Back to Languages

Hausa - Chapter 43 - Az-Zukhruf

Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink

Verse 1 — Surah Az-Zukhruf 43:1

Verse 2 — Surah Az-Zukhruf 43:2

Ina rantsuwa da Littãfi Mabayyani

Verse 3 — Surah Az-Zukhruf 43:3

Lalle Mũ, Mun sanya shi abin karãtu na Lãrabci, tsammãninku, kunã hankalta

Verse 4 — Surah Az-Zukhruf 43:4

Kuma lalle, shĩ, a cikin uwar littãfi a wurin Mu, haƙĩƙa, maɗaukaki ne, bayyananne

Verse 5 — Surah Az-Zukhruf 43:5

Shin, zã Mu kau da kai daga saukar da hukunci daga gare ku ne dõmin kun kasance mutane mãsu ɓarna

Verse 6 — Surah Az-Zukhruf 43:6

Alhãli kuwa sau nawa Muka *aika wani Annabi a cikin mutãnen fãrko

Verse 7 — Surah Az-Zukhruf 43:7

Kuma wani Annabi bai je musu ba fãce sun kasance, game da shi, sunã mãsu yin izgili

Verse 8 — Surah Az-Zukhruf 43:8

Sai Muka halakar da waɗanda suke sũ ne mafiya ƙarfin damƙa daga gare su. Kuma abin misãlin mutãnen farkon ya shũɗe

Verse 9 — Surah Az-Zukhruf 43:9

Kuma lalle ne, idan ka tambaye su, "Wãne ne ya halitta sammai da ƙasa?" Lalle zã su ce, "Mabuwãyi Mai ilmi ne Ya halitta su

Verse 10 — Surah Az-Zukhruf 43:10

Wanda Ya sanya muku ƙasa shimfiɗa kuma Ya sanya muku hanyõyi a cikinta, tsammãninku za ku nẽmi shiryuwa

Verse 11 — Surah Az-Zukhruf 43:11

Kuma Wanda Ya saukar da ruwa daga sama, a kan wani gwargwado, sai Muka rãyar da gari matacce game da shi. Kamar haka nan ake fitar da ku (daga kabari)

Verse 12 — Surah Az-Zukhruf 43:12

Kuma Wanda Ya halitta ma'aura dukansu, kuma Ya sanya muku, daga jirgi da dabbõbin ni'ima, abin da kuke hawa

Verse 13 — Surah Az-Zukhruf 43:13

Domin ku daidaitu a kan bãyansa, sa'an nan ku tuna ni'imar Ubangijinku a lõkacin da kuka daidaita a kansa kuma ku ce, "Tsarki ya tabbata ga Wanda Ya hõre mana wannan alhãli kuwa ba mu kasance mãsu iya rinjãya gare Shi ba

Verse 14 — Surah Az-Zukhruf 43:14

Kuma lalle mũ haƙĩƙa mãsu* jũyãwa muke, zuwa ga Ubangijinmu

Verse 15 — Surah Az-Zukhruf 43:15

Kuma suka sanya *Masa juz'i daga bãyinsa. Lalle ne mutum, haƙĩƙa, mai yawan kãfirci ne, mai bayyanãwar kãfircin

Verse 16 — Surah Az-Zukhruf 43:16

Kõ zã Ya ɗauki 'ya'ya mãtã daga abin da Yake halittawa ne, kuma Ya zãɓe ku da ɗiya maza

Verse 17 — Surah Az-Zukhruf 43:17

Alhãli kuwa idan an bãyar da bushãra ga ɗayansu da abin da ya buga misãli da shi ga Mai rahama, sai fuskarsa ta yini tanã wadda aka baƙanta launinta, kuma yanã cike da baƙin ciki

Verse 18 — Surah Az-Zukhruf 43:18

Ashe, kuma (Allah zai zãɓi) wanda ake rẽno a cikin ƙawa alhãli kuwa gã shi a husũma bã mai iya bayyanawar magana ba

Verse 19 — Surah Az-Zukhruf 43:19

Kuma suka mayar da malã'iku ('yã'ya) mãtã, alhãli kuwa sũ, waɗanda suke bãyin (Allah) Mai rahama ne! Shin, sun halarci halittarsu ne? zã a rubũta shaidarsu kuma a tambaye su

