Back to Languages
Hausa - Chapter 18
Translation by Abubakar Mahmood Jummi
Verse 1
Godiya ta tabbata ga Allah wanda Ya saukar da Littafi a kan bawansa kuma bai sanya karkata ba a gare shi
Verse 2
Madaidaici, domin Ya yi gargaɗi da azaba mai tsanani daga gare shi, kuma Ya yi bushara ga muminai, waɗanda suke aikata ayyuka na ƙwarai da (cewa) suna da wata lada mai kyau
Verse 3
Suna masu zama a cikinta har abada
Verse 4
Kuma Ya yi gargaɗi ga waɗanda* suka ce: "Allah yana da ɗa
Verse 5
Ba su da wani ilmi game da wannan magana, kuma iyayensu ba su da shi, abin da ke fita daga bakunansu ya girma ga ya zama kalmar faɗa! Ba su faɗan kome face ƙarya
Verse 6
To, ka yi kusa ka halaka ranka a gurabbansu, wai domin ba su yi imani da wannan labari ba saboda baƙin ciki
Verse 7
Lalle ne Mu, Mun sanya abin da ke kan ƙasa wata ƙawa* ce gare ta, domin Mu jarraba su; wanne daga cikinsu zai zama mafi kyau ga aiki
Verse 8
Kuma lalle Mu, Masu sanya abin da ke a kanta (ya zama) turɓaya ƙeƙasasshiya ne
Verse 9
Ko kuwa ka yi zaton cewa ma'abuta kogo* da allo sun kasance abin mamaki daga ayoyin Allah
Verse 10
A lokacin da samarin suka tattara zuwa ga kogon, sai suka ce: "Ya Ubangijinmu*! Ka ba mu wata rahama daga gare Ka, kuma Ka sauƙaƙe mana (samun) shiriya daga al'amarinmu
Verse 11
Sai Muka yi duka a kan kunnunwansu,* a cikin kogon, shekaru masu yawa
Verse 12
Sa'an nan Muka tayar da su, domin Mu san wane ɗayan ƙungiyoyin biyu suka fi lissafi ga abin da suka zauna na lokacin
Verse 13
Mu ne ke jeranta maka labarinsu da gaskiya. Lalle ne su, waɗansu samari ne. Sun yi imani da Ubangijinsu, kuma Muka ƙara musu wata shiriya
Verse 14
Kuma Muka ɗaure a kan zukatansu, a lokacin da suka tsayu, sa'an nan suka ce: "Ubangijinmu Shi ne Ubangijin sammai daƙasa. Ba za mu kirayi wanin Sa abin bautawa ba. (Idan mun yi haka) lalle ne, haƙiƙa, mun faɗi abin da ya ƙetare haddi a sa'an nan
Verse 15
Ga waɗannan mutanenmu sun riƙi waninSa abin bautawa! Don me ba su zuwa da wata hujja bayyananna a kansu (waɗanda ake bautawar)? To, wane ne mafi zalunci daga wanda ya ƙaga ƙarya ga Allah
Verse 16
Kuma idan kun nisance su su da abin da suke bautawa, face Allah, to, ku tattara zuwa ga kogon sai Ubangijinku Ya watsa muku daga rahamar Sa kuma Ya sauƙaƙe muku madogara daga al'amarinku
Verse 17
Kuma kana ganin rana idan ta fito tana karkata daga kogonsu wajen dama kuma idan ta faɗi tana gurgura su wajen hagu, kuma su, suna a cikin wani fili daga gare shi. Wannan abu yana daga ayoyin Allah. Wanda Allah Ya shiryar, to shi ne mai shiryuwa, kuma wanda Allah Ya ɓatar to ba za ka samar masa wani majiɓinci mai shiryarwa ba
Verse 18
Kuma kana zaton su farkakku ne, alhali kuwa su masu barci ne. Muna juya su wajen dama da wajen hagu, kuma karensu yana shimfiɗe da zira'o'in ƙafafuwansa ga farfajiya (ta kogon). Da ka leka (a kan) su (da) lalle ne, ka juya daga gare su a guje kuma (da) lalle ne ka cika da tsoro daga gare su
Verse 19
