Back to Languages

Hausa - Chapter 39 - Az-Zumar

Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink

Verse 1 — Surah Az-Zumar 39:1

Saukar da Littãfin daga Allah ne, Mabuwãyi, Mai hikima

Verse 2 — Surah Az-Zumar 39:2

Mun saukar da littafi a gareka da Gaskiya ka bautawa Allah kana mai tsarkake Addini a gare shi

Verse 3 — Surah Az-Zumar 39:3

To, addini tsarkakakke na Allah ne, kuma waɗanda suka riƙi waɗansu majibinta, bã Shi ba, (sunã cẽwa) "Ba mu bauta musu ba fãce dõmin su kusantar da mu zuwa ga Allah, kusantar daraja." Lalle Allah nã yin hukunci a tsakãninsu ga abin da suka zama sunã sãɓãwa a cikinsa. Lalle Allah ba Ya shiryar da wanda yake mai ƙarya, mai kãfirci

Verse 4 — Surah Az-Zumar 39:4

Dã Allah Yã yi nufin Ya riƙi ɗã, to, lalle sai Ya zãɓa daga abin da Yake halittãwa abin da Yake so. Tsarki ya tabbata a gare Shi. Shĩ ne Allah, Makaɗaici, Mai tĩlastãwa

Verse 5 — Surah Az-Zumar 39:5

Ya halitta sammai da ƙasã da gaskiya. Yanã shigar da dare a kan rãna, kuma Yanã shigar da rãnã a kan dare kuma Yã hõre rãnã da watã, kõwannensu yanã gudãna zuwa ga ajali ambatacce. To, Shĩ ne Mabuwãyi, Mai gãfara

Verse 6 — Surah Az-Zumar 39:6

Yã halitta ku daga rai guda, sa'an nan Ya sanya ma'auranta daga gare shi. Kuma ya saukar muku daga dabbõbin gida nau'i takwas Yanã halitta ku a cikin cikunnan uwayenku, halitta a bãyan wata halitta, a cikin duffai uku. Wannan shĩ ne Allah Ubangijin ku. Mulki a gare shi yake. Bãbu abin bautãwa fãce Shi. To, yãya ake karkatar da ku

Verse 7 — Surah Az-Zumar 39:7

Idan kun kãfirta to, lalle Allah Wadãtacce ne daga barinku, kuma bã Shi yarda da kãfirci ga bãyin Sa, kuma idan kun gõde, Zai yarda da ita (gõdiyar) a gare ku, kuma wani rai mai ɗaukar nauyi, bã ya ɗaukar nauyin wani. Sa'an nan kuma makõmarku zuwa ga Ubangijinku take, dõmin Ya bã ku lãbãri game da abin da kuka kasance kunã aikatãwa. Lalle Shĩ, Masani ne ga abin da yake a ainihin zukata

Verse 8 — Surah Az-Zumar 39:8

Kuma idan wata cũta ta shãfi mutum, sai ya kira Ubangijinsa, yanã mai mai da al'amari zuwa gare Shi, sa'an nan idan Ya jũyar da cũtar da ni'ima ta daga gare Shi, sai ya manta da abin da ya kasance yanã kira zuwa gare shi a gabãnin haka, kuma ya sanya wa Allah waɗansu abõkan tarẽwa dõmin ya ɓatar (da su) daga hanyarSa. Ka ce (masa), "Ka ji dãɗi da kãfircinka, a ɗan lõkaci, lalle kai daga 'yan wutã ne

Verse 9 — Surah Az-Zumar 39:9

Shin, wanda yake mai tawãli'u sã'õ'in dare, yanã mai sujada kuma yanã mai tsayi ga salla, yanã tsõron Lãhira, kuma yanã fãtan rahamar Ubangijinsa, (yanã daidai da waninsa?) Ka ce: "Ashe, waɗanda suka sani, sunã daidaita da waɗanda ba su sani ba?" Mãsu hankali kawai ke yin tunãni

