Back to Languages
Hausa - Chapter 1
Translation by Abubakar Mahmood Jummi
Verse 1
Da sunan Allah, Mai rahama, Mai jin ƙai
Verse 2
Godiya ta tabbata ga Allah, Ubangijin halittu
Verse 3
Mai rahama, Mai jin ƙai
Verse 4
Mai nuna Mulkin Ranar Sakamako
Verse 5
Kai muke bautawa, kuma Kai kadai muke neman taimakonKa
Verse 6
Ka shiryar da mu ga hanya madaidaiciya
Verse 7
Hanyar waɗanda Ka yi wa ni'ima, ba waɗanda aka yi wa fushi ba, kuma ba ɓatattu ba