Back to Languages

Hausa - Chapter 20 - Ta-Ha

Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink

Verse 1 — Surah Ta-Ha 20:1

Verse 2 — Surah Ta-Ha 20:2

Ba Mu saukar da Alƙur'ani a gare ka domin ka wahala ba

Verse 3 — Surah Ta-Ha 20:3

Face domin tunatarwa ga wanda ke tsoron Allah

Verse 4 — Surah Ta-Ha 20:4

(An saukar da shi) saukarwa daga wanda Ya halitta ƙasa da sammai maɗaukaka

Verse 5 — Surah Ta-Ha 20:5

Mai rahama, Ya daidaita* a kan Al'arshi

Verse 6 — Surah Ta-Ha 20:6

Abin da yake a cikin sammai nasa ne, da abin da yake a cikin ƙasa da abin da yake a tsakaninsu da abin da ke ƙarƙashin turɓaya

Verse 7 — Surah Ta-Ha 20:7

Kuma idan ka bayyana da magana, to, lalle Shi, Yana sanin asiri da mafi boyuwa

Verse 8 — Surah Ta-Ha 20:8

Allah babu abin bautawa face Shi. Yana da sunaye mafiya kyau

Verse 9 — Surah Ta-Ha 20:9

Kuma shin, labarin Musa yaje maka

Verse 10 — Surah Ta-Ha 20:10

A lokacin da ya ga wata wuta, sai ya ce wa iyalinsa, "Ku dakata. Lalle ne ni, na tsinkayi wata wuta tsammanina in zo mukuda makamashi daga gare ta, ko kuwa in sami wata shiriya a kan wutar

Verse 11 — Surah Ta-Ha 20:11

Sa'an nan a lokacin da ya je mata, aka kira shi, "Ya Musa

Verse 12 — Surah Ta-Ha 20:12

Lalle ne, Ni ne Ubangijnka, sai ka ɗebe takalmanka* Lalle ne kana a rafin nan abin tsarkakewa, ¦uwa

Verse 13 — Surah Ta-Ha 20:13

Kuma Ni na zaɓe ka. Sai ka saurara ga abin da ake yin wahayi

Verse 14 — Surah Ta-Ha 20:14

Lalle, Ni Ni ne Allah. Babu abin bautawa face Ni. Sai ka bauta Mini, kuma ka tsayar da salla domin tuna Ni

Verse 15 — Surah Ta-Ha 20:15

Lalle ne Sa'a mai zuwa ce, lna kusa da In ɓoye ta domin a saka wa dukan rai da abin da yake aikatawa

Verse 16 — Surah Ta-Ha 20:16

Saboda haka, kada wanda ba ya yin imani da ita kumaya bi son zuciyarsa, ya taushe ka daga gare ta har ka halaka

Verse 17 — Surah Ta-Ha 20:17

Kuma wace ce waccan ga damanka ya Musa

Verse 18 — Surah Ta-Ha 20:18

Ya ce: "Ita sandata ce, ina dogara a kanta, kuma ina kakkaɓar ganye da ita a kan ƙananan bisashena kuma ina da waɗansu bukatoci* na dabam a gare ta

Verse 19 — Surah Ta-Ha 20:19

Ya ce: "Ka yi jifa da ita, ya Musa

Verse 20 — Surah Ta-Ha 20:20

Sai ya jefa ta. Sai ga ta dabbar macijiya, tana tafiya da gaggawa

Verse 21 — Surah Ta-Ha 20:21

Ya ce: "Ka kama ta kuma kada ka ji tsoro. Za Mu mayar da ita ga halinta na farko

Verse 22 — Surah Ta-Ha 20:22

Kuma ka haɗa hannunka zuwa ga damtsenka, ya fita yana fari, babu sofane, wata aya ta dabam

Verse 23 — Surah Ta-Ha 20:23

Domin Mu nuna maka daga ayoyin Mu manya

Verse 24 — Surah Ta-Ha 20:24

Ka tafi zuwa ga Fir'auna. Lalle shi ya ƙetare haddi (da girman kai)

