Back to LanguagesPrevious ChapterNext Chapter EnglishArabicUrduHindiTamilBengali
Hausa - Chapter 44 - Ad-Dukhan
Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink
Verse 1 — Surah Ad-Dukhan 44:1
Verse 2 — Surah Ad-Dukhan 44:2
Inã rantsuwa da Littãfi Mabayyani
Verse 3 — Surah Ad-Dukhan 44:3
Lalle ne, Mũ, Muka saukar da shi a cikin wani dare mai albarka. Lalle Mũ' Mun kasance Mãsu yin gargaɗi
Verse 4 — Surah Ad-Dukhan 44:4
A cikinsa (shi daren) ake rarrabe kõwane umurui bayyananne
Verse 5 — Surah Ad-Dukhan 44:5
Umurni na daga wurin Mu. Lalle Mũ ne Muka kasance Mãsu aikãwã
Verse 6 — Surah Ad-Dukhan 44:6
Sabõda rahama daga Ubangijinka. Lalle Shĩ, Shi ne Mai ji, Mãsani
Verse 7 — Surah Ad-Dukhan 44:7
(Shĩ ne) Ubangijin sammai da ƙasa da abin da ke a tsakãninsu, idan kun kasance mãsu yaƙĩni (za ku gãne haka)
Verse 8 — Surah Ad-Dukhan 44:8
Babu abin bautãwa fãce Shi. Yana rãyarwa Kuma Yana kashẽwa. (Shi ne) Ubangijinku, kuma Ubangijin ubanninku na farko
Verse 9 — Surah Ad-Dukhan 44:9
A'a sũ, sunã wãsã a cikin shakka
Verse 10 — Surah Ad-Dukhan 44:10
Sabõda haka, ka dakata rãnar da sama zã tã zo da hayãƙi bayyananne
Verse 11 — Surah Ad-Dukhan 44:11
Yanã rufe mutãne. Wannan wata azãba ce mai raɗaɗi
Verse 12 — Surah Ad-Dukhan 44:12
Ya Ubangijinmu! Ka kuranye mana azãba. Lalle Mũ, mãsu ĩmãni ne
Verse 13 — Surah Ad-Dukhan 44:13
Inã tunãwa take a gare su, alhãli kuwa, haƙĩƙa, Manzo mai bayyanãwa Ya je musu (da gargaɗin saukar azãbar, ba su karɓa ba)
Verse 14 — Surah Ad-Dukhan 44:14
Sa'an nan suka jũya baya daga gare shi, Kuma suka ce: "Wanda ake gayãwa* ne, mahaukaci
Verse 15 — Surah Ad-Dukhan 44:15
Lalle Mũ, Mãsu kuranyẽwar azãba ne, a ɗan lõkaci kaɗan, lalle kũ, mãsu kõmãwa ne (ga laifin)
Verse 16 — Surah Ad-Dukhan 44:16
Rãnar da Muke damƙa, damƙa mafi girma, lalle ne Mũ mãsu azãbar rãmuwa ne
Verse 17 — Surah Ad-Dukhan 44:17
Kuma lalle ne haƙĩƙa a gabaninsu, Mun fitini mutãnen Fir'auna, kuma wani Manzo karĩmi ya jẽ musu
Verse 18 — Surah Ad-Dukhan 44:18
(Mazon ya ce): "Ku kãwo mini (ĩmãninku) ya bayin Allah! Lalle ni, Manzo ne amintacce zuwa gare ku
Verse 19 — Surah Ad-Dukhan 44:19
Kuma kada ku nẽmi ɗaukaka a kan Allah. Lalle nĩ mai zo muku ne da dalĩli bayyananne
Verse 20 — Surah Ad-Dukhan 44:20
Kuma lalle nĩ na nẽmi tsari da Ubangijĩna, kuma Ubangijinku, dõmin kada ku jẽfe ni
Verse 21 — Surah Ad-Dukhan 44:21
Kuma idan ba ku yi ĩmãni sabõda nĩ ba, to, ku nĩsance ni
Verse 22 — Surah Ad-Dukhan 44:22
Sai ya kirayi Ubangjinsa cẽwa waɗannan mutãnene mãsu laifi
Verse 23 — Surah Ad-Dukhan 44:23
(Allah Ya ce): "To, ka yi tafiyar dare da bayiNa, da dare. Lalle kũ, waɗanda ake bĩ ne (dõmin a kãma ku)
Verse 24 — Surah Ad-Dukhan 44:24
Kuma ka bar tẽku rarrabe. Lalle sũ, runduna ce abar nutsarwa
Verse 25 — Surah Ad-Dukhan 44:25
Da yawa suka bar gõnaki da marẽmari
Verse 26 — Surah Ad-Dukhan 44:26
Da shuke-shuke da matsayi mai kyau
Verse 27 — Surah Ad-Dukhan 44:27
Da wata ni'ima da suka kasance a cikinta sunã mãsu hutu
Verse 28 — Surah Ad-Dukhan 44:28
Kamar haka! Kuma Muka gãdar da ita ga waɗansu mutãne na dabam
Verse 29 — Surah Ad-Dukhan 44:29
