Mu, Muna bayar da labari a gare ka, mafi kyawon labari ga abin da Muka yi wahayin wannan Alƙur'ani zuwa gare ka. Kuma lalle ne ka kasance a gabaninsa, haƙiƙa, daga gafalallu
Kuma kamar wancan ne, Ubangijinka Yake zaɓen ka, kuma Ya sanar da kai daga fassarar labarai, kuma ya cika ni'imominSa a kanka, kuma a kan gidan Yaƙuba kamar yadda ya cika su a kan ubanninka biyu, a gabani, Ibrahim da Is'haƙa. Lalle Ubangijinka ne Masani, Mai hikima
A lokacin da suka ce:* lalle ne Yusufu da ɗan'uwansa ne mafiya soyuwa ga ubanmu daga gare mu, alhali kuwa mu jama'a guda ne. Lalle ubanmu, haƙiƙa, yana cikin ɓata bayyananniya
Wani mai magana daga cikinsu ya ce: "Kada ku kashe Yusufu. Ku jefa shi a cikin duhun rijiya, wasu matafiya su tsince shi, idan kun kasance masu aikatawa ne
To, a lokacin* da suka tafi da shi, kuma suka yi niyyar su sanya shi a cikin duhun rijiya, Muka yi wahayi zuwa gare shi, "Lalle ne, kana ba su labari game da wannan al'amari nasu, kuma su ba su sani ba
Suka ce: "Ya babanmu!* Lalle ne, mun tafi muna tsere, kuma muka bar Yusufu a wurin kayanmu, sai kerkeci ya cinye shi, kuma kai, ba mai amincewa da mu ba ne, kuma ko da mun kasance masu gaskiya
Kuma suka je, a jikin rigarsa akwai wani jinin ƙarya. Ya ce: "A'a, zukatanku suka ƙawata muku wani al'amari. Sai haƙuri mai kyau! Kuma Allah ne wanda ake neman taimako (a gunSa) a kan abin da kuke siffantawa
Kuma wani ayari* ya je, sai suka aika mai neman musu ruwa, sai ya zura gugansa, ya ce: "Ya busharata! Wannan yaro ne." Kuma suka ɓoye shi yana abin sayarwa. Kuma Allah ne Masani ga abin da suke aikatawa
Kuma wanda ya saye shi daga Masar* ya ce wa matarsa, "Ki girmama mazauninsa, akwai tsammanin ya amfane mu, ko kuwa mu riƙe shi ɗa."Kuma kamar wancan ne Muka tabbatar ga Yusufu, a cikin ƙasa kuma domin Mu sanar da shi daia fassarar luburu, kuma Allah ne Marinjayi a kan al'amarinSa, kuma amma mafi yawan mutane ba su sani ba
Kuma wadda yake *a cikin ɗakinta, ta neme shi ga kansa, kuma ta kukkulle ƙofofi, kuma ta ce, "Ya rage a gare ka!" ya ce: "Ina neman tsarin Allah! Lalle shine Ubangijina. Ya kyautata mazaunina. Lalle ne shi, masu zalunci ba su cin nasara
Kuma lalle ne, ta himmantu da shi. Kuma ya himmantu da ita in ba domin ya ga dalilin Ubangijinsa ba. Kamar haka dai, domin Mu karkatar da mummunan aiki da alfasha daga gare shi. Lalle ne shi, daga bayinMu zaɓaɓɓu yake
Kuma suka yi tsere* zuwa ga ƙofa. Sai ta tsage rigarsa daga baya, kuma suka iske mijinta a wurin ƙofar. Ta ce: "Menene sakamakon wanda ya yi nufin cuta game da iyalinka? Face a ɗaure shi, ko kuwa a yi masa wata azaba mai raɗaɗi
Ya ce: "Ita ce ta neme ni a kaina."Kuma wani mai shaida daga mutanenta ya bayar da shaida: *"Idan rigarsa ta kasance an tsage ta daga gaba, to, ta yi gaskiya, kuma shi ne daga maƙaryata
Kuma waɗansu mata* a cikin Birnin suka ce: "Matar Aziz tana neman hadiminta daga kansa! Haƙiƙa, ya rufe zuciyarta da so. Lalle ne mu, Muna ganin taa cikin ɓata bayyananna
Sa'an nan a lokacin da ta ji labari game da makircinsu, sai ta aika kiran liyafa zuwa gare su, kuma ta yi tattalin abincin da ake dogara wajen cinsa, kuma ta bai wa kowace ɗaya daga cikinsu wuƙa, kuma ta ce: "Ka fito a kansu." To, a lokacin da, suka gan shi, suka girmama shi, kuma suka yanyanke hannayensu, kuma suka ce: "Tsarki yana ga Allah! Wannan ba mutum ba ne! Wannan bai zama ba face Mala'ika ne mai daraja
