Sammai nã kusan su tsãge daga bisansu, kuma malã'iku nã yin tasĩhi game da gõdẽ wa Ubangijinsu kuma sunã istigfãri dõmin wanda ke cikin ƙasa. To, lalle Allah Shĩ ne Mai gãfara, Mai jin ƙai
Kuma kamar haka ne Muka yi wahayin abin karãntãwa (Alƙur'ãni) na Lãrabci zuwa gare ka, dõmin ka yi gargaɗi ga Uwar Alƙaryu (Makka) da wanda ke a kẽwayenta, kuma ka yi gargaɗi game da rãnar taruwa, bãbu shakka gare ta, wata ƙungiya tanã a cikin Aljanna kuma wata ƙungiya tãna a cikin sa'ĩr
Kuma dã Allah Ya so, da Ya haɗã su al'umma guda, kuma Amma Yanã shigar da wanda Ya so a cikin rahamarSa alhãli kuwa azzãlumaii bã su da, wani majiɓinci, kuma bã su da wani mataimaki
Kuma abin da kuka sãɓã wa jũna a cikinsa kõ mêne ne, to, hukuncinsa (a mayar da shi) zuwa ga Allah. Wancan Shĩ ne Allah Ubangijĩna, a gare Shi na dõgara, kuma zuwa gare Shi nake mayar da al'amarĩna
(Shĩ ne) Mai ƙãga halittar sammai da ƙasai, Ya sanya muku ma'aura daga jinsinku, kuma (Ya sanya) daga dabbõbi maza da mãtã, Yanã halitta ku a cikinsu, wani abu bai zama kamar tamkarSa ba, kuma Shĩ ne Mai ji, Mai gani
Ya shar'anta muku, game da addini, abin da Ya yi wasiyya da shi ga Nũhu da abin da Muka yi wahayi da shi zuwa gare ka, da abin da Muka yi wasiyya da shi ga Ibrãhĩm da Mũsã da Ĩsã, cẽwa ku tsayar da addini sõsai kuma kada ku rarrabu a cikinsa. *Abin da kuke kira zuwa gare shi,** ya yi nauyi a kan mãsu shirki. Allah na zãɓen wanda Yake so zuwa gare Shi, kuma Yanã shiryar da wanda ke tawakkali gare Shi, ga hanyar Sa
Kuma ba su rarraba ba fãce bãyan da ilmi ya jẽ musu, dõmin zãlunci a tsakãninsu kuma bã dõmin wata kalma* tã gabata ba daga Ubangijinka, zuwa ga wani ajali ambatacce, dã an yi hukunci a tsakaninsu. Kuma lalle ne waɗanda aka gãdar wa Littafi daga bãyansu, haƙiƙa, sunã cikin shakka a gare shi, mai sanya kokanto
Sabõda haka, sai ka yi kira kuma kai ka daidaitu kamar yadda aka umurce ka, kuma kada ka bi son zũciyõyinsu, kumaka ce, "Nã yi ĩmãni da abin da Allah Ya saukar na littãfi, kuma an umurce ni da in yi ãdalci a tsakãninku. Allah ne Ubangijinmu, kuma Shĩ ne Ubangijinku, ayyukanmu nã gare mu, kuma ayyukanku nã gare ku, kuma bãbu wata hujja a tsakãninmu da tsakãninku. Allah zai tara mu, kuma zuwa gare Shi makõma take
Kuma waɗannan da ke jãyayya a cikin al'amarin Allah daga bãyan an karɓa masa, hujjarsu ɓãtãcciya ce a wurin Ubangijinsu, kuma akwai fushi a kansu, kuma sunã da wata azãba mai tsanani
Waɗanda ba su yi ĩmãni da ita ba, (sũ) ke nẽman gaggautõwarta. Alhãli kuwa waɗanda suka yi ĩmãni, mãsu tsõro ne daga gare ta, kuma sun sani, cẽwa ita gaskiya ce. To, lalle ne waɗanda ke shakka a cikin Sa'a, haƙĩƙa, sunã a cikin ɓata Mai nĩsa
Wanda ya kasance yanã nufin nõman Lãhira zã Mu ƙãra masa a cikin nõmansa, kuma wanda ya kasance yanã nufin nõman dũniya, zã Mu sam masa daga gare ta, alhãli kuwa bã shi da wani rabo a cikin Lãhira
Kõ sunã da waɗansu abõkan tãrayya (da Allah) waɗanda suka shar'anta musu, game da addini, abin da Allah bai yi izni ba da shi? Kuma bã dõmin kalmar hukunci ba, da lalle, an yi hukunci a tsakãninsu. Kuma lalle azzãlumai sunã da azãba mai raɗaɗi
Kanã ganin azzãlumai sunã mãsu tsõro daga abin da suka sanã'anta alhãli kuwa shi abin tsoron, mai aukuwa ne gare su, kuma waɗanda suka yi ĩmãni kuma suka aikata ayyukan ƙwarai sunã a cikin fadamun Aljanna sunã da abin da suke so a wurin Ubangijinsu. Waccan fa ita ce falala mai girma
