Back to Languages

Hausa - Chapter 104 - Al-Humazah

Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink

Verse 1 — Surah Al-Humazah 104:1

Bone ya tabbata ga duk mai nune, mai zunɗe (mai raɗa)

Verse 2 — Surah Al-Humazah 104:2

Wanda ya tara dukiya, kuma ya mayar da ita abar tattalinsa

Verse 3 — Surah Al-Humazah 104:3

Yana zaton cewa dukiyarsa za ta dawwamar da shi

Verse 4 — Surah Al-Humazah 104:4

A'aha! Lalle ne za a jefa shi a cikin Huɗama

Verse 5 — Surah Al-Humazah 104:5

Kuma me ya sanar da kai abin da ake ce wa Huɗama

Verse 6 — Surah Al-Humazah 104:6

Wutar Allah ce wadda ake hurawa

Verse 7 — Surah Al-Humazah 104:7

Wadda take leƙawa a kan zukata

Verse 8 — Surah Al-Humazah 104:8

Lalle ne ita abar kullewa ce a kansu

Verse 9 — Surah Al-Humazah 104:9

A cikin wasu ginshiƙai miƙaƙƙu