surah As-Saffat 37:74

Fãce bãyin Allah waɗanda aka tsarkake

Verse 75 — Surah As-Saffat 37:75

Kuma lalle, haƙĩƙa' Nũhu ya kira Mu. To, madalla da mãsu karɓãwa, Mu

Verse 76 — Surah As-Saffat 37:76

Kuma Mun tsĩrar da shi da mutãnensa daga bakin ciki babba

Verse 77 — Surah As-Saffat 37:77

Muka sanya zurriyarsa sunã mãsu wanzuwa

Verse 78 — Surah As-Saffat 37:78

Kuma Muka bar masa (yabo) a cikin jama'ar ƙarshe

Verse 79 — Surah As-Saffat 37:79

Aminci ya tabbata ga Nũhu, a cikin halittu

Verse 80 — Surah As-Saffat 37:80

Lalle Mũ kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa

Verse 81 — Surah As-Saffat 37:81

Lalle shi, yanã daga bãyin Mu mũminai

Verse 82 — Surah As-Saffat 37:82

Sã'an nan Muka nutsar da waɗansunsu

Verse 83 — Surah As-Saffat 37:83

Kuma lalle daga ƙungiyarsa, haƙĩƙa, Ibrahĩm yake

Verse 84 — Surah As-Saffat 37:84

A lõkacin da ya je wa ubangijinsa da zũciya kuɓutacciya

Verse 85 — Surah As-Saffat 37:85

A lõkacin da ya ce wa ubansa da mutãnensa, "Mẽne ne kuke bautãwa

Verse 86 — Surah As-Saffat 37:86

Shin, ƙiren ƙarya (wãtau) gumãka, wanin Allah, kuke bautãwa

Verse 87 — Surah As-Saffat 37:87

To, mẽne ne zatonku game da Ubangijin halittu

Verse 88 — Surah As-Saffat 37:88

Sai ya yi dũbi, dũba ta sõsai, a cikin taurãri

Verse 89 — Surah As-Saffat 37:89

Sã'an nan ya ce: "Nĩ mai rashin lãfiya ne

Verse 90 — Surah As-Saffat 37:90

Sai suka jũya ga barinsa, sunã mãsu jũyãwa da bãya

Verse 91 — Surah As-Saffat 37:91

Sai ya karkata zuwa ga gumãkansu, sa'an nan ya ce: "Ashe bã zã ku ci ba

Verse 92 — Surah As-Saffat 37:92

Me ya sãme ku, bã ku magana

Verse 93 — Surah As-Saffat 37:93

Sai ya zuba dũka a kansu da hannun dãma

Verse 94 — Surah As-Saffat 37:94

Sai suka fuskanto zuwa gare shi, sunã gaggãwa

Verse 95 — Surah As-Saffat 37:95

Ya ce, "Kunã bauta wa abin da kuke sassaƙawa

Verse 96 — Surah As-Saffat 37:96

Alhãli, Allah ne Ya halitta ku game da abin da kuke aikatãwa

Verse 97 — Surah As-Saffat 37:97

Suka ce: "Ku gina wani gini sabõda shi, sa'an nan ku jẽfa shi a cikin Jahĩm

Verse 98 — Surah As-Saffat 37:98

Sabõda haka suka yi nufin makĩda game da shi. Sai Muka sanya su, sũ ne mafi ƙasƙanci

Verse 99 — Surah As-Saffat 37:99

Kuma (Ibrahĩm] ya ce: "Lalle, nĩ mai tafiya ne zuwa ga Ubangijĩna, zai shiryar da ni

Verse 100 — Surah As-Saffat 37:100

Ya Ubangijĩna! Ka bã ni (abõkin zama) daga sãlihan mutãne

Verse 101 — Surah As-Saffat 37:101

Sai Muka yi masa bushãra da wani yãro *mai haƙuri

Verse 102 — Surah As-Saffat 37:102

To, a lõkacin da ya isa aiki tãre da shi, ya ce: "Ya ƙaramin ɗãna! Lalle ne inã gani, a ciki barci, lalle inã yanka ka. To, ka dũba mẽ ka gani?" (Yãron) ya ce: "Ya, Bãbãna! Ka aikata abin da aka umurce ka, zã ka sãme ni, in Allah Ya so, daga mãsu haƙuri

Verse 103 — Surah As-Saffat 37:103

Yayin da suka mika wuya sai muka fansheshi da Rago

Verse 104 — Surah As-Saffat 37:104

Kuma Muka kira shi cẽwa "Ya Ibrahĩm

Verse 105 — Surah As-Saffat 37:105

Haƙĩƙa kã gaskata mafarkin." Lalle kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa

