Back to Languages

Hausa - Chapter 16 - An-Nahl

Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink

Verse 1 — Surah An-Nahl 16:1

Al'amarin Allah ya zo, saboda haka kada ku nemi hanzartawarsa. Tsarkin Allah ya tabbata, kuma Ya ɗaukaka daga abin da suke yi na shirka

Verse 2 — Surah An-Nahl 16:2

Yana sassaukar da mala'iku da Ruhi* daga umurninSaa kan wanda Yake so daga bayinSa, cewa ku yi gargaɗi cewa: Lalle ne shi, babu abin bautawa face Ni, saboda haka ku bi Ni da taƙawa

Verse 3 — Surah An-Nahl 16:3

Ya halicci sammai da ƙasa da gaskiya. Ya ɗaukaka daga abin da suke yi na shirka

Verse 4 — Surah An-Nahl 16:4

Ya halicci mutum daga maniyyi, sai ga shi yana mai husuma bayyananniya

Verse 5 — Surah An-Nahl 16:5

Da dabbobin ni'ima, Ya halicce su dominku. A cikinsu akwai abin yin ɗumi da waɗansu amfanoni, kuma daga gare su kuke ci

Verse 6 — Surah An-Nahl 16:6

Kuma kuna da kyau a cikinsu a lokacin da suke komowa daga kiwo da maraice da lokacin da suke sakuwa

Verse 7 — Surah An-Nahl 16:7

Kuma suna ɗaukar kayanku masu nauyi zuwa ga wani gari, ba ku kasance masu isa gare shi ba, face da tsananin wahalar rayuka, Lalle ne Ubangijinka ne, haƙiƙa, Mai tausayi, Maijin ƙai

Verse 8 — Surah An-Nahl 16:8

Kuma da dawaki* da alfadarai da jakuna, domin ku hau su, kuma da ƙawa. Kuma Yana halitta abin da ba ku sani ba

Verse 9 — Surah An-Nahl 16:9

Kuma ga Allah madaidaiciyar hanya take kuma daga gare ta akwai mai karkacewa. Kuma da Ya so, da Ya shiryar da ku gaba ɗaya

Verse 10 — Surah An-Nahl 16:10

Shi ne Wanda Ya saukar da ruwa daga sama dominku, daga gare shi akwai abin sha, kuma daga gare shi itace yake, a cikinsa kuke yin kiwo

Verse 11 — Surah An-Nahl 16:11

Yana tsirar da shuka game da shi, dominku zaituni da dabinai da inabai, kuma daga dukan 'ya'yan itace. Lalle ne a cikin wancan haƙiƙa, akwai aya ga mutane waɗanda suke yin tunani

Verse 12 — Surah An-Nahl 16:12

Kuma Ya hore muku dare da wuni da rana da wata kuma taurari horarru ne da umurninSa. Lalle ne a cikin wancan, haƙiƙa, akwai ayoyi ga mutane waɗanda suke hankalta

Verse 13 — Surah An-Nahl 16:13

Kuma abin da Ya halitta muku a cikin ƙasa, yana mai saɓanin launukansa. Lalle ne a cikin wancan, haƙiƙa, akwai aya ga mutane waɗanda suke tunawa

Verse 14 — Surah An-Nahl 16:14

Kuma Shi ne Ya hore teku domin ku ci wani nama sabo daga gare shi, kuma kuna fitarwa, daga gare shi, ƙawa wadda kuke yin ado da ita. Kuma kuna ganin jirage suna yankan ruwa a cikinsa kuma domin ku yi neman (fatauci) daga falalarSa. Kuma mai yiwuwa ne kuna godewa

Verse 15 — Surah An-Nahl 16:15

Kuma Ya jefa, a cikin ƙasa, tabbatattun duwatsu domin kada ta karkata da ku, da koguna da hanyoyi, ɗammanin ku kuna shiryuwa

Verse 16 — Surah An-Nahl 16:16

Kuma da waɗan su alamomi, kuma da taurari suna masu neman shiryuwa (ga tafiyarsu ta fatauci)

Verse 17 — Surah An-Nahl 16:17

Shin, wanda Yake yin halitta yana yin kama da wanda ba ya yin halitta? Shin fa, ba ku tunawa

Verse 18 — Surah An-Nahl 16:18

Kuma idan kun ƙidaya ni'imar Allah, ba ku iya lissafa ta. Lalle ne Allah, haƙiƙa, Mai gafara ne, Mai jin ƙai

