Back to LanguagesPrevious ChapterNext Chapter
Hausa - Chapter 15 - Al-Hijr
Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink
Verse 1 — Surah Al-Hijr 15:1
L.R. Waɗan can ayoyin littafi ne da abin karantawa mai bayyanawa
Verse 2 — Surah Al-Hijr 15:2
Da yawa waɗanda suka kafirta suke gurin da dai sun kasance Musulmi
Verse 3 — Surah Al-Hijr 15:3
Ka bar su su ci kuma su ji dadi, kuma guri ya shagaltar da su, sa'an nan da sannu za su sani
Verse 4 — Surah Al-Hijr 15:4
Kuma ba Mu halakar da wata alƙarya ba face tana da littafi sananne
Verse 5 — Surah Al-Hijr 15:5
Wata al'umma ba ta gabatar ajalinta, kuma ba za su jinkirta ba
Verse 6 — Surah Al-Hijr 15:6
Suka ce: "Ya kai wanda aka saukar da Ambato (Alƙur'ani) a kansa! Lalle ne kai, haƙiƙa, mahaukaci ne
Verse 7 — Surah Al-Hijr 15:7
Domin me ba za ka zo mana da mala'iku ba idan ka kasance daga masu gaskiya
Verse 8 — Surah Al-Hijr 15:8
Ba Mu sassaukar da mala'iku face da gaskiya,* ba za su kasance, a wannan lokacin, waɗanda ake yi wa jinkiri ba
Verse 9 — Surah Al-Hijr 15:9
Lalle Mu ne, Muka saukar da Ambato (Alƙur'ani), kuma lale Mu, haƙiƙa, Masu kiyayewane gare shi
Verse 10 — Surah Al-Hijr 15:10
Kuma lalle ne, haƙiƙa, Mun aika Manzanni a cikin ƙungiyoyin farko, gabanin ka
Verse 11 — Surah Al-Hijr 15:11
Kuma wani Manzo ba ya zuwa gare su face sun kasance suna masu, izgili a gare shi
Verse 12 — Surah Al-Hijr 15:12
Kamar wancan ne Muke shigar da shi* a cikin zukatan masu laifi
Verse 13 — Surah Al-Hijr 15:13
Ba su yin imani da shi,(4( kuma haƙiƙa, hanyar mutanen farko ta shige)
Verse 14 — Surah Al-Hijr 15:14
Kuma da Mun buɗe wata ƙofa daga sama a kansu har suka wuni a ciki suna takawa
Verse 15 — Surah Al-Hijr 15:15
Lalle ne da sun ce: "Abin sani kawai, an rufe idanuwanmu ne. A'a, mu mutane ne waɗanda aka sihirce
Verse 16 — Surah Al-Hijr 15:16
Kuma lalle ne, haƙiƙa Mun sanya waɗansu masaukai a, cikin sama, kuma Muka ƙawata ta ga masu kallo
Verse 17 — Surah Al-Hijr 15:17
Kuma Muka kiyaye ta daga dukan Shaiɗani wanda ake jifa
Verse 18 — Surah Al-Hijr 15:18
Face wanda ya saci saurare sai wutar yula bayyananniya ta bi shi
Verse 19 — Surah Al-Hijr 15:19
Kuma ƙasa Mun mike ta kuma Mun jefa duwatsu tabbatattu a cikinta kuma Mun tsirar a cikinta, daga dukan abu wanda ake aunawa da sikeli
Verse 20 — Surah Al-Hijr 15:20
Kuma Muka sanya muku, a cikinta, abubuwan rayuwa* da wanda ba ku zama masu ciyarwa gare shi ba
Verse 21 — Surah Al-Hijr 15:21
Kuma babu wani abu face a wurinMu, akwai taskokinsa kuma ba Mu saukar da shi ba face kan gwargwado sananne
Verse 22 — Surah Al-Hijr 15:22
Kuma Muka aika iskoki masu barbarar juna sa'an nan Muka saukar da ruwa daga sama, sa'an nan Muka shayar da ku shi, kuma ba ku zama masu taskacewa a gare shi ba
