Back to LanguagesPrevious ChapterNext Chapter
Hausa - Chapter 19 - Maryam
Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink
Verse 1 — Surah Maryam 19:1
K.H. Y.I. S
Verse 2 — Surah Maryam 19:2
Ambaton rahamar Ubangijinka ne ga BawanSa Zakariyya
Verse 3 — Surah Maryam 19:3
A lokacin da ya kirayi Ubangijinsa, kira ɓoyayye
Verse 4 — Surah Maryam 19:4
Ya ce: "Ya Ubangijina! Lalle ne ni, ƙashi na daga gare ni ya yi rauni, kuma kaina ya kunnu da furfura, kuma ban kasance marashin arziki ba game da kiranKa, ya Ubangiji
Verse 5 — Surah Maryam 19:5
Kuma lalle ni, na ji tsoron* dangi a bayana, kuma matata ta kasance bakarariya! Sai ka ba ni wani mataimaki daga wajenKa
Verse 6 — Surah Maryam 19:6
Ya gaje ni, kuma ya yi gado daga gidan Yaƙuba. Kuma Ka sanya shi yardajje, ya Ubangiji
Verse 7 — Surah Maryam 19:7
(Allah Ya karɓa) "Ya zakariyya! Lalle ne Mu, Muna yi maka bushara da wani yaro, sunansa Yahaya. Ba Mu sanya masa wani takwara ba a gabani
Verse 8 — Surah Maryam 19:8
Ya ce: "Ya Ubangijina! Yaya wani yaro zai kasance a gare ni, alhali kuwa matata ta kasance bakarariya, kuma ga shi na kai ga matuƙa ta tsufa
Verse 9 — Surah Maryam 19:9
Ya ce: "Kamar wancan Ubangijinka Ya ce. Shi, a gare Ni mai sauƙi ne, kuma haƙiƙa Na halitta ka a gabanin haka, alhali ba ka kasance kome ba
Verse 10 — Surah Maryam 19:10
Ya ce: "Ya Ubangijina! Ka sanya mini alama." Ya ce: "Alamarka ita ce ka kasa yi wa mutane magana a daruruwa uku daidai
Verse 11 — Surah Maryam 19:11
Sai ya fita ga mutanensa daga masallaci, sa'an nan ya yi ishara zuwa gare su da cewa, "Ku yi tasbihi safe da yamma
Verse 12 — Surah Maryam 19:12
Ya kai Yahaya! Ka kama littafi da ƙarfi. Kuma Muka ba shi hukunci yana yaro
Verse 13 — Surah Maryam 19:13
Kuma (Muka sanya shi) abin girmamawa daga gun Mu, kuma mai albarka, kuma ya kasance mai ɗa'a da taƙawa
Verse 14 — Surah Maryam 19:14
Kuma mai biyayya ga mahaifan sa biyu, kuma bai kasance mai girman kai mai saɓo ba
Verse 15 — Surah Maryam 19:15
Kuma aminci ya tabbata a gare shi a ranar da aka haife shi da ranar da yake mutuwa da ranar da ake tayar da shi yana mai rai
Verse 16 — Surah Maryam 19:16
Kuma ka ambaci Maryamu* a cikin Littafi, a lokacin da ta tsallake daga mutanenta a wani wuri, a gefen gabas
Verse 17 — Surah Maryam 19:17
Sa'an nan ta riƙi wani shamaki daga barinsu. Sai Muka aika ruhinMu zuwa gare ta. Sai ya bayyana a gare ta da siffar mutum madaidaci
Verse 18 — Surah Maryam 19:18
Ta ce: "Lalle ni ina neman tsari ga Mai, rahama daga gare ka, idan ka kasance mai tsaron addini
Verse 19 — Surah Maryam 19:19
Ya ce: "Abin sani kawai, ni Manzon Ubangijinki ne domin in bayar da wani yaro tsarkakke gare ki
Verse 20 — Surah Maryam 19:20
Ta ce: "A ina yaro zai kasance a gare ni alhali kuwa wani mutum bai shafe ni ba, kuma ban kasance karuwa ba
