Back to Languages

Hausa - Chapter 40 - Ghafir

Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink

Verse 7 — Surah Ghafir 40:7

Waɗanda ke ɗaukar Al'arshi da waɗanda ke kẽwayenta, sunã tasbĩhi game da gõde wa Ubangijinsu, kuma sunã yin ĩmãni da Shi, kuma sunã yin istigfãri dõmin waɗanda suka yi ĩmãni, (sunã cẽwa), "Yã Ubangijinmu! Kã yalwaci dukan kõme da rahama da ilmi to Ka yi gãfara ga waɗanda suka tũba kuma suka bi hanyarKa, kuma Ka tsare musu azãbar Jahĩm