Back to Languages

Hausa - Chapter 22 - Al-Hajj

Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink

Verse 1 — Surah Al-Hajj 22:1

Ya ku mutane! Ku bi Ubangijinku da taƙawa. Lalle ne girgizar* ƙasa ta tsayuwar Sa'a wata aba ce mai girma

Verse 2 — Surah Al-Hajj 22:2

A ranar da kuke ganin ta dukan mai shayar da mama tana shagala daga abin da ta shayar, kuma dukan mai ciki tana haihuwar cikinta, kuma kana ganin mutane suna masu maye alhali kuwa su ba masu maye ba, amma azabar Allah ce mai tsanani

Verse 3 — Surah Al-Hajj 22:3

Akwai daga mutane* wanda yake yin musu ga sha'anin Allah ba da wani ilmi ba, kuma yana biyar kowane Shaiɗan mai taurin kai

Verse 4 — Surah Al-Hajj 22:4

An wajabta masa cewa wanda ya jiɓince shi, to, lalle ne sai ya ɓatar da shi, kuma ya shiryar da shi zuwa ga azabar sa'ir

Verse 5 — Surah Al-Hajj 22:5

Ya ku mutane! Idan kun kasance a cikin shakka a Tashin ¡iyama, to, lalle ne Mu, Man halittaku daga turɓaya, sa'an nan kuma daga gudajin jini, sa'an nan kuma daga taoka wadda ake halittawa da wadda ba a halittawa domin, Mu bayyana muku. Kuma Muna tab batar da abin da Muke so a cikin mahaifa zuwa ga wani ajali ambatacce, sa'an nan kuma Muna fitar da ku kuna jariri, sa'an nan kuma domin ku kai ga cikar ƙarfinku. Kuma daga cikin ku akwai wanda ke mutuwa, kuma daga gare ku akwai wanda ake mayarwa zuwa ga mafi ƙasƙancin rayuwa domin kada ya san kome a bayan ya sani. Kuma kana ganin ƙasa shiru, sa'an nan idan Muka saukar da ruwa a kanta, sai ta girgiza kuma ta kumbura, kuma ta tsirar da tsirrai daga kowane nau'i mai ban sha'awa

Verse 6 — Surah Al-Hajj 22:6

Wancan ne domin lalle Allah Shi ne Gaskiya, kuma lalle ne shi Yake rayar da matattu, kuma lalle Shi Mai ikon yi ne a kan kome

Verse 7 — Surah Al-Hajj 22:7

Kuma lalle ne Sa'ar Tashin alkiiyama mai zuwa ce, babu shakka a cikinta kuma lalle ne Allah Yana tayar da waɗanda suke a cikin ƙaburbura

Verse 8 — Surah Al-Hajj 22:8

Kuma daga mutane akwai mai yin musu* ga Allah ba da wani ilmi ba kuma ba da wata shiriya ba, kuma ba da wani littafi mai haskakawa ba

Verse 9 — Surah Al-Hajj 22:9

Yana mai karkatar da sashensa domin ya ɓatar (da wasu) daga tafarkin Allah! Yana da wani wulakanci a duniya, kuma Muna ɗanɗana masa azabar gobara a Ranar ¡iyama

Verse 10 — Surah Al-Hajj 22:10

(A ce masa): "Wancan azaba saboda abin da hannayenka biyu suka gabatar ne, kuma lalle ne Allah bai zama Mai zalunci ga bayinSa ba

Verse 11 — Surah Al-Hajj 22:11

Kuma daga mutane akwai mai bauta* wa Allah a kan wani gefe. Sa'an nan idan wani alheri ya same shi, sai ya natsu da shi, kuma idan wata fitina ta same shi, sai ya juya baya a kan fuskarsa. Ya yi hasarar duniya da Lahira. Waccan ita ce hasara bayyananna

Verse 12 — Surah Al-Hajj 22:12

Yana kiran baicin Allah, abin da ba ya cutarsa da abin da ba ya amfaninsa! waccan ita ce ɓata mai nisa

Verse 13 — Surah Al-Hajj 22:13

Yana kiran wanda yake lalle cutarwarsa ce mafi kusa daga amfaninsa! Lalle ne, tir da shi ya zama majiɓinci, kuma tir da ya zama abokin zama

Verse 14 — Surah Al-Hajj 22:14

Lalle ne Allah Yana shigar da waɗanda suka yi imani* kuma suka aikata ayyukan ƙwarai a cikin gidajen Aljanna, ƙoramu na gudana daga ƙarƙashinsu. Lalle ne Allah Yana aikata abin da Yake nufi

Verse 15 — Surah Al-Hajj 22:15

Wanda ya kasance yana zaton cewa Allah ba zai taimake shi ba a cikin duniya da Lahira to sai ya miƙa wata igiya zuwa sama, sa'an nan kuma ya yanke ta, sa'an nan ya duba. Shin, ko lalle kaidinsa zai gusar da abin da yake ji na takaici