Verse 21 — Surah Maryam 19:21
Ya ce: "Kamar wancan Ubangijinki Ya ce. Shi, a gare Ni mai sauƙi* ne. Kuma domin Mu sanya shi wata alama ga mutane, kuma wata rahama ce daga gare Mu.' Kuma abin ya kasance wani al'amari hukuntacce
Verse 22 — Surah Maryam 19:22
Sai ta yi cikinsa, sai ta tsallake da shi ga wani wuri mai nisa
Verse 23 — Surah Maryam 19:23
Sai naƙuda ta kai ta zuwa ga wani kututturen dabiniya, ta ce "Kaitona, da dai na mutu a gabanin wannan kuma na kasance wani abu wulakantacce wanda aka manta
Verse 24 — Surah Maryam 19:24
Sai (yaron da ta haifa) ya* kira ta daga ƙarƙashinta, "Kada ki yi baƙin ciki! Haƙiƙa Ubangijinki Ya sanya wani marmaro a ƙarƙashinki
Verse 25 — Surah Maryam 19:25
Kuma ki girgiza zuwa gare ki game da kututturen dabinon ya zuba a kanki yana 'ya'yan dabino, ruɗabi nunannu
Verse 26 — Surah Maryam 19:26
Sai ki ci kuma ki sha kuma ki ji sanyi ga idanunki*. To, idan kin ga wani aya daga mutane, sai ki ce, 'Lalle ni, na yi alwashin azumi domin Mai rahama saboda haka ba zan yi wa wani mutum magana ba
Verse 27 — Surah Maryam 19:27
Sai ta je wa mutanenta tana auke da shi. Suka ce: "Ya Maryamu! Lalle ne, haƙiƙa kin zo da wani abu mai girma
Verse 28 — Surah Maryam 19:28
Ya 'yar'uwar Haruna! Ubanki bai kasance mutumin alfasha ba, kuma uwarki ba ta kasance karuwa ba
Verse 29 — Surah Maryam 19:29
Sai ta yi ishara zuwa gare shi, suka ce: "Yaya za mu yi magana da wanda ya kasance a cikin shimfiar tsumma yana jariri
Verse 30 — Surah Maryam 19:30
Ya ce: "Lalle ne, ni bawan Allah ne Allah Ya ba ni Littafi kuma Ya sanya ni Annabi
Verse 31 — Surah Maryam 19:31
Kuma Ya sanya ni mai albarka a inda duk na kasance kuma Ya umurce ni da yin salla da zakka matuƙar ina da rai
Verse 32 — Surah Maryam 19:32
Kuma mai biyayya ga uwata, kuma bai sanya ni mai kaushin zuciya ba marashin alheri
Verse 33 — Surah Maryam 19:33
Kuma aminci ya tabbata a gare ni a ranar da aka haife ni da ranar da nake mutuwa da ranar da ake tayar da ni ina mai rai
Verse 34 — Surah Maryam 19:34
Wancan ne Isa ɗan Maryamu, maganar gaskiya wadda suke shakka a cikinta
Verse 35 — Surah Maryam 19:35
Ba ya kasancewa ga Allah Ya riƙi wani ɗa*. Tsarki ya tabbata a gare shi! Idan Ya hukunta wani al'amari sai kawai Ya ce masa, "Kasance." Sai ya dinga kasan cewa
Verse 36 — Surah Maryam 19:36
Kuma lalle Allah ne Ubangijina* kuma Ubangijinku, sai ku bauta Masa. Wannan shi ne tafarki madaidaici
Verse 37 — Surah Maryam 19:37
Sai ƙungiyoyin* suka saɓa wa juna a tsakanins u. To, bone ya tabbata ga waɗanda suka kafirta daga halartar yini mai girma
Verse 38 — Surah Maryam 19:38
Mene ne ya yi jinsu*, kuma mene ne ya yi ganinsu a ranar da suke zo Mana! Amma azzalumai suna a cikin ɓata bayyananna
Verse 39 — Surah Maryam 19:39