Verse 10 — Surah Az-Zumar 39:10

Ka ce: (Allah Ya ce): "Yã bãyĩ Na waɗanda suka yi ĩmãni! Ku bi Ubangijinku da taƙawa. Waɗanda suka kyautata a cikin wannan dũniya sunã da sakamako mai kyau, kuma ƙasar Allah mai fãɗi *ce. Mãsu haƙuri kawai ake cika wa ijãrarsu, bã da wani lissãfi ba

Verse 11 — Surah Az-Zumar 39:11

Ka ce: "Lalle nĩ, an umurce ni da in bauta wa Allah, inã tsarkake addini a gare Shi

Verse 12 — Surah Az-Zumar 39:12

Kuma an umurce ni da in kasance farkon mãsu miƙa wuya (ga umurnin Allah)

Verse 13 — Surah Az-Zumar 39:13

Ka ce: "Lalle nĩ inã tsõro, idan na sãɓã wa Ubangijĩna, ga azãbar yini mai girma

Verse 14 — Surah Az-Zumar 39:14

Ka ce: "Allah nake bautã wa, inã mai tsarkake addinĩna a gare Shi

Verse 15 — Surah Az-Zumar 39:15

To, ku bauta wa abin da kuke so, waninSa." Ka ce: "Lalle mãsu hasãra, sũ ne waɗanda suka yi hasarar rãyukansu da iyãlansu, a Rãnar ¡iyãma. To, waccan fa, ita ce hasãra bayyananna

Verse 16 — Surah Az-Zumar 39:16

Sunã da waɗansu inuwõwi na wutã daga samansu, kuma daga ƙasansu akwai waɗansu inuwõwi. Wancan Shĩ ne Allah ke tsõratar da bãyin Sa da shi. Yã bãyĩNa! To, ku bĩ Ni da taƙawa

Verse 17 — Surah Az-Zumar 39:17

Kuma waɗanda suka nĩsanci Shaiɗannu ga bauta musu, kuma suka mai da al'amari ga Allah, sunã da bushãra. To, ka bãyar da bushãra ga bãyiNa

Verse 18 — Surah Az-Zumar 39:18

Waɗanda ke sauraren* magana, sa'an nan su bi mafi kyaunta. waɗancan sũ ne Allah Ya shiryar da su, kuma waɗancan su ne mãsu hankali

Verse 19 — Surah Az-Zumar 39:19

Shin fa, wanda kalmar azãba ta wajaba a kansa? Shin fa, kanã iya tsãmar da wanda ke a cikin wutã

Verse 20 — Surah Az-Zumar 39:20

Amma waɗanda suka bi Ubangijinsu da taƙawa, sunã da bẽnãye, daga samansu akwai waɗansu bẽnãye ginannu, ƙoramu na gudãna daga ƙarƙashinsu. Alkawarin Allah. Allah bã Ya sãɓã wa alkawarinSa

Verse 21 — Surah Az-Zumar 39:21

Shin, ba ka gani ba cẽwa lalle Allah Yã saukar da ruwa daga sama, sa'an nan Yã gudãnar da shi yanã marẽmari a cikin ƙasã sa'an nan Yã fitar da shũka game da shi, launukan shũkar mãsu sãɓãnin jũna sa'annan shũkar ta ƙeƙashe har ka gan ta fatsifatsi, sa'an nan Allah Ya sanya ta dandaƙaƙƙiya? Lalle ne ga wancan akwai tunãtarwa ga mãsu hankali (ga iyãwar gudãnar da ruwa a cikin gidãjen Aljanna)

Verse 22 — Surah Az-Zumar 39:22

Shin fa, wanda Allah Ya buɗa ƙirjinsa, dõmin Musulunci sa'an nan shi yanã a kan haske daga Ubangijinsa, (zai zama kamar waninsa)? To, bone yã tabbata ga maƙeƙasa zukãtansu daga ambaton Allah. Waɗancan sunã a cikin wata ɓata bayyananna