Kuma kamar wannan ne Muka tayar da su, domin* su tambayi juna a tsakaninsu. Wani mai magana daga cikinsu ya ce: "Mene ne lokacin da kuka zauna?" suka ce: "Mun zauna yini ɗaya ko sashen yini." Suka ce: "Ubangijinku ne Mafi sani ga abin da kuka zauna. To, ku aika da ɗayanku, game da azurfarku wannan, zuwa ga birnin**. Sai ya duba wanne ne mafi tsarki ga abin dafawa, sai ya zo muku da abinci daga gare shi. Kuma sai ya yi da hankali, kada ya sanar da ku ga wani mutum
Verse 20
Lalle ne su idan sun kama ku, za su jefe ku, ko kuwa su mayar da ku a cikin addininsu kuma ba za ku sami babban rabo, ba, a sa'an nan har abada
Verse 21
Kuma kamar wancan ne, Muka nuna su (gare su) domin su san lalle wa'adin Allah gaskiya ne, kuma lalle ne Sa'a babu shakka a cikinta. A lokacin da suke jayayyar al'amarinsu a tsakaninsu* sai suka ce: "Ku gina wani gini a kansu, Ubangijinsu ne Mafi sani game da su." Waɗanda suka rinjaya a kan al'amarinsu suka ce: "Lalle mu riƙi masallaci a kansu
Verse 22
Za su ce: "Uku ne da na huɗunsu karensu."Kuma suna cewa, "Biyar ne da na shidansu karensu," a kan jifa a cikin duhu. Kuma suna cewa, "Bakwaine da na takwas ɗinsu karensu."Ka ce: "Ubangijina* ne Mafi saniga ƙidayarsu, babu wanda ya san su face kaɗan."Kada ka yi jayayya bayyananna. Kuma kada ka yi fatawa** ga kowa daga gare su a cikin al'amarinsu
Verse 23
Kuma kada lalle ka ce ga wani abu, "Lalle ni, mai aikatawa ne ga wancan a gobe
Verse 24
Face idan Allah Ya so. Kuma ka ambaci Ubangijinka idan ka manta, kuma ka ce: "¦ammani ga Ubangijina, Ya shiryar da ni ga abin da yake shi ne mafi kusa ga wannan na shiriya
Verse 25
Kuma suka zauna a cikin kogonsu shekaru ɗari uku kuma suka daɗa tara
Verse 26
Ka ce: "Allah ne Mafi sani ga abin da suka zauna. Shi ne da (sanin) gaibin sammai da ƙasa. Mune ne ya yi ganin Sa da jin Sa! Ba su da wani majiɓinci baicin Sa kuma ba Ya tarayya da kowa a cikin hukuncinsa
Verse 27
Ka karanta abin da aka yi wahayi zuwa gare ka, na littafin Ubangijinka. Babu mai musanyawa ga kalmominSa kuma ba za ka sami wata madogara ba daga waninsa
Verse 28
Ka haƙurtar da ranka tare da waɗanda ke kiran Ubangijinsu, safe da maraice, suna nufin yardar Sa. Kuma kada idanunka su juya daga barinsu, kana nufin ƙawar rayuwar duniya.* Kuma kada ka biwanda Muka shagaltar da zuciyarsa daga hukuncin Mu, kuma ya bi son zuciyarsa, alhali kuwa al'amarinsa ya kasance yin ɓarna
Verse 29
Kuma ka ce: "Gaskiya daga Ubangijinku take." Saboda haka wanda ya so, to, ya yi imani, kuma wanda ya so, to, ya kafirta. Lalle ne Mu, Mun yi tattali domin azzalumai wata wuta wadda shamakunta, sun ƙewaye da su. Kuma idan sun nemi taimako sai a taimake su da wani ruwa kamar dabzar mai, yana soye fuskoki. Tir da abin shansu, kuma wutar ta yi munin zama mahutarsu
Verse 30
Lalle ne waɗanda suka yi imani kuma suka aikata ayyukan ƙwarai lalle ne Mu ba Mu tozartar da ladar wanda ya kyautata aiki
Verse 31
Waɗannan suna da gidajen Aljannar zama, ƙoramu na gudana daga ƙarƙashinsu, ana sanya musu ƙawa, a cikinsu, daga mundaye na zinariya, kuma suna tufantar waɗansu tufafi kore, na alharini raƙiƙi da alharini mai kauri suna kishingiɗe a cikinsu, a kan, karagu. Madalla da sakamakonsu. Kuma Aljanna ta kyautatu da zama wurin hutawa
Verse 32