Kuma ka yi musu gargaɗi da ranar nadama a lokacin da aka hukunta al'amari alhali kuwa suna a cikin ɓata, kuma su ba su yin imani
Verse 40 — Surah Maryam 19:40
Lalle ne Mu, Mu ne ke gadon ƙasa* da wanda yake a kanta, kuma zuwa gare Mu ake mayar da su
Verse 41 — Surah Maryam 19:41
Kuma ambaci Ibrahim* a cikin Littafi. Lalle shi ya kasance mai yawan gaskatawa, Annabi
Verse 42 — Surah Maryam 19:42
A lokacin da ya ce wa ubansa, "Ya baba! Don me kake bauta wa abin da ba ya ji, kuma ba ya ga ni, kuma ba ya wadatar da kome daga barinka
Verse 43 — Surah Maryam 19:43
Ya baba! Lalle ni, haƙiƙa abin da bai je maka ba na ilmi ya zo mini, saboda haka ka bi ni in shiryar da kai wani tafarki madaidaici
Verse 44 — Surah Maryam 19:44
Ya baba! Kada ka bauta wa Shaiɗan. Lalle Shaiɗan ya kasance mai saɓawa ga Mai rahama
Verse 45 — Surah Maryam 19:45
Ya baba! Lalle ne ni ina tsoron wata azaba daga Mai rahama ta shafe ka, har ka zama masoyi ga Shaiɗan
Verse 46 — Surah Maryam 19:46
Ya ce: "Ashe, mai gudu ne kai daga gumakana? Ya Ibraim! Lalle ne, idan ba ka hanu ba, haƙi ƙa, zan jefe ka. Kuma ka ƙaurace mini tun kana mai mutunci
Verse 47 — Surah Maryam 19:47
Ya ce: "Aminci ya tabbata a gare ka! zan nemi Ubangijina Ya gafarta maka.* Lalle Shi Ya kasance Mai girmamawa gare ni
Verse 48 — Surah Maryam 19:48
Kuma ina nisantar ku da abin da kuke kira, baicin Allah kuma ina kiran Ubangijina, tsammanin kada in zama marashin arziki game da kiran Ubangijina
Verse 49 — Surah Maryam 19:49
To, sa'ad da ya nisance su da abin da suke bautawa baicin Allah, Muka ba shi Is'haƙa da Ya'aƙuba alhali kuwa kowanensu Mun mayar da shi Annabi
Verse 50 — Surah Maryam 19:50
Kuma Muka yi musu kyauta daga Rahamar Mu, kuma Muka sanya musu harshen gaskiya* maɗaukaki
Verse 51 — Surah Maryam 19:51
Kuma ka ambaci Musa a cikin Littafi. Lalle ne shi, ya kasance zaɓaɓɓe, kuma ya kasance Manzo, Annabi
Verse 52 — Surah Maryam 19:52
Kuma Muka kira shi daga gefen dutse na dama kuma Muka kusanta shi yana abokin ganawa
Verse 53 — Surah Maryam 19:53
Kuma Muka yi masa kyauta daga Rahamar Mu da ɗan'uwan sa Haruna, ya zama Annabi
Verse 54 — Surah Maryam 19:54
Kuma ka ambaci Isma'ila a cikin Littafi. Lalle shi, ya kasance mai gaskiyar alkawari, kuma ya kasance Manzo, Annabi
Verse 55 — Surah Maryam 19:55
Kuma ya kasance yana umurnin mutanens *da salla da zakka. Kuma ya kasance yardajje a wurin Ubangijinsa
Verse 56 — Surah Maryam 19:56
Kuma ka ambaci Idrisa a cikin Littafi. Lalle shi, ya kasance mai yawan gaskatawa, Annabi
Verse 57 — Surah Maryam 19:57
Muka ɗaukaka shi a wuri maɗaukaki
Verse 58 — Surah Maryam 19:58
Waɗancan su ne waɗanda Allah Ya yi wa ni'ima daga Annabawa daga zurriyar Adamu, kuma daga waɗanda muka ɗauka tare da Nuhu, kuma daga zurriyar Ibrahim da Isra'ila, kuma daga waɗanda Muka shiryar kuma Muka zaɓe su. Idan ana karatun ayoyin Mai rahama a kansu, sai su faɗi suna masu sujada kuma masu kuka