Verse 20 — Surah Az-Zukhruf 43:20

Kuma suka ce: "Dã Mai rahama ya so, dã ba mu bauta musu ba." Bã su da wani ilmi game da wancan! Bãbu abin da suke yi fãce yanki-faɗi

Verse 21 — Surah Az-Zukhruf 43:21

Kõ Mun bã su wani littãfi ne a gabãninsa (Alƙur'ãni) sabõda haka da shĩ suke riƙe

Verse 22 — Surah Az-Zukhruf 43:22

Ã'a, sun ce dai, "Lalle mũ, mun sãmi ubanninmu a kan wani addini (na al'ãda) kuma lalle mũ, a kan gurãbansu muke mãsu nẽman shiryuwa

Verse 23 — Surah Az-Zukhruf 43:23

Kuma kamar haka, ba Mu aika wani mai gargaɗi ba a gabãninka, a cikin wata alƙarya, fãce mani'imtanta sun ce, "Lalle mũ, mun sãmi ubanninmu a kan wani addini kuma lalle mũ, mãsu kõyi nea kan gurãbansu

Verse 24 — Surah Az-Zukhruf 43:24

(Sai mai gargaɗin) ya ce: "Shin, ban zo muku da abin da ya fi zama shiriya daga abin da kuka sãmi ubanninku a kansa ba?" Suka ce, "Lalle mũ dai mãsu kafirta ne game da abin da aka aiko ku da shi

Verse 25 — Surah Az-Zukhruf 43:25

Sabõda haka Muka yi musu azãbar rãmuwa. To, ka dũbi yadda ãƙibar mãsu ƙaryatãwa take

Verse 26 — Surah Az-Zukhruf 43:26

Kuma (ka ambaci) lõkacin da Ibrãhĩm ya ce wa ubansada mutãnensa, "Lalle nĩ mai barranta ne daga abin da kuke bautãwa

Verse 27 — Surah Az-Zukhruf 43:27

Fãce wannan *da Ya ƙãga halittata, to, lalle Shĩ ne zai shiryar da ni

Verse 28 — Surah Az-Zukhruf 43:28

Kuma (Ibrãhĩm) ya sanya (ita wannan magana) kalma mai wanzuwa a cikin zuriyarsa, tsammãninsu su kõmo daga ɓata

Verse 29 — Surah Az-Zukhruf 43:29

Ã'a, Na jiyar da waɗannan mutãne dãɗi sũ da ubanninsu har gaskiya, da Manzo mai bayyanawar gaskiyar, ya zo musu

Verse 30 — Surah Az-Zukhruf 43:30

Kuma a lõkacin da gaskiyar ta jẽ musu sai suka ce: "Wannan sihiri ne kuma mũ mãsu kãfirta da shi ne

Verse 31 — Surah Az-Zukhruf 43:31

Kuma suka ce: "Don me ba a saukar da wannan Alƙur'ãni a kan wani mutum mai girma daga alƙaryun* nan biyu ba

Verse 32 — Surah Az-Zukhruf 43:32

Shin, sũ ne ke raba rahamar Ubangijinka? Mũ ne, Muka raba musu abincinsu a cikin rãyuwar dũniya, kuma Muka ɗaukaka waɗansunsu a kan waɗansu da darajõji dõmin waɗansunsu su riƙi waɗansu lẽburori kumarahamar Ubangijinka (ta Annabci*), ita ce mafificiya daga abin da suke tãrãwa

Verse 33 — Surah Az-Zukhruf 43:33

Kuma bã dõmin mutane su kasance al'umma ɗaya ba, lalle ne, dã Mun sanya wa mãsu kãfircẽ wa Mai Rahama, a gidãjensu, rufi na azurfa, kuma da matãkalai, ya zama a kanta suke tãƙãwa

Verse 34 — Surah Az-Zukhruf 43:34

(Kuma a gidãjensu, Mu sanya) ƙyamãre da gadãje, a kansu suke kishingiɗa

Verse 35 — Surah Az-Zukhruf 43:35

Da zĩnãriya. Kuma dukan wancan abu bai zama ba, sai jin dãɗin rãyuwar dũniya nekawai' alhãli kuwa Lãhira, a wurin Ubangijinka, ta mãsu taƙawa ce