Verse 106 — Surah As-Saffat 37:106

Lalle wannan ita ce jarrabãwa bayyananna

Verse 107 — Surah As-Saffat 37:107

Kuma Muka yi fansar yãron da wani abin yanka, mai girma

Verse 108 — Surah As-Saffat 37:108

Kuma Muka bar (yabo) a kansa a cikin mutãnen ƙarshe

Verse 109 — Surah As-Saffat 37:109

Aminci ya tabbata ga Ibrãhĩm

Verse 110 — Surah As-Saffat 37:110

Kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa

Verse 111 — Surah As-Saffat 37:111

Lalle shĩ, yanã daga bãyinMu mũminai

Verse 112 — Surah As-Saffat 37:112

Kuma Muka yi masa bushãra* Da Is'hãƙa ya zama Annabi daga sãlihan mutãne

Verse 113 — Surah As-Saffat 37:113

Kuma Muka yi albarka a gare shi, kuma ga Is'hãka. Kuma daga cikin zurriyarsu akwai mai kyautatãwa da kuma maizãlunci dõmin kansa, mai bayyanãwa (ga zãluncin)

Verse 114 — Surah As-Saffat 37:114

Kuma lalle, Mun yi ni'ima ga Mũsã da Hãrũna

Verse 115 — Surah As-Saffat 37:115

Kuma Muka tsĩrar da su da mutãnensu daga bakin ciki mai girma

Verse 116 — Surah As-Saffat 37:116

Kuma Muka taimake su, sabõda haka suka kasance mãsu rinjãya

Verse 117 — Surah As-Saffat 37:117

Kuma Muka ba su Littãfi mai iyãkar bayãni

Verse 118 — Surah As-Saffat 37:118

Kuma Muka shiryar da su ga hanya mĩƙaƙƙiya

Verse 119 — Surah As-Saffat 37:119

Kuma Muka bar (yabo) a gare su a cikin mutãnen karshe

Verse 120 — Surah As-Saffat 37:120

Aminci ya tabbata ga Mũsã da Hãruna

Verse 121 — Surah As-Saffat 37:121

Lalle kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa

Verse 122 — Surah As-Saffat 37:122

Lalle, sunã daga bãyin Mu mũminai

Verse 123 — Surah As-Saffat 37:123

Kuma lalle Ilyãs, haƙĩƙa, yanã daga Manzanni

Verse 124 — Surah As-Saffat 37:124

A lõkacin da yake ce wa mutãnensa, "Ashe, bã zã ku yi taƙawa ba

Verse 125 — Surah As-Saffat 37:125

Shin, kunã bauta wa Ba'al ne, kuma kunã barin Mafi kyautatãwar mãsu halitta

Verse 126 — Surah As-Saffat 37:126

Allah Ubangijinku, kuma Ubangijin ubanninku farko

Verse 127 — Surah As-Saffat 37:127

Sai suka ƙaryata shi. Sabõda haka sũ lalle waɗanda zã a halartãwa ne (a wutã)

Verse 128 — Surah As-Saffat 37:128

Sai bãyin Allah waɗanda aka tsarkake

Verse 129 — Surah As-Saffat 37:129

Kuma Muka bar (yabo) a gare shi, a cikin mutãnen ƙarshe

Verse 130 — Surah As-Saffat 37:130

Aminci ya tabbata ga Ilyãs

Verse 131 — Surah As-Saffat 37:131

Lalle Mũ kamar haka Muke sãka wa mãsu kyautatãwa

Verse 132 — Surah As-Saffat 37:132

Lalle shĩ, yanã daga bãyin Mu mũminai

Verse 133 — Surah As-Saffat 37:133

Kuma lalle Lũdu, haƙĩƙa, yanã daga Manzanni

Verse 134 — Surah As-Saffat 37:134

A lõkacin da Muka tsĩrar da shi, da mutãnensa gabã ɗaya

Verse 135 — Surah As-Saffat 37:135

Sai wata tsõhuwa tanã a cikin mãsu wanzuwa (a cikin azãba)

Verse 136 — Surah As-Saffat 37:136

Sã'an nan Muka darkãke waɗansu mutãnen

Verse 137 — Surah As-Saffat 37:137

Kuma lalle kũ, haƙĩƙa, kunã shũɗewa a kansu, kunã mãsu asubanci

Verse 138 — Surah As-Saffat 37:138

Kuma da dare. Shin fa, bã zã ku hankalta ba

Verse 139 — Surah As-Saffat 37:139

Kuma lalle Yũnusa, haƙĩƙa, yanã daga Manzanni

Verse 140 — Surah As-Saffat 37:140

A lõkacin da ya gudu zuwa ga jirgin ruwa wanda aka yi wa lõdi

Verse 141 — Surah As-Saffat 37:141

Sã'an nan ya yi ƙuri'a, sai ya kasance a cikin waɗanda aka rinjaya

Verse 142 — Surah As-Saffat 37:142

Sai kĩfi ya yi lõma da shi, alhãli kuwa yanã wanda ake zargi

Verse 143 — Surah As-Saffat 37:143

To, ba dõmin lalle shi ya kasance daga mãsu tasbĩhi ba

Verse 144 — Surah As-Saffat 37:144

Lalle dã ya zauna a cikin cikinsa har ya zuwa rãnar da zã a tãyar da su

Verse 145 — Surah As-Saffat 37:145

Sai Muka jẽfa shi ga wani fĩli alhãli kuwa yanã mai raunin rashin lãfiya

Verse 146 — Surah As-Saffat 37:146

Kuma Muka tsirar da wata itãciya ta kankana a kusa da shi

Verse 147 — Surah As-Saffat 37:147

Kuma Muka aika shi zuwa ga waɗansu mutãne dubuɗari, kõ sunã ƙaruwa (a kan haka)