Verse 19 — Surah An-Nahl 16:19

Kuma Allah Yana sanin abin da kuke asirtawa da abin da kuke bayyanawa

Verse 20 — Surah An-Nahl 16:20

Kuma waɗanda suke kira, baicin Allah, ba su halicci kome ba, kuma su ne ake halittawa

Verse 21 — Surah An-Nahl 16:21

Matattu ne, ba su da rai, kuma ba su san a wane lokaci ake tayar da su ba

Verse 22 — Surah An-Nahl 16:22

Abin bautawarku, abin bautawa ne guda, to, waɗanda ba su yin imani da Lahira, zukatansu masu musu ne, kuma su makangara ne

Verse 23 — Surah An-Nahl 16:23

Haƙiƙa, lalle ne, Allah Yana sanin abin da suke asirtawa da abin da suke bayyanawa. Lalle ne Shi, ba Ya Son masu girman kai

Verse 24 — Surah An-Nahl 16:24

Idan aka ce musu: "Mene ne Ubangijinku Ya saukar?" Sai su ce: "Tatsuniyoyin mutanen farko

Verse 25 — Surah An-Nahl 16:25

Domin su ɗauki zunubansu cikakku a Ranar ¡iyama, kuma daga zunuban waɗanda suke ɓatarwa ba da wani ilmi ba. To, abin da suke ɗauka na zunubi ya munana

Verse 26 — Surah An-Nahl 16:26

Lalle ne waɗanda suke a gabaninsu sun yi makirci, sai Allah Ya je wa gininsu daga harsashensa,* sai rufi ya faɗa a kansu daga bisansu, kuma azaba ta je musu daga inda ba su sani ba

Verse 27 — Surah An-Nahl 16:27

Sa'an nan a Ranar ¡iyama (Allah) Yana kunyata su, kuma Yana cewa: "Ina abokan tarayyaTa, waɗanda kuka kasance kuna gaba a cikin ɗaukaka sha'aninsu?" Waɗanda aka bai wa ilmi suka ce: "Lalle ne wulakanci a yau da cuta sun tabbata a kan kafirai

Verse 28 — Surah An-Nahl 16:28

Waɗanda malaiku suke karɓar rayukansu suna masu zaluntar kansu. Sai suka jefa neman sulhu (suka ce) "Ba mu kasance muna aikata wani mummunan aiki ba." Kayya! Lalle Allah ne Masani ga abin da kuka kasance kuna aikatawa

Verse 29 — Surah An-Nahl 16:29

Sai ku shiga ƙofofin Jahannama, kuna madawwama a cikinta. Sa'an nan tir da mazaunin masu girman kai

Verse 30 — Surah An-Nahl 16:30

Kuma aka ce wa waɗanda suka yi taƙawa, "Mene ne Ubangijinku Ya saukar?" Suka ce, "Alheri Ya saukar, ga waɗanda suka kyautata a cikin wannan duniya akwai wani abu mai kyau, kuma haƙiƙa, Lahira ce mafi alheri." Kuma haƙiƙa, madalla da gidan masu taƙawa

Verse 31 — Surah An-Nahl 16:31

Gidajen Aljannar zama suna shigarsu, ƙoramu suna gudana daga ƙarƙashinsu, suna da abin da suke so a cikinsu. Kamar haka Allah ke saka wa masu taƙawa

Verse 32 — Surah An-Nahl 16:32

Waɗanda mala'iku suke karɓar rayukansu suna masu jin daɗin rai, mala'ikun suna cewa. "Aminci ya tabbata a kanku. Ku shiga Aljanna saboda abin da kuka kasance kuna aikatawa

Verse 33 — Surah An-Nahl 16:33

Shin suna jiran wani abu? Face mala'iku su je musu ko kuwa umurnin Ubangijinka. Kamar wancan ne waɗanda suke a gabaninsu, suka aikata. Kuma Allah bai zalunce su ba, kuma amma kansu suka kasance suna zalunta

Verse 34 — Surah An-Nahl 16:34

Sai munanan abubuwan da suka aikata ya same su, kuma abin da suka kasance suna yi na izgili ya wajaba a kansu

Verse 35 — Surah An-Nahl 16:35

Kuma waɗanda suka yi shirki suka ce: "Da Allah Ya so, da bamu bauta wa kome ba, baicinSa, mu ko ubannimmu kuma da ba mu haramta kome ba, baicin abin da Ya haramta." Kamar wancan ne waɗanda suke a gabaninsu suka aikata. To, shin, akwai wani abu a kan Manzanni, face iyarwa bayyananniya