Verse 23 — Surah Az-Zumar 39:23

Allah Ya sassaukar da mafi kyaun lãbãri, Littãfi mai kama da jũna, wanda ake konkoma karãtunsa fãtun waɗanda ke tsõron Ubangijinsu, sunã tãƙura sabõda Shi, sa'an nan fãtunsu da zukãtansu su yi laushi zuwa ga ambaton Allah. Waccan ita ce shiryarwar Allah, Yanã shiryar da wanda Ya so game da ita. Kuma wanda Allah Ya ɓatar, to, bã shi da wani mai shiryarwa

Verse 24 — Surah Az-Zumar 39:24

Shin fa, wanda ke kãre mũguwar azãba da fuskarsa (yanã zama kamar waninsa) a Rãnar ƙiyãma? Kuma a ce wa azzãlumai, "Ku ɗanɗani abin da kuka kasance kunã aikatãwa

Verse 25 — Surah Az-Zumar 39:25

Waɗanda ke a gabãninsu, sun ƙaryata, sai azãba ta jẽ musu daga inda ba su sani ba

Verse 26 — Surah Az-Zumar 39:26

Sai Allah Ya ɗanɗana musu azãbar wulãkanci a cikin rãyuwar dũniya, kuma lalle azãbar Lãhira ita ce mafi girma, dã sun kasance sunã da sani

Verse 27 — Surah Az-Zumar 39:27

Kuma lalle ne haƙĩƙa Mun buga wa mutãne a, cikin wannan Alƙur'ãni, daga kõwane misãli, ɗammãninsu su yi tunãni

Verse 28 — Surah Az-Zumar 39:28

Abin karantãwa ne na Lãrabci, ba mai wata karkata ba, ɗammãninsu, su yi taƙawa

Verse 29 — Surah Az-Zumar 39:29

Allah Yã buga misãli; wani mutum (bãwa) a cikinsa akwai mãsu tarayya, mãsu mũgun hãlin jãyayya, da wani mutum (bãwa) dukansa ga wani mutum. Shin, zã su daidaita ga misãli? Gõdiya ta tabbata ga Allah (a kan bayãni). Ã'a, mafi yawan mutãne ba su sani ba

Verse 30 — Surah Az-Zumar 39:30

Lalle kai mai mutuwa ne, kuma su mã lalle mãsu mutuwa ne

Verse 31 — Surah Az-Zumar 39:31

Sa'an nan, lalle kũ, a Rãnar ¡iyãma, a wurin Ubangijinku, zã ku yi ta yin husũma

Verse 32 — Surah Az-Zumar 39:32

To, wãne ne mafi zãlunci daga wanda ya yi ƙarya ga Allah, kuma ya ƙaryata gaskiya a lõkacin da ta jẽ masa? Shin bãbu mazauni a cikin Jahannama ga kãfirai

Verse 33 — Surah Az-Zumar 39:33

Kuma wanda ya zo da gaskiya, kuma ya gaskata a game da ita, waɗancan sũ ne mãsu taƙawa

Verse 34 — Surah Az-Zumar 39:34

Sunã da abin da suke so wajen Ubangijinsu. Wancan shĩ ne sakamakon mãsu kyautatãwa

Verse 35 — Surah Az-Zumar 39:35

Dõmin Allah Ya kankare musu mafi mũnin abin da suka aikata, kuma Ya sãkã musu ijãrarsu da mafi kyaun abin da suka kasance sunã aikatãwa

Verse 36 — Surah Az-Zumar 39:36

Ashe Allah bai zama Mai isa ga BãwanSa ba? Kuma sunã tsõratar da kai ga waɗanda suke wanin Sa, kuma wanda Allah Ya ɓatar to, bã, shi da mai shiryarwa

Verse 37 — Surah Az-Zumar 39:37

Kuma wanda Allah Ya shiryar, to, bã shi da mai ɓatarwa. Ashe, Allah bai zama Mabuwãyi ba, Mai azãbar rãmuwa