Kuma ka buga musu misali* da waɗansu maza biyu. Mun sanya wa ɗayansu gonaki biyu na inabobi, kuma Muka kewayesu da itacen dabinai, kuma Muka sanya shuka a tsakaninsu (su gonakin)
Verse 33
Kowace gona daga biyun, ta bayar da amfaninta, kuma ba ta yi zaluncin kome ba daga gare shi. Kuma Muka ɓuɓɓugar da ƙoramu a tsakaninsu
Verse 34
Kuma ɗan itace ya kasance gare shi. Sai ya ce wa abokinsa, alhali kuwa yana muhawara da shi, "Ni ne mafifici daga gare ka a wajen dukiya, kuma mafi izza a wajen jama'a
Verse 35
Kuma ya shiga gonarsa, alhali yana mai zalunci ga kansa, ya ce: "Ba ni zaton wannan za ta halaka har abada
Verse 36
Kuma ba ni zaton sa'a mai tsayuwa ce, kuma lalle ne, idan an mayar da ni zuwa ga Ubangijiina, to, lalle ne, zan sami abin da yake mafi alheri daga gare ta ya zama makoma
Verse 37
Abokinsa ya ce masa, alhali kuwa yana muhawara da shi, "Ashe ka kafirta da wanda Ya halitta ka daga turɓaya, sa'an nan daga ɗigon maniyi, sa, an nan Ya daidaita ka, ka zama mutum
Verse 38
Amma ni, shi ne Allah Ubangijina, kuma ba zan tara kowa da Ubangijina ba
Verse 39
Kuma don me, a lokacin da ka shiga gonarka, ka, ce, 'Abin da Allah ya so (shi ke tabbata) babu wani ƙarfi face game da Allah.' Idan ka gan ni, ni ne mafi ƙaranci daga gare ka a wajen dukiya da ɗiya
Verse 40
To, akwai fatan Ubangijina Ya ba ni abin da yake mafi alheri daga gonarka, kuma ya aika azaba a kanta (ita gonarka) daga sama, sai ta wayi gari turɓaya mai santsi
Verse 41
Ko kuma ruwanta ya wayi gari faƙaƙƙe, saboda haka, ba za ka iya nemo shi ba dominta
Verse 42
Kuma aka halaka dukan 'ya'yan itacensa, sai ya wayi gari yana juyar da tafunansa biyu, saboda abin da ya kashe a cikinta, alhali kuwa ita tana kwance a kan rassanta, kuma yana cewa, "Kaitona, da dai ban tara* wani da Ubangijina ba
Verse 43
Kuma wata jama'a ba ta kasance a gare shi ba, waɗanda ke taimakon sa, baicin Allah, kuma bai kasance mai taimakon kansa ba
Verse 44
A can taimako da jiɓinta ga Allah yake. Shi ne kawai Gaskiya, shi ne Mafifici ga lada kuma Mafi fici ga aƙiba
Verse 45
Ka buga musu misalin rayuwar duniya, kamar ruwane wanda Muka saukar da shi daga sama sa'an nan tsirin ƙasa ya garwaya da shi, sa'an nan ya wayi gari dudduga, iska tana shiƙar sa. Kuma Allah Ya kasance Mai yawan ikon yi ne a kan dukan kome
Verse 46
Dukiya da ɗiya,* su ne ƙawar rayuwar duniya, kuma ayyuka masu wanzuwa na ƙwarai sun fi zama alheri a wurin Ubangijinka ga lada kuma sun fi alheri ga buri
Verse 47
Kuma a ranar da Muke tafiyar da duwatsu, kuma ka ga ƙasa bayyane, kuma Mu tara su har ba Mu bar kowa ba daga gare su
Verse 48
Kuma a gitta* su ga Ubangijinka suna sahu guda, (Mu ce musu), "Lalle ne haƙiƙa kun zo Mana, kamar yadda Muka halitta ku a farkon lokaci. A'a, kun riya cewa ba za Mu sanya mukuwani lokacin haɗuwa ba
Verse 49
Kuma aka aza littafin ayyuka, sai ka ga masu laifi suna masu jin tsoro daga abin da ke cikinsa, kuma suna cewa "Kaitonmu! Mene ne ga wannan littafi, ba ya barin ƙarama, kuma ba ya barin babba, face ya ƙididdige ta?" Kuma suka sami abin da suka aikata halarce. Kuma Ubangijinka ba Ya zaluntar kowa
