Back to LanguagesPrevious ChapterNext Chapter
Hausa - Chapter 105 - Al-Fil
Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink
Verse 1 — Surah Al-Fil 105:1
Ashe, ba ka ga yadda Ubangijin ka Ya aikata ga mutanen giwa* ba
Verse 2 — Surah Al-Fil 105:2
Ashe, bai sanya kaidin su a cikin ɓata ba
Verse 3 — Surah Al-Fil 105:3
Kuma Ya sako, a kansu, wasu tsuntsaye, jama'a-jama'a
Verse 4 — Surah Al-Fil 105:4
Suna jifar su da wasu duwatsu na yumɓun wuta
Verse 5 — Surah Al-Fil 105:5
Sa'an nan Ya sanya su kamar karmami wanda aka cinye