Back to Languages

Hausa - Chapter 38 - Sad

Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink

Verse 1 — Surah Sad 38:1

Ṣ̃, Inã rantsuwa da Al-ƙur'ãni mai hukunce-hukunce

Verse 2 — Surah Sad 38:2

Ã'a, waɗanda suka kãfirta sunã cikin girman kai (ga rikon al'ãdunsu) da sãɓãni (tsakãnin jũnansu)

Verse 3 — Surah Sad 38:3

Da yawa Muka halakar da wani ƙarni, a gabãninsu, suka yi kira (nẽman cẽto), bãbu lõkacin kuɓucewa

Verse 4 — Surah Sad 38:4

Kuma suka yi mãmãki dõmin Mai gargaɗi, daga cikinsu, ya je musu. Kuma kãfirai sukace, "Wannan mai sihiri ne, maƙaryaci

Verse 5 — Surah Sad 38:5

Shin, yã sanya gumãka duka su zama abin bautawa guda? Lalle wannan, haƙĩƙa, abu ne mai ban mãmaki

Verse 6 — Surah Sad 38:6

Shũgabanni daga cikinsu, suka tafi (suka ce),"Ku yi tafiyarku, ku yi haƙuri a kan abũbuwan bautawarku. Lalle wannan, haƙiƙa, wani abu ne ake nufi

Verse 7 — Surah Sad 38:7

Ba mu taɓa ji ba, game da wannan a cikin addinin ƙarshe. Wannan bai zama ba fãce ƙiren ƙarya

Verse 8 — Surah Sad 38:8

Shin, an saukar da Alƙur'ãni ne a kansa, a tsakãninmu (mũ kuma ba mu gani ba)?" Ã'a, su dai sunã cikin shakka daga hukunciNa Ã'a, ba su i da ɗanɗanar azãba ba

Verse 9 — Surah Sad 38:9

Ko kuma a wurinsu ne ake ajiye taskõkin rahamar Ubangijinka, Mabuwãyi, Mai yawan kyauta

Verse 10 — Surah Sad 38:10

Kõ kuma sũ ne da mallakar sammai da ƙasã da abin da ke a tsakãninsu? To sai su hau a cikin sammai (dõmin, su hana saukar Alƙur'ãni ga Muhammadu)

Verse 11 — Surah Sad 38:11

Rundunõni ne abin da ke can, rusassu, na ƙungiyõyinsu

Verse 12 — Surah Sad 38:12

Mutãnen Nũhu sun ƙaryata, a gabãninsu, da Ãdãwa da Fir'auna mai turãkun (da suka kafe mulkinsa)

Verse 13 — Surah Sad 38:13

Da Samũdãwa da mutãnen Luɗu da ma'abũta ƙunci, *waɗancan ne ƙungiyõyin

Verse 14 — Surah Sad 38:14

Bãbu kõwa a cikinsu fãce ya ƙaryata Manzanni, sabõda haka azãbãTa ta wajaba

Verse 15 — Surah Sad 38:15

Kuma waɗannan *bã su jiran kõme fãce tsãwã guda, wadda bã ta da hani

Verse 16 — Surah Sad 38:16

Kuma suka ce: "Ya Ubangijinmu! Ka gaggauta mana da rabonmu, a gabãnin rãnar bincike

Verse 17 — Surah Sad 38:17

Ka yi haƙuri bisa ga abin da suke faɗa (na izgili), kuma ka ambaci bãwan Mu Dãwũda ma'abũcin ƙarfin ibãda. Lalle, shi, mai mayar da al'amari ga Allah ne

Verse 18 — Surah Sad 38:18

Lalle Mũ, Mun hõre duwãtsu tãre da shi, sunã yin tasbĩhi maraice da fitõwar rãnã

Verse 19 — Surah Sad 38:19

Da tsuntsãye waɗanda ake tattarawa, kõwannensu mai kõmãwa ne a gare shi

Verse 20 — Surah Sad 38:20

Kuma Muka ƙarfafa mulkinsa, kuma Muka bã shi hikima* da rarrabẽwar magana

Verse 21 — Surah Sad 38:21

Kuma shin, lãbãrin mãsu husũma ya zo maka, a lõkacin da suka haura gãrun masallaci