Verse 25 — Surah Ta-Ha 20:25

Ya ce: "Ya Ubangiji! Ka buɗa* mini, ƙirjina

Verse 26 — Surah Ta-Ha 20:26

kuma ka sawwake mun Al'amari na

Verse 27 — Surah Ta-Ha 20:27

Kuma Ka warware mini wani ƙulli daga harshena

Verse 28 — Surah Ta-Ha 20:28

Verse 29 — Surah Ta-Ha 20:29

Kuma Ka sanya mini wani mataimaki daga mutanena

Verse 30 — Surah Ta-Ha 20:30

Verse 31 — Surah Ta-Ha 20:31

Ka ƙarfafa halittata da shi

Verse 32 — Surah Ta-Ha 20:32

Kuma Ka shigar da shi a cikin al'amarina

Verse 33 — Surah Ta-Ha 20:33

Domin mu tsarkake Ka da yawa

Verse 34 — Surah Ta-Ha 20:34

Kuma mu tuna Ka da yawa

Verse 35 — Surah Ta-Ha 20:35

Lalle Kai, Ka kasance Mai gani gare mu

Verse 36 — Surah Ta-Ha 20:36

Ya ce: "Lalle ne, an ba ka roƙonka, ya Musa

Verse 37 — Surah Ta-Ha 20:37

Kuma lalle ne haƙiƙa, Mun yi wata baiwa gare ka a wani lokacin na dabam

Verse 38 — Surah Ta-Ha 20:38

A lokacin da Muka yi wahayin abin da aka yi wahayi zuwa ga uwarka

Verse 39 — Surah Ta-Ha 20:39

Cewa, Ki jefa shi a cikin akwatin nan, sa'an nan ki jefa shi a cikin kogi, sa'an nan kogin ya jefa shi a gaɓa, wani maƙiyi Nawa kuma maƙiyi nasa ya ɗauke shi.' Kuma Na jefa wani so daga gare Ni a kanka. Kuma domin a riƙe ka da kyau a kan gan iNa

Verse 40 — Surah Ta-Ha 20:40

A sa'ad da 'yar'uwrka ke tafiya har ta ce, shin, in shiryar da ku ga wanda ke renonsa?' Sai Muka mayar da kai zuwa ga uwarka domin idonta ya yi sanyi* kuma ba za ta yi baƙin ciki ba. Kuma ka kashe wani rai, sa'an nan Muka tserar da kai daga baƙin ciki, kuma Muka fitine ka da waɗansu fitinoni. Sa'an nan ka zauna shekaru a cikin mutanen Madyana. Sa'an nan kuma ka zo a kan wata ƙaddara, ya Musa

Verse 41 — Surah Ta-Ha 20:41

Kuma Na zaɓe ka domin Kaina

Verse 42 — Surah Ta-Ha 20:42

Ka tafi kai da ɗan uwanka game da ayoyi Na, kuma kada ku yi rauni ga ambato Na

Verse 43 — Surah Ta-Ha 20:43

Ku tafi ku biyu zuwa ga Fir'auna. Lalle shi ya ƙetare haddi (ga girman kai)

Verse 44 — Surah Ta-Ha 20:44

Sai ku gaya masa magana mai laushi,* tsammaninsa yana tunawa ko kuwa ya ji tsoro

Verse 45 — Surah Ta-Ha 20:45

Su biyu suka ce: "Ya Ubangijinmu! Lalle ne muna tsoron ya yi gaggawa a kanmu, ko ya ƙetare haddi

Verse 46 — Surah Ta-Ha 20:46

Ya ce: "Kada ku ji tsoro. Lalle Ni, Ina tare da ku, Inaji, kuma Ina gani

Verse 47 — Surah Ta-Ha 20:47

Sai ku je masa sa'an nan ku ce, Lalle mu, Manzanni biyune na Ubangijinka, sai ka saki Bani Isra'ila tare da mu. Kuma kada ka yi musu azaba. Haƙiƙa mun zomaka da wata aya daga, Ubangijinka. Kuma aminci ya tabbata ga wanda ya bi shiriya

Verse 48 — Surah Ta-Ha 20:48

Lalle mu, haƙiƙa, an yi wahayi zuwa gare mu, cewa azaba tana a kan wanda ya ƙaryata, kuma ya juya baya