Verse 16 — Surah Al-Hajj 22:16

Kuma kamar haka Muka saukar da shi (Alƙur'ani) yana ayoyi bayyanannu. Kuma lalle ne Allah Yana shiryar da wanda Yake nufi

Verse 17 — Surah Al-Hajj 22:17

Lalle ne waɗanda suka yi imani da waɗanda suka tuba (Yahudu) da waɗanda suka karkace (Saba'awa) da Nasara da Majusawa da waɗanda suka yi shirka, lalle ne Allah Yana yin hukunci a tsakaninsu a Ranar ¡iyama. Lalle ne Allah Mahalarci ne a kan dukkan kome

Verse 18 — Surah Al-Hajj 22:18

Ashe, ba ka gani ba, lalle Allah, wanda yake a cikin sammai da wanda yake a cikin ƙasa yana yin sujada a gare shi, da kuma rana da wata da taurari da duwatsu da itace da dabbobi, da kuma masu yawa daga mutane? Kuma waɗansu masu yawa azaba ta tabbata a kansu. Kuma wanda Allah Ya wulakantar, to, ba ya da wani mai girmamawa. Kuma Lalle ne Allah Yana aikata abin da Yake so

Verse 19 — Surah Al-Hajj 22:19

waɗannan ƙungiyoyi biyu* ne masu husuma, sun yi husuma ga sha'anin Ubangijinsu. To, waɗanda suka kafirta an yanka musu waɗansu tufafi daga wata irin wuta, ana zuba tafasasshen ruwa daga bisa kawunansu

Verse 20 — Surah Al-Hajj 22:20

Da shi ake narkar da abin da yake a cikin cikunansu da fatun jikinsu

Verse 21 — Surah Al-Hajj 22:21

Kuma suna da waɗansu gwalmomin duka na baƙin ƙarfe

Verse 22 — Surah Al-Hajj 22:22

A koyaushe suka yi nufin fita daga gare ta, daga baƙin ciki, sai a mayar da su a cikinta, (a ce musu) "Ku ɗanɗani azabar gobara

Verse 23 — Surah Al-Hajj 22:23

Lalle ne, Allah Yana shigar da waɗanda suka yi imani kuma suka aikata ayyukan ƙwarai a cikin gidajen Aljanna, ƙoramu suna gudana daga ƙarƙashinsu, ana ƙawata su, a cikinsu, da waɗansu mundaye na zinari da lu'u-lu'u. Kuma tufafinsu a cikinsu alharini ne

Verse 24 — Surah Al-Hajj 22:24

Kuma an shiryar da su zuwa ga mai kyau na zance kuma an shiryar da su zuwa ga, hanyar wanda ake gode wa

Verse 25 — Surah Al-Hajj 22:25

Lalle ne waɗanda suka kafirta kuma suka taushe (mutane) daga hanyar Allah da masallaci mai alfarma wanda Muka sanya shi ga mutane alhali kuwa mazauni a ciki da baƙauye daidai suke kuma wanda ya yi nufin karkatar* da gaskiya a cikinsa da zalunci za Mu ɗanɗana masa daga wata azaba mai raɗadi

Verse 26 — Surah Al-Hajj 22:26

Kuma a lokacin da Muka iyakance* wa Ibrahim wurin ¦akin (Muka ce masa), "Kada ka haɗa kome da Ni ga bauta, kuma ka tsarkake daki Na domin masu ɗawafi da masu tsayuwa da masu ruku'u da masu sujada

Verse 27 — Surah Al-Hajj 22:27

Kuma ka yi yekuwa ga mutane da wajabcin Hajji su je maka suna masu tafiya da ƙafafu da kuma a kan kowane maɗankwarin raƙumi masu zuwa daga kowane rango mai zurfi

Verse 28 — Surah Al-Hajj 22:28

Domin su halarci abubuwan amfani a gare su, kuma su ambaci sunan Allah a cikin 'yan kwanuka sanannu saboda abin da Ya azurta su da shi daga dabbobin jin daɗi. Sai ku ci daga gare su, kuma ku ciyar da matsattse matalauci

Verse 29 — Surah Al-Hajj 22:29

Sa'an nan kuma sai su ƙare ibadarsu da gusar da ƙazanta, knma sai su cika alkawuransu kuma sai su yi ɗawafi (suna gewaya) ga ¦akin nin 'yantacce

Verse 30 — Surah Al-Hajj 22:30

Wancan ne. Kuma wanda ya girmama hukunce-hukuncen Allah to shi ne mafifici a gare shi, a wurin Ubangijinsa. Kuma an halatta muku dabbobin ni'ima* face abin da ake karantawa a kanku. Saboda haka ku nisanci ƙazanta daga gumaka kuma ku nisanci ƙazanta daga shaidar zur

Verse 31 — Surah Al-Hajj 22:31

Kuna masu tsayuwa ga gaskiya domin Allah, ba masu yin shirka da Shi ba. Kuma wanda ya yi shirka da Allah, to, yana kamar abin da ya faɗo daga sama, sa'an nan tsuntsaye su cafe shi, ko iska ta faɗa da shi a cikin wani wuri mai nisa

