Back to Languages

Hausa - Chapter 35 - Fatir

Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink

Verse 43 — Surah Fatir 35:43

Dõmin nũna girman kai a cikin ƙasã da mãkircin cũta. Kuma mãkirci na cũta bã ya fãdãwa fãce a kan mutãnensa. To shin sunã jiran (wani abu ne) fãce dai hanyar (kãfiran) farko. To, bã zã ka sãmi musanya ba ga hanyar Allah. Kuma bã zã ka sãmi jũyarwa ba ga hanyar Allah