Verse 49 — Surah Ta-Ha 20:49

Ya ce: "To, wane ne Ubangijinku? Ya Musa

Verse 50 — Surah Ta-Ha 20:50

Ya ce: "Ubangijin mu Shi ne wanda Ya bai wa dukan kome halittarsa, sa'an nan Ya shiryar

Verse 51 — Surah Ta-Ha 20:51

Ya ce: "To, mene halin ƙarnonin farko

Verse 52 — Surah Ta-Ha 20:52

Ya ce: "Saninsu yana a wurin Ubangijina, Ubangijina ba Ya ɓacewa kuma ba Ya mantuwa

Verse 53 — Surah Ta-Ha 20:53

Wanda Ya sanya muku ƙasa shimfiɗa, kuma Ya shigar muku da hanyoyi a cikinta, kuma Ya saukar da ruwa daga sama." Sa'an nan game da shi* Muka fitar da nau'i-nau'i daga tsiruruwa dabam-dabam

Verse 54 — Surah Ta-Ha 20:54

Ku ci kuma ku yi kiwon dabbobin ni'imarku. Lalle ne, a cikin wannan akwai ayoyi ga masu hankali

Verse 55 — Surah Ta-Ha 20:55

Daga gare ta* Muka halitta ku, kuma a cikinta Muke mayar da ku, kuma daga gare ta Muke fitar da ku a wani lokaci na dabam

Verse 56 — Surah Ta-Ha 20:56

Kuma lalle, haƙiƙa, Mun nuna masa ayoyin Mu dukansu sai ya ƙaryata, kuma ya ƙiya

Verse 57 — Surah Ta-Ha 20:57

Ya ce: "Shin ka zo mana ne domin ka fitar da mu daga ƙasarmu game da sihirinka, ya Musa

Verse 58 — Surah Ta-Ha 20:58

To, lalle ne muna zo maka da wani sihiri irinsa. Sai ka sanya wani wa'adi a tsakaninmu da tsakaninka ba mu saɓa masa mu kai kuma, ba ka saɓawa, a wani wuri mai dacewa

Verse 59 — Surah Ta-Ha 20:59

Ya ce: "Wa'adinku shi ne ranar ƙawa kuma a tara mutane da hantsi

Verse 60 — Surah Ta-Ha 20:60

Sai Fir'auna ya juya, sa'an nan ya tara mugunyar dabararsa, sa'an nan kuma ya zo

Verse 61 — Surah Ta-Ha 20:61

Musa ya ce musu, "Kaitonku! Kada ku ƙirƙira ƙarya ga Allah har Ya tumɓuke ku da wata azaba. Kuma wanda ya ƙirƙira ƙarya, ya taɓe

Verse 62 — Surah Ta-Ha 20:62

Sai suka yi jayayya ga al'amarinsu a tsakanin su kuma suka asirta ganawa

Verse 63 — Surah Ta-Ha 20:63

Suka ce: "Lalle ne waɗannan biyun, haƙiƙa masihirta ne suna nufin su fitar da ku daga ƙasarku* game da sihirinsu kuma su tafi da tabi'arku mafificiya

Verse 64 — Surah Ta-Ha 20:64

Sai ku haɗa dabararku sa'an nan kuma ku tafi a sahu guda, kuma haƙiƙa, wanda ya rinjaya, a yau, ya rabbanta

Verse 65 — Surah Ta-Ha 20:65

Suka ce: "Ya Musa! Imma ka jefa, ko kuma mu kasance farkon mai jefawa

Verse 66 — Surah Ta-Ha 20:66

Ya ce: "A'a, ku jefa." Sai ga igiyoyinsu da sandunansu ana suranta su a gare shi, daga sihirinsu, lalle suna tafiya da sauri

Verse 67 — Surah Ta-Ha 20:67

Sai Musa ya ji tsoro a cikin ransa

Verse 68 — Surah Ta-Ha 20:68

Muka ce: "Kada ka ji tsoro. lalle kai ne mafi ɗaukaka

Verse 69 — Surah Ta-Ha 20:69

Kuma ka jefa abin da ke a cikin hannun damanka, ta cafe abin da suka aikata. Lalle ne abin da suka aikata makircin masihirci ne kuma masihirci ba ya cin nasara a duk inda ya je