Verse 32 — Surah Al-Hajj 22:32

Wancan ne. Kuma wanda ya girmama ibadodin Allah, to, lalle ne ita (girmamawar) tana daga ayyukan zukata na ibada

Verse 33 — Surah Al-Hajj 22:33

Kuna da waɗansu abubuwan amfani* a cikinta (dabbar hadaya) har ya zuwa ga wani ajali ambatacce, sa'an nan kuma wurin halattata zuwa ga ¦akin 'yantacce ne

Verse 34 — Surah Al-Hajj 22:34

Kuma ga kowace al'umma Mun sanya ibadar yanka, domin su ambaci sunan Allah a kan abin da Ya azurta su da shi daga dabbobin ni'ima. Sa'an nan kuma Abin bautawarku Abin bautawa ne Guda, sai ku sallama Masa. Kuma ka yi bushara ga masu ƙanƙantar da kai

Verse 35 — Surah Al-Hajj 22:35

Waɗanda suke idan an ambaci Allah sai zukatansu su firgita, da masu haƙuri a kan abin da ya same su, da masu tsayar da salla, kuma suna ciyarwa daga abin da Muka azurta su

Verse 36 — Surah Al-Hajj 22:36

Kuma raƙuman, Mun sanya su a gare ku, a ibadojin Allah. Kuna da wani alheri babba a cikinsu. Sai ku ambaci sunan Allah a kansu suna tsaye* a kan ƙafafu uku. Sa'an nan idan sasanninsu suka faɗi, to, ku ci daga gare su, kuma ku ciyar da mai wadar zuci da mai bara. Kamar haka Muka hore muku su, tsammaninku kuna godewa

Verse 37 — Surah Al-Hajj 22:37

Namominsu ba za su sami Allah ba haka jinainansu amma taƙawa daga gare ku tana, samun Sa. Kamar haka Ya hore su saboda ku domin ku girmama Allah saboda shiriyar da Ya yi muku. Kuma ka yi bushara ga masu kyautata yi

Verse 38 — Surah Al-Hajj 22:38

Lalle ne, Allah Yana yin faɗa* saboda waɗanda suka yi imani. Lalle ne Allah ba Ya son dukkan mayaudari, mai yawan kafirci

Verse 39 — Surah Al-Hajj 22:39

An yi izni ga waɗanda ake yaƙar su da cewa lalle an zalunce su, kuma lalle ne Allah, haƙiƙa, Mai ikon yi ne a kan taimakonsu

Verse 40 — Surah Al-Hajj 22:40

Waɗanda aka fitina daga gidajensu ba da wani hakki ba face suna cewa, Ubangijinmu Allah ne."Kuma ba domin tunkuɗewar Allah ga mutane ba, sashensu da sashe, haƙiƙa, da an rusa sauma'o'in (Ruhbanawa) da majami'o'in Nasara da gidajen ibadar Yahudu da masallatai waɗanda ake ambatar Allah a cikinsu da yawa. Kuma lalle, haƙiƙa, Allah Yana taimakon wanda yake taimakon Sa. Lalle Allah ne haƙiƙa Mai ƙarfi Mabuwayi

Verse 41 — Surah Al-Hajj 22:41

Waɗanda suke idan Muka ba su iko a cikin ƙasa sai su tsai da salla, kuma su baybr da zakka kuma su yi umurni da abin da aka sani,* kuma su hana daga abin da ba a sani ba. Kuma aƙibar al'amura ga Allah take

Verse 42 — Surah Al-Hajj 22:42

Kuma idan sun ƙaryata ka, to lalle haƙiƙa, mutanen Nuhu da Adawa da Samudawa, sun ƙaryata a gabaninsu

Verse 43 — Surah Al-Hajj 22:43

Da mutanen Ibrahim da mutanen Luɗu

Verse 44 — Surah Al-Hajj 22:44

Da masu Madyana, kuma an ƙaryata Musa. Sai Na jinkirtawa kafiran, sa'an nan kuma Na kama su. To, yaya musuNa (gare su) ya kasance

Verse 45 — Surah Al-Hajj 22:45

Sa'an nan da yawa daga alƙarya, Muka halaka ta, alhali kuwa tana mai zalunci sai ta zama faɗaɗɗa a kan rassanta, da yawa daga rijiya wadda aka wofintar, da kuma gidajen sarauta maɗaukaka

Verse 46 — Surah Al-Hajj 22:46

Shin, to, ba su yi tafiya ba a cikin ƙasa domin zukata waɗanda za su yi hankali da su da kunnuwa da za su yi saurare da su su kasance a gare su? Domin lalle ne idanun ba su makanta, amma zukata waɗanda ke a cikin ƙiraza su ke makanta

Verse 47 — Surah Al-Hajj 22:47

Kuma suna neman ka yi gaggawa da azaba, alhali kuwa Allah ba zai saɓa wa'adinSa ba kuma lalle ne, yini* ɗaya a wurin Ubangijinka kamar shekara dubu yake daga abin da kuke