Verse 38 — Surah Az-Zumar 39:38

Kuma lalle idan ka tambaye su: "Wane ne ya halitta sammai da ƙasã?" Haƙĩƙa, zã su ce, "Allah ne." Ka ce: "Ashe, to, kun gani abin da kuke kira, waɗanda suke wanin Allah ne, idan Allah Ya nufe ni da wata cũta, shin sũ abũbuwan nan mãsu kuranye, cutarsa ne? Kõ kuma Ya nufe ni da wata rahama, shin, su abũbuwan nan mãsu kãme rahamarSa ne?" Ka ce: "Mai isata Allah ne, gare Shi mãsu tawakkali ke dõgara

Verse 39 — Surah Az-Zumar 39:39

Ka ce: "Yã mutãnena! Ku yi aiki a kan hãlinku, lalle nĩ, inã aiki a kan hãlĩna. Sa'an nan zã ku sani

Verse 40 — Surah Az-Zumar 39:40

Wanda azãba ta je masa, zã ta wulãkanta shi, kuma wata azãba mai dawwama za ta sauka a kansa

Verse 41 — Surah Az-Zumar 39:41

Lalle Mũ Mun saukar da littãfi a gare ka dõmin mutãne da gaskiya. Sa'an nan wanda ya nẽmi shiriya, to, dõmin kansa, kuma wanda ya ɓace, to, yanã ɓacẽwa ne a kanta. Kuma ba ka zama wakĩli a kansu ba

Verse 42 — Surah Az-Zumar 39:42

Allah ne ke karɓar rãyuka a lõkacin mutuwarsu, da waɗannan da ba su mutu ba, a cikin barcinsu. Sa'an nan Ya riƙe wanda Ya hukunta mutuwa a kansa kuma Ya saki gudar, har zuwa ga ajali ambatacce. Lalle a cikin wancan, haƙĩƙa, akwai ãyõyi ga mutãne waɗanda ke yin tunãni

Verse 43 — Surah Az-Zumar 39:43

Kõ kuma sun riƙi mãsu cẽto ne, waɗansun Allah? Ka ce: "Shin, kuma kõ dã sun kasance bã su da mallakar kõme, kuma bã su hankalta

Verse 44 — Surah Az-Zumar 39:44

Ka ce: "Cẽto gabã ɗaya ga Allah yake. Mulkin sammai da ƙasã Nãsa ne. Sa'an nan zuwa gare Shi ake mayar da ku

Verse 45 — Surah Az-Zumar 39:45

Kuma idan aka ambaci Allah Shi kaɗai zukãtan waɗanda ba su yi ĩmãni ba da Lãhira, su yi ƙiyãma, kuma idan an ambaci waɗanda suke kiran, wasun Sa, sai gãsu sunã yin bushãrar farin ciki

Verse 46 — Surah Az-Zumar 39:46

Ka ce: "Ya Allah, Mai ƙãga halittar sammai da ƙasã, Masanin gaibi da bayyane! Kai ne ke yin hukunci a tsakãnin bãyinKa a cikin abin da suka kasance sunã sãɓa wa jũna a cikinsa

Verse 47 — Surah Az-Zumar 39:47

Kuma dã waɗanda suka yi zãlunci sunã da abin da ke cikin ƙasã gaba ɗaya, da misãlinsa a tãre da shi lalle dã sun yi fansa da shi daga mummunar azãba, a Rãnar ¡iyãma. Kuma abin da ba su kasance sunã zato ba, daga Allah, ya bayyana a gare su

Verse 48 — Surah Az-Zumar 39:48

Mũnãnan ayyuka da suka aikata, suka bayyana a gare su, kuma abin da suka kasance sunã yi, na izgili, ya wajaba a kansu

