Back to Languages

Hausa - Chapter 8 - Al-Anfal

Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink

Verse 11 — Surah Al-Anfal 8:11

A lõkacin da (Allah) Yake rufe ku da gyangyaɗi, ɗõmin aminci daga gare Shi, kuma Yanã saukar da ruwa* daga sama, a kanku, dõmin Ya tsarkake ku da shi, kuma Ya tafiyar da ƙazantar Shaiɗan daga barinku, kuma dõmin Ya ɗaure a kan zukãtanku, kuma Ya tabbatar da ƙafãfu da shi