Verse 22 — Surah Sad 38:22

A lõkacin da suka shiga ga Dãwũda, sai ya firgita daga gare su. Suka ce: "Kada kaji tsõro, masu husuma biyu ne; sãshenmu ya zãlunci sãshe. Sabõda haka, ka yi hakunci a tsakãninmu da gaskiya. Kada ka ƙẽtare haddi kuma ka shiryar da mu zuwa, ga tsakar hanya

Verse 23 — Surah Sad 38:23

Lalle wannan dan'uwãna ne, yanã da tunkiya casa'in da tara, kuma inã da tunkiya guda, sai ya ce: 'Ka lãmunce mini ita. Kuma ya buwãye ni ga magana

Verse 24 — Surah Sad 38:24

(Dãwũda) ya ce: "Lalle, haƙiƙa ya zãlunce* ka game da tambayar tunkiyarka zuwa ga tumakinsa. Kuma lalle ne mãsu yawa daga abõkan tarayya, haƙiƙa, sãshensu na zambatar sãshe fãce waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai." Kuma Dãwũda ya tabbata cẽwa Mun fitine shi ne, sabõda haka, ya nẽmi Ubangijinsa gãfara, kuma ya fãɗi yanã mai sujada, kuma ya mayar da al'amari ga Allah

Verse 25 — Surah Sad 38:25

Sabõda haka Muka gãfarta masa wancan, kuma lalle yanã da wata kusantar daraja a wurin Mu, da kyaun makõma

Verse 26 — Surah Sad 38:26

Yã Dãwũda! Lalle Mũ Mun sanya ka Halĩfa a cikin ƙasã. To, ka yi hukunci tsakãnin mutãne da gaskiya, kuma kada ka biye wa son zũciyar, har ya ɓatar dakai daga hanyar Allah. Lalle waɗanda ke ɓacẽwa daga hanyar Allah sunã da wata azãba mai tsanani dõmin abin da suka manta, a rãnar hisãbi

Verse 27 — Surah Sad 38:27

Kuma ba Mu halitta sama da ƙasã da abin da ke a tsakãninsu ba a kan ƙarya. Wannan shĩ ne zaton waɗanda suka kãfirta. To, bone ya tabbata ga waɗanda suka kãfirta daga wutã

Verse 28 — Surah Sad 38:28

Kõ zã Mu sanya waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai kamar waɗanda suke mãsu barna ne a cikin ƙasa? Ko kuma za Mu sanya masu bin Allah da taƙawa kamar fãjirai makarkata

Verse 29 — Surah Sad 38:29

(Wannan) Littãfi ne, Mun saukar da shi zuwa gare ka, yanã, mai albarka, dõmin su lũra da ãyõyinsa, kuma don mãsu hankali su riƙa yin tunãni

Verse 30 — Surah Sad 38:30

Kuma Muka bai wa Dãwũda Sulaimãn. Mãdalla da bãwanMu, shi. Lalle shi (Sulaimãn) mai mayar da al'amari ne ga Allah

Verse 31 — Surah Sad 38:31

A lõkacin da aka gitta masa dawãki mãsu asali, *a lõkacin maraice

Verse 32 — Surah Sad 38:32

Sai ya ce: "Lalle nĩ, na fĩfĩta son dũkiya daga tunãwar Ubangijina, har (rãnã) ta faku da shãmaki

Verse 33 — Surah Sad 38:33

Ku mayar da su a gare ni." Sai ya shiga yankansu* da takõbi ga ƙwabrukansu da wuyõyinsu

Verse 34 — Surah Sad 38:34

Kuma lalle haƙĩƙa, Mun fitini* Sulaiman kuma Muka jẽfa wani jikin mutum a kan karagarsa. Sa'an nan ya mayar da al'amari zuwa gare Mu

Verse 35 — Surah Sad 38:35

Ya ce: "Ya Ubangijĩna! Ka gãfarta mini, kuma Ka bã ni mulki wanda bã ya kamãta da kõwa daga bãyãna.* Lalle Kai, Kai ne Mai yawan kyauta

Verse 36 — Surah Sad 38:36

Sabõda haka Muka hõre masa iska* tanã gudu da umurninsa, tãna tãshi da sauƙi, inda ya nufa

Verse 37 — Surah Sad 38:37

Da shaiɗanu dukan mai gini, da mai nutsa (a cikin kõguna)