Verse 36 — Surah An-Nahl 16:36

Kuma lalle ne, haƙiƙa, Mun aika a cikin kowace al'umma da wani Manzo (ya ce): "Ku bauta wa Allah, kuma ku nisanci ¦agutu." To, daga gare su akwai wanda Allah Ya shiryar, kuma daga cikinsu akwai wanda ɓata ta wajaba a kansa. Sai ku yi tafiya a cikin ƙasa, sa'an nan ku duba yadda aƙibar masu ƙaryatawa ta kasance

Verse 37 — Surah An-Nahl 16:37

Idan ka yi kwaɗayi a kan shiryuwarsu, to, lalle ne, Allah ba Ya shiryar da wanda yake ɓatarwa, kuma ba su da waɗansu mataimaka

Verse 38 — Surah An-Nahl 16:38

Kuma suka rantse da Allah iyakar rantsuwarsu (cewa) Allah ba ya tayar da wanda yake mutuwa! Na'am, Yana tayarwa. Wa'adi ne (Allah) Ya yi a kanSa tabbatacce, kuma amma mafi yawan mutane ba su sani ba

Verse 39 — Surah An-Nahl 16:39

Domin Ya bayyana musu abin da suke saɓa wa juna a cikinsa, kuma domin waɗan da suka kafirta su sani cewa lalle su ne suka kasance maƙaryata

Verse 40 — Surah An-Nahl 16:40

Abin sani kawai, Maganar Mu ga wani abu idan Mun nufe shi, Mu ce masa, "Ka kasance; sai yana kasancewa

Verse 41 — Surah An-Nahl 16:41

Kuma waɗanda suka yi hijira a cikin sha'anin Allah daga bayan an zalunce su, haƙiƙa Muna zaunar da su a cikin duniya da alheri kuma lalle ladar Lahira ce mafi girma, da sun kasance suna sani

Verse 42 — Surah An-Nahl 16:42

Waɗanda suka yi haƙuri, kuma ga Ubangijinsu suke dogara

Verse 43 — Surah An-Nahl 16:43

Kuma ba Mu aika daga gabaninka ba, face waɗansu mazaje Muna yin wahayi zuwa gare su. Sai ku tambayi mutanen Ambato idan kun kasance ba ku sani ba

Verse 44 — Surah An-Nahl 16:44

Da hujjoji bayyanannu da littattafai kuma Mun saukar da Ambato zuwa gare ka, domin ka bayyana wa mutane abin da aka sassaukar zuwa gare su, kuma don ɗammanin hisu su yi tunani

Verse 45 — Surah An-Nahl 16:45

Shin fa, waɗanda suka yi makircin munanan ayyuka sun amince da Allah, ba zai shafe ƙasa da su ba ko kuwa azaba ba za ta je musu daga inda ba su sani ba

Verse 46 — Surah An-Nahl 16:46

Ko kuwa Ya kama su a cikin jujjuyawarsu? Saboda haka ba su zama masu buwaya ba

Verse 47 — Surah An-Nahl 16:47

Ko kuwa Ya kama su a kan naƙasa? To, lalle ne Ubangijinka haƙiƙa Mai tausayi ne, Mai jin ƙai

Verse 48 — Surah An-Nahl 16:48

Shin, ba su Iura ba da abin da Allah Ya halitta ko mene ne inuwoyinsu suna karkata daga dama da wajajen hagu, suna masu sujada ga Allah, alhali suna masu ƙasƙantar da kai

Verse 49 — Surah An-Nahl 16:49

Kuma ga Allah, abin da yake a cikin sammai da ƙasa na dabba da mala'iku, suke yin sujada, kuma ba su kangara

Verse 50 — Surah An-Nahl 16:50

Suna tsoron Ubangijinsu daga bisansu, kuma suna aikata abin da ake umuruin su

Verse 51 — Surah An-Nahl 16:51

Kuma Allah Ya ce: "Kada ku riƙi abubuwan bautawa biyu. Abin sani kawai, wanda ake bautawa guda ne, sa'an nan sai kuji tsoro Na, Ni kawai

Verse 52 — Surah An-Nahl 16:52

Kuma Yana da abin da yake a cikin sammai da ƙasa, kuma Yana da addini wanda yake dawwamamme. Shin fa, wanin Allah kuke bi da taƙawa