Verse 59 — Surah Maryam 19:59
Sai waɗansu 'yan baya* suka maye a bayansu suka tozarta salla, kuma suka bi sha'awowinsu. To, da sannu za su hau da wani sharri
Verse 60 — Surah Maryam 19:60
Face wanda ya tuba, kuma ya yi imani, kuma ya aikata aiki na ƙwarai. To, waɗannan suna shiga Aljanna, kuma ba a zaluntar su da kome
Verse 61 — Surah Maryam 19:61
Gidajen Aljannar zama wadda Mai rahama ya yi alkawarin bayarwa ga bayinSa (masu aikin imani) a fake. Lalle ne shi, alkawarin ya kasance abin riskuwa
Verse 62 — Surah Maryam 19:62
Ba su jin yasassar magana a cikinta, face sallama. Kuma suna da abinci, a cikinta, safe da maraice
Verse 63 — Surah Maryam 19:63
Wancan Aljannar ce wadda Muke gadar da wanda ya kasance mai aiki da taƙawa daga bayiNa
Verse 64 — Surah Maryam 19:64
(Suna masu cewa) "Kuma ba mu sauka* Face da umuruin Ubangijinka (Muhammad). Shi ne da mulkin abin da ke a gaba gare mu da abin da ke a bayanmu da abin da ke a tsakanin wannan." Kuma** (Ubangijinka bai kasance wanda ake mantawa ba)
Verse 65 — Surah Maryam 19:65
Shi ne Ubangijin sammai da ƙasa da abin da yake a tsakanin su. sai ka bauta Masa, kuma ka yi haƙuri ga bautar sa. Shin ka san wani takwara a gare shi
Verse 66 — Surah Maryam 19:66
Kuma mutum yana cewa, "Shin idan na mutu lalle ne haƙi ƙa da sannu za a fitar da ni ina mai rai
Verse 67 — Surah Maryam 19:67
Shin, kuma mutum ba zai tuna ba cewa lalle ne Mun halitta shi a gabani, alhali kuwa bai kasance kome ba
Verse 68 — Surah Maryam 19:68
To, Muna rantsuwa da Ubangijin ka, lalle ne, Muna tayar da su da kuma shaianun sa'an nan, kuma lalle Muna halatar da su da kuma Shaiɗanun sa'an nan, kuma, lalle Muna halatar da su a gefen Jahannama suna gurfane
Verse 69 — Surah Maryam 19:69
Sa'an nan kuma lalle Muna fizge wanda yake mafi tsananin girman kai ga Mai rahama daga kowace ƙungiya
Verse 70 — Surah Maryam 19:70
Sa'an nan kuma lalle Mu ne Mafi sani ga waɗan da suke su ne mafiya cancantar ƙonuwa da ita
Verse 71 — Surah Maryam 19:71
Kuma babu kowa daga gare ku sai mai tuzga mata.* Ya kasance wajibi ga Ubangijinka, hukuntacce
Verse 72 — Surah Maryam 19:72
Sa'an nan kuma Mu tserar da waɗanda suka yi aiki da taƙawa, kuma Mu bar azzalumai a cikinta gurfane
Verse 73 — Surah Maryam 19:73
Kuma idan ana karatun ayoyinMu, bayyanannu a kansu, sai waɗanda suka kafirta su ce wa waɗanda suka yi imani, "Wanne daga ƙungiyoyin biyu ya fi zama mafi alheri ga matsayi, kuma mafi kyaun majalisa
Verse 74 — Surah Maryam 19:74
Kuma da yawa daga mutanen ƙarni Muka halakar a gabaninsu su (waɗandaMuka halakar) in ne mafi kyaun kayan aki da magana
Verse 75 — Surah Maryam 19:75