Verse 38 — Surah Sad 38:38

Waɗansu, ɗaɗɗaure a cikin marũruwa

Verse 39 — Surah Sad 38:39

Wannan kyautar Mu ce. Sai ka yi kyauta ga wanda kake so, ko kuma ka riƙe, bãbu wani bincike

Verse 40 — Surah Sad 38:40

Kuma lalle, haƙĩƙa yanã da kusantar daraja a wurin Mu da kyaun makõma

Verse 41 — Surah Sad 38:41

Kuma ka ambaci bãwan Mu Ayyũba* a lõkacin da ya kirãyi Ubangijinsa, ya ce: "Lalle nĩ, Shaiɗan yã shãfe ni da wahala da kuma wata azãba

Verse 42 — Surah Sad 38:42

Ka shura da ƙafarka. Wannan abin wanka ne mai sanyi da abin shã

Verse 43 — Surah Sad 38:43

Kuma Muka bã shi iyalansa da kwatankwacinsu tãre da su sabõda rahama daga gare Mu, da tunãtarwa ga mãsu hankali

Verse 44 — Surah Sad 38:44

Kuma ka riƙi wata ƙulla da hannunka, ka yi dũka da ita kuma kada ka karya rantsuwarka. Lalle Mũ, Mun sãme shi mai haƙuri. Madalla da bãwa, shĩ Lalle shĩ mai mayar da al'amari ga Allah ne

Verse 45 — Surah Sad 38:45

Kuma ka ambaci bãyin Mu: Ibrahĩm da ls'hãƙa da Ya'aƙũba, ma'abũta ƙarfin (ɗaukar umurnin Mu) da basĩra

Verse 46 — Surah Sad 38:46

Lalle Mũ, Mun keɓance su game da wata, tsattsarkar aba: Hukunce-hukuncen gidan dũniya (mai tunãtar da su Lãhira)

Verse 47 — Surah Sad 38:47

Kuma lalle sũ a wurin Mu, tabbas, sunã daga zãɓaɓɓu, mafĩfĩta

Verse 48 — Surah Sad 38:48

Kuma ka ambaci Isma'ĩla da llyãs da Zulkifli, kuma dukansu sunã daga zãɓaɓɓu

Verse 49 — Surah Sad 38:49

Wannan tunãtarwa ce, kuma lalle mãsu bin Allah da taƙawa, sunã da kyakkyawar makõma

Verse 50 — Surah Sad 38:50

Gidãjen Aljannar zama, alhãli kuwa tanã abar buɗe wa kõfõfi sabõda su

Verse 51 — Surah Sad 38:51

Sunã gingincire a cikinsu, sunã kira a cikinsu, ga 'ya'yan itãcen marmari mãsu yawa, da abin shã

Verse 52 — Surah Sad 38:52

Kuma a wurinsu akwai mãtan aure mãsu gajarta ganinsu ga mazansu, tsãrar jũna

Verse 53 — Surah Sad 38:53

Wannan shĩ ne abin da ake yi muku wa'adi ga rãnar hisãbi

Verse 54 — Surah Sad 38:54

Lalle wannan, haƙĩƙa, azurtarwar Mu ce, bã ta ƙãrẽwa

Verse 55 — Surah Sad 38:55

Wannan shĩ ne kuma lalle makangara, haƙĩƙa, sunã da mafi sharrin makõma

Verse 56 — Surah Sad 38:56

Jahannama, sunã shigarta. To, shimfiɗar tã mũnana, ita

Verse 57 — Surah Sad 38:57

Wannan shĩ ne! To, su ɗanɗane shi: ruwan zãfi ne da ruɓaɓɓen jini

Verse 58 — Surah Sad 38:58

Da wani daga siffarsa nau'i-nau'i

Verse 59 — Surah Sad 38:59

Wannan wani yanki ne mai kũtsawa tãre da ku, bãbu marãba a gare su, lalle sũ, mãsu shiga Wutã ne

Verse 60 — Surah Sad 38:60

Suka ce: "Ã'a, ku ne bãbu marãba a gare ku, kũ ne kuka gabãtar da shi a gare mu." To, matabbatar tã mũnana (ita wutar)

Verse 61 — Surah Sad 38:61

Suka ce: "Ya Ubangijinmu! Wanda ya gabãtar da wannan a gare mu, to, Ka ƙãra masa azãba, ninki, a cikin wutã