Verse 23 — Surah Al-Hijr 15:23
Kuma lalle ne Mu Muke rayarwa, kuma Muke kashewa kuma Mu ne magada
Verse 24 — Surah Al-Hijr 15:24
Kuma lalle ne, haƙiƙa, Mun san masu gabata daga cikinku, kuma Mun san masu jinkiri
Verse 25 — Surah Al-Hijr 15:25
Kuma lalle ne Ubangijinka Shi ne Yake tara su, lalle Shi ne Mai hikima, Masani
Verse 26 — Surah Al-Hijr 15:26
Kuma lalle ne Mun halicci mutum daga ƙeƙasasshiyar laka, daga baƙin yumɓu wanda ya canja
Verse 27 — Surah Al-Hijr 15:27
Kuma Aljani Mun halicce shi daga gabani, daga wutar* iskar zafi
Verse 28 — Surah Al-Hijr 15:28
Kuma a lokacin da Ubangijinka ya ce wa mala'iku: "Lalle Ni mai halittar wani jiki ne daga ƙeƙasasshen yumɓu wanda ya canja
Verse 29 — Surah Al-Hijr 15:29
To idan Na daidaita shi kuma Na hura daga RuhiNa* a cikinsa, to, ku faɗi a gare shi, kuna masu yin sujada
Verse 30 — Surah Al-Hijr 15:30
Sai mala'iku suka yi sujada dukkansu gaba ɗaya
Verse 31 — Surah Al-Hijr 15:31
Face Iblis, ya ƙi kasancewa daga masu yin sujadar
Verse 32 — Surah Al-Hijr 15:32
Ya ce: "Ya Iblis mene ne a gare ka, ba ka kasance tare da masu yin sujuda ba
Verse 33 — Surah Al-Hijr 15:33
Ya ce: "Ban kasance ina yin sujada ba ga mutum wanda Ka halicce shi daga busasshen yumɓun laka wadda ta canja
Verse 34 — Surah Al-Hijr 15:34
Ya ce: "To, ka fita daga gare ta, domin lalle kai abin jifa ne
Verse 35 — Surah Al-Hijr 15:35
Kuma lalle ne akwai la'ana a kanka har ya zuwa ranar sakamako
Verse 36 — Surah Al-Hijr 15:36
Ya ce: "Ya Ubangjina! Sai Ka yi mini jinkiri zuwa ranar da ake tashin su
Verse 37 — Surah Al-Hijr 15:37
Ya ce: "To, lalle ne kana daga waɗanda ake yi wa jinkiri
Verse 38 — Surah Al-Hijr 15:38
Zuwa ga Yinin Lokacin nan sanan ne
Verse 39 — Surah Al-Hijr 15:39
Ya ce: "Ya Ubangijina! Ina rantsuwa da abin da Ka ɓatar da ni da shi, haƙiƙa ina ƙawata musu (rayuwa) a cikin ƙasa kuma haƙiƙa ina ɓatar da su gaba ɗaya
Verse 40 — Surah Al-Hijr 15:40
Face bayinKa daga gare su, waɗanda Ka tsarkake
Verse 41 — Surah Al-Hijr 15:41
Ya ce: "Wannan tafarki ne a gare Ni, madaidaici
Verse 42 — Surah Al-Hijr 15:42
Lalle ne bayiNa, ba ka da iko a kansu, face wanda ya bi ka daga ɓatattu
Verse 43 — Surah Al-Hijr 15:43
Kuma lalle Jahannama ce haƙiƙa, ma'akawartarsu gaba ɗaya
Verse 44 — Surah Al-Hijr 15:44
Tana da ƙofofi bakwai,* ga kowace ƙofa akwai wani juz'i daga gare su rababbe
Verse 45 — Surah Al-Hijr 15:45
Lalle masu taƙawa suna a cikin gidajen Aljanna mai idandunan ruwa
Verse 46 — Surah Al-Hijr 15:46
Ku shige ta da aminci, kuna amintattu
Verse 47 — Surah Al-Hijr 15:47
Kuma Muka ɗebe abinda ke a cikin zukatansu na daga ƙullin zuci, suka zama 'yan'uwa a kan gadaje, suna masu fuskantar juna
Verse 48 — Surah Al-Hijr 15:48
Wata wahala ba za ta shafe su ba a cikinta kuma ba su zama masu fita daga, cikin ta ba
