Allah Shi ne wanda Ya ɗaukaka sammai, ba da ginshiƙai ba waɗanda kuke ganin su. Sa'an nan kuma Ya daidaita a kan Al'arshi, kuma Ya hore rana da wata, kowane yana gudana zuwa ga ajali ambatacce. Yana shirya al'amari, Yana rarrabe ayoyi daki-daki, mai yiwuwa ne ku yi yaƙini da haɗuwa da Ubangijinku
Kuma shi, ne wanda Ya shimfiɗa kasa, kuma Ya sanya duwatsu da koguna a cikinta, kuma daga dukan 'ya'yan itace Ya sanya ma'aura biyu cikinsu. Yana sanya dare ya rufe yini. Lalle ne a cikin wancan, haƙiƙa akwai ayoyi ga mutane waɗanda suke yin tunani
Kuma a cikin ƙasa akwai yankuna masu maƙwabtaka, da gonaki na inabobi da shuka da dabinai iri guda, da waɗanda ba iri guda ba, ana shayar da su da ruwa guda. Kuma Muna fifita sashen sa a kan sashe a wajen ci. Lalle ne a cikin wancan akwai ayoyi ga muiane waɗan da suke hankalta
Kuma idan ka yi mamaki, to, mamakin kam shi ne maganarsu, "Shin, idan muka kasance turɓaya, za mu zama a cikin wata halitta sabuwa?" Waɗancan ne waɗanda suka kafirta da Ubangijinsu, kuma waɗanda akwai ƙuƙumai a cikin wuyoyinsu, kuma waɗancan ne abokan wuta. Su, a cikinta, masu dawwama ne
Kuma suna neman ka da gaggawa da azaba a gabanin rahama, alhali kuwa abubuwan misali sun gabata a gabaninsu. Kuma lalle ne Ubangijinka, haƙiƙa, Ma'abucin gafara ne ga mutane a kan zaluncinsu, kuma lalle ne Ubangijinka, haƙiƙa, Mai tsananin uƙuba ne
Kuma waɗanda suka kafirta suna cewa don me ba a saukar da wata aya a gare shi ba daga Ubangijin sa? Abin sani kawai, kai dai mai gargaɗi ne kuma a cikin kowaɗanne mutane akwai mai shiryarwa
Allah Yana sanin abin da kowace mace take ɗauke da shi a cikinta da abin da mahaifu suke ragewa* da abin da suke ƙarawa. Kuma dukkan kome, a wurinSa, da gwargwado yake
Daidai ne daga gare ku, wanda ya asirta magana da wanda ya bayyana game da ita, da wanda yake shi mai neman ɓoyewa ne da dare, da mai bayyana a cikin tafiyarsa a hanya da rana
(Kowannenku) Yana da waɗansu mala'iku masu maye wa juna a gaba gare shi da baya gare shi, suna tsare shi daga umurnin Allah. Lalle ne Allah ba Ya canja abin da yake ga, mutane sai sun canja abin da yake ga zukatansu. Kuma idan Allah Ya yi nufin wata azaba game da mutane, to, babu mai mayar da ita, kuma ba su da wani majiɓinci* baicin Shi
Kuma aradu tana tasbihi game da gode Masa, da mala'iku domin tsoronsa. Kuma Yana aiko tsawawwaki, sa'an nan Ya sami wanda Yake so da su alhali kuwa su, suna jayayya a cikin (al'amarin) Allah kuma shi ne mai tsananin hila
Yana da kiran gaskiya, kuma waɗanda (kafirai) suke kira baicinsa, ba su karɓa musu da kome face kamar mai shimfiɗa tafukansa Zuwa ga ruwa (na girgije) domin (ruwan) ya kai ga bakinsa, kuma shi ba mai kaiwa gare shi ba. Kuma kiran kafirai (ga wanin Allah) bai zama* ba face yana a cikin ɓata
Ka ce: "Wane ne Ubangijin sammai da ƙasa?" Ka ce: "Allah". Ka ce: "Ashe fa, kun riƙi waɗansu masoya baicin Shi, waɗanda ba su mallaka wa kansu wani amfani ba kuma haka ba su ture wata cuta?" Ka ce: "Shin makaho da mai gani suna daidaita? Ko shin duhu da haske suna daidaita? ko sun sanya ga Allah waɗansu abokan tarayya waɗanda suka yi halitta kamar halittarSa sa'an nan halittar ta yi kama da juna a gare su?" Ka ce: "Allah ne Mai halitta kome kuma Shi ne Maɗaukaki, Marinjayi
Ya saukar da ruwa daga sama*, sai magudanai suka gudana da gwargwadonsu, Sa'an nan kogi ya ɗauki kumfa mai ƙaruwa, kuma daga abin da suke zuga a kansa (azurfa ko zinari ko ƙarfe) a cikin wuta domin neman ado ko kuwa kayan ɗaki akwai kumfa misalinsa (kumfar ruwa). Kamar wancan ne Allah Yake bayyana gaskiya da ƙarya. To, amma kumfa, sai ya tafi ƙeƙasasshe, kumaamma abin da yake amfanin mutane sai ya zauna a cikin ƙasa. Kamar wancan ne Allah Yake bayyana misalai
Ga waɗanda* suka karɓa wa Ubangijinsu akwai abu mafi kyau a gare su, kuma waɗanda suke ba su karɓa Masa ba, to, lalle da suna da abin da yake a cikin ƙasa gaba ɗaya da misalinsa tare da shi, haƙiƙa, da sun yi fansa da shi. Waɗancan suna da mummunan bincike kuma matabbatarsu Jahannama ce, kuma tir da ita ta zama shimfida
Shin, fa, wanda yake sanin cewa lalle abin da aka saukar zuwa gare ka daga Ubangijinka ne gaskiya yana zama kamar wanda yake makaho? Abin sani kawai masu hankali su ke yin tunani