Verse 70 — Surah Ta-Ha 20:70

Sai aka jefar da masihirtan suna masu sujada, suka ce: "Mun yi imani da Ubangijin Haruna da Musa

Verse 71 — Surah Ta-Ha 20:71

Ya ce: "Kun yi imani saboda shi a gabanin in yi muku izni? Lalle shi, haƙiƙa, babbanku ne wanda ya sanar da ku sihirin! To, lalle ne zan kakkatse hannayenku da ƙafafunku a tarnaƙi kuma lalle zan tsire ku a cikin kututturan itacen dabino, kuma lalle za ku sani wanenmu ne mafi tsananin azaba kuma wane ne mafi wanzuwar (azaba)

Verse 72 — Surah Ta-Ha 20:72

Suka ce: "Ba za mu fifita ka ba faufau a kan abin da ya zo mana na hujjoji. Muna rantsuwa da wanda Ya ƙaga halittarmu sai ka hukunta abin da kake mai hukuntawa, ai kana ƙare wannan rayuwar duniya kawai ne

Verse 73 — Surah Ta-Ha 20:73

Lalle mu, mun yi imani da Ubangijinmu domin Ya gafarta mana laifuffukanmu da abin da ka tilasta mu a kansa na sihiri. Kuma Allah ne Mafi alheri, kuma Mafi wanzuwa

Verse 74 — Surah Ta-Ha 20:74

Lalle* shi wanda ya je wa Ubangijinsa yana mai laifi, to lalle ne yana da Jahannama, ba ya mutuwa a cikinta kuma ba ya rayuwa

Verse 75 — Surah Ta-Ha 20:75

Kuma wanda ya je Masa yana mai imani, alhali kuwaya aikata aikin ƙwarai to waɗannan suna da darajoji maɗaukaka

Verse 76 — Surah Ta-Ha 20:76

Gidajen Aljannar zama koguna na gudana daga ƙarƙashinsu, suna madawwama a cikinsu. Kuma wannan ne sakamakon wanda ya tsarkaku

Verse 77 — Surah Ta-Ha 20:77

Kuma lalle ne haƙiƙa Mun yi wahayi zuwa ga Musa cewa, "Ka yi tafiyar dare da bayiNa. Sa'an nan ka doka musu hanya a cikin teku tana ƙeƙasasshiya, ba ka tsoron riska, kuma ba ka fargabar nutsewa

Verse 78 — Surah Ta-Ha 20:78

Sai Fir'auna ya bi su game da rundunarsa. Sai abin da ya rufe su daga teku ya rufe su

Verse 79 — Surah Ta-Ha 20:79

Kuma Fir'auna ya ɓatar da mutanensa, kuma bai shiryar (dasu) ba

Verse 80 — Surah Ta-Ha 20:80

Ya Bani Isra'ila! Lalle Mun tserar da ku daga maƙiyinku, kuma mun yi muku wa'adi a gefen Dutsen nan na dama, kuma Mun sassaukar da darɓa da tattabaru dominku

Verse 81 — Surah Ta-Ha 20:81

Ku ci daga masu daɗin abin da Muka azurta ku kuma kada ku ƙetare haddi a cikinsa har fushi Na ya sauka a kanku. Kuma wanda fushi Na ya sauka a kansa, to, lalle ne, ya faɗi

Verse 82 — Surah Ta-Ha 20:82

Kuma lalle Ni haƙiƙa Mai gafara ne ga wanda ya tuba kuma ya yi imani, kuma ya aikata aikin ƙwarai, sa'an nan kuma ya nemi shiryuwa

Verse 83 — Surah Ta-Ha 20:83

Kuma mene ne ya gaggautar* da kai ga barin mutanenka? Ya Musa

Verse 84 — Surah Ta-Ha 20:84

Ya ce: "Su ne waɗannan a kan sawuna, kuma na yi gaggawa zuwa gare Ka, ya Ubangiji! Domin Ka yarda

Verse 85 — Surah Ta-Ha 20:85

Ya ce: "To, lalle ne, haƙiƙa, Mun fitini, mutanenka daga bayanka, kuma samiri ya ɓatar da su

