Back to Languages

Hausa - Chapter 6 - Al-Anam

Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink

Verse 140 — Surah Al-Anam 6:140

Lalle ne waɗanda suka kashe ɗiyansu sabõda wauta, ba da ilmi ba, sun yi hasãra! Kuma suka haramta abin da Allah Ya azurta su, bisa ƙirƙira ƙarya ga Allah. Lalle ne sun ɓace, kuma ba su kasance mãsu shiryuwa ba