Verse 36 — Surah Az-Zukhruf 43:36

Kuma wanda ya makanta daga barin hukuncin Mai rahama, to, zã Mu lulluɓe shi da shaiɗan, watau shĩ ne abõkinsa

Verse 37 — Surah Az-Zukhruf 43:37

Kuma lalle su haƙĩƙa sunã kange su daga hanya, kuma sunã Zaton cẽwa sũ mãsu shiryuwa ne

Verse 38 — Surah Az-Zukhruf 43:38

Har a lõkacin da (abõkin Shaiɗan) ya zo Mana (ya mutu) sai ya ce: (wa Shaiɗan) "Dã dai a tsakãnina da tsakãninka akwai nĩsan gabas da yamma, sabõda haka, tir da kai ga zama abõkin mutum

Verse 39 — Surah Az-Zukhruf 43:39

Kuma (wannan magana) bã za ta amfãne ku ba, a yau, dõmin kun yi zãlunci, lalle ku mãsu tãrẽwa ne a cikin azãba

Verse 40 — Surah Az-Zukhruf 43:40

Shin to, kai kanã jiyar da kurma ne, ko kanã shiryar da makãho da wanda ke a cikin ɓata bayyananna

Verse 41 — Surah Az-Zukhruf 43:41

To, kõ dai Mu tafi *da kai to, lalle Mũ, mãsu yin azãbarrãmu, wa ne a kansu

Verse 42 — Surah Az-Zukhruf 43:42

Kõ kuma Mu nũna maka abin da Muka yi musu wa'adi, to, lalle Mũ, Mãsu ĩkon tasarrufi a kansu ne

Verse 43 — Surah Az-Zukhruf 43:43

Sabõda haka, ka yi riƙo ga abin da aka yi wahayi da shi zuwa gaie ka. Lalle ne kai, kanã a kan hanya madaidaiciya

Verse 44 — Surah Az-Zukhruf 43:44

Kuma shi (abin wahayin) ambato (na ɗaukaka) ne a gare ka da kuma ga mutãnenka, kuma zã a tambaye ku

Verse 45 — Surah Az-Zukhruf 43:45

Kuma ka tambayi waɗanda Muka aika a gabãninka daga Manzannin Mu, "Shin, Mun sanya waɗansu gumãka, wasun (Allah), Mai rahama, anã bauta musu

Verse 46 — Surah Az-Zukhruf 43:46

Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun aika Mũsã, game da ãyõyin Mu, zuwa ga Fir'auna da mashãwartansa, sai ya ce: "Lalle nĩ, Manzo ne daga Ubangijin halittu

Verse 47 — Surah Az-Zukhruf 43:47

To, a lõkacin da ya jẽ musu da ãyõyin Mu, sai gã su sunã yi musu dãriya

Verse 48 — Surah Az-Zukhruf 43:48

Kuma ba Mu nũna musu wata ãyã ba, fãce ita ce mafi girma daga 'yar'uwarta. Kuma Muka kãma su da azãba, tsammãninsu kõ sunã kõmõwa

Verse 49 — Surah Az-Zukhruf 43:49

Kuma suka ce: "Yã kai mai sihiri! Ka rõƙa mana Ubangijinka da albarkacin abin da yi alkawari a wurinka, lalle mũ, haƙĩƙa, mãsu shiryuwa ne

Verse 50 — Surah Az-Zukhruf 43:50

To, a lõkacin da duk Muka kuranye musu azãba, sai gã su sunã warware alkawarinsu

Verse 51 — Surah Az-Zukhruf 43:51

Kuma Fir'auna ya yi kira a cikin mutãnensa, ya ce: "Ya mutãnẽna! Ashe mulkin Masar bã a gare ni yake ba, kuma waɗannan kõguna sunã gudãna daga ƙarƙashĩna? Ashe, ba ku gani ba

Verse 52 — Surah Az-Zukhruf 43:52

Kõ kuma bã nĩ ne mafĩfĩci ba daga wannan wanda yake shĩ wulakantacce ne kuma bã ya iya bayyanawar magana sai da ƙyar