Verse 49 — Surah Al-Hijr 15:49
Ka bai wa bayiNa labari cewa lalle ne Ni, Mai gafarane, Mai jin ƙai
Verse 50 — Surah Al-Hijr 15:50
Kuma azabaTa ita ce Azaba mai raɗaɗi
Verse 51 — Surah Al-Hijr 15:51
Kuma ka ba su labarin baƙin Ibrahim
Verse 52 — Surah Al-Hijr 15:52
A lokacin da suka shiga gunsa, sai suka ce: "Sallama." Ya ce: "Lalle mu, daga gare ku, masu firgita ne
Verse 53 — Surah Al-Hijr 15:53
Suka ce: "Kada ka firgita. Lalle ne mu, muna yi makabushara game da wani yaro masani
Verse 54 — Surah Al-Hijr 15:54
Ya ce: "Shin kun ba ni bushara* ne a kan tsufa ya shafe ni? To, da me kuke ba ni bushara
Verse 55 — Surah Al-Hijr 15:55
Suka ce: "Muna yi maka bushara da gaskiya ne, saboda haka, kada da kasance daga masu yanke tsammani
Verse 56 — Surah Al-Hijr 15:56
Ya ce: "Kuma wane ne yake yanke tsammani daga rahamar Ubangijin sa, face ɓatattu
Verse 57 — Surah Al-Hijr 15:57
Ya ce: "To, mene ne babban al'amarinku? Ya ku manzanni
Verse 58 — Surah Al-Hijr 15:58
Suka ce: "Lalle ne mu, an aika mu zuwa ga wasu mutane masu laifi
Verse 59 — Surah Al-Hijr 15:59
Face mutanen Luɗu, lalle ne mu, haƙiƙa, masu tsirar dasu ne gaba ɗaya
Verse 60 — Surah Al-Hijr 15:60
Face matarsa mun ƙaddara cewa lalle ne ita, haƙiƙa, tana daga masu halaka
Verse 61 — Surah Al-Hijr 15:61
To, a lokacin da mazannin suka je wa mutanen Luɗu
Verse 62 — Surah Al-Hijr 15:62
Ya ce: "Lalle ne ku mutane ne waɗanda ba a sani ba
Verse 63 — Surah Al-Hijr 15:63
Suka ce: "A'a, mun zo maka saboda abin da suka kasance suna shakka a cikinsa
Verse 64 — Surah Al-Hijr 15:64
Kuma mun zo maka da gaskiya. Kuma lalle ne mu, haƙiƙa, masu gaskiya ne
Verse 65 — Surah Al-Hijr 15:65
Sai ka yi tafiya da iyalinka, a wani yanki na dare, kuma ka bi bayansu, kuma kada wani daga cikinku ya yi waiwaye, kuma ku bi ta inda aka aumurce ku
Verse 66 — Surah Al-Hijr 15:66
Kuma Muka hukunta wancan al'amarin zuwa gare shi cewa lalle ne ƙarshen waɗancan abin yankewa ne a lokacin da suke masu shiga Asuba
Verse 67 — Surah Al-Hijr 15:67
Kuma mutanen alƙaryar suka je suna masu bushara
Verse 68 — Surah Al-Hijr 15:68
Ya ce: "Lalle ne waɗannan baƙina ne, saboda haka kada ku kunyata ni
Verse 69 — Surah Al-Hijr 15:69
Kuma ku bi Allah da taƙawa, kuma kada ku sanya ni a baƙin ciki
Verse 70 — Surah Al-Hijr 15:70
Suka ce: "Ashe ba mu hana ka daga talikai ba
Verse 71 — Surah Al-Hijr 15:71
Ya ce: "Ga waɗannan, 'ya'yana* idan kun kasance masu aikatawa ne
Verse 72 — Surah Al-Hijr 15:72
Rantsuwa da* rayuwarka! Lalle ne su a cikin mayensu suna ta ɗimuwa
Verse 73 — Surah Al-Hijr 15:73
Sa'an nan tsawa ta kama su, suna masu shiga lokacin hudowar rana
Verse 74 — Surah Al-Hijr 15:74
Sa'an nan Muka sanya samanta ya koma ƙasanta, kuma Muka yi ruwan duwatsu na lakar wuta a kansu
