Back to Languages

Hausa - Chapter 35 - Fatir

Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink

Verse 12 — Surah Fatir 35:12

Kuma kõguna biyu ba su daidaita: Wannan mai ruwan dãɗi, mai zãƙi, mai sauƙin haɗiya kuma wannan mai ruwan gishiri mai zartsi, kuma daga kõwane, kunã cin wani nama sãbo, kuma kunã fitar da kawa wadda kuke tufantarta, kuma kanã ganin jirãge a cikinsa sunã mãsu gudãna, dõmin ku nẽmo daga falalar Sa, kuma tsammãninku zã ku dinga gõdẽwa