Wancan shĩ ne Allah ke bãyar da bushãra da shi ga bãyin Sa waɗanda suka yi ĩmãni kuma suka aikata ayyukan ƙwarai. Ka ce: "Bã ni tambayar ku wata ijãra a kansa, fãce dai sõyayya ta cikin zumunta." Kuma wanda ya aikata wani abu mai kyau, zã Mu ƙarã masa kyau a cikinsa, lalle Allah Mai gãfara ne, Mai gõdiya
Kõ zã su ce: "Ya ƙirƙira ƙarya ga Allah ne?" To, idan Allah Ya so, zai yunƙe a kan zũciyarka, kuma Allah Yana shãfe ƙarya kuma Yana tabbatar da gaskiya da kalmõminSa. Lalle ne Shĩ Masani ne ga abin da ke cikin zukata
Kuma Yanã karɓa wa waɗannan da suka yi ĩmãni kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, kuma Yanã ƙãra musu (sakamako) daga falalar Sa. Kuma kãfirai sunã da wata azãba mai tsanani
Kuma dã Allah Ya shimfiɗa arziki ga bãyinSa, dã sun yi zãluncin rarraba jama'a a cikin ƙasa, kuma amma Yanã sassaukarwa gwargwado ga abin da Yake so. Lalle ne Shĩ, game da bãyinSa, Mai labartawa ne, Mai gani
Idan Ya so, sai Ya kwantar da iskar, sai jirãgen su yini sunã mãsu kawaici a kan bãyan tẽkun, Lalle ne ga wancan, haƙĩƙa, akwai ãyõyi ga dukan mai haƙuri, Mai gõdiya
Sabõda haka abin da aka bã ku, kõ mẽne ne, to, jin dãɗin rayuwar dũniya ne, kuma abin da ke a wurin Allah Shĩ ne mafĩfĩci, kuma Shĩ ne mafi wanzuwa ga waɗanda suka yi ĩmãni kuma sunã dõgara a kan Ubangijinsu kawai
Da waɗanda suka karɓa kira ga Ubangijinsu, kuma suka tsayar da salla, kuma al'amarinsu shãwara ne a tsakãninsu, kuma daga abin da Muka azurta su sunã ciyarwa
Kuma sakamakon cũta shĩ ne wata cũta kamarta, sai dai wanda Ya yãfe kuma ya kyautata, to lãdarsa nã ga Allah. Lalle ne, Shĩ (Allah) bã Ya son azzãlumai
lnda hanyar zargi kawai take, shĩ ne a kan waɗanda ke zãluntar mutãne kuma sunã ƙẽtare haddin shari'a cikin ƙasa bã tare da haƙƙi ba. Waɗannan sunã da azãba Mai raɗaɗi
Kuma wanda* (Allah Ya ɓatar, to, bã shi da wani majiɓinci bãyan Sa, kuma zã ka ga azzãlumai, a lõkacin da suka ga azãba, sunã cẽwa, "Shin, akwai hanya zuwa ga kõmãwa)
Kuma kanã ganin su anã gitta su a kanta, sunã ƙasƙantattu sabõda wulãkanci, sunã hange daga gefen gani ɓoyayye. Kuma waɗanda suka yi ĩmãni sai su ce, "Lalle ne, mãsu hasãra, sũ ne waɗanda suka yi hasãrar rãyukansu da iyãlansu a Rãnar ¡iyãma." To, lalle ne, azzãlumai sunã a cikin wata azãba zaunanniya
Kuma waɗansu majiɓinta ba su kasance ba a gare su, waɗanda ke iya taimakonsu, baicin Allah. Kuma wanda Allah Ya ɓatar, to, bã shi da wani gõdabe na tsĩra
To, idan sun bijire, to, ba Mu aike ka kanã mai tsaro a kansu ba, bãbu abin da ke a kanka fãce iyar da Manzanci. Kuma lalle ne, Mũ idan Mun ɗanɗana wa mutum wata rahama daga gare Mu, sai ya yi farin ciki da ita, kuma idan wata masĩfa ta sãme su sabõda abin da hannayensu suka gabãtar, to, lalle ne mutum mai tsananin kãfirci ne
Mulkin sammai da ƙasa na Allah kawai ne. Yanã halitta abin da Yake so. Yanã bãyar da 'ya'ya mãtã ga wanda yake so, kuma Yanã bãyar da ɗiya maza ga wanda Yake so
Kuma bã ya kasancẽwa ga wani mutum Allah Ya yi masa magana* fãce da wahayi, kõ daga bãyan wani shãmaki, kõ Ya aika wani Manzo, sa'an nan Ya yi wahayi, da izninsa ga abin da Yake so. Lalle Shĩ, Maɗaukaki ne Mai hikima
Kuma kamar wancan Mun aika wani rũhi (rai mai haɗa jama'a) zuwa gare ka, daga gare Mu. Ba ka kasance kã san abin da yake littãfi ba, kõ abin da Yake ĩmãni, kuma amma Mun sanya shi (rũhin, watau Alƙur'ãni) wani haske ne, Munã shiryar da wanda Muke so daga cikin bãyĩn Mu game da shi. Kuma Lalle kai, haƙĩƙa, kanã shiryarwa zuwa ga hanya, madaidaiciya