Verse 62 — Surah Sad 38:62

Kuma suka ce: "Mẽ ya sãme mu, bã mu ganin waɗansu mazãje, mun kasance munã ƙidãya su daga asharãrai

Verse 63 — Surah Sad 38:63

Shin, mun riƙe su abin izgili ne kõ idãnunmu sun karkata daga gare su ne

Verse 64 — Surah Sad 38:64

Lalle wannan, haƙĩƙa, gaskiya ne, husũmar mutãnen wutã

Verse 65 — Surah Sad 38:65

Ka ce: "Nĩ mai gargaɗikawai ne, kuma babu wani abin bautawa sai Allah, Makaɗaici, Mai tilastawa

Verse 66 — Surah Sad 38:66

Ubangijin sammai da ƙasã da abin da ke a tsakãninsu Mabuwãyi, Mai gãfara

Verse 67 — Surah Sad 38:67

Ka ce: "Shĩ (Alkur'ãni) babban lãbãri ne mai girma

Verse 68 — Surah Sad 38:68

Kũ, mãsu bijirẽwa ne daga gare shi

Verse 69 — Surah Sad 38:69

Wani ilmi bai kasance a gare ni ba game da jama'a (malã'iku) mafi ɗaukaka a lõkacin da suke yin husũma

Verse 70 — Surah Sad 38:70

Ba a yi mini wahayin kõme ba face cẽwa ni mai gargaɗi kawai ne, mai bayyanãwa

Verse 71 — Surah Sad 38:71

A lõkacin da Ubangijinka Ya ce wa malã'iku, "Lalle Nĩ Mai halitta mutum ne daga lãkã

Verse 72 — Surah Sad 38:72

Sa'an nan idan Nã daidaita shi, kuma Na hũra (wani abu) daga Ruhĩ Na a cikinsa to ku fãɗi kunã mãsu sujada a gare; shi

Verse 73 — Surah Sad 38:73

Sai malã'ikun suka yi sujada dukansu, gabã ɗaya

Verse 74 — Surah Sad 38:74

Fãce Iblis, ya yi girman kai, kuma ya kasance daga kãfirai

Verse 75 — Surah Sad 38:75

(Allah) Ya ce, "Yã Ibilis! Mẽ ya hana ka, ka yi sujada ga abin da Nã halitta da HannayeNa biyu? Shin, kã yi girman kai ne, kõ kuwa kã kasance daga maɗaukaka ne

Verse 76 — Surah Sad 38:76

Ya ce, "Nĩ, mafifici ne daga gare shi: Kã halitta ni daga wutã, kuma Kã halitta shi daga lãkã

Verse 77 — Surah Sad 38:77

Ya ce, "To, ka fita daga gare ta, dõmin lalle kai la'ananne ne

Verse 78 — Surah Sad 38:78

Kuma lalle a kanka akwai la'anaTa har zuwa rãnar sakamako

Verse 79 — Surah Sad 38:79

Ya ce, "Ya Ubangijina! To, Ka yi mini jinkiri zuwa ga rãnar da ake tãyar da su

Verse 80 — Surah Sad 38:80

Ya ce, "To, lalle kanã daga waɗanda aka yi wa jinkiri

Verse 81 — Surah Sad 38:81

Zuwa ga yinin lõkaci sananne

Verse 82 — Surah Sad 38:82

Ya ce, "To, inã rantsuwa da buwãyar Ka, lalle, inã ɓatar da su gabã ɗaya

Verse 83 — Surah Sad 38:83

Fãce bãyin Ka tsarkakakku daga gare su

Verse 84 — Surah Sad 38:84

(Allah) Ya ce, "To, (wannan magana ita ce) gaskiya. Kuma gaskiya Nake faɗa

Verse 85 — Surah Sad 38:85

Lalle zã Ni cika Jahannama daga gare ka, kuma daga wanda ya bĩ ka daga gare su, gabã ɗaya

Verse 86 — Surah Sad 38:86

Ka ce: "Bã ni tambayar ku wata ijãra, a kansa kuma bã ni daga mãsu ƙãƙalen faɗarsa

Verse 87 — Surah Sad 38:87

Shĩ (Alkur'ãn) bai zama ba fãce ambato ne ga dukan halitta

Verse 88 — Surah Sad 38:88

Kuma lalle zã ku san babban lãbãrinsa* a bayan ɗan lõkaci