Verse 50
Kuma a lokacin da Muka ce wa malaiku, "Ku yi sujada ga Adamu." Sai suka yi sujada face Iblisa, ya kasance daga aljannu sai ya yi fasiƙanci ga barin umurnin Ubangijinsa, To fa, ashe, kuna riƙon sa, shi da zuriyarsa, su zama majiɓinta baicin Ni, alhali kuwa su maƙiya ne a gare ku? Tir da ya zama musanya ga azzalumai
Verse 51
Ban shaida musu halittar sammai da ƙasa ba, kuma ban (shaida musu) halittar rayukansu ba kuma ban kasance mai riƙon masu ɓatarwa (da wani) su zama mataimaka ba
Verse 52
Kuma da ranar da Allah Yake cewa, "Ku kirayi abokan tarayyaTa, waɗanda kuka riya." Sai su kiraye su, sai ba za su karɓa musu ba, kuma Mu sanya Maubiƙa* (Mahalaka) a tsakaninsu
Verse 53
Kuma masu laifi suka ga wuta suka tabbata lalle ne, su masu, auka mata ne, kuma ba su sami majuya ba daga gare ta
Verse 54
Kuma lalle ne, haƙiƙa, Mun jujjuya, a cikin wannan Alƙur'ani, daga kowane irin misali ga mutane (domin su gane, su bi shari'a), kuma mutum ya kasance mafi yawan abu ga jidali
Verse 55
Kuma babu abin da ya hana mutane su yi imani a lokacinda shiriya ta zo musu, kuma su nemi gafara daga Ubangijinsu, face hanyar farko* ta je musu ko kuma azaba ta je musu nau'i-nau'i
Verse 56
Kuma ba Mu aika Manzanni ba face suna masu bayar da bushara kuma masu gargaɗi, kuma waɗanda suka kafirta suna jidali da ƙarya domin su ɓata gaskiya da ita, kuma suka riƙi ayoyi Na da abin da aka yi musu gargaɗi da shi abin izgili
Verse 57
Kuma wane ne mafi zalunci daga wanda aka tunatar game da ayoyin Ubangijinsa, sai ya bijire daga barinsu, kuma ya manta abin da hannayensa suka gabatar? Lalle ne Mu, Mun sanya abubuwan rufi a kan zukatansu domin kada su fahimce shi, kuma a cikin kunnuwansu (Mun sanya) wani nauyi, kuma idan ka kiraye su zuwa ga shiriya, to, ba za su shiryu ba, a sa'an nan, har abada
Verse 58
Kuma Ubangijinka Mai gafara ne, Ma'abucin rahama. Da Yana kama su saboda abin da suka sana'anta, lalle ne, da Ya gaggauta azaba a gare su. A'a, suna da lokacin alkawari, (wanda) ba za su sami wata makoma ba, baicinSa
Verse 59
Kuma waɗancan alƙaryu* Mun halaka su, a lokacin da suka yi zalunci, kuma Muka sanya lokacin alkawarin, ga halaka** su
Verse 60
Kuma a lokacin da Musa* ya ce wa yaronsa, "Ba zan gushe ba sai na isa mahaɗar teku biyu, ko in shuɗe da tafiya shekara da shekaru
Verse 61
To, a lokacin da suka isa mahaɗar tsakaninsu sai suka manta kifinsu, sai ya kama tafarkinsa a cikin teku kamar biga
Verse 62
To, a lokacin da suka wuce ya ce wa yaronsa, "Ka kawo mana kalacinmu. Lalle ne haƙiƙa mun haɗu da wahala daga tafiyarmu wannan
Verse 63
(Yaron) ya ce: "Ka gani! A lokacin da muka tattara zuwa ga falalen nan to, lalle ni, na manta kifin, kuma babu abin da yamantar da ni shi, face Shaiɗan, domin kada in tuna shi, sai ya kama tafarkinsa a cikin teku, da mamaki
Verse 64
Ya ce: "Wancan ne abin da muka kasance muna biɗa." Sai suka koma a kan gurabunsu, suna bibiya
Verse 65
Sai suka sami wani bawa daga bayin Mu, Mun ba shi wata rahama* daga wurin Mu, kuma Mun sanar da shi wani ilmi daga gun Mu
Verse 66