Ta ce: "To wannan ne fa wanda kuka, zarge* ni a cikinsa! Kuma lalle ne, haƙeƙa na neme shi daga kansa, sai ya tsare gida, kuma ni ina rantsuwa, idan bai aikata abin da nake umurnin sa ba, haƙeƙa ana ɗaure shi. Haƙiƙa, yana kasan, cewa daga ƙasƙantattu
Ya ce: "Ya Ubangijina! Kurkuku ne mafi soyuwa a gare ni daga abin da suke kira na zuwa gare shi. Kuma idan ba Ka karkatar da kaidinsu daga gare ni ba, zan karkata zuwa gare su, kuma in kasance daga jahilai
Kuma waɗansu samari biyu suka shiga kurkuku tare da shi.* ¦ayansu ya ce: "Lalle ne ni, na yi mafarkin ga ni ina matsar giya." Kuma ɗayan ya ce: "Lalle ne ni, na yi Mafarkin ga ni ina ɗauke da waina a bisa kaina, tsuntsaye suna ci daga gare ta. Ka ba mu labari game da fassararsu. Lalle ne mu, Muna ganin ka daga masu kyautatawa
Ya ce: "Wani abinci ba zai zo muku ba wanda ake azurta ku da shi face na ba ku labarin fassararsa,* kafin ya zo muku. Wannan kuwa yana daga abin da Ubangijina Ya sanar da ni. Lalle ne ni na bar addinin mutane waɗanda ba su yi imani da Allah ba, kuma game da lahira, su kafirai ne
Kuma na bi addinin iyayena, Ibrahim da Is'haka da Yaƙuba. Ba ya yiwuwa a gare mu mu yi shirka da Allah da kome. Wannan yana daga falalar Allah a kanmu da mutane, amma mafi yawan mutane ba su godewa
Ba ku bauta wa kome, baicinSa, face waɗansu sunaye waɗanda kuka ambace su, ku da ubanninku. Allah bai saukar da wani dalili ba game da su. Babu hukunci face na Allah. Ya yi umurnin kada ku bauta wa kowa face Shi. Wancan ne addini madaidaici, kuma amma mafi yawan mutane ba su sani ba
Ya abokaina biyu, na kurkuku! Amma ɗayanku, to, zai shayar da uban gidansa giya, kuma gudan, to, za a tsire shi, sa'an nan tsuntsaye su ci daga kansa. An hukunta al'amarin, wanda a cikinsa kuke yin fatawa
Kuma ya ce da wanda ya tabbatar da cewa shi mai kuɓuta ne daga gare su, "Ka ambace ni a wurin uban gidanka." Sai Shaiɗan ya mantar da shi tunawar Ubangijinsa, saboda haka ya zauna a cikin kurkuku 'yan shekaru
Kuma sarki ya ce: "Lalle ne, na yi mafarki*; na ga shanu bakwai masu ƙiba, waɗansu bakwai ramammu, suna cin su, da zangarku bakwai kore-kore da waɗansu ƙeƙasassu. Ya ku jama'a! Ku yi mini fatawa a cikin mafarkina, idan kun kasance ga mafarki kuna fassarawa
Ya Yusufu! Ya kai mai yawan gaskiya! Ka yi mana fatawa a cikin shanu bakwai masu ƙiba, waɗansu bakwai ramammu suna cin su, da zangarku bakwai koraye da waɗansu ƙeƙasassu, tsammanina in koma ga mutane, tsammaninsu za su sani
Kuma sarkin ya ce: "Ku zo mini da shi." To, a lokacin da manzo ya je masa (Yusufu), ya ce: "Ka koma zuwa ga uban gidanka, sa' an nan ka tambaye shi; Menene halin matayen nan waɗanda suka yanyanke hannayensu? Lalle ne Ubangijina ne Masani game da kaidin su
Ya ce: "Mene ne babban al'amarinku, a lokacin da kaka nemi Yusufu daga kansa?" Suka ce: "Tsarki ga Allah yake! Ba mu san wani mummunan aiki a kansaba." Matar Aziz ta ce: "Yanzu fagaskiya* ta bayyana. Ni ce na neme shi daga kansa. Kuma lalle ne shi, haƙiƙa, yana daga masu gaskiya
Kuma ba ni kuɓutar da kaina. Lalle ne rai, haƙiƙa, mai yawan umurni ne da mummunan aiki, face abin da Ubangjina Ya yi na; rahama. Lalle Ubangjina Mai gafara ne, Mai jin ƙai
