Back to Languages

    Hausa - Chapter 111

    Translation by Abubakar Mahmood Jummi

    Verse 1

    Hannaye biyu na Abulahabi sun halaka, kuma ya halaka

    Verse 2

    Dukiyarsa ba ta tsare masa kome ba, da abin da ya tara

    Verse 3

    Za ya shiga wuta mai huruwa

    Verse 4

    Tare da matarsa mai ɗaukar itacen (wuta)

    Verse 5

    A cikin kyakkyawan wuyanta akwai igiya ta kaba (Ranar ¡iyama)