Kuma su ne waɗan da suke sadar da abin da Allah Ya yi umurni da shi domin a sadar da shi kuma suna tsoron Ubangijinsu, kuma suna tsoron mummunan bincike
Kuma waɗanda suka yi haƙuri domin neman yardar Ubangijinsu, kuma suka tsayar da salla, kuma suka ciyar da abin da Muka azurta su da shi, a asirce da bayyane, kuma suna tunkuɗe mummunan aiki da mai kyau. Waɗancan suna da aƙibar gida mai kyau
Gidajen Aljannar zama suna shigarsu, su da waɗandasuka kyautatu daga iyayensu, da matansu da zuriyarsu. Kuma mala'iku suna shiga zuwa gunsu ta kowace kofa
Kuma waɗanda* suka warware alkawarin Allah daga bayan ƙulla shi, kuma suna yanke abin da Allah Ya yi umurui da shi domin a sadar da shi kuma suna ɓarna a cikin ƙasar. Waɗancan suna da wata la'ana, kuma suna da munin gida
Allah ne Yake* shimfiɗa arziki ga wanda Yake so, kuma Yana ƙuntatawa. Kuma sun yi farin ciki da rayuwar duniya, alhalikuwa rayuwar duniya ba ta zama ba dangane ga ta Lahira face jin daɗi kaɗan
Kuma wanɗanda suka kafirta, suna cewa, "Don me ba a saukar da wata aya ba a kansa daga Ubangijinsa?" Ka ce: "Lalle ne Allah Yana ɓatar da wanda Yake so kuma Yana shiryar da wanda ya tuba zuwa gare shi
Kamar wancan ne Muka aika ka a cikin al'umma wanda take waɗansu al'ummai sun shuɗe daga gabaninta, domin ka karanta musu abin da Muka yi wahayi zuwa a gare ka, alhali kuwa su, sunakafirta da Rahaman.* Ka ce: "Shi ne Ubangijina, babu abin, bautawa face Shi, a gare Shi na dogara, kuma zuwa gare Shi tubata take
Kuma da lalle an saukar da wani littafi abin karatu wanda ake tafiyar da duwatsu game da shi, ko kuma aka yanyanke ƙasa da shi, ko kuwa aka yi magana da matattu da shi (da ba su yi imani ba). A'a ga Allah al'amari yake gaba ɗaya! Shin fa, waɗanda suka yi imani ba su yanke tsammani ba da cewa da Allah Ya so, da Ya shiryar da mutane gaba ɗaya? Kuma waɗanda suka yi kafirci ba za su gushe ba wata masifa tana samun su saboda abin da suka aikata, ko kuwa ka sauka* kusa da gidajensu, har wa'adin Allah ya zo. Kuma lalle ne Allah ba ya saɓa wa lokacin alkawari
Shin fa, wanda shi Yake tsaye a kan kowane rai game da abin da ya tanada (zai zama kamar wanda ba haka ba)? Kuma suka sanya abokan tarayya ga Allah! Ka ce: "Ku ambaci sunayensu."Ko kuna bai wa Allah labari ne game da abin da bai sani ba a cikin ƙasa? Ko da bayyananniyar magana kuke yin shirka, (banda a cikin zuciya)? A'a, an dai ƙawata wa waɗanda suka kafirta makircinsu kuma an kange su daga hanya. Kuma wanda Allah Ya ɓatar to, babu wani mai shiryarwa a gare shi
Misalin Aljanna wadda aka yi alkawarinta ga masu taƙawa, ƙoramu suna gudana daga ƙarƙashinta. Abincinta yana madawwami da inuwarta. Waccan ce aƙibar waɗanda suka yi taƙawa, kuma aƙibar kafirai, ita ce wuta
Kuma waɗanda Muka ba su Littafi suna farin ciki da abin da aka saukar zuwa gare ka, kuma daga ƙungiyoyi akwai mai musun sashensa. Ka ce: "Abin sani kawai, an umurce ni da in bauta wa Allah kuma kada in yi shirka da Shi, zuwa gare Shi nake kira, kuma zuwa gare Shi makomata take
Kuma kamar wancan ne Muka saukar da shi*, Hukunci a cikin Larabci. Kuma lalle ne idan ka bi son zuciyoyinsu a bayan abin da ya zo maka na ilmi, babu wani masoyi a gare ka mai kare ka daga Allah, kuma babu matsari
Kuma lalle ne haƙiƙa Mun aika waɗansu manzanni, daga gabaninka, kuma Muka sanya matan aure a gare su da zuriyya, kuma ba ya kasancewa ga wani Manzo ya zo da wata aya, sai da iznin Allah. Ga kowane ajali* akwai littafi
Kuma imma lalle Mu nuna* maka sashen abin da Muke yi musu wa'adi, ko kuwa lalle Mu karɓi ranka to abin sani kawai iyarwa ce a kanka, kuma hisabi yana gare Mu
Shin, kuma ba su gani ba cewa lalle ne, Muna je wa ƙasar (su), Muna rage ta daga gefunanta? Kuma Allah ne Yake yin hukuncinsa. Babu mai bincike ga hukuncinsa. Kuma shi ne Mai gaggawar sakamako
Kuma lalle ne waɗanda suke a gabaninsu sun yi makirci. To, ga Allah makircin yake gaba ɗaya. Ya san abin da kowane rai yake tanada. Kuma kafirai za su sani, ga wane aƙibar gida take
Kuma waɗanda suka kafirta suna cewa: "Ba a aiko ka ba." Ka ce, "Allah Ya isa zama shaida a tsakanina da tsakaninku da wanda yake a wurinsa akwai ilmin* Littafi