Back to Languages

Hausa - Chapter 6 - Al-Anam

Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink

Verse 143 — Surah Al-Anam 6:143

Nau'õ'i takwas daga tumãkai biyu, kuma daga awãkai biyu; ka ce: Shin mazan biyu ne Ya haramta ko mãtan biyu, ko abin da mahaifar mãtan biyu suka tattara a kansa? Ku bã ni lãbãri da ilmi, idan kun kasance mãsu gaskiya