Back to Languages

Hausa - Chapter 35 - Fatir

Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink

Verse 25 — Surah Fatir 35:25

Kuma idan sunã ƙaryata ka, to, haƙĩƙa, waɗanda suke a gabãninsu sun ƙaryata. Manzanninsu sun jẽ musu da hujjõji, kuma da takardu, kuma da Littafi mai haske