Ka ce: "Wanda ya kasance a cikin ɓata sai Mai rahama Ya yalwata masa yalwatawa, har idan sun ga abin da ake yi musu wa'adi, imma azaba ko sa'a, to za su sani, wane ne yake shi ne, mafi sharri ga wuri, kuma mafi rauni ga runduna
Verse 76 — Surah Maryam 19:76
Kuma Allah na ƙara wa wa ɗanda suka nemi shiryuwa da shiriya. Kuma ayyuka masu wanzuwa na ƙwarai ne mafi alheri awurin Ubangijinka ga lada, kuma mafi alheri ga makoma
Verse 77 — Surah Maryam 19:77
Shin, ka ga wanda ya kafirta da ayoyinMu, kuma ya ce: "Lalle ne za a ba ni dukiya da ɗiya
Verse 78 — Surah Maryam 19:78
Shin, ya tsinkayi gaibi ne, ko kuwa ya ɗauki wani alkawari daga Mai rahama ne
Verse 79 — Surah Maryam 19:79
A'aha! za mu rubuta abin da yake faɗa, kuma Mu yalwata masa, daga azaba, yalwatawa
Verse 80 — Surah Maryam 19:80
Kuma Mu gade shi ga abin da yake faɗa, kuma ya zo Mana yana shi kɗai
Verse 81 — Surah Maryam 19:81
Kuma suka riƙi gumaka,* baicin Allah, domin su kasance mataimaka a gare su
Verse 82 — Surah Maryam 19:82
A'aha! Za su kafirta da ibadarsu, kuma su kasance maƙiya a kansu
Verse 83 — Surah Maryam 19:83
Shin, ba ka gani ba cewa Mun saki shaiɗanu* a kan kafirai suna shushuta su ga zunubi shushutawa
Verse 84 — Surah Maryam 19:84
Saboda haka kada ka yi gaggawa a kansu, Muna yi musu ƙidayar Ajali ne kawai, ƙidayawa
Verse 85 — Surah Maryam 19:85
A ranar da Muka tara masu taƙawa zuwa ga Mai rahama suna baƙin girma
Verse 86 — Surah Maryam 19:86
Kuma Muna kora masu laifi zuwa Jahannama, gargaawa
Verse 87 — Surah Maryam 19:87
Ba su malakar ceto face wanda ya riƙi alkawari a wurin Mai rahama
Verse 88 — Surah Maryam 19:88
Kuma suka ce: "Mai rahama Ya riƙi a
Verse 89 — Surah Maryam 19:89
Lalle ne haƙiƙa kun zo da wani abu mai girman muni
Verse 90 — Surah Maryam 19:90
Sammai suna kusa su tsattsage saboda shi, kuma ƙasa ke kece kuma duwatsu su faɗi suna karyayyu
Verse 91 — Surah Maryam 19:91
Domin sun yi da'awar ɗa ga Mai rahama
Verse 92 — Surah Maryam 19:92
Alhali ba ya kamata ga Mai rahama ya riƙi wani ɗa
Verse 93 — Surah Maryam 19:93
Dukkan wanda yake a cikin sammai da ƙasa bai zama ba face mai je wa Mai rahama ne yana bawa
Verse 94 — Surah Maryam 19:94
Lalle ne haƙiƙa Ya lissafe su, kuma ya ƙidaye su, ƙidaya
Verse 95 — Surah Maryam 19:95
Kuma dukan kowanensu mai je Masa ne a Ranar ¡iyama yana shi kaɗai
Verse 96 — Surah Maryam 19:96
Lalle ne waɗanda suka yi imani, kuma suka aikata ayyuka na ƙwarai, Mai rahama zai sanya musu so
Verse 97 — Surah Maryam 19:97
Sa'an nan Ibin sani kawai Mun sauƙaƙar da shi (Alƙur'ani) a harshenka, domin ka yi bushara da shi ga masu aiki da taƙawa kuma ka yi gargaɗi da shi ga mutane masu tsananin husuma
Verse 98 — Surah Maryam 19:98
Kuma da yawa Muka halakar da mutanen ƙarnoni a gabaninsu. Shin kana jin motsin wani guda daga gare su, ko kuwa kana jin wata ɗuriya tasu