Verse 86 — Surah Ta-Ha 20:86

Sai Musa ya koma zuwa ga mutanensa yana mai hushi, mai baƙin ciki, ya ce: "Ya mutanena! shin, Ubangijinku bai yi muku wa'adi ba, wa'adi mai kyau? Shin, lokacin ya yi tsawo a kanku ne, ko kun yi nufi ne wani hushi ya sauka a kanku daga Ubangijinku, saboda haka kuka saɓa wa alkawarina

Verse 87 — Surah Ta-Ha 20:87

Suka ce: "Ba mu saɓa wa alkawarinka* ba da ikonmu kuma amma an ɗora mana waɗansu kaya masu nauyi daga abin ƙawar mutanen ne, sai muka jefar da su. Sa'an nan kamar haka ne samiri ya jefa

Verse 88 — Surah Ta-Ha 20:88

Sai ya fitar musu da wani maraƙi, jikin mutane, yana ruri, sa'an nan suka ce: wannan ne gunkinku kuma gunkin Musa, sai ya manta

Verse 89 — Surah Ta-Ha 20:89

Shin, to, ba su ganin cewaba ya mayar musu da magana, kuma ba ya mallakar wata cuta a gare su, kuma ba ya mallakar amfani

Verse 90 — Surah Ta-Ha 20:90

Kuma, haƙiƙa, Haruna ya ce musu daga gabani, "Ya mutanena! Lalle an fitine ku da shi ne kawai. Kuma lalle Ubangijinku Mai rahama ne, sai ku bi ni, kuma ku yi ɗa'a ga umarnina

Verse 91 — Surah Ta-Ha 20:91

Suka ce ba zamu gushe ba muna bauta a gareshi ba har sai Musa dawo

Verse 92 — Surah Ta-Ha 20:92

(Musa) ya ce: "Ya Haruna! Me ya hane ka, sa'ad da kagan su sun ɓace

Verse 93 — Surah Ta-Ha 20:93

Ba ka bi ni ba! Shin, to, ka saɓa wa umarnina ne

Verse 94 — Surah Ta-Ha 20:94

(Haruna) ya ce: "Ya ɗan'uwana! Kada ka yi kamu ga gemuna ko ga kaina. Lalle ni, na ji tsoron ka ce: Ka rarraba a tsakanin Bani Isra'ila kuma ba ka tsare maganata ba

Verse 95 — Surah Ta-Ha 20:95

(Musa) ya ce: "Mene ne babban al'amarinka? Kai Samiri

Verse 96 — Surah Ta-Ha 20:96

(Samiri) ya ce: "Na ga abin da ba su gan shi ba shi, sai na yi damƙa, damƙa guda daga kufan sawun Manzon, sa'an nan na jefa ta. Kuma haka dai raina ya ƙawata mini

Verse 97 — Surah Ta-Ha 20:97

(Musa) ya ce: "To, ka tafi, saboda haka lalle ne kana da a cikin rayuwarka, ka ce 'Babu shafa' kuma kana da wani ma'alkawarta, ba za a saɓa maka gare ta ba. Kuma ka duba zuwa ga gunkinka wanda ka yini a kansa kana mai lazimta. Lalle ne muna ƙone shi,* sa'an nan kuma muna sheƙe shi, a cikin teku, sheƙewa

Verse 98 — Surah Ta-Ha 20:98

Abin sani kawai abin bautawarku Allah kawai ne wanda babu wani abin bautawa, face Shi kuma Ya yalwaci* dukkan kome da ilmi

Verse 99 — Surah Ta-Ha 20:99

Kamar wancan ne Muke labartawa* a gare ka, daga labaran abin da ya gabata, alhali kuwa haƙiƙa, Mun ba ka zikiri (Alƙur'ani) daga gun Mu

Verse 100 — Surah Ta-Ha 20:100

Wanda ya kau da kai daga gare shi, to, lalle shi, yana ɗaukar wani nauyi a Ranar ¡iyama

Verse 101 — Surah Ta-Ha 20:101

Suna madawwama a cikinsa, kuma ya munana ya zama abin ɗauka, a Ranar ¡iyama

Verse 102 — Surah Ta-Ha 20:102

A Ranar da ake hurawa a cikin ƙaho kuma Muna tara masu laifi, a ranar nan, suna masu shuɗayen idanu

