Abin da yake a cikin sammai da wanda yake a cikin ƙasã sunã tasbĩhi ga Allah. Gare Shi mulki yake, kuma gare Shi gõdiya take. Kuma Shi, a kan kõme, Mai ikon yi ne
Yanã sanin abin da ke a cikin sammai da ƙassai. Kuma Yanã sanin abin da kuke bõyẽwa da abin da kuke bayyanãwa. Kuma Allah Masani ne ga abin da ke cikin ƙirãza
Wancan sabõda lalle su Manzanninsu sun kasance sunã jẽ musu da hujjõji bayyanannu, sai suka ce: "Ashe, wasu mutane za su shiryar da mũ?" Sai suka kãfirta kuma suka jũya bãya, kuma Allah Ya wadãtu (daga gare su). Kuma Allah wadãtacce ne, Gõdadde
Waɗanda suka kãfirta sun riya cẽwa bã zã a tãyar da su ba. Ka ce: "Ni, inã rantsuwa da Ubangijĩna. Lalle zã a tãyar da ku haƙĩƙatan, sa'an nan kuma lalle anã bã ku lãbãri game da abin da kuka aikata. Kuma wannan ga Allah mai sauƙi ne
A rãnar da Yake tattara ku dõmin rãnar tãruwa. Wancan ne rãnar kãmunga. Kuma wanda ya yi ĩmãni da Allah, kuma ya aikata aikin ƙwarai, zai kankare masa mũnãnan ayyukansa, kuma Yashigar da shi gidãjen Aljanna, ƙoramu na gudãna daga ƙarƙashinsu, sunã madawwama a cikinsu har abada. Wannan ne babban rabo mai girma
Wata masĩfa bã zã ta sãmu ba fãce da iznin Allah. Kuma wanda ya yi ĩmãni da Allah, Allah zai shiryar da zuciyarsa. Kuma Allah, ga dukan kõme, Masani ne
Yã kũ waɗanda suka yi ĩmani! Lalle ne daga mãtanku da ɗiyanku akwai wani maƙiyi* a gare ku, sai ku yi saunarsu. Kuma idan kuka yãfe, kuma kuka kau da kai, kuma kuka gãfarta, to, lalle Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai
Sai ku bi Allah da taƙawa gwargwadon abin da kuka sãmi ĩko. Kuma ku saurãra kuma ku yi ɗã'ã, kuma ku ciyar, ya fi zama alhẽri gare ku. Kuma wandaya sãɓã wa rõwar ransa, to, waɗannan sũ ne mãsu babban rabo