Verse 53 — Surah An-Nahl 16:53

Kuma abin da yake a gare ku na ni'ima, to, daga Allah ne. Sa'an nan kuma idan cuta ta shafeku, to, zuwa gare Shi kuke hargowa

Verse 54 — Surah An-Nahl 16:54

sa'an nan idan Ya kuranye cutar daga gare ku, sai ga wani ɓangare daga gare ku game da Ubangijin su suna shirki

Verse 55 — Surah An-Nahl 16:55

Domin su kafirta da abin da Muka ba su. To, ku ji daɗi, sa'an nan da sannu za ku sani

Verse 56 — Surah An-Nahl 16:56

Kuma suna sanya rabo *ga abin da ba su sani ba daga abin da Muka azurta su. Ranstuwa da Allah! Lalle ne za a tambaye ku daga abin da kuka kasance kuna ƙirƙirawa

Verse 57 — Surah An-Nahl 16:57

Kuma suna danganta 'ya'ya mata ga Allah. Tsarkinsa ya tabbata! Kuma su ne da abin da suke sha'awa

Verse 58 — Surah An-Nahl 16:58

Kuma idan aka yi wa ɗayansu bushara da mace* sai fuskarsa ta wuni baƙa ƙirin, alhali kuwa yana mai cike da baƙin ciki

Verse 59 — Surah An-Nahl 16:59

Yana ɓoyewa daga mutane domin munin abin da aka yimasa bushara da shi. Shin, zai riƙe shi a kan wulakanci ko zai turbuɗe shi a cikin turɓaya To, abin da suke hukuntawa ya munana

Verse 60 — Surah An-Nahl 16:60

Ga waɗan da ba su yi imani* da Lahira ba akwai sifar cuta kuma ga Allah akwai sifa mafi ɗaukaka. Kuma shi ne Mabuwayi, Mai hikima

Verse 61 — Surah An-Nahl 16:61

Kuma da Allah Yana kama mutane da zaluncinsu,* da bai bar wata dabba ba a kan ƙasa. Kuma amma Yana jinkirta musu zuwa ga ajali ambatacce. Sa'an nan idan ajalinsu ya zo, ba za a yi musu jinkiri ba ko da sa'a guda, kuma ba za su gabata ba

Verse 62 — Surah An-Nahl 16:62

Kuma suna sanya wa Allah abin da suke ƙi, kuma harsunansu na siffanta ƙarya cewa lalle ne suna da abubuwa masu kyau. Babu shakka lalle ne suna da wuta, kuma lalle su, waɗanda ake ƙyalewa ne (a cikinta)

Verse 63 — Surah An-Nahl 16:63

Rantsuwar Allah! Lalle ne haƙiƙa Mun aika zuwa ga al'ummomi daga gabaninka, sai Shaiɗan ya ƙawace musu ayyukansu, saboda haka shi ne majiɓincinsu, a yau, kuma suna da azaba mai raɗaɗi

Verse 64 — Surah An-Nahl 16:64

Lalle ba Mu saukar da Littafi ba a kanka, face domin ka bayyana musu abin da suka saɓa wa juna a cikinsa, kuma domin shiriya da rahama ga mutane waɗanda suke yin imani

Verse 65 — Surah An-Nahl 16:65

Kuma Allah Ya saukar da ruwa daga sama, sa'an nan Ya rayar da ƙasa da shi a bayan mutuwarta. Lalle ne a cikin wannan haƙiƙa akwai aya ga mutane waɗanda suke saurare

Verse 66 — Surah An-Nahl 16:66

Kuma lalle ne, kuna da abin lura a cikin dabbobin ni'ima; Muna shayar da ku daga abin da yake a cikin cikunansu, daga tsakanin tukar tumbi da jini nono tsantsan mai sauƙin haɗiya ga masu sha

Verse 67 — Surah An-Nahl 16:67

Kuma daga 'ya'yan itacen dabino da inabi. Kuna samudaga gare shi, abin maye* da abinci mai kyau. Lalle a cikin wannan, haƙiƙa, akwai aya ga mutane waɗanda suke hankalta

Verse 68 — Surah An-Nahl 16:68

Kuma Ubangjinka Ya yi wahayi* zuwa ga ƙudan zuma cewa: "Ki riƙi gidaje daga duwatsu, kuma daga itace, kuma daga abin da suke ginawa

