Back to Languages

Hausa - Chapter 14 - Ibrahim

Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink

Verse 1 — Surah Ibrahim 14:1

L.R. Littafi ne mun saukar da shi zuwa gare ka domin ka fitar da mutane daga duhunhuna zuwa ga haske, da iznin Ubangijinsu, zuwa ga tafarkin Mabuwayi, Abin godewa

Verse 2 — Surah Ibrahim 14:2

Allah wanda Yake Yana da abin da ke cikin sammai da cikin ƙasa. Kuma bone ya tabbata ga kafirai daga azaba mai tsanani

Verse 3 — Surah Ibrahim 14:3

Waɗanda suka fi son rayuwar duniya fiye da ta Lahira, kuma suna kangewa daga hanyar Allah, kuma suna neman ta karkace. Waɗancan na a cikin ɓata mai nisa

Verse 4 — Surah Ibrahim 14:4

Kuma ba Mu aika wani Manzo ba face da harshen mutanensa domin ya bayyana musu. Sa'an nan Allah Ya ɓatar da wanda Yake so kuma Ya shiryar da wanda Yake so, Kuma shi ne Mabuwayi, Mai hikima

Verse 5 — Surah Ibrahim 14:5

Kuma lalle ne haƙiƙa Mun aika Musa game, da ayoin Mu cewa, "Ka fitar da mutanenkadaga duhu zuwa ga haske. Kuma ka tunar musu da kwanukan (masifun) Allah." Lalle ne a cikin wancan akwai ayoyi domin dukan mai yawan haƙuri, mai godiya

Verse 6 — Surah Ibrahim 14:6

Kuma a lokacin da Musa yace wa mutanensa, "Ku tuna ni'imar Allah a kanku a lokacin da Ya tsirar da ku daga mutanen Fir'auna, suna yi muku mummunar azaba, kuma suna yanyanka ɗiyanku, kuma suna rayar da matanku. Kuma a cikin wancan akwai jarrabawa mai girma daga Ubangijinku

Verse 7 — Surah Ibrahim 14:7

Kuma a lokacin da Ubangijin ku Ya sanar, "Lalle ne idan kun gode, haƙiƙa, Ina ƙaramuku, kuma lalle ne idan kun kafirta haƙiƙa azabata, tabbas, mai tsanani ce

Verse 8 — Surah Ibrahim 14:8

Kuma Musa ya ce: "Idan kun kafirta ku da waɗanda suke a cikin ƙasa, gaba ɗaya, to, lalle ne Allah haƙiƙa Mawadaci ne, Mai yawan godiya

Verse 9 — Surah Ibrahim 14:9

Shin labarin waɗanda suke a gabaninku, mutanen Nuhu da Adawa da Samudawa bai zomuku ba? Kuma da waɗanda suke daga bayansu babu wanda yake sanin su face Allah? Manzanninsu sun je musu da hujjoji mabayyana, sai suka mayar da hannayensu a cikin bakunansu, kuma suka ce: "Lalle ne mu, mun kafirta da abinda aka aiko ku da shi. Kuma lalle ne mu haƙiƙa muna a cikin shakkada abin do kuke kiran mu zuwa gare shi, mai sanya kokanto

Verse 10 — Surah Ibrahim 14:10

Manzannin su suka ce "Ashe, akwai shakka a cikin (sha'anin) Allah, Mai ƙaga halittar sammai da ƙasa Yana kiran ku domin Ya gafarta muku zunubanku, kuma Ya jinkirta muku zuwa ga ajali ambatacce?" Suka ce: "Ba ku zama ba face mutane misalinmu kuma nufinku ku kange mu daga abin da iyayenmu suka kasance suna bautawa sai ku zo mana da dalili mabayyani

Verse 11 — Surah Ibrahim 14:11

Manzanninsu suka ce musu, "Ba mu zama ba face mutane misa, linku, kuma amma Allah Yana yin falala a kan wanda Yake so daga bayinsa, kuma ba ya kasancewa a gare mu, mu zo muku da wani dalili face da iznin Allah. Kuma ga Allah sai muminai su dogara