Verse 53 — Surah Az-Zukhruf 43:53

To, don me, ba a jẽfa mundãye na zĩnãriya a kansaba, kõ kuma malã'iku su taho tãre da shi haɗe

Verse 54 — Surah Az-Zukhruf 43:54

Sai ya sassabce hankalin mutãnensa, sabõda haka suka bĩ shi. Lalle sũ, sun kasance waɗansu irin mutãne ne fãsiƙai

Verse 55 — Surah Az-Zukhruf 43:55

Sabõda haka a lõkacin da suka husãtar da Mu, Muka yi musu azãbar rãmuwa sai Muka nutsar da su gabã ɗaya

Verse 56 — Surah Az-Zukhruf 43:56

Sai Muka sanya su magabãta kuma abin misãli ga mutãnen ƙarshe

Verse 57 — Surah Az-Zukhruf 43:57

Kuma a lõkacin da aka buga misãli da ¦an Maryama, sai gã mutãnenka daga gare shi (shi misalin) sunã dãriya da izgili

Verse 58 — Surah Az-Zukhruf 43:58

Kuma suka ce: "Shin, gumãkanmu ne mafĩfĩta kõ shi (¦an Maryama)?" Ba su buga wannan misãli ba a gare ka fãce dõmin yin jidãli.* Ã'a, sũ mutãne nemãsu husũma

Verse 59 — Surah Az-Zukhruf 43:59

Shi (¦an Maryama) bai zama ba fãce wani bãwa ne, Mun yi ni'ima a gare shi, kuma Muka sanya shi abin kõyi ga Banĩ Isrã'ĩla

Verse 60 — Surah Az-Zukhruf 43:60

Kuma dã Munã so lalle ne dã Mun sanya malã'iku, daga ci, kinku, a cikin ƙasa, sunã mayẽwa

Verse 61 — Surah Az-Zukhruf 43:61

Kuma lalle shĩ, haƙĩƙa, wani ilmi ne na Sa'a, sabõda haka, kada ku yi shakka a gare ta, kuma ku bĩ Ni. Wannan ita ce hanya madaidaiciya

Verse 62 — Surah Az-Zukhruf 43:62

Kuma kada Shaiɗan ya taushe ku (daga hanyar). Lalle shĩ maƙiyi ne a gare ku, mai bayyanãwar ƙiyayya

Verse 63 — Surah Az-Zukhruf 43:63

Kuma a lõkacin da Ĩsã ya jẽ da hujjõji bayyanannu, ya ce: "Lalle ne nã zo muku da hikima kuma dõmin in bayyana muku, sãshen abin da kuke sãɓã wa jũna acikinsa, sabõda haka ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗã'a

Verse 64 — Surah Az-Zukhruf 43:64

Lalle ne, Allah Shĩ ne Ubangijina kuma Shi ne Ubangijinku sabõda haka ku bauta Masa. Wannan ita ce hanya madaidaiciya

Verse 65 — Surah Az-Zukhruf 43:65

Sai ƙungiyõyi *suka sãɓa a tsakãninsu. To, bone yã tabbata ga waɗanda suka yi zãlunci daga azãbar yini mai raɗaɗi

Verse 66 — Surah Az-Zukhruf 43:66

Shin sunã jiran wani abu ne? sai dai Sa'a ta jẽ musu bisaga abke, alhãli kuwa ba su sani ba

Verse 67 — Surah Az-Zukhruf 43:67

Masõya a yinin nan, sãshensu zuwa ga sãshe maƙiya ne, fãce mãsu taƙawa (sũ kam mãsu son jũna ne)

Verse 68 — Surah Az-Zukhruf 43:68

Ya bãyĩNa! Bãbu tsõro a kanku a yau, kuma bã zã ku yi baƙin ciki ba

Verse 69 — Surah Az-Zukhruf 43:69

Waɗanda suka yi ĩmãni da ãyõyin Mu, kuma suka kasance mãsu sallamawar al'amari (ga Allah)

