Back to Languages

    Hausa - Chapter 114

    Translation by Abubakar Mahmood Jummi

    Verse 1

    Ka ce "Ina neman tsari ga Ubangijin mutane

    Verse 2

    Mamallakin mutane

    Verse 3

    Abin bautawar mutane

    Verse 4

    Daga sharrin mai sanya wasuwasi, mai ɓoyewa

    Verse 5

    Wanda ke sanya wasuwasi a cikin ƙirazan mutane

    Verse 6

    Daga aljannu da mutane