Verse 75 — Surah Al-Hijr 15:75
Lalle ne a cikin wancan akwai ayoyi ga masu tsokaci da hankali
Verse 76 — Surah Al-Hijr 15:76
Kuma lalle ne ita, haƙiƙa suna a gefen wata hanya tabbatacciya
Verse 77 — Surah Al-Hijr 15:77
Lalle ne a cikin wancan akwai aya ga masu imani
Verse 78 — Surah Al-Hijr 15:78
Kuma lalle ne ma'abuta Al'aika* sun kasance, haƙiƙa, masu zalunci
Verse 79 — Surah Al-Hijr 15:79
Sai Muka yi azabar ramuwa a gare su, kuma lalle su biyun, haƙiƙa, suna a gefen wani tafarki mabayyani
Verse 80 — Surah Al-Hijr 15:80
Kuma lalle ne haƙiƙa ma'abuta Hijiri* sun ƙaryata Manzanni
Verse 81 — Surah Al-Hijr 15:81
Kuma Kuka kai musu ayoyinMu, sai suka kasance masu bijirewa daga gare su
Verse 82 — Surah Al-Hijr 15:82
Kuma sun kasance suna sassaƙa gidaje daga duwatsu, alhali suna amintattu
Verse 83 — Surah Al-Hijr 15:83
Sai tsawa ta kama su suna masu shiga Asuba
Verse 84 — Surah Al-Hijr 15:84
Sa'an nan abin da suka kasance suna tsirfantawa bai wadatar ga barinsu ba
Verse 85 — Surah Al-Hijr 15:85
Kuma ba Mu halicci sammai da ƙasa da abin da yake a tsakaninsu ba face da gaskiya. Kuma lalle ne Sa'a (Ranar Alƙiyama) haƙiƙa mai zuwa ce. Sabodahaka ka yi rangwame, rangwame mai kyau
Verse 86 — Surah Al-Hijr 15:86
Lalle ne Ubangijinka, shi ne Mai yawan halitta, Masani
Verse 87 — Surah Al-Hijr 15:87
Kuma lalle ne, haƙiƙa, Mun ba ka bakwai waɗan da ake maimaita karatunsu* da Alƙur'ani mai girma
Verse 88 — Surah Al-Hijr 15:88
Kada lalle kaƙiƙa idanunka biyu zuwa ga abin da Muka jiyar da su daɗi game da shi, nau'i-nau'i a gare su, kuma kada ka yi baƙin ciki a kansu, kuma sassauta fikafikanka ga masu imani
Verse 89 — Surah Al-Hijr 15:89
Kuma ka ce: "Lalle ni ni ne mai gargaɗi bayyanan ne
Verse 90 — Surah Al-Hijr 15:90
Kamar yadda Muka saukar a kan masu yin rantsuwa
Verse 91 — Surah Al-Hijr 15:91
Waɗanda suka sanya Alƙur'ani tatsuniyoyi
Verse 92 — Surah Al-Hijr 15:92
To, rantsuwa da Ubangijinka!* Haƙiƙa, Muna tambayarsugaba ɗaya
Verse 93 — Surah Al-Hijr 15:93
Daga abin da suka kasance suna aikatawa
Verse 94 — Surah Al-Hijr 15:94
Sai ka tsage gaskiya game da abin da ake umurnin ka kuma ka kau da kai daga masu shirki
Verse 95 — Surah Al-Hijr 15:95
Lalle ne Mu Mun isar maka daga masu* izgili
Verse 96 — Surah Al-Hijr 15:96
Waɗanda suke sanyawar wani abin bautawa na dabam tare da Allah, sa'an nan da sannu za su sani
Verse 97 — Surah Al-Hijr 15:97
Kuma lalle ne haƙiƙa Muna sanin cewa lalle kai, ƙirjinka yana yin ƙunci game da abin da suke faɗa (na izgili)
Verse 98 — Surah Al-Hijr 15:98
Saboda haka ka yi tasbihi game da gode wa Ubangijinka, kuma ka kasance daga masu sujada
Verse 99 — Surah Al-Hijr 15:99
Kuma ka bauta wa Ubangijinka, har mutuwa ta zo maka