Musa ya ce masa, "Ko in bi ka a kan ka sanar da ni daga abin da aka sanar da kai na shiriya
Verse 67
Ya ce: "Lalle ne kai ba za ka iya yin haƙuri tare da ni, ba
Verse 68
Kuma yaya za ka yi haƙuri a kan abin da ba ka kewayeda shi ba ga jarrabawa
Verse 69
Ya ce: "Za ka same ni, in Allah Ya so mai haƙuri kuma ba zan saɓa maka ba ga wani umurni
Verse 70
Ya ce: "To idan ka bi ni to kada ka tambaye ni daga kome sai na labarta maka ambato* daga gare shi
Verse 71
Sai suka tafi har a lokacin da suka hau a cikin jirgi, ya huje shi, ya ce, "Ka huje shi domin ya nutsar da mutanensa? Lalle ne, haƙiƙa, ka zo da wani babban abu
Verse 72
Ya ce: "Ashe ban ce, lalle kai, ba za ka iya yin haƙuri tare da ni ba
Verse 73
Ya ce: "Kada ka kama ni da abin da na manta kuma kada ka kallafa mini tsanani ga al'amarina
Verse 74
Sai suka tafi, har suka haɗu da wani yaro, sai ya kashe shi. Ya ce: "Ashe ka kashe rai tsarkakakke, ba da wani rai ba? Lalle ne haƙiƙa ka zo da wani abu na ƙyama
Verse 75
Ya ce: "Shin, ban ce maka ba, lalle ne kai ba za ka iya yin haƙuri tare da ni ba
Verse 76
Ya ce: "Idan na tambaye* ka daga wani abu a bayanta, to, kada ka abuce ni. Lalle ne, ka isa ga iyakar uzuri daga gare ni
Verse 77
Sai suka tafi, har a lokacin da suka je wa mutanen wata alƙarya, suka nemi mutanenta da su ba su abinci, sai suka ƙi su yi musu liyafa. Sai suka sami wani bango a cikinta yana nufin ya karye, sai (Halliru) ya tayar da shi miƙe. (Musa) ya ce: "Da ka so, lalle ne da ka karɓi ijara a kansa
Verse 78
Ya ce: "Wannan shi ne rabuwar tsakanina da tsakaninka. Za ni gaya maka fassarar abin da ba ka iya yin haƙuri ba a kansa
Verse 79
Amma Jirgin, to, ya zama na waɗansu matalauta ne suna aiki* a cikin teku, sai na yi niyyar in aibanta shi, alhali kuwa wani sarki ya kasance a gaba gare su, yana karɓewar kowane jirgi (lafiyayye) da ƙwace
Verse 80
Kuma amma yaron, to, uwayensa sun kasance muminai, to, sai muka ji tsoron ya kallafa musu kangara da kafirci
Verse 81
Sai muka yi nufin Ubangijinsu Ya musanya musu mafi alheri daga gare shi ga tsarkakuwa, kuma mafi kusantar tausayi
Verse 82
Kuma amma bangon, to, ya kasance na waɗansu yara biyu ne, marayu a cikin birnin, kuma akwai wata taska tasu a ƙarƙashinsa, kuma ubansu ya kasance sahihin mutum* ne, domin haka Ubangijinka Ya yi nufin su isa iyakar ƙarfinsu, kuma su, su fitar da taskarsu, saboda rahama ne daga Ubangijinka. Kuma ban yi shi ba daga umurnina. Wancan shi ne fassarar abin da ba ka iya yin haƙuri ba a kansa
Verse 83
Kuma suna tambayar ka daga zulƙarnaini*, ka ce: "Zan karanta muku ambato daga gare shi
Verse 84
Lalle ne Mu Mun ba shi mulki a cikin ƙasa kuma Muka ba shi daga kowane abu, hanya (zuwa ga muradinsa)
Verse 85
Sai ya bi hanya
Verse 86
Har a lokacin da ya isa ga mafaɗar rana, kuma ya same ta tana ɓacewa a cikin wani ruwa mai baƙar laka, kuma ya sami waɗansu mutane a wurinta. Muka ce: "Ya Zulƙarnaini imma dai ka azabtar kuma imma ka riƙi kyautatawa a cikinsu
Verse 87
Ya ce: "Amma wanda ya yi zalunci, to za mu azabta shi, sa'an nan a mayar da shi zuwa ga Ubangijinsa, sai kuma Ya yi masa azaba, azaba abar ƙyama
Verse 88
