Back to Languages
Hausa - Chapter 10
Translation by Abubakar Mahmood Jummi
Verse 1
L.R. Waɗancan ayoyin littafi ne kyautatacce
Verse 2
Shin, ya zama abin mamaki ga mutane domin Mun yi wahayi zuwa ga wani namiji daga gare su cewa, "Ka yi gargaɗi ga mutane kuma ka yi bushara ga waɗanda suka yi imani da cewa: Lalle ne suna da abin gabatarwar gaskiya a wurin Ubangijinsu."Kafirai suka ce: "Lalle ne wan nan, haƙiƙa, masihirci ne bayyananne
Verse 3
Lalle Allah ne Ubangijinku wanda Ya halicci sammai da ƙasa a cikin kwana shida, sa'an nan kuma Ya daidaita a kan Al'arshi Yana gudanar da al'amari. Babu wani maceci face a bayan izninSa. Wannan ne Allah, Ubangijinku, sai ku bauta Masa. Shin fa, ba ku tunani
Verse 4
zuwa gare Shi makomarku take gaba ɗaya, wa'adin Allah gaskiya ne. Haƙiƙa, Shi ne Yake fara halitta, sa'an nan kuma Ya mayar da ita domin Ya saka wa waɗanda suka yi imani kuma suka aikata ayyukan ƙwarai da adalci, kuma waɗanda suka kafirta suna da abin sha daga ruwan zafi, da azaba mai raɗaɗi, saboda abin da suka kasance suna yi na kafirci
Verse 5
Shi ne wanda Ya sanya muku rana, babban haske, da wata mai haske, kuma Ya ƙaddara shi ga Manziloli, domin ku san ƙidayar shekaru da lissafi. Allah bai halitta wan nan ba, face da gaskiya, Yana bayyana ayoyi daki-daki domin mutane waɗan da suke sani
Verse 6
Lalle ne a cikin saɓawar dare da yini, da abin da Allah Ya halitta a cikin sammai da ƙasa, haƙiƙaakwai ayoyi ga mutane waɗan da suke yin taƙawa
Verse 7
Lalle ne waɗanda ba su ƙaunar gamuwa da Mu, kuma suka yarda da rayuwar duniya kuma suka natsu da ita, da waɗanda suke gafalallu ne daga ayoyin Mu
Verse 8
Waɗannan matattararsu Jahannama ce saboda abin da suka kasance suna tsirfatawa
Verse 9
Lalle ne waɗanda suka yi imani kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, Ubangijinsu Yana shiryar da su saboda imaninsu, ƙoramu suna gudana daga ƙarƙashinsu, a cikin gidajen Aljannar ni'ima
Verse 10
Kiransu a cikinta, "Tsarkin Ka ya Allah!" Kuma gaisuwarsu a cikinta,"Salamun", kuma ƙarshen kiransu, cewa, "Godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin halittu
Verse 11
Kuma da Allah Yana gaggawa ga mutane da sharri kamar yadda Yake gaggauta musu da alheri, haƙiƙa da an hukunta ajalinsu zuwa gare su. Saboda haka Muna barin waɗanda ba su ƙaunar gamuwa da Mu, a cikin kangararsu suna ta ɗimuwa
Verse 12
Kuma idan cuta ta shafi mutum, sai ya kiraye Mu, yana (kwance) ga sashensa ko kuwa zaune, ko kuwa a tsaye. To, a lokacin, da Muka kuranye cutar daga gare shi, sai ya shuɗe kamar ɗai bai kiraye Mu ba zuwa ga wata cuta wadda ta shafe shi. Kamar wannan ne aka ƙawata ga maɓannata, abin da suka kasance suna aikatawa
Verse 13
Kuma, haƙiƙa, Mun halakar da al'ummomi daga gabaninku, a lokacin da suka yi zalunci, kuma manzanninsu suka je musu da hujjoji bayyanannu, amma ba su kasance suna imani ba. Kamar wannan ne, Muke sakawa ga mutane masu laifi
Verse 14