Verse 12 — Surah Ibrahim 14:12

Kuma mene ne a gare mu, ba za mu dogara ga Allah ba, alhali kuwa haƙiƙa Ya shiryar da mu ga hanyoyinmu? Kuma lalle ne muna yin haƙuri a kan abin da kuka cutar da mu, kuma ga Allah sai masu dogaro su dogara

Verse 13 — Surah Ibrahim 14:13

Kuma waɗanda suka kafirta suka ce wa Manzanninsu, "Lalle ne muna fitar da ku daga ƙasarmu, ko kuwa haƙiƙa, kuna komowa acikin addininmu." Sai Ubangijinsu Ya yi wahayi zuwa gare su, "Lalle ne, Muna halakar da Azzalumai

Verse 14 — Surah Ibrahim 14:14

Kuma haƙiƙa, Muna zaunar da ku ga ƙasa a bayansu. Wancan ne abin gargaɗi ga wanda ya ji tsoron matsayiNa, kuma ya ji tsoron ƙyacewaTa

Verse 15 — Surah Ibrahim 14:15

Kuma suka yi addu'ar alfanu*. Kuma kowane kangararre mai tsaurin kai ya taɓe

Verse 16 — Surah Ibrahim 14:16

Daga bayansa akwai Jahannama, kuma ana shayar da shi daga wani ruwa, surkin jini

Verse 17 — Surah Ibrahim 14:17

Yana kwankwaɗarsa, kuma ba ya jin sauƙin haɗiyarsa, kuma mutuwa ta je masa daga kowane wuri kuma bai zama mai mutuwa ba, kuma daga bayansa akwai azaba mai kauri

Verse 18 — Surah Ibrahim 14:18

Misalin waɗanda suka kafirta da Ubangijinsu, ayyukansu sun yi kama da toka wadda iska ta yi tsananin bugawa da ita a cikin yini mai guguwa. Ba su iya amfani daga abin da suka yi tsirfa a kan kome. Wancan ita ce ɓata mai nisa

Verse 19 — Surah Ibrahim 14:19

Shin, ba ka gani ba cewa lalle ne Allah Ya halicci sammai bakwai da ƙasa da mallakarSa.* Idan Ya so zai tafiyar da ku, kuma Ya zo da wata halitta sabuwa

Verse 20 — Surah Ibrahim 14:20

Kuma wancan bai zama mabuwayi ba ga Allah

Verse 21 — Surah Ibrahim 14:21

Kuma suka bayyana ga Allah gaba daya, sai masu rauni suka ce wa waɗanda suka kangara, "Lalle ne mu, mun kasance masu bi a gare ku, to, shin, ku masu karewa ga barinmu ne daga azabar Allah daga wani abu?*" Suka ce: "Da Allah Ya shiryar da mu, da mun shiryar da ku, daidai ne a kanmu, mun yi raki ko mun yi haƙuri ba mu da wata mafaka

Verse 22 — Surah Ibrahim 14:22

Kuma Shaiɗan ya ce a lokacin da aka ƙare al'amarin, "Lalle ne Allah Ya yi muku wa'adi, wa'adin gaskiya, kuma na yi muku wa'adi, sa'an nan na saɓa muku. Kuma babu wani dalili a gare ni a kanku face na kira ku, sa'an nan kun karɓa mini. Saboda haka kada ku zarge ni, kuma ku zargi kanku. Ban zama mai amfaninku ba, kuma ba ku zama masu amfanina ba. Lalle na barranta da abin da kuka haɗa ni da shi gabanin wannan (matsayi). Lalle azzalumai suna da azaba mai raɗaɗi