Verse 69 — Surah An-Nahl 16:69

Sa'an nan ki ci daga dukan 'ya'yan itace, saboda haka ki shiga hanyoyin Ubangijinka, suna horarru." Wani abin sha yana fita daga cikunanta, mai saɓawar launukansa a cikinsa akwai wata warkewa ga mutane. Lalle ne, a cikin wannan, haƙiƙa, akwaiayoyi ga mutane waɗanda suke yin tunani

Verse 70 — Surah An-Nahl 16:70

Kuma Allah ne Ya halicce ku, sa'an nan Yana karɓar rayukanku, kuma daga gare ku akwai wanda ake mayarwa zuwa ga mafi ƙasƙncin rayuwa, domin kada ya san kome a bayan da ya zama mai ilmi. Lalle Allah ne Masani Mai ikon yi

Verse 71 — Surah An-Nahl 16:71

Kuma Allah Ya fifita sashenku* a kan sashe a arziki. Sa'an nan waɗanda aka fifita ba su zama masu mayar da arzikinsu a kan abin da hannayensu na dama suka mallaka ba, har su zama daidai a cikinsa. Shin fa, da ni'imar Allah suke musu

Verse 72 — Surah An-Nahl 16:72

Kuma Allah Ya sanya muku matan aure daga kawunanku, kuma Ya sanya muku daga matan aurenku ɗiya da jikoki, kuma Ya arzuta ku daga abubuwa masu daɗi. Shin fa, da ƙarya suke yin imani, kuma da ni'imar Allah su, suke kafirta

Verse 73 — Surah An-Nahl 16:73

Kuma suna bauta wa, baicin Allah, abin da yake ba ya mallakar wani arziki dominsu, daga sammai da ƙasa game da kome, kuma ba su iyawa (ga aikata kome)

Verse 74 — Surah An-Nahl 16:74

Sa'an nan kada ku bayar da waɗansu misalai ga Allah. Lalle ne Allah Yana sani, kuma ku, ba ku sani ba

Verse 75 — Surah An-Nahl 16:75

Allah Ya buga wani misali da wani bawa wanda ba ya iya samun iko a kan yin kome, da (wani bawa) wanda Muka azurta shi daga gare Mu da arziki mai kyau. Sa'an nan shi yana ciyarwa daga arzikin, a asirce da bayyane. Shin suna daidaita? Godiya ta tabbata ga Allah. A'a mafi yawansu ba su sani ba

Verse 76 — Surah An-Nahl 16:76

Kuma Allah Ya buga wani misali, maza biyu, ɗayansu bebe ne, ba ya iya samun ikon yin kome, kuma shi nauyi ne a kan mai mallakarsa, inda duk ya fuskantar da shi, ba ya zuwa da wani alheri. Shin, yana daidaita, shi da (namiji na biyu) wanda yake umurni da a yi adalci kuma yana a kan tafarki madaidaici

Verse 77 — Surah An-Nahl 16:77

Kuma ga Allah gaibin* sammai da ƙasa yake, kuma al'amarin Sa'a bai zama ba face kamar walƙawar gani, ko kuwa shi ne mafi kusa! Lalle Allah a kan dukan kome Mai ikon yi ne

Verse 78 — Surah An-Nahl 16:78

Kuma Allah ne Ya fitar da ku daga cikunan iyayenku, ba da kuna sanin kome ba, kuma Ya sanya muku ji da gannai da zukata, tsammaninku za ku gode

Verse 79 — Surah An-Nahl 16:79

Shin ba su ga tsuntsaye* ba suna horarru cikin sararin sama babu abin da yake riƙe su face Allah? Lalle ne a cikin wancan haƙiƙa, akwai ayoyi ga mutane waɗanda suke yin imani

Verse 80 — Surah An-Nahl 16:80

Kuma Allah ne Ya sanya muku daga gidajenku wurin natsuwa, kuma Ya sanya muku daga fatun dabbobin ni'ima wasu gidaje kuna ɗaukar su da sauƙi a ranar tafiyarku da ranar zamanku, kuma daga sufinsu* da gashinsu da gezarsu (Allah) Ya sanya muku kayan ɗaki da na jin daɗi zuwa ga wani loƙaci

Verse 81 — Surah An-Nahl 16:81

Kuma Allah ne Ya sanya muku inuwa daga abin da Ya halitta, kuma Ya sanya muku ɗakuna daga duwatsu, kuma Ya sanya muku waɗansu riguna suna tsare muku zafi, da waɗansu riguna *suna tsare muku makaminku. Kamar wancan ne (Allah) Yake cika ni'imarSa a kanku, tsammanin ku, kuna sallamawa