Verse 148 — Surah As-Saffat 37:148

Sai suka yi ĩmãni sabõda haka Muka jiyar da su dãdi har wani lõkaci

Verse 149 — Surah As-Saffat 37:149

Sabõda haka, ka tambaye su, "Shin, Ubangijinka ne da 'ya'ya mãtã, kuma su da ɗiya maza

Verse 150 — Surah As-Saffat 37:150

Kõ kuma Mun halitta malã'iku mãtã ne, alhãli kuwa sũ sunãhalarce

Verse 151 — Surah As-Saffat 37:151

To! Lalle sũ, daga ƙiren ƙaryarsu sunã cẽwa

Verse 152 — Surah As-Saffat 37:152

Allah Yã haihu," alhãli kuwa lalle sũ, haƙĩƙa maƙaryata ne

Verse 153 — Surah As-Saffat 37:153

Shin, Yã zãɓi 'yã'ya mãtã ne a kan ɗiya maza

Verse 154 — Surah As-Saffat 37:154

Mẽ ya same ku? Yãya kuke hukuntãwa (wannan hukunci)

Verse 155 — Surah As-Saffat 37:155

Verse 156 — Surah As-Saffat 37:156

Ko kuma kunã da wani dalĩli bayyananne ne

Verse 157 — Surah As-Saffat 37:157

To, ku zo da littãfinku idan kun kasance mãsu gaskiya

Verse 158 — Surah As-Saffat 37:158

Kuma suka sanya nasaba a tsakãnin Sa da tsakãnin aljannu. Alhãli kuwa Lalle aljannu sun sani, "Lalle sũ, haƙĩƙa waɗanda ake halartarwa ne (a cikin wutã)

Verse 159 — Surah As-Saffat 37:159

Tsarki ya tabbata ga Allah daga abin da suke siffantãwa

Verse 160 — Surah As-Saffat 37:160

Sai bãyin Allah waɗanda aka tsarkake

Verse 161 — Surah As-Saffat 37:161

To, lalle, ku da abin da kuke bautãwa

Verse 162 — Surah As-Saffat 37:162

Ba ku zama mãsu buwãya ba a gare Shi

Verse 163 — Surah As-Saffat 37:163

Sai wanda yake mai shiga babbar wutã Jahĩm

Verse 164 — Surah As-Saffat 37:164

Kuma bãbu kõwa daga cikinmu,* fãce yanã da matsayi sananne

Verse 165 — Surah As-Saffat 37:165

Kuma lalle mu, haƙĩƙa, mũ ne mãsu yin sahu-sahu (dõmin ibãda)

Verse 166 — Surah As-Saffat 37:166

Kuma lalle mũ haƙĩƙa, mũ ne mãsu yin tasbĩhi

Verse 167 — Surah As-Saffat 37:167

Kuma lalle sũ, sun kasance sunã cẽwa

Verse 168 — Surah As-Saffat 37:168

Dã lalle munã da wani littãfi irin na mutãnen farko

Verse 169 — Surah As-Saffat 37:169

Lalle dã mun kasance bãyin Allah waɗanda aka tsarkake

Verse 170 — Surah As-Saffat 37:170

Sai suka kãfirta da shi. Sabõda haka zã su sani

Verse 171 — Surah As-Saffat 37:171

Kuma lalle, haƙĩƙa kalmar Mu ta gabãta ga bãyinMu, Manzanni

Verse 172 — Surah As-Saffat 37:172

Lalle sũ, haƙĩƙa, sũ ne waɗanda ake taimako

Verse 173 — Surah As-Saffat 37:173

Kuma lalle rundunarMu, haƙĩƙa, sũ ne marinjaya

Verse 174 — Surah As-Saffat 37:174

Sabõda haka juya daga barinsu, har a wani lõkaci

Verse 175 — Surah As-Saffat 37:175

Ka nũna musu (gaskiya), da haka zã su dinga gani

Verse 176 — Surah As-Saffat 37:176

Shin fa, da azabarMu suke nẽman gaggãwa

Verse 177 — Surah As-Saffat 37:177

To, idan ta sauka ga farfãjiyarsu, to, sãfiyar wadanda ake yi wa gargaɗi ta mũnana

Verse 178 — Surah As-Saffat 37:178

Kuma ka jũya daga barinsu har a wani lõkaci

Verse 179 — Surah As-Saffat 37:179

Ka nũna (musu gaskiya), da haka zã su dinga nũnãwa

Verse 180 — Surah As-Saffat 37:180

Tsarki ya tabbata ga Ubangijinka, Ubangijin rinjãye, daga barin abin da suke siffantãwa

Verse 181 — Surah As-Saffat 37:181

Kuma aminci ya tabbata ga Manzanni

Verse 182 — Surah As-Saffat 37:182

Kuma gõdiya ta tabbata ga Allah Ubangijin halittu