Verse 103 — Surah Ta-Ha 20:103

Suna ɓoye magana a tsakaninsu, (Suna ce wa juna) "Ba ku zauna ba (a cikin duniya) face kwana goma

Verse 104 — Surah Ta-Ha 20:104

Mu ne mafi sani ga abin da suke faɗa a sa'ad da mafificinsu ga hanya ke cewa, "Ba ku zauna ba face a yini guda

Verse 105 — Surah Ta-Ha 20:105

Kuma suna tambayar ka daga duwatsu* sai ka ce: "Ubangijina Yana sheƙe su sheƙewa

Verse 106 — Surah Ta-Ha 20:106

Sa'an nan Yana barin (wurinsu) faƙo mai santsi

Verse 107 — Surah Ta-Ha 20:107

Ba ka ganin karkata a cikinsa, kuma ba ka ganin wani tudu

Verse 108 — Surah Ta-Ha 20:108

A ranar nan suna biyar mai kira, babu karkata a gare shi, kuma sautuka suka yi kawaici ga Mai rahama, ba ka sauraren kome face sautin tafiya

Verse 109 — Surah Ta-Ha 20:109

A yinin nan ceto ba ya yin amfani face wanda Mai rahama Ya yi masa izni kuma Ya yarda da shi, da ya yi magana

Verse 110 — Surah Ta-Ha 20:110

Yana sanin* abin da ke a gaba gare su da abin da ke bayansu, kuma ba su kewayewa da shi ga sani

Verse 111 — Surah Ta-Ha 20:111

Kuma fuskoki suka ƙanƙan da kai ga Rayayye, Tsayayye, alhali kuwa wanda ya ɗauko wani zalunci ya taɓe

Verse 112 — Surah Ta-Ha 20:112

Kuma wanda ya aikata wani abu daga ayyukan ƙwarai alhali kuwa yana mai imani, to, ba ya tsoron wani zalunci ko wata naƙasa

Verse 113 — Surah Ta-Ha 20:113

Kuma haka Muka saukar da shi, Alƙur'ani, yana abin karantawa, da Larabci kuma Muka jujjuya misalai, a cikinsa, na tsoratarwa, tsammaninsu, suna yin taƙawa ko ya sabbaba musu wata wa'aztuwa

Verse 114 — Surah Ta-Ha 20:114

Sa'an nan Allah Mamallaki, Tabbatacce Ya ɗaukaka. Kuma kada ka yi gaggawa* da Alƙur'ani a gabanin a ƙare wahayinsa zuwa gare ka. Kuma ka ce: "Ya Ubangiji! Ka ƙara mini ilmi

Verse 115 — Surah Ta-Ha 20:115

Kuma lalle, haƙiƙa, Mun yi alkawari zuwa ga Adamu a gabanin wannan, sai ya manta, kuma ba Mu sami ƙarfin zuciya a gare shi ba

Verse 116 — Surah Ta-Ha 20:116

Kuma sa'ad da Muka ce wa mala'iku, "Ku yi sujada ga Adamu." Sai suka yi sujada, face Iblisa, ya ƙiya

Verse 117 — Surah Ta-Ha 20:117

Sai Muka ce: "Ya Adamu! Lalle ne wannan maƙiyi* ne gare ka da kuma ga matarka, saboda haka kada ya fitar da ku daga Aljanna har ku wahala

Verse 118 — Surah Ta-Ha 20:118

Lalle ne ka samu ba za ka ji yunwa ba a cikinta, kuma ba za ka yi tsiraici ba

Verse 119 — Surah Ta-Ha 20:119

Lalle kai, ba za ka ji ƙishirwa ba, kuma ba za ka shiga hantsi ba

Verse 120 — Surah Ta-Ha 20:120

Sai shaiɗan ya sanya waswasi zuwa gare shi, ya ce: "Ya Adamu! Shin, in shiryar da kai ga itaciyar dawwama da mulki wanda ba ya ƙarewa