Verse 82 — Surah An-Nahl 16:82

To, idan sun juya, to, abin da ya wajaba a kanka, shi ne iyarwa kawai, bayyananniya

Verse 83 — Surah An-Nahl 16:83

Suna sanin ni'imar Allah, sa'an nan kuma suna musunta, kuma mafi yawansu kafirai ne

Verse 84 — Surah An-Nahl 16:84

Kuma a ranar da Muke tayar da mai shaida daga kowace al'umma, sa'an nan kuma ba za a yi izni ba ga waɗanda suka kafirta, kuma ba su zama ana neman komawarsu ba

Verse 85 — Surah An-Nahl 16:85

Kuma idan waɗanda suka yi zalunci suka ga azaba, sa'an nan ba za a saukake ta daga gare su ba, kuma ba su zama ana yi musu jinkiri ba

Verse 86 — Surah An-Nahl 16:86

Kuma idan waɗanda suka yi shirka suka ga abubuwan shirkarsu sai su ce: "Ya Ubangijinmu! Waɗannan ne abubuwanshirkarmu waɗanda muka kasance muna kira baicinKa". Sai su jefamagana zuwa gare su, "Lalle ne ku, haƙiƙa, maƙaryata ne

Verse 87 — Surah An-Nahl 16:87

Kuma su shiga neman sulhu zuwa ga Allah a ranar nan, kuma abin da suka kasance suna ƙirƙirawa ya ɓace daga gare su

Verse 88 — Surah An-Nahl 16:88

Waɗanda suka kafirta kuma suka kange daga hanyar, Allah, Mun ƙara musu wata azaba bisa ga azabar, saboda abin da suka kasance suna yi na fasadi

Verse 89 — Surah An-Nahl 16:89

Kuma a ranar da Muke tayar da shaidu a cikin kowace al'umma a kansu daga kawunansu, kuma Muka zo da kai kana mai bayar da shaida a kan waɗannan, kuma Mun saussaukar da Littali a kanka domin yin bayani ga dukkan kome da shiriya da rahama da bushara ga masu miƙa wuya (Musulmi)

Verse 90 — Surah An-Nahl 16:90

Lalle Allah na yin umurni da adalci da kyautatawa, da bai wa ma'abucin zumunta, kuma yana hani ga alfasha da abin da aka ƙi da rarrabe jama'a. Yana yi muku gargaɗi, ɗammanin ku, kuna tunawa

Verse 91 — Surah An-Nahl 16:91

Kuma ku cika da alkawarin* Allah idan kun yi alkawari, kuma kada ku warware rantsuwoyinku a bayan ƙarfafa su, alhali kuma haƙiƙa kun sanya Allah Mai lamuncewa a kanku. Kuma lalle Allah ne Yake sanin abin da kuke aikatawa

Verse 92 — Surah An-Nahl 16:92

Kuma kada ku kasance kamar wadda ta warware zarenta a bayan tukka, ya zama warwararku, kuna riƙon rantsuwoyinku domin yaudara a tsakaninku, domin kasancewar wata al'umma tafi riba daga wata al'umma! Abin sani kawai Allah Yana jarrabar ku da shi, kuma lalle ne yana bayyana muku a Ranar ¡iyama, abin da kuka kasance, a cikinsa, kuna saɓa wajuna

Verse 93 — Surah An-Nahl 16:93

Kuma da Allah Ya so, haƙi ƙa, da Ya sanya ku al'umma guda, kuma Yana ɓatar da wanda Ya so. kuma Yana shiryar da wanda Ya so. Lalle ne ana tambayarku abin da kuka kasance kuna aikatawa

Verse 94 — Surah An-Nahl 16:94

Kada ku riƙi rantsuwoyin ku domin yaudara a tsakanin ku, har ƙafa ta yi sulɓi a bayan tabbatarta, kuma ku ɗanɗani azaba saboda abin da kuka kange daga hanyar Allah. Kuma kuna da wata azaba mai girma

Verse 95 — Surah An-Nahl 16:95

Kada ku sayi 'yan kuɗi kaɗan da alkawarin Allah. Lalle ne abin da yake a wurin Allah shi ne mafi alheri a gare ku, idan kun kasance kuna sani