Kuma sarkin ya ce: "Ku zo mini da shi in keɓe shi ga kaina." To, a lokacin da Yusufu ya yi masa magana sai ya ce: "Lalle ne kai a yau, a gunmu, mai daraja ne, amintacce
Kuma kamar wancan ne Muka bayar da iko ga Yusufu a cikin ƙasa* yana sauka a inda duk yake so. Muna samun wanda Muke so da rahamar Mu, kuma ba Mu tozartar da ladar masu kyautatawa
Kuma a lokacin da ya yi musu tattali da tattalinsu, ya ce: "Ku zo mini da wani ɗan'uwa naku daga ubanku. Ba ku gani ba cewa lalle ne ni, ina cika ma'auni, kuma ni ne mafi alherin masu saukarwa
To, a lokacin da suka koma zuwa ga ubansu, suka ce: "Ya babanmu! An hana mu awo sai ka aika ɗan'uwanmu tare da mu. Za mu yi awo. Kuma lalle ne, haƙiƙa mu, masu lura da Shi ne
Ya ce: "Ashe, za ni amince muku a kansa? Face dai kamar yadda na amince muku a kan ɗan'uwansa daga gabani, sai dai Allah ne Mafificin masu tsari, kuma Shi ne Mafi rahamar masu rahama
Kuma a lokacin da suka buɗe kayansu, suka sami hajjarsu an mayar musu da ita, suka ce: "Ya babanmu! Ba mu zalunci! Wannan hajjarmu ce an mayar mana da ita, kuma mu nemo wa iyalinmu abinci, kuma mu kiyaye ɗan'uwanmu, kuma mu ƙara awon kayan raƙumi guda, wancan awo ne mai sauki
Ya ce: "Ba zan sake shi tare da ku ba, sai kun kawo mini alkawarinku baga Allah, haƙiƙa, kuna dawo mini da shi, sai fa idan an kewaye ku." To, a, lokacinda suka yi masa alkawari, ya ce: "Allah ne wakili a kan abin da muke faɗa
Kuma ya ce: "Ya ɗiyana! Kada ku shiga ta ƙofa guda, ku shiga ta ƙofofi dabam-dabam,* kuma ba na wadatar muku kome daga Allah. Babu hukunci face daga Allah, a gare Shi na dogara, kuma a gare Shi masu dogara sai su dogara
Kuma a lokacin da suka shiga daga inda ubansu ya umurce su wani abu bai kasance yana wadatarwa ga barinsu daga Allah ba face wata bukata ce a ran Yaƙubu, ya bayyana ta. Kuma lalle ne shi, haƙiƙa, ma'abucin wani ilmi ne ga abin da Muka sanar da shi, kuma mafi yawan mutane ba su sani ba
Kuma a lokacin da suka shiga wajen Yusufu, ya tattara ɗan'uwansa zuwa gare shi, ya ce: "Lalle ni ne ɗan'uwanka, saboda haka kada ka yi baƙin ciki da abin da suka kasance suna aikatawa
Sa'an nan a lokacin da ya yi musu tattali da tattalinsu, sai ya sanya ma'auni a cikin kayan ɗan'uwansa sa'an nan kuma mai yekuwa ya yi yekuwa," Ya ku ayari! lalle ne, haƙiƙa ku ɓarayi ne
To, sai ya fara (bincike) da jikunansu a gabanin jakar ɗan'uwansa. Sa'an nan ya fitar da ita daga jakar ɗan'uwansa. Kamar wancan muka shirya wa Yusufu. Bai kasance ya kama ɗan'uwansa a cikin addinin (dokokin) sarki ba, face idan Allah Ya so. Muna ɗaukaka darajoji ga wanda Muka so, kuma a saman kowane ma'abucin ilmi akwai wani masani
Suka ce: "Idan ya yi sata, to, lalle ne wani ɗan'uwansa ya taɓa yin sata a gabaninsa." Sai Yusufu ya boye* ta a cikin ransa. Kuma bai bayyana ta ba a gare su, ya ce: "Ku ne mafi sharri ga wuri. Kuma Allah ne Mafi sani daga abin da kuke siffantawa
Suka ce: "Ya kai Azizu! Lalle ne yana da wani uba, tsoho mai daraja, saboda haka ka kama ɗayanmu amatsayinsa. Lalle ne mu, muna ganin ka daga masu kyautatawa
