Idan munãfukai* suka jẽ maka suka ce: "Munẽ shaidar lalle kai haƙĩƙa Manzon Allah ne," Kuma Allah Yanã sane da lalle Kai, haƙĩƙa Manzon Sa ne, kuma Allah Yanã shaida lalle munafukan haƙĩƙa, maƙaryata ne
Kuma idan kã gan su, sai jikunansu su bã ka sha'awa kuma idan sun faɗa,* zã ka saurãra ga maganarsu. Kamar dai sũ ƙyami ne wanda aka jingine. Sunã zaton kõwace tsãwa a kansu take. Sũ ne maƙiyan, sai ka yi saunarsu. Allah Yã la'ane su. Yãya ake karkatar da su
Sũ ne waɗanda ke cẽwa "Kada ku ciyar a kan wanda ke wurin Manzon Allah har su wãtse," alhali kuwa taskõkin sammai da ƙasa ga Allah suke kuma amma munãfukai bã su fahimta
Sunã cẽwa "Lalle ne idan mun kõma* zuwa Madĩnar, haƙĩƙa mafi rinjaya zai fitar da mafi ƙasƙanta daga gare ta, alhãli kuwa rinjãyar ga Allah take kuma da ManzonSa, kuma da mũminai, kuma amma munãfikai ba su sani ba
Kuma ku ciyar daga abin da Muka azurta ku daga gãbanin mutuwa ta je wa ɗayanku har ya ce: "Yã Ubangijina! Don me ba Ka yi mini jinkiri ba zuwa ga wani ajali makusanci dõmin in gaskata kuma in kasance daga sãlihai