Back to Languages

Hausa - Chapter 8 - Al-Anfal

Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink

Verse 48 — Surah Al-Anfal 8:48

Kuma a lõkacin da Shaiɗan* ya ƙawãce musu ayyukansu, kuma ya ce: "Bãbu marinjayi a gareku a yau daga mutãne, kuma nĩ maƙwabci ne gare ku." To, a lõkacin da ƙungiya biyu suka haɗu, ya kõma a kan digãdigansa, kuma ya ce: "Lalle ne nĩ barrantacce ne daga gare ku! Nĩ inã ganin abin da bã ku gani; ni inã tsõron Allah: Kuma Allah Mai tsananin uƙũba ne