Verse 23 — Surah Ibrahim 14:23

Kuma aka shigar da waɗanda suka yi imani, kuma suka aikata ayyuka na ƙwarai, a gidajen Aljanna, koramu suna gudana daga ƙarƙashinsu suna madawwama a cikinsu da iznin Ubangijinsu, gaisuwarsu a cikinta "Salam", (watau Aminci)

Verse 24 — Surah Ibrahim 14:24

Shin, ba ka gani ba, yadda Allah Ya buga wani misali, kalma mai kyau* kamar itaciya ce mai kyau, asalinta yana tabbatacce, kuma reshenta yana cikin sama

Verse 25 — Surah Ibrahim 14:25

Tana bayar da abincinta a kowane lokaci da iznin Ubangijinta! Kuma Allah Yana buga misali ga mutane, mai yiwuwa ne, suna tunawa

Verse 26 — Surah Ibrahim 14:26

Kuma misalin kalma mummuna* kamar itaciya mummuna ce, an tumɓuke ta daga bisa ga ƙasa, ba ta da wata tabbata

Verse 27 — Surah Ibrahim 14:27

Allah Yana tabbatar da waɗanda suka yi imani da magana tabbatacciya a cikin rayuwar duniya, da cikin Lahira, Kuma Allah Yana ɓatar da azzalumai, kuma Allah Yana aikata abin da Yake so

Verse 28 — Surah Ibrahim 14:28

Shin ba ka lura ba da waɗanda suka musanya* ni'imar Allah da kafirci kuma suka saukar da mutanensu a gidan halaka

Verse 29 — Surah Ibrahim 14:29

Suna ƙonuwa a wutar jahannama, kuma tir da matabbatar su

Verse 30 — Surah Ibrahim 14:30

Kuma suka sanya wa Allah kishiyoyi, domin ɓatarwa daga hanyarSa, Ka ce: "Ku ji daɗi, sa'an nan, lalle ne, makomarku Wutar ce

Verse 31 — Surah Ibrahim 14:31

Ka ce wa bayiNa waɗanda suka yi imani su tsayar da salla kuma su ciyar daga abin da Muka azurta su, a asirce da bayyane, daga gabanin wani wuni ya zo, babu ciniki a ciki, kuma babu abotaka

Verse 32 — Surah Ibrahim 14:32

Allah ne wanda Ya halicci sammai da ƙasa kuma Ya saukar da ruwa daga sama, sa'an nan Ya fitar game da shi, daga 'ya'yan itace arziki dominku kuma Ya hore jirgin ruwa domin ya yi gudu a cikin teku da umurninSa, kuma Ya hore muku koguna

Verse 33 — Surah Ibrahim 14:33

Kuma Ya hore muku rana da wata suna madawwama biyu, kuma Ya hore muku dare da wuni

Verse 34 — Surah Ibrahim 14:34

Kuma Ya ba ku dukkan abin da kuka roƙe Shi kuma idan kun ƙidaya, ni'imar Allah ba za ku lissafe ta ba. Lalle ne mutum, haƙiƙa, mai yawan zalunci ne, mai yawan kafirci

Verse 35 — Surah Ibrahim 14:35

Kuma a lokacin da Ibrahim ya ce: "Ya Ubangijina! Ka sanya wannan gari* amintacce kuma Ka nisanta ni, ni da ɗiyana daga bauta wa gumaka

Verse 36 — Surah Ibrahim 14:36

Ya Ubangijina! Lalle ne su, sun ɓatar da masu yawa daga mutane sa'an nan wanda ya bi ni, to, lalle shi, yana daga gare ni, kuma wanda ya saɓa mini, to, lalle ne Kai Mai gafara ne, Mai jin ƙai

Verse 37 — Surah Ibrahim 14:37

Ya Ubangijinmu! Lalle ne ni, na zaunar da zuriyata ga rafi wanda ba ma'abucin shuka ba, a wurin ¦akinka mai alfarma. Ya Ubangijinmu! Domin su tsayar da salla. Sai Ka sanya zukata daga mutane suna gaggawar begenzuwa gare su, kuma ka azurta su daga 'ya'yan itace, mai yiwuwa ne suna godewa