Verse 70 — Surah Az-Zukhruf 43:70

Ku shiga Aljanna, kũ da mãtan aurenku, anã girmama ku

Verse 71 — Surah Az-Zukhruf 43:71

Anã kẽwayãwa a kansu da akussa na zĩnãriya da kõfuna, alhãli kuwa a cikinsu akwai abin da rãyuka ke marmari kuma idãnu su ji dãɗi, kuma kũ, a cikinta (Aljannar), madawwama ne

Verse 72 — Surah Az-Zukhruf 43:72

Kuma waccan ita ce Aljannar, wannan da aka gãdar da ku ita sabõda abin da kuka kasance kunã aikatãwa

Verse 73 — Surah Az-Zukhruf 43:73

Kunã sãmu, a cikinta, 'yã'yan itãcen marmari mãsu yawa, daga cikinsu kuke ci

Verse 74 — Surah Az-Zukhruf 43:74

Lalle mãsu laifi madawwama ne a cikin azãbar Jahannama

Verse 75 — Surah Az-Zukhruf 43:75

Bã a sauƙaƙar da ita (azãbar) daga gare su, alhãli kuwa sũ, a cikinta, mãsu kãsa magana ne

Verse 76 — Surah Az-Zukhruf 43:76

Kuma ba Mu zãlunce su ba, amma sũ ne suka kasance azzãlumai

Verse 77 — Surah Az-Zukhruf 43:77

Kuma suka yi kira, "Ya Mãliku! Ubangijinka Ya kashe mu mana* " (Mãliku) ya ce: "Lalle kũ mazauna ne

Verse 78 — Surah Az-Zukhruf 43:78

Lalle ne, haƙĩƙa, Mun jẽ muku da gaskiya, kuma amma mafi yawanku mãsu ƙi ga gaskiyar ne

Verse 79 — Surah Az-Zukhruf 43:79

Kõ kuma sun tukka wani al'amari ne? To, lalle Mũ, Mãsu tukkãwa ne

Verse 80 — Surah Az-Zukhruf 43:80

Ko sunã zaton lalle Mũ, bã Mu jin asĩrinsu da gãnãwarsu? Na'am! Kuma manzannin Mu na tãre da su sunã rubũtãwa

Verse 81 — Surah Az-Zukhruf 43:81

Ka ce: "Idan har akwai ɗã ga Mai rahama, to, nĩ ne farkon mãsu bauta (wa ɗan)

Verse 82 — Surah Az-Zukhruf 43:82

Tsarkin Ubangijin sammai da ƙasa, Ubangijin Al'arshi, ya tabbata daga abin da suke sifantãwa

Verse 83 — Surah Az-Zukhruf 43:83

Sabõda haka, ka ƙyãlẽ su, su kũtsa kuma su yi wãsã har su haɗu da yininsu, wanda ake yi musu wa'adi da shi

Verse 84 — Surah Az-Zukhruf 43:84

Kuma Shĩ ne wanda ke abin bautãwa a sama kuma abin bautãwa a ƙasa, kuma, Shĩ ne Mai hikima, Masani

Verse 85 — Surah Az-Zukhruf 43:85

Kuma albarkar wanda ke da mulkin sammai da ƙasã abin da ke a tsakãninsu tã bayyana, kuma a wurin Sa ne ilmin Sa'a yake, kuma zuwa gare Shi ake mayar da ku

Verse 86 — Surah Az-Zukhruf 43:86

Kuma waɗanda suke kira baicin Sa ba su mallaki cẽto ba, fãce wanda ya yi shaida da gaskiya, kuma sũ, sunã sane* (da haka)

Verse 87 — Surah Az-Zukhruf 43:87

Kuma lalle idan ka tambaye su: "Wãne ne ya halitta su?" Lalle ne zã su ce Allah ne. To, yãya ake jũyar da su

Verse 88 — Surah Az-Zukhruf 43:88

Kuma da (ilmin) maganar Sa (Annabi) "Ya Ubangijĩna! Lalle waɗannan mutãne ne waɗanda bã zã su yi ĩmãni ba

Verse 89 — Surah Az-Zukhruf 43:89

To, sai ka kau da kai daga gare su, kuma ka ce, "salãmã." Sa'an nan kuma zã su sani