Kuma amma wanda ya yi imani kuma ya aikata aikin ƙwarai to, za mu yi sakamako a gare shi (watau kyauta) mai kyau*, kuma za mu gaya masa sauƙi daga umurninmu
Verse 89
Sa'an nan kuma ya bi hanya
Verse 90
Har a lokacin da ya isa ga mafitar rana, ya same ta tana fita a kan waɗansu mutane (waɗanda) ba Mu sanya musu wata kariya ba daga barinta
Verse 91
Kamar wancan alhali kuwa haƙiƙa, Mun kewaye da jarrabawa ga abin da ke gunsa
Verse 92
Sa'an nan kuma ya bi hanya
Verse 93
Har a lokacin da ya isa a tsakanin duwatsu biyu, ya sami waɗansu mutane daga gabaninsu. Ba su yi kusa su fahimci magana ba
Verse 94
Suka ce: "Ya Zulƙarnaini! Lalle ne Yajuja da Majuja masu ɓarna ne a cikin ƙasa. To, ko za mu Sanya haraji saboda kai, a kan ka sanya wani danni a tsakaninmu da tsakaninsu
Verse 95
Ya ce: "Abin da Ubangijina Ya mallaka mini, a cikinsa ya fi zama alheri. Sai ku taimakeni da ƙarfi, in sanya babbar katanga a tsakaninku da tsakaninsu
Verse 96
Ku kawo mini guntayen baƙin ƙarfe". (Suka kai masa) har a lokacin da ya daidaita a tsakanin duwatsun biyu (ya sanya wuta a cikin ƙarfen) ya ce: "Ku hura (da zugazugai)." Har a lokacin da ya mayar da shi wuta, ya ce: "Ku kawo mini gaci (narkakke) in zuba a kansa
Verse 97
Domin haka ba za su iya hawansa ba, kuma ba za su iya hujewa gare shi ba
Verse 98
Ya ce: "Wannan wata rahama ce daga Ubangijina. Sai idan wa'adin* Ubangijina ya zo, ya mayar da shi niƙaƙƙe. Kuma wa'adin Ubangijina ya kasance tabbatacce
Verse 99
Kuma Muka bar sashensu a ranar nan, yana garwaya a cikin sashe, kuma aka busa a cikin ƙaho sai muka tara su, tarawa
Verse 100
Kuma Muka gitta Jahannama, a ranar nan ga kafirai gittawa
Verse 101
Waɗanda idanunsu suka kasance a cikin rufi daga tuna* Ni, kuma sun kasance ba su iya saurarawa
Verse 102
Shin fa, waɗanda suka kafirta sun yi zaton (daidai ne) su riƙi waɗansu bayiNa*, majiɓinta baic iNa? Lalle ne, Mun yi tattalin Jahannama ta zama liyafa ga kafirai
Verse 103
Ka ce: "Ko mu gaya muku game da mafifita hasara ga ayyuka
Verse 104
Waɗanda aikinsu ya ɓace a cikin rayuwar duniya, alhali kuwa suna zaton lalle ne su, suna kyautata, (abin da suke gani) aikin ƙwarai
Verse 105
Waɗancan ne waɗanda suka kafirta da ayoyin Ubangijinsu, da kuma haɗuwa da Shi, sai ayyukansu suka ɓaci. Saboda haka ba za Mu tsayar musu da awo* ba a Ranar ¡iyama
Verse 106
Wancan ne sakamakonsu shi ne Jahannama, saboda kafircinsu, kuma suka riƙi ayoyi Na da Manzanni Na abin izgili
Verse 107
Lalle ne, waɗanda suka yi imani kuma suka aikata ayyuka na ƙwarai, Aljannar Firdausi ta kasance ita ce liyafa a gare su
Verse 108
Suna madawwama a cikinta, ba su neman makarkata daga barinta
Verse 109
Ka ce: "Da teku* ta kasance tawada ga (rubutun) kalmomin Ubangijina, lalle ne da tekun ta ƙare a gabanin kalmomin Ubangijina su ƙare, kuma koda mun je da misalinsa domin ƙari
Verse 110
Ka ce: "Ni, mutum ne kawai kamarku, ana yin wahayi zuwa gare ni cewa: Lalle ne, Abin bautawarku, Abin bautawa Guda ne, saboda haka wanda ya kasance yana fatan haɗuwa da Ubangijinsa, to, sai ya yi aiki na ƙwarai. Kuma kada ya haɗa kowa ga bauta wa Ubangijinsa