Saboda haka, a lokacin da suka yanke tsammani daga gare shi, sai suka fita suna masu ganawa.* Babbansu ya ce: "Shin, ba ku sani ba cewa lalle ne ubanku yariƙi alkawari daga Allah a kanku, kuma daga gabanin haka akwai abin da kuka yi na sakaci game da Yusufu? Saboda haka, ba zan gushe daga ƙasar nan ba face ubana ya yi mini izni, ko kuwa Allah Ya yi hukunci a gare ni, kuma Shi ne Mafi alherin mahukunta
Ku koma zuwa ga ubanku, ku gaya masa: Ya babanmu, lalle ne ɗanka ya yi sata, kuma ba mu yi shaida ba face da abin da muka sani, kuma ba mu kasance mun san gaibu ba
Ya ce: "A'a, zukatanku sun ƙawata wani al'amari a gare ku. Sai haƙuri mai kyawo, akwai tsammanin Allah Ya zo mini da su gaba ɗaya (Yusufu da 'yan'uwansa). Lalle ne Shi ne Masani, Mai hikima
Ya ɗiyana! Sai ku tafi ku nemo labarin Yusufu* da ɗan'uwansa. Kada ku yanke tsammani daga rahamar Allah. Lalle ne, babu Mai yanke tsammani daga rahamar Allah face mutane kafirai
Sa'an nan a lokacin da suka shiga gare shi suka ce: "Ya kai Azizu! Cuta ta shafe mu, mu da iyalinmu, kuma mun zo da wata haja maras kuma. Sai ka cika mana ma'auni, kuma ka yi sadaka a gare mu. Lalle ne Allah Yana saka wa masu yin sadaka
Saka ce: "Shin ko, lalle ne, kai ne Yusufu?" Ya ce: "Ni ne Yusufu, kuma wamian shi ne ɗan'uwana. Hƙiƙa Allah Ya yi falala a gare mu. Lalle ne, shi wanda ya bi Allah da taƙawa, kuma ya yi haƙuri, to, Lalle ne Allah ba Ya tozarta ladar masu kyautatawa
Sa'an nan a lokacin da mai bayar da bushara ya je, sai ya jefa ta a kan fuskarsa, sai ya koma mai gani. Ya ce: "Shin, ban gaya muku ba, lalle ne, ni ina sanin abin da ba ku sani ba, daga Allah
Kuma ya ɗaukaka iyayensa biyu a kan karaga, sa'an nan suka faɗi a gare shi, suna masu sujada.* Kuma ya ce: "Ya babana! Wannan ita ce fassarar mafarkin nan nawa. Lalle ne Ubangijina Ya sanya shi ya tabbata sosai, kuma lalle ne Ya kyautata game da ni a lokacin da Ya fitar da ni daga kurkuku. Kuma Ya zo da ku daga ƙauye, a bayan Shaiɗan ya yi fisgar ɓarna a tsakanina da tsakanin 'yan'uwana, Lalle ne Ubangijina Mai tausasawa ne ga abin da Yake so. Lalle ne Shi, Shi ne Masani, Mai hikima
Ya Ubangijina* lalle ne Ka ba ni daga mulki, kuma Ka sanar da ni daga fassarar labaru. Ya Mahaliccin sammai da ƙasa! Kai ne Majiɓincina a duniya da Lahira Ka karɓi raina ina Musulmi, kuma Ka riskar da ni ga salihai
Wannan daga* labarun gaibi ne, Muna yin wahayinsa zuwa gare ka, kuma ba ka kasance a wurinsu ba a lokacin da suke yin niyyar zartar da al'amarinsu, alhali suna yin makirci
Ka ce: "Wannan ce hanyata;* ina kira zuwa ga Allah a kan basira, ni da waɗanda suka bi ni, kuma tsarki ya tabbata ga Allah! Ni kuma, ban zama daga masu shirki ba
Kuma ba Mu aika ba a gabaninka face mazaje, Muna wahayi zuwa gare su, daga mutanen ƙauyuka. Shin fa, ba su yi tafiya a cikin ƙasa ba, domin su dubayadda aƙibar waɗanda suka kasance daga gabaninsu ta zama? Kuma lalle ne gidan Lahira shi ne mafi alheri ga waɗanda suka yi taƙawa? Shin fa, ba ku hankalta
Har a lokacin da Manzanni suka yanke tsammani, kuma suka yi zaton cewa an jingina suga ƙarya, sai taimakonMu ya je masu, Sa'an nan Mu tserar da wanda Muke so, kuma ba a mayar da azabarMu daga mutane masu laifi
Lalle ne haƙiƙa abin kula ya kasance a cikin ƙissoshinsu ga masu hankali. Bai kasance wani ƙirƙiran labari ba kuma amma shi gaskatawa ne ga, abin da yake a gaba gare shi, da rarrabewar dukan abubuwa, da shiriya da rahama ga mutane waɗanda suka yi imani