Verse 96 — Surah An-Nahl 16:96

Abin da yake a wurinku yana ƙarewa, kuma abin da yake a wurin Allah ne mai wanzuwa. Kuma lalle ne, Muna saka wa waɗanda suka yi haƙuri da ladarsu da mafi kyawun abin da suka kasance suna aikatawa

Verse 97 — Surah An-Nahl 16:97

Wanda ya aikata aiki na ƙwarai daga namiji ko kuwa mace, alhali yana mumini, to, haƙiƙa Muna rayar da shi, rayuwa mai daɗi. Kuma haƙiƙa Muna saka musu ladarsu da mafi kyawun abin da suka kasance suna aikatawa

Verse 98 — Surah An-Nahl 16:98

Sa'an nan idan ka karanta *Alƙur'ani, sai ka nemi tsari ga Allah daga shaiɗan jefaffe

Verse 99 — Surah An-Nahl 16:99

Lalle ne shi, ba shi da wani ƙarfi a kan waɗan da suka yi imani, kuma suna dogara ga Ubangijin su

Verse 100 — Surah An-Nahl 16:100

Abin sani kawai ƙarfinsa yana a kan waɗanda suke jiɓintar sa, kuma waɗanda suke su, game da shi, masu shirki ne

Verse 101 — Surah An-Nahl 16:101

Kuma idan Muka musanya wata aya a matsayin wata aya, kuma Allah ne Mafi sani ga abin da Yake saukarwa sai su ce: "Abin sani kawai, kai, aƙirƙiri ne." A'a, mafi yawansu ba swa sani

Verse 102 — Surah An-Nahl 16:102

Ka ce: "Ruhul ¡udusi* ne ya sassaukar da shi, daga Ubangijinka da gaskiya, domin ya tabbatar da waɗanda suka yi imani, kuma (domin) shiriya da bushara ga Musulmi

Verse 103 — Surah An-Nahl 16:103

Kuma lalle ne, haƙiƙa Muna sanin (cewa) lalle ne su, suna cewa, "Abin sani kawai wani mutum ne yake karantar da shi." Harshen wanda suke karkatai da maganar zuwa gare shi, Ba'ajame ne, kuma wannan (Alƙur'ani) harshe ne Balarabe bayyanan ne

Verse 104 — Surah An-Nahl 16:104

Lalle ne waɗanda ba su yin imani da ayoyin Allah, Allahba zai shiryar da su ba, kuma suna da azaba mai raɗaɗi

Verse 105 — Surah An-Nahl 16:105

Abin sani kawai waɗanda ba su yin imani da ayoyin Allah, su ne suke ƙirƙira ƙarya. Kuma waɗannan su ne maƙaryata

Verse 106 — Surah An-Nahl 16:106

Wanda ya kafirta da Allah daga bayan imaninsa, face wanda aka tilasta alhali kuwa zuciyarsa tana natse da imani kuma wanda ya yi farin ciki da kafirci, to, akwai fushi a kansa daga Allah, kuma suna da wata azaba mai girma

Verse 107 — Surah An-Nahl 16:107

Waɗancan ne kafirai domin sun fifita son duniya a kan Lahira, kuma lalle ne Allah ba Ya shiryar da mutane kafirai

Verse 108 — Surah An-Nahl 16:108

Waɗancan ne waɗanda Allah Ya bice hasken zukatansu da jinsu da gannansu. Kuma waɗan can su ne gafalallu

Verse 109 — Surah An-Nahl 16:109

Babu shakka lalle ne a Lahira su ne masu hasara

Verse 110 — Surah An-Nahl 16:110

Sa'an nan kuma lalle ne Ubangijinka ga waɗanda suka yi hijira daga bayan an fitine su, sa'an nan kuma suka yi jihadi, kuma suka yi haƙuri, lalle ne Ubangijinka, daga bayanta haƙiƙa Mai gafara ne, Mai jin ƙai

Verse 111 — Surah An-Nahl 16:111

A ranar da kowane rai zai je yana jayayyar tunkuɗewa daga kansa, kuma a cika wa kowane rai (sakamakon) abin da ya aikata, kuma su ba za a zalunce su ba

Verse 112 — Surah An-Nahl 16:112

Kuma Allah Ya buga misali,* wata alƙarya ta kasance amintacciya, natsattsiya, arzikinta yana je mata a wadace daga kowane wuri sai ta kafirta da ni'imomin Allah, saboda haka Allah ya ɗanɗana mata tufafin yunwa da tsoro, saboda abin da suka kasance suna sana'antawa