Verse 49 — Surah Az-Zumar 39:49

To, idan wata cũta ta shãfi mutum, sai ya kirãye Mu, sa'an nan idan Muka canza masa ita, ya sãmi ni'ima daga gare Mu, sai ya ce: "An bã ni ita ne a kan wani ilmi nãwa kawai." Ã'a ita wannan (magana) fitina ce, kuma amma mafi yawansu ba su sani ba

Verse 50 — Surah Az-Zumar 39:50

Lalle waɗanda ke a gabãninsu, sun faɗe ta, sabõda haka abin da suka kasance sunã aikatãwa bai wadãtar da su da kõme ba

Verse 51 — Surah Az-Zumar 39:51

Sai (sakamakon) mũnãnan abin da suka aikata ya same su. Kuma waɗanda suka yi zãlunci daga waɗannan, (sakamakon) munãnan abin da suka aikata zai sãme su, kuma ba su zama mabuwãya ba

Verse 52 — Surah Az-Zumar 39:52

Ashe kuma ba su sani ba cẽwa Allah, na shimfiɗa arziƙi ga wanda Yake so, kuma Yanã ƙuƙuntawa? Lalle a cikin wancan akwai ãyõyi ga mutãne waɗanda ke yin ĩmãni

Verse 53 — Surah Az-Zumar 39:53

Ka ce: (Allah Ya ce): "Yã bãyĩ Na waɗanda suka yi barna a kan rãyukansu! Kada ku yanke ƙauna daga rahamar Allah. Lalle Allah na gãfarta zunubai gabã ɗaya. Lalle Shĩ, Shĩ ne Mai gãfara, Mai jin ƙai

Verse 54 — Surah Az-Zumar 39:54

Kuma ku mayar da al'amari zuwa ga Ubangijinku, kuma ku sallama Masa, a gabãnin azãba ta zo muku, sa'an nan kuwa bã zã a taimake ku ba

Verse 55 — Surah Az-Zumar 39:55

Kuma ku bi mafi kyaun abin da aka saukar zuwa gare ku daga Ubangijinku, a gabãnin azãba ta zo muku, bisa auke, kuma kũ ba ku sani ba

Verse 56 — Surah Az-Zumar 39:56

Kada wani rai ya ce: 'Yã nadãmãta a kan abin da na yi sakaci a cikin sãshen Allah' kuma lalle na kasance, haƙĩƙa, daga mãsu izgili

Verse 57 — Surah Az-Zumar 39:57

Ko kuma (kada) ya ce: 'Da Allah Ya shiryar da ni, dã na kasance daga mãsu taƙawa

Verse 58 — Surah Az-Zumar 39:58

Ko kuma (kada (ya ce: a lõkacin da yake ganin azãba, 'Dã lalle a ce inã da wata kõmawa (zuwa dũniya) dõmin in kasance daga mãsu kyautatãwa

Verse 59 — Surah Az-Zumar 39:59

Na'am! Lalle ne ãyõyiNa sun jẽ maka, sai ka ƙaryata a game da su, kuma ka yi girman kai, kuma ka kasance daga kãfirai

Verse 60 — Surah Az-Zumar 39:60

Kuma a Rãnar ¡iyãma kanã ganin waɗanda suka yi ƙarya ga Allah fuskõkinsu sunã mãsu yin baƙi. Ashe bãbu mazauni a cikin Jahannama ga mãsu girman kai

Verse 61 — Surah Az-Zumar 39:61

Kuma Allah na tsĩrar da waɗanda suka yi taƙawa a game da wurin sãmun babban rabonsu, cũta bã zã tashãfe su ba, kuma ba su zama sunã baƙin ciki ba

Verse 62 — Surah Az-Zumar 39:62

Allah ne Mai halitta dukan kõme, kuma Shĩ ne Wakĩli a kan kõme

Verse 63 — Surah Az-Zumar 39:63

Shĩ ke da mabũɗan sammai da ƙasã. Kuma waɗanda suka kãfirta da ãyõyin Allah, waɗannan sũ nemãsu hasãra