Verse 121 — Surah Ta-Ha 20:121

Sai suka ci daga gare ta, saboda haka al'aurunsu suka bayyana, kuma suka shiga suna lulluɓawa a kansu daga ganyen Aljanna. Kuma Adamu ya saɓa wa Ubangijinsa, saboda haka ya ɓace

Verse 122 — Surah Ta-Ha 20:122

Sa'an nan kuma Ubangjinsa Ya zaɓe shi, Ya karɓi tuba gare shi, kuma Ya shiryar (da shi)

Verse 123 — Surah Ta-Ha 20:123

Ya ce: "Ku sauka ku biyu daga gare ta gaba ɗaya, sashenku yana maƙiyi ga sashe. To, imma dai wata shitiya ta je muku daga gare Ni, to, wanda ya bi shiryarwata, to, ba ya ɓacewa, kuma ba ya wahala

Verse 124 — Surah Ta-Ha 20:124

Kuma wanda ya bijire* daga ambatoNa (Alƙur'ani) to, lalle ne rayuwa mai ƙunci ta tabbata a gare shi, kuma Muna tayar da shi a Ranar ¡iyama yana makaho

Verse 125 — Surah Ta-Ha 20:125

Ya ce: "Ya Ubangiji! Don me Ka tayar da ni makaho alhali kuwa na kasance mai gani

Verse 126 — Surah Ta-Ha 20:126

Ya ce: "Kamar wancan ne ayoyin Mu suka je maka sai ka mance su, kuma kamar hakar a yau ake mance ka

Verse 127 — Surah Ta-Ha 20:127

Kuma kamar haka Muke saka wa wanda ya yawaita,* kuma bai yi imani da ayoyin Ubangijinsa ba. Kuma lalle ne azabar Lahira ce mafi tsanani, kuma mafi wanzuwa

Verse 128 — Surah Ta-Ha 20:128

Shin, to, bai shiryar da su ba cewa da yawa Muka halakarda (kafirai) daga ƙarnuka, a gabaninsu, suna tafiya a cikin masaukansu? Lalle ne, a cikin wancan akwai ayoyi ga masu hankula

Verse 129 — Surah Ta-Ha 20:129

Kuma ba domin wata kalma ba wadda ta gabata daga Ubangijinka, da kuma ajali ambatacce haƙiƙa, da azabarta kasance mai lazimta

Verse 130 — Surah Ta-Ha 20:130

Sai ka yi haƙuri* a kan abin da suke cewa, kuma ka yi tasbihi da gode wa Ubangijinka a gabanin fitowar rana da gabanin ɓacewarta, kuma daga sa'o'in dare sai ka yi tasbihi da sasannin yini, tsammaninka za ka sami yarda

Verse 131 — Surah Ta-Ha 20:131

Kuma kada ka miƙar da idanunka zuwa ga abin da Muka jiyar da su daɗi da shi, nau'i-nau'i daga gare su, kamar huren rayuwar duniya yake, domin Mu fitine su a cikin sa, alhali kuwa arzikin Ubangijinka, ne mafi alheri kuma mafi wanzuwa

Verse 132 — Surah Ta-Ha 20:132

Kuma ka umurci iyalanka da salla, kuma ka yi haƙuri a kanta. Ba Mu tambayar ka wani Arziki Mu ne Muke azurta ka. Kuma aƙiba mai kyau tana ga taƙawa

Verse 133 — Surah Ta-Ha 20:133

Kuma suka ce: "Don me ba ya zo mana da wata aya daga Ubangijinsa?" Shin, kuwa hujjar abin da ke a cikin littattafan farko, ba ta je musu ba

Verse 134 — Surah Ta-Ha 20:134

Kuma da dai Mun halaka su da wata azaba daga gabaninsa, lalle ne da sun ce: "Ya Ubangijinmu! Da Ka aiko da wani Manzo zuwa gare mu har mu bibiyi ayoyinKa daga gabanin mu ƙasƙanta, kuma mu wulakantu

Verse 135 — Surah Ta-Ha 20:135

Ka ce: "Kowa mai tsumaye ne. Sai ku yi tsumaye. Sa'an nan za ku san su wa ne ma'abuta tafarki madaidaici, kuma wane ne ya nemi shiryuwa