Verse 113 — Surah An-Nahl 16:113

Kuma lalle ne haƙiƙa wani Manzo daga gare su, ya jemusu, sai suka ƙaryata shi, saboda haka azaba ta kama su, alhali kuwa su ne masu zalunci

Verse 114 — Surah An-Nahl 16:114

Sa'an nan ku ci daga* abin da Allah Ya azurta ku da shi, halas, kuma mai daɗi, kuma ku gode wa ni'imar Allah idan kun kasance shi kuke bautawa

Verse 115 — Surah An-Nahl 16:115

Abin sani kawai (Allah) Ya haramta* muku mussai da jini da naman alade da abin da aka ambaci sunan wanin Allah game da shi. Sa'an nan wanda aka tilastaa kan jama'a kuma baicin mai zalunci, to, lalle Allah ne Mai gafara, Mai jin ƙai

Verse 116 — Surah An-Nahl 16:116

Kuma kada ku ce, domin abin da harsunanku suke siffantawa da ƙarya, "Wannan halas ne, kuma wannan haramun ne." Domin ku ƙirƙira ƙarya ga Allah. Lalle ne, waɗanda suke ƙirƙira ƙarya ga Allah ba za su ci nasara ba

Verse 117 — Surah An-Nahl 16:117

Jin daɗi ne kaɗan. Kuma suna da wata azaba mai raɗaɗi

Verse 118 — Surah An-Nahl 16:118

Kuma kan waɗanda suka tuba (Yahudu) Mun haramta abin da Muka bayar da labari a gare ka daga gabani,* kuma ba Mu zalunce su ba, amma sun kasance kansu suke zalunta

Verse 119 — Surah An-Nahl 16:119

Sa'an nan kuma lalle ne Ubangijinka ga waɗanda suka aikata mummunan aiki* da jahilci, sa'an nan suka tuba daga bayan wancan, kuma suka gyara, lalle ne Ubangijinka, daga bayanta haƙiƙa Mai gafara ne, Mai jin ƙai

Verse 120 — Surah An-Nahl 16:120

Lalle ne Ibrahim* ya kasance shugaba, mai ƙasƙantar da kai ga Allah, mai karkata zuwa ga gaskiya, kuma bai kasance daga masu shirki ba

Verse 121 — Surah An-Nahl 16:121

Mai godiya* ga ni'imominSa (Allah), Ya zaɓe shi, kuma Ya shiryar da shi zuwa ga tafarki madaidaici

Verse 122 — Surah An-Nahl 16:122

Kuma Muka ba shi alheri a cikin duniya, Kuma lalle shi, a Lahira, yana daga salihai

Verse 123 — Surah An-Nahl 16:123

Sa'an nan kuma Muka yi wahayi zuwa gare ka (cewa), "Ka* bi aƙidar Ibrahim, mai karkata zuwa ga gaskiya, kuma bai kasance daga masu shirka ba

Verse 124 — Surah An-Nahl 16:124

Abin sani kawai, an sanya Asabar a kan waɗanda suka saɓa wajuna a cikin sha'aninsa.* Kuma lalle ne Ubangijinka, haƙiƙa, Yana yin hukunci a tsakaninsu a Ranar ¡iyama a cikin abin da suka kasance a cikinsa suna saɓa wa juna

Verse 125 — Surah An-Nahl 16:125

Ka yi kira zuwa ga hanyar Ubangijinka da hikima* da wa'azi mai kyau kuma ka yi jayayya da su da magana wadda take mafi kyau. Lalle ne Ubangijinka Shi neMafi sani ga wanda ya ɓace daga hanyarSa, kuma Shi ne Mafi sani ga masu shiryuwa

Verse 126 — Surah An-Nahl 16:126

Kuma idan kuka saka* wa uƙuba to ku saka wa uƙuba da misalin abin da aka yi muku uƙubar da shi. Kuma idan kun yi haƙuri, lalle shi ne mafi alheri ga masu haƙuri

Verse 127 — Surah An-Nahl 16:127

Kuma ka yi haƙuri, kuma haƙurinka ba zai zama ba face domin Allah, kuma kada ka yi baƙin ciki sabo da su, kuma kada ka kasance a cikin ƙuncin rai daga abin da suke yi na makirci

Verse 128 — Surah An-Nahl 16:128

Lalle Allah Yana tare da waɗanda suka yi taƙawa da waɗanda suke su masu kyautatawa ne