Verse 38 — Surah Ibrahim 14:38

Ya Ubangijinmu! Lalle ne Kai Kana sanin abin da muke ɓoyewa, da abin da muke bayyanawa. Kuma babu abin da yake ɓoyewa ga Alah, daga wani abu a cikin ƙasa, kuma babu a cikin sama

Verse 39 — Surah Ibrahim 14:39

Godiya ta tabbata ga Allah wanda Yake Ya ba ni ina a cikin tsufa Isma'ila da Is'haƙa. Lalle ne Ubangijina, haƙiƙa, Mai jin addu'a ne

Verse 40 — Surah Ibrahim 14:40

Ya Ubangijina! Ka sanya ni mai tsayar da salla. Kuma daga zuriyyata. Ya Ubangijinmu! Kuma Ka karɓi addu'ata

Verse 41 — Surah Ibrahim 14:41

Ya Ubangijinmu! Ka yi gafara gare ni, kuma ga mahaifana, kuma da muminai, a ranar da hisabi yake tsayawa

Verse 42 — Surah Ibrahim 14:42

Kuma kada ka yi zaton Allah Mai shagala ne daga abin da azzalumai suke aikatawa. Abin sani kawai, Yana jinkirta musu ne zuwa ga wani wuni, wanda idanuwa suke fita turu- turu a cikinsa

Verse 43 — Surah Ibrahim 14:43

Suna masu gaggawa, masu ɗaukaka kawunansu zuwa sama ƙiftawar ganinsu ba ta komawa gare su. Kuma zukatansu wofintattu

Verse 44 — Surah Ibrahim 14:44

Kuma ka yi gargaɗi ga mutane ga ranar da azaba take je musu, sai waɗanda suka yi zalunci su ce: "Ya Ubangijinmu! Ka yi mana jinkiri zuwa ga wani ajali makusanci, mu karɓa wa kiranKa, kuma mu bi Manzanni."(Allah Ya ce musu) "Ashe, ba ku kasance kun yi rantsuwa ba daga gabani, cewa ba ku da wata gushewa

Verse 45 — Surah Ibrahim 14:45

Kuma kuka zauna a cikin gidajen waɗanda suka zalunci kansu, kuma ya bayyana a gare ku yadda Muka aikata game da su, kuma Muka buga muku misalai

Verse 46 — Surah Ibrahim 14:46

Kuma lalle sun yi makirci irin makircinSu kuma a wurin Allah makircinsu, yake, kuma lalle ne makircinsu ya kasance, haƙiƙa, duwatsu suna gushewa saboda shi

Verse 47 — Surah Ibrahim 14:47

Saboda haka, kada ka ƙarfafa zaton Allah Mai saɓa wa'adinSa ne ga ManzanninSa. Lalle ne Allah ne Mabuwayi, Ma'abucin azabar ramuwa

Verse 48 — Surah Ibrahim 14:48

A ranar da ake musanya ƙasa* ba ƙasar nan ba, da sammai kuma su bayyana ga Allah Makaɗaici, Mai tanƙwasawa

Verse 49 — Surah Ibrahim 14:49

Kuma kana ganin masu laifi, a ranar nan, suna waɗanda aka yi wa ciri daidai a cikin maruruwa

Verse 50 — Surah Ibrahim 14:50

Rigunansu daga farar wuta ne, kuma wuta ta rufe fuskokinsu

Verse 51 — Surah Ibrahim 14:51

Domin Allah Ya saka wa kowane rai da abin da ya tsuwurwurta. Lalle ne, Allah Mai gaggawar hisabi ne

Verse 52 — Surah Ibrahim 14:52

Wannan iyarwa ce ga mutane, kuma domin a yi musu gargaɗi da shi, kuma domin su sani cewa, abin sani kawai, shi ne abin bautawa guda. Kuma domin masu hankali su riƙa tunawa