Sa'an nan samã da ƙasã ba su yi kũka *a kansu ba, Kuma ba su kasance waɗanda ake yi wa jinkiri ba
Verse 30 — Surah Ad-Dukhan 44:30
Kuma lalle ne, haƙĩƙa Mun tsĩrar da Banĩ Isrã'ĩla daga, azãba mai wulãkantãwa
Verse 31 — Surah Ad-Dukhan 44:31
Daga Fir'auna. Lalle shi, ya kasance maɗaukaki daga cikin mãsu ɓarna
Verse 32 — Surah Ad-Dukhan 44:32
Kuma lalle ne, haƙĩƙa, Mun zãɓe su sabõda wani ilmi (na Taurata) a kan mutãne
Verse 33 — Surah Ad-Dukhan 44:33
Kuma Muka bã su, daga ãyõyin mu'ujizõji, abin da yake a cikinsa, akwai ni'ima bayyananna
Verse 34 — Surah Ad-Dukhan 44:34
Lalle waɗannan mutãne*, haƙĩka, sunã cẽwa
Verse 35 — Surah Ad-Dukhan 44:35
Babu wani abu sai mutuwarmu ta farko, kuma ba mu zama waɗanda ake tãyarwa ba
Verse 36 — Surah Ad-Dukhan 44:36
Sai ku zo da ubanninmu, idan kun kasance mãsu gaskiya
Verse 37 — Surah Ad-Dukhan 44:37
shin, sũ ne mafĩfĩta kõ kuwa mutãnen Tubba'u, kuma da waɗanda ke a gabãninsu? Mun halaka su, lalle sũ, sun kasance mãsu laifi
Verse 38 — Surah Ad-Dukhan 44:38
Kuma ba Mu halitta slmmai da ƙasa da abin da ke a tsakãninsu ba, alhãli kuwa Munã mãsu wãsã
Verse 39 — Surah Ad-Dukhan 44:39
Ba Mu halitta su ba fãce da manufa ta gaskiya, kuma amma mafi yawansu, ba su sani ba
Verse 40 — Surah Ad-Dukhan 44:40
Lalle rãnar rarrabẽwa, ita ce lõkacin wa'adinsu gabã ɗaya
Verse 41 — Surah Ad-Dukhan 44:41
Rãnar da wani zumu bã ya amfãnin wani zumu da kõme kuma ba su zama anã taimakon su ba
Verse 42 — Surah Ad-Dukhan 44:42
fãce wanda Allah Ya yi wa rahama. Lalle Shi (Allah), shĩ ne Mabuwãyi, Mai jin ƙai
Verse 43 — Surah Ad-Dukhan 44:43
Lalle itãciyar zaƙƙũm (ɗanyen wutã)
Verse 44 — Surah Ad-Dukhan 44:44
Ita ce abincin mai laifi
Verse 45 — Surah Ad-Dukhan 44:45
Kamar narkakken kwalta yanã tafasa a cikin cikunna
Verse 46 — Surah Ad-Dukhan 44:46
Kamar tafasar ruwan zãfi
Verse 47 — Surah Ad-Dukhan 44:47
(A cẽ wa malã'ikun wutã), "Ku kãmã shi, sa'an nan ku fizge shi zuwa ga tsakiyar Jahĩm
Verse 48 — Surah Ad-Dukhan 44:48
Sa'an nan ku zuba, a kansa, daga azãbar ruwan zãfi
Verse 49 — Surah Ad-Dukhan 44:49
(A ce masã), "Ka ɗanɗana! Lalle kai, kai ne mabuwãyi mai girma
Verse 50 — Surah Ad-Dukhan 44:50
Lalle wannan, shi ne abin da kuka kasance kunã shakka game da shi
Verse 51 — Surah Ad-Dukhan 44:51
Lalle mãsu taƙawa sunã cikin matsayi amintacce
Verse 52 — Surah Ad-Dukhan 44:52
A cikin gidãjen Aljanna da marẽmari
Verse 53 — Surah Ad-Dukhan 44:53
Sunã tufanta daga tufãfin alharĩni raƙĩƙi, da mai kauri, sunã mãsu zaman fuskantar jũna
Verse 54 — Surah Ad-Dukhan 44:54
Kamar haka, kuma Mun aurar da su da mãtã mãsu kyawun idãnu, mãsu girmansu
Verse 55 — Surah Ad-Dukhan 44:55
Sunã kira, a cikinsu (gidẽjen) ga dukan 'ya'yan itãcen marmari, sunã amintattu (daga dukan abin tsõro)
Verse 56 — Surah Ad-Dukhan 44:56
Bã su ɗanɗanar mutuwa, a cikinsu, fãce mutuwar farko, kuma (Allah), Ya tsare musu azãbar Jahĩm
Verse 57 — Surah Ad-Dukhan 44:57
Sabõda falala daga Ubangijinka. Wancan shi ne babban rabo, mai girma
Verse 58 — Surah Ad-Dukhan 44:58
Dõmin haka kawai Muka sauƙaƙar da shi (Alƙur'ãni) da harshenka, tsammãninsu, su riƙa tunãwa
Verse 59 — Surah Ad-Dukhan 44:59
Sai ka yi jira. Lalle sũ, mãsu jira ne