Verse 64 — Surah Az-Zumar 39:64

Ka ce: "Shin, wanin Allah kuke umurni na da in bauta wa? Yã ku jãhilai

Verse 65 — Surah Az-Zumar 39:65

Kuma an yi wahayi zuwa gare ka da kuma zuwa ga waɗanda suke a gabãninka, "Lalle idan ka yi shirki haƙĩƙa aikinka zai ɓãci, kuma lalle zã ka kasance daga mãsu hasãra

Verse 66 — Surah Az-Zumar 39:66

Ã'aha! Ka bauta wa Allah kaɗai, kuma ka kasance daga mãsu gõdiya

Verse 67 — Surah Az-Zumar 39:67

Kuma ba su ƙaddara Allah a kan haƙĩƙanin* ĩkon yinsa ba: ¡asã duka damƙarSa ce, a Rãnar ¡iyãma, kuma sammai abũbuwan naɗewa ne ga dãmanSa. Tsarki ya tabbata a gare Shi, kuma Ya ɗaukaka daga barin abin da suke shirki da shi

Verse 68 — Surah Az-Zumar 39:68

Kuma aka busa a cikin ƙaho, sai waɗanda ke a cikin sammai da ƙasã suka sũma sai wanda Allah Ya so (rashin sumansa) sa'an nan aka hũra a cikinsa, wata hũrãwa, sai gã su tsaitsaye, sunã kallo

Verse 69 — Surah Az-Zumar 39:69

Kuma ƙasã ta yi haske da hasken Ubangijinta, kuma aka aza littãfi, kuma aka zo da Annabãwa da mãsu shaida, kuma aka yi hukunci a tsakãninsu, da gaskiya, alhãli kuwa, sũ, bã zã a zãlunce su ba

Verse 70 — Surah Az-Zumar 39:70

Kuma aka cika wa kõwane rai abin da ya aikata. Kuma (Allah) Shĩ ne Mafi sani game da abin da suke aikatãwa

Verse 71 — Surah Az-Zumar 39:71

Kuma aka kõra waɗanda suka kãfirta zuwa Jahannama, jama'a-jama'a har a lõkacin da suka je mata, sai aka buɗe ƙõfõfinta, kuma matsaranta suka ce musu, "Ashe, waɗansu Manzanni, daga cikinku ba su je muku ba, sunã karanta ãyõyin Ubangijinku a kanku, kuma sunã yi muku gargaɗin gamuwa da yininku wannan?" Suka ce, "Na'am, "kuma amma kalmar azãba ita ce ta wajaba a kan kãfirai

Verse 72 — Surah Az-Zumar 39:72

Aka ce, "Ku shiga ƙõfõfin Jahannama, kaunã madawwama a cikinta. Sa'an nan mazaunin makangara yã munana

Verse 73 — Surah Az-Zumar 39:73

Kuma aka kõra waɗanda suka bi Ubangijinsu da taƙawa zuwa Aljanna jama'a-jama'a har a lõkacin da suka jẽ mata, alhãli kuwa an buɗe kõfõfinta, kuma matsaranta suka ce musu, "Aminci ya tabbata a gare ku, kun ji dãɗi, sabõda haka ku shige ta, kunã madawwama (a cikinta)

Verse 74 — Surah Az-Zumar 39:74

Kuma suka ce: "Gõdiya ta tabbata ga Allah Wanda Ya yi mana gaskiya ga wa'adinSa, kuma Ya gãdar da mu ƙasã, munã zama a cikin Aljanna a inda muke so." To, madalla da ijãrar ma'aikata

Verse 75 — Surah Az-Zumar 39:75

Kuma kanã ganin malã'iku sunã mãsu tsayãwa da haƙƙoƙin da aka ɗõra musu daga kẽwayen Al'arshi, sunã tasbĩhi game da gõde wa Ubangijinsu. Kuma aka yi hukunci a tsakãninsu da gaskiya. Kuma aka ce, "Gõdiya ta tabbata ga Allah, Ubangijin halittu