Back to Languages

Hausa - Chapter 8 - Al-Anfal

Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink

Verse 72 — Surah Al-Anfal 8:72

Lalle ne waɗanda suka yi ĩmãni, kuma suka yi hijira, kuma suka yi jihãdi da dũkiyõyinsuda rãyukansu, a cikin hanyar Allah, da waɗanda suka bãyar da masauki, kuma suka yi taimako. Waɗancan, sãshensu waliyyai ne ga sãshe. Kuma waɗanda suka yi ĩmãni kuma ba su yi hijira* ba, bã ku da wani abu daga waliccinsu, sai sun yi hijira. Kuma idan suka nẽme ku taimako a cikin addini, to taimako yã wajaba a kanku, fãce a kan mutãne waɗanda a tsakãninku da tsakãninsu akwai wani alkwari. Kuma Allah ne, ga abin da kuke aikatãwa, Mai gani