Back to Languages

Hausa - Chapter 58 - Al-Mujadila

Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink

Verse 4 — Surah Al-Mujadila 58:4

To, wanda bai sãmu ba, sai azumin wata biyu jẽre a gabãnin su shãfi jũna, sa'an nan wanda bai sãmi ĩkon yi ba, to, sai ciyar da miskĩnai sittin. Wannan dõmin ku yĩ ĩmãni da Allah da Manzonsa. Kuma waɗannan hukunce-hukunce haddõdin Allah ne. Kuma kãfirai, sunã da azãba mai raɗadi