Sa'an nan kuma Muka sanya ku masu mayewa a cikin ƙasa daga bayansu, domin Mu ga yaya kuke aikatawa
Verse 15
Kuma idan ana karatun ayoyinMu bayyanannu a kansu, sai waɗanda ba su ƙaunar gawuwa da Mu, su ce: "Ka zo da wani Alƙur'ani, wanin wannan, ko kuwa ka musunya shi.*" Ka ce: "Ba ya kasancewa a gare ni in musanya shi da kaina. Ba ni biyar kome face abin da aka yiwo wahayi zuwa gare ni. Kuma, haƙiƙa ni ina tsoro idan na saɓa wa Ubangijina, ga azabar wani yini mai girma
Verse 16
Ka ce: "Da Allah Ya so da ban karanta shi ba a kanku, kuma da ban sanar da ku ba gameda shi, domin lalle ne na zauna a cikinku a zamani mai tsawo daga gabanin (fara saukar) sa. Shin fa, ba ku hankalta
Verse 17
Saboda haka wane ne mafi Zalunci daga wanda ya ƙirƙira ƙarya ga Allah, ko kuwa ya ƙaryata ayoyinSa? Haƙiƙa, masu laifiba su cin nasara
Verse 18
Kuma suna bauta wa, baicin Allah, abin da ba ya cutar dasu kuma ba ya amfaninsu, kuma suna cewa: "Waɗannan ne macetanmu a wurin Allah."Ka ce: "Shin, kuna bai wa Allah labari ne, ga abin da bai sani ba, a cikin sammai ko a cikin ƙasa? TsarkinSa ya tabbata kuma Ya ɗaukaka daga gabin da duk suke yin shirki da Shi
Verse 19
Kuma mutane ba su kasance ba face Al'umma guda, sa'an nan kuma suka saɓa wa juna, kuma ba domin wata kalma ba wadda ta gabata daga Ubangijin ka, da an yi hukunci a tsakaninsu a kan abin da yake a cikin sa suke saɓa wa juna
Verse 20
Kuma suna cewa: "Don me ba a saukar da wata aya ba a gare shi, daga Ubangijin sa?" To, ka ce: "Abin sani kawai, gaibi ga Allah yake. Sai ku yi jira. Lalle ne ni, tare da ku, ina daga masu jira
Verse 21
Kuma idan Muka ɗanɗana wa mutane wata rahama, a bayan wata cuta ta shafe su, sai ga su da makirci a cikin ayoyinMu. Ka ce: "Allah ne mafi gaggawar (sakamakon) makirci." Lalle ne Manzannin Mu suna rubuta abin da kuke yi na makirci
Verse 22
Shi ne wanda Yake tafiyar da ku a cikin tudu da (kuma) teku, sai idan kun kasance a cikin jirage, su gudana tare da su da iska mai daɗi, kuma su yi farin ciki da ita, sai wata guguwa ta je wa jiragen, kuma taguwar ruwa ta je musu daga kowane wuri, kuma su tabbata cewa su, an kewaye su, sai su kirayi Allah, suna masu tsarkake addini gare Shi, (suna cewa): Lalle ne idanKa kuɓutar da mu daga wannan, haƙiƙa muna kasancewa daga masu godiya
Verse 23
To, a lokacin da Ya kuɓutar da su, sai, ga su suna zalunci a cikin ƙasa, ba da wani hakki ba. Ya ku mutane! Abin sani kawai, zaluncinku a kanku yake, a bisa rayuwar duniya. Sa'an nan kuma zuwa gare Mu makomarku take, sa'an nan Mu ba ku labari game da abin da kuka kasance kuna aikatawa
Verse 24
Abin sani kawai, misalin rayuwar duniya kamar ruwa ne Muka saukar da shi daga sama, sa'an nan tsiron ƙasa ya garwaya da shi. Daga abin da mutane da dabbobi suke ci, har idan ƙasa ta riƙi zinariyarta kuma ta yi ƙawa, kuma mutanenta suka zaci cewa su ne masu ikon yi a kanta, sai umurnin Mu ya je mata da dare ko kuma da rana, sai Mu maisheta girbabba kamar ba ta wadata ba a jiya. Kamar wannan ne Muke rarrabe ayoyi, daki-daki, ga mutane waɗan da suke tunani
Verse 25
Kuma Allah Yana kira zuwa ga gidan aminci, kuma, Yana shiryar da wanda Yake so zuwa ga tafarki madaidaici
Verse 26
(Waɗanda suka kyautata yi, suna da abu mai kyawo kuma da ƙari)1), wata ƙura ba ta rufe fuskokinsu, kuma haka wani ƙasƙanci. waɗancan ne abokan Aljanna, suna madawwama a cikinta
Verse 27
Kuma waɗanda suka yi tsirfar munanan ayyuka, sakamakon mummuna da kamarsa yake, kuma ƙasƙanci yana rufe su. Ba su da wani matsari daga Allah, kamar an rufe fuskokinsu da guntayen ƙiraruwa daga dare mai duhu. Waɗannan ne abokan wuta, suna madawwama a cikinta
Verse 28
Kuma a ranar da Muke tara su gaba ɗaya, sa'an nan kuma Mu ce wa waɗanda suka yi shirki, "Ku kama matsayinku, ku da abubuwan shirkinku." Sa'an nan Mu rarrabe a tsakaninsu, kuma abubuwan shirkinsu su ce: "Ba mu kuka kasance kuna bauta wa ba
Verse 29
To, kuma Allah Ya isa zama shaida a tsakaninmu da tsakaninku. Haƙiƙa mun kasance ba mu san kome ba na bautawarku a gare mu
Verse 30
A can ne kowane rai yake jarraba abin da ya bayar bashi, kuma aka mayar da su zuwa ga Allah, Majiɓincinsu Tabbatacce kuma, abin da suka kasance suna ƙirƙirawa ya ɓace musu
Verse 31
Ka ce: "Wane ne Yake azurta ku daga sama da ƙasa? Shin ko kuma Wane ne Yake mallakar ji da gani, kuma Wane ne Yake fitar da mai rai daga mamaci, kuma Ya fitar da mamaci daga mai rai, Kuma Wane ne Yake shirya al'amari?" To, za su ce: "Allah ne." To, ka ce: "Shin fa, ba za ku yi taƙawa ba
Verse 32
To, Wancan ne Allah, Ubangijinku Tobbatacce. To, mene ne a bayan gaskiya face ɓata? To, yaya ake karkatar da ku
Verse 33
Kamar wancan ne kalmar Ubangijinka, ta tabbata a kan waɗanda suka yi fasiƙanci, cewa haƙiƙa su, ba za su yi imani ba
Verse 34
Ka ce: "Shin, daga abubuwan shirkinku akwai wanda yake fara halitta, sa'an nan kuma ya mayar da ita?" Ka ce: "Allah ne Yake fara halitta, sa'an nan kuma Ya mayar da ita. To, yaya akejuyar da ku
Verse 35
Ka ce: "Shin, daga abubuwan shirkinku akwai wanda yake shiryarwa zuwa ga gaskiya?" Ka ce: "Allah ne Yake shiryarwa zuwa ga gaskiya. Shin fa, wanda Yake shiryarwa ne mafi cancantar a bi Shi, ko kuwa wanda ba ya shiryarwa face dai a shiryar da shi? To, mene ne a gare ku? Yaya kuke yin hukunci
Verse 36
Kuma mafi yawansu ba su biyar kome face zato. Lalle ne zato ba ya wadatar da kome daga gaskiya. Lalle Allah ne Masani ga abin da suke aikatawa
Verse 37
Kuma wan nan Alƙur'ani bai kasance ga a ƙirƙira shi ba daga wanin Allah, kuma amma shi gaskatawar wannan ne da yake a gabanin sa da bayanin hukuncin littaffan Allah, Babu shakka a cikinsa, daga Ubangijin halittu yake
Verse 38
Ko suna cewa, "Ya ƙirƙira shi?" Ka ce: "Ku zo da sura guda misalinsa, kuma ku kirayi wanda kuka iya duka, baicin Allah, idan kun kasance masu gaskiya
Verse 39
A'a, sun ƙaryata game da abin da ba su kewaye da saninsa ba, kuma fassarar sa ba ta riga ta je musu ba. Kamar waɗancan ne waɗanda suke a gabaninsu. Sai ka duba, yaya aƙibar Azzalumai ta kasance
Verse 40
Kuma daga cikin su akwai wanda yake yin imani da Shi, kuma daga cikinsu akwai wanda ba ya yin imani da Shi. Kuma Ubangijinka ne Mafi sani ga maɓarnata
Verse 41
Kuma idan sun ƙaryata ka, to, ka ce: "Ina da aikina kuma kuna da aikinku, ku kuɓutattu ne daga abin da nake aikatawa kuma ni kuɓutacce ne daga abin da kuke aikatawa
Verse 42
Kuma daga cikinsu akwai waɗanda suke saurare zuwa gare ka. Shin fa, kai kana jiyar da kurma, kuma ko da sun kasance ba su hankalta
Verse 43
Kuma daga cikinsu akwai wanda yake tsokaci zuwa gare ka. Shin fa, kai kana shiryar da makafi, kuma ko da sun kasance ba su gani
Verse 44
Lalle ne Allah ba Ya zaluntar mutane da kome, amma mutanen ne ke zaluntar kansu
Verse 45
Kuma ranar da Yake tara su, kamar ba su zauna ba face sa'a guda daga yini. Suna gane juna a tsakaninsu. Haƙiƙa, waɗanda suka ƙaryata game da gamuwa da Allah sun yi hasara. Kuma ba su kasance masu shiryuwa ba
Verse 46
Kuma imma dai, haƙiƙa, Mu nuna maka sashen abin da Muke yi musu alkawari, ko kuwa Mu karɓi ranka, to, zuwa gare Mu makomarsu take. Sa'an nan kuma Allah ne shaida a kan abin da suke aikatawa
Verse 47
Kuma ga kowace al'umma akwai Manzo*. Sa'an nan idan Manzonsu ya je, sai a yi hukunci a tsakaninsu da adalci, kuma su, ba a zaluntar su
Verse 48
Kuma suna cewa, "A yaushe wannan wa'adi zai auku, idan kun kasance masu gaskiya
Verse 49
Ka ce: "Ba na mallaka wa kaina wata cuta, haka kuma wani amfani, sai abin da Allah Ya so. Ga kowace al'umma akwai ajali, idan ajalinsu ya zo, to, ba za su yi jinkiri daga gare shi ba, ko da sa'a guda, kuma ba za su gabata ba
Verse 50
Ka ce: "Shin, kun gani, idan azabarSa ta zo muku da dare ko da rana? Mene ne daga gare shimasu laifi suke neman gaggawarsa
Verse 51
Shin sa'an nan kuma idan har ya auku, kun yi imani da shi? Ashe? Yanzu kuwa, alhali kun kasance game da shi kuna neman gaggawar aukuwarsa
Verse 52
Sa'an nan kuma aka ce ga waɗanda suka yi zalunci, "Ku ɗanɗani azabar dawwama! Shin, ana saka muku face da abin da kuka kasance kuna aikatawa
Verse 53
Kuma suna tambayar ka: Shin gaskiya ne? Ka ce: "I, ina rantsuwa da Ubangijina. Lalle gaskiya ne, kuma ba ku zama masu buwaya ba
Verse 54
Kuma da kowane rai wanda ya yi zalunci ya mallaki duka abin da yake a cikin ƙasa, to, da ya yi fansa da shi. Kuma suka dinga nadama a lokacin da suka ga azaba. Sa'an nan aka yi hukunci a tsakaninsu da adalci, kuma ba za a zalunce su ba
Verse 55
To! Haƙiƙa Allah Ya mallaki abin da yake a cikin sammai da ƙasa. To! Haƙiƙa wa'adin Allah gaskiya ne. Amma kuma mafi yawansu ba su sani ba
Verse 56
Shi ne Yake rayarwa kuma Yake matarwa. Kuma zuwa gare Shi ne ake mayar da ku
Verse 57
Ya ku mutane! Lalle wa'azi ya je muku daga Ubangijinku, da waraka ga abin da yake a cikin ƙiraza, da shiriya da rahama ga muminai
Verse 58
Ka ce: "Da falalar Allah da rahamar Sa. Sai su yi farin ciki da wannan." Shi ne mafi alheri daga abin da suke tarawa
Verse 59
Ka ce: "Shin, kun ga abin da Allah Ya saukar saboda ku na arziki, sai kuka sanya hukuncin haramci da halacci a gare shi?" Ka ce: "Shin, Allah ne Ya yi muku izni, ko ga Allah kuke ƙirƙirawar ƙarya
Verse 60
Kuma mene ne zaton waɗanda suke ƙirƙira ƙarya ga Allah, a Ranar ¡iyama? Lalle haƙiƙa, Allah Ma, abucin falala ne a kan mutane, amma kuma mafi yawansu ba su godewa
Verse 61
Kuma ba ka kasance a cikin wani sha'ani ba, kuma ba ka karanta wani abin karatu daga gare shi ba, kuma ba ku aikata wani aiki ba, face Mun kasance Halarce a lokacin da kuke zubuwa a cikinsa. Kuma wani ma'aunin zarra ba zai yi nisa ba daga Ubangijinka a cikin ƙasa, haka kuma a cikin sama, kuma babu wanda yake mafi ƙaranci daga haka, kuma babu mafi girma, face yana a cikin littafi bayyananne
Verse 62
To, Lalle ne masoyan* Allah babu tsoro a kansu, kuma ba za su kasance suna yin baƙin ciki ba
Verse 63
Waɗanda suka yi imani kuma suka kasance suna yin taƙawa
Verse 64
Suna da bushara a cikin rayuwar duniya da ta Lahira. Babu musanyawa ga kalmomin Allah. Wancan shi ne babban rabo mai girma
Verse 65
Kada maganarsu* ta sanya ka a cikin baƙin ciki. Lalle ne alfarma ga Allah take gaba ɗaya. Shi ne Mai ji, Masani
Verse 66
To! Haƙiƙa Allah Yana da mulkin wanda ke a cikin sammai da wanda ke a cikin ƙasa kuma waɗanda suke kiran wanin Allah, ba su biyar waɗansu abokan tarewa (ga Allah a Mulkin Sa). Ba su biyar kome face zato. Kuma ba su zama ba face suna ƙiri faɗi kawai
Verse 67
Shi ne wanda Ya sanya muku dare, domin ku natsu a cikinsa, da yini mai sanya a yi gani. Lalle ne a cikin wannan akwai ayoyi ga mutane waɗanda suke ji
Verse 68
Suka ce: "Allah Ya riƙi ɗa." Tsarkinsa ya tabbata! Shi ne wadatacce Yana da mallakar abin da yake, a cikin sammai da abin da yake a cikin ƙasa, A wurinku babu wani dalili game da wannan! Shin, kuna faɗar abin da ba ku sani ba game da Allah
Verse 69
Ka ce: "Haƙiƙa waɗanda suke ƙirƙira ƙarya ga Allah, ba za su ci nasara ba
Verse 70
Jin daɗi ne a cikin duniya, sa'an nan kuma makomarsu zuwa gare Mu take, sa'an nan Mu ɗanɗana musu azaba mai tsanani saboda abin da suka kasance suna yi na kafirci
Verse 71
Kuma ka karanta musu labarin Nuhu, a lokacin da ya ce wa mutanensa, "Ya mutanena! Idan matsayina da tunatarwata ameda ayoyin Allah sun kasance sun yi nauyi a kanku, to, ga Allah na dogara. Sai ku tara al'amarinku, ku da abubuwan shirkinku, sa'annan kuma kada al'amarinku ya kasance rufaffe a kanku, sa'an nan kuma ku kashe ni, kada ku yi mini jinkiri
Verse 72
Kuma idan kuka juya baya, to, ban tambaye ku wata ijara ba. ljarata ba ta zama ba face daga Allah, kuma an umurce ni da in kasance daga masu sallamawa
Verse 73
Sai suka ƙaryata shi, sa'an nan Muka kuɓutar da shi da wanda yake tare da shi, a cikin jirgi, kuma Muka sanya su masu mayewa, kuma Muka nutsar da waɗanda suka ƙaryata ayoyinMu. Sai ka duba yadda aƙibar waɗan da aka yi wa gargaɗi ta kasance
Verse 74
Sa'an nan kuma Muka aika waɗansu Manzanni daga bayansa zuwa ga mutanensu, suka jemusu da hujjoji bayyanannu, to, ba su kasance za su yi imani ba saboda sun ƙaryata shi a gabani. Kamar wannan ne Muke rufewa a kan zukatan masu ta'addi
Verse 75
Sa'an nan kuma a bayansu Muka aika Musa da Haruna zuwa ga Fir'auna da mashawartansa, tare da ayoyin Mu. Sai suka kangara kuma sun kasance mutane masu laifi
Verse 76
Sa'an nan a lokacin da gaskiya ta je musu daga gare Mu, suka ce: "Wannan haƙiƙa sihiri ne bayyananne
Verse 77
Musa ya ce: " Shin, kuna cewa ga gaskiya a lokacin data zo muku? Shin, sihiri ne wannan? Lalle masihirci, ba ya cin Nasara
Verse 78
Suka ce: "Shin, ka zo mana ne domin ka juyar da mu daga abin da muka iske ubanninmu a kansa, kuma girma ya kasance gare ku, ku biyu a cikin ƙasa? Ba za mu zama masu imani ba saboda ku
Verse 79
Kuma Fir'auna ya ce: "Ku zo mini da dukan masihirci, masani
Verse 80
To, a lokacin da masihirta suka je, Musa ya ce musu,"Ku jefa abin da kuke jefawa
Verse 81
To, a lokacin da suka jefa, Musa ya ce: "Abin da kuka zo da shi sihiri ne. Lalle ne Allah zai ɓata shi. Haƙiƙa Allah ba Ya gyara aikin maɓarnata
Verse 82
Kuma Allah Yana tabbatar da gaskiya da kalmomin Sa, ko da masu laifi sun ƙi
Verse 83
Sa'an nan babu wanda ya yi imani da Musa face zuriya daga mutanensa, a kan tsoron kada Fir'auna da shugabanninsu su fitine su. Lalle, haƙiƙa, Fir'auna marinjayi ne a cikin ƙasa, kuma lalle shi haƙiƙa, yana daga masu ɓarna
Verse 84
Kuma Musa ya ce: "Ya ku mutanena! Idan kun kasance kun yi imani da Allah, to, a gare Shi sai ku dogara, idan kun kasance Musulmi
Verse 85
Sai suka ce: "Ga Allah muka dogara. Ya Ubangijinmu! Kada Ka sanya mu fitina ga mutane Azzalumai
Verse 86
Kuma Ka kuɓutar da mu domin RahamarKa, daga mutane kafirai
Verse 87
Kuma Muka yi wahayi zuwa ga Musa da ɗan'uwansa, cewa: Ku biyu, ku zaunar da mutanenku a Masar a cikin wasu gidaje. Kuma ku sanya gidajenku su fuskanci Alƙibla*, kuma ku tsayar da salla. Kuma ku bayar da bushara ga masu imani
Verse 88
Sai MuSa ya ce: "Ya Ubangijinmu! Haƙiƙa Kai ne Ka bai wa Fir'auna da majalisarsa ƙawa da dukiyoyi a cikin rayuwar duniya, ya Ubangijinmu, domin su ɓatar (damutane) daga hanyarKa. Ya Ubangijinmu! Ka shafe a kan dukiyarsu kuma Ka yi ɗauri* a kan zukatansu yadda ba za su yi imani ba har su ga azaba mai raɗaɗi
Verse 89
(Allah) Ya ce: "Lalle ne an karɓi addu'arku. Sai ku daidaitu kuma kada ku bi hanyar waɗanda ba su sani ba
Verse 90
Kuma Muka ƙetarar da Bani Isra'ila teku sai Fir'auna da rundunarsa suka bi su bisa ga zalunci da ƙetare haddi, har a lokacin da nutsewa ta riske shi ya ce: "Na yi* imani cewa, haƙiƙa, babu abin bautawa face wannan da Banu Isra'il suka yi imani da Shi, kumani, ina daga Musulmi
Verse 91
Ashe! A yanzu! Alhali kuwa, haƙiƙa ka saɓa a gabani, kuma ka kasance daga masu ɓarna
Verse 92
To, a yau Muna kuɓutar* da kai game da jikinka, domin ka kasance aya ga waɗanda suke a bayanka. Kuma lalle ne masu yawa daga mutane, haƙiƙa, gafalallu ne ga ayoyinMu
Verse 93
Kuma lalle ne haƙiƙa Mun zaunar* da Bani Isra'ilamazaunar gaskiya kuma Muka arzuta su daga abubuwa masu daɗi. Sa'an nan ba su saɓa ba har ilmi ya je musu. Lalle ne Ubangijinka Yana yin hukunci a tsakaninsu a Ranar Kiyama a cikin abin da suka kasance suna saɓa wa juna
Verse 94
To, idan ka kasance a cikin shakka daga abin da Muka saukar zuwa gare ka, sai ka tambayi waɗanda suke karatun Littafi daga gabaninka. Lalle ne, haƙiƙa, gaskiya ta je maka daga Ubangijinka domin haka kada ka kasance daga masu kokanto
Verse 95
Kuma kada ka kasance daga waɗanda suke ƙaryatawa game da ayoyin Allah, har ka kasance daga masu hasara
Verse 96
Lalle ne waɗan da kalmar Ubangijinka ta wajaba a kansu, ba za su yi imani ba
Verse 97
Kuma ko da kowace aya ta je musu, sai sun ga Azaba mai raɗaɗi
Verse 98
To, domin me wata alƙarya ba ta kasance ta yi* imaniba har imaninta ya amfane ta, facemutanen Yunus? A lokacin da suka yi imani, Munjanye Azabar wulakanci daga gare su a cikin rayuwar duniya. Kuma Muka jiyar da su daɗi zuwa wani lokaci
Verse 99
Kuma da Ubangijinka Ya so, da waɗanda suke a cikin ƙasa sun yi imani dukansu gaba ɗaya. Shin, kai kana tilasta mutanene har su kasance masu imani
Verse 100
Kuma ba ya kasancewa ga wani rai ya yi imani face da iznin Allah, kuma (Allah) Yana sanya ƙazanta a kan waɗan da ba su yin hankali
Verse 101
Ka ce: "Ku dubi abin da yake cikin sammai da ƙasa."Kuma ayoyi da gargaɗi ba su wadatarwa ga mutane waɗanda ba su yin imani
Verse 102
To, Shin suna jiran wani abu face kamar misalin kwanukan waɗanda suka shuɗe daga gabanin su? Ka ce: "Ku yi jira! Lalle ni tare da ku, ina daga masu jira
Verse 103
Sa'an nan kuma Muna kuɓutar da manzanninMu da waɗanda suka yi imani, kamar wannan ne, tabbatacce ne a gare Mu, Mu kuɓutar da masu imani
Verse 104
Ka ce: "Ya ku mutane! Idan kun kasance a cikin kokanto daga addinina, to ba ni bauta wa, waɗanda kuke, bauta wa, baicin Allah, kuma amma ina bauta wa Allah wanda Yake karɓar rayukanku. Kuma an umurce ni da in kasance daga masu imani
Verse 105
Kuma (an ce mini): Ka tsayar da fuskarka ga Addini, kana karkatl zuwa ga gaskiya, kuma kada ka kasance daga masu shirka
Verse 106
Kuma kada ka kirayi, baicin Allah, abin da ba ya amfanin ka kuma ba ya cutar ka. To, idan ka aikata haka, sa'an nan lalle kai, a lokacin, kana daga masu zalunci
Verse 107
Kuma idan Allah Ya shafe ka da wata cuta, to, babu mai yaye ta face shi, kuma idan Yana nufin ka da wani alheri, to, babumai mayar da falalarSa. Yana samun wanda Yake so daga cikin bayinSa da shi. Kuma Shi ne Mai gafara, Mai jin ƙai
Verse 108
Ka ce: "Ya ku mutane! Lalle ne gaskiya, ta zo muku daga Ubangijinku. To, wanda ya shiryu, ya shiryu ne domin kansa kawai, kuma wanda ya ɓace yana ɓacewa ne a kansa kawai. Kuma ban zama wakili a kanku ba
Verse 109
Kuma ka bi abin da ake yin wahayinsa zuwa gare ka, kuma ka yi haƙuri har Allah Ya yi hukunci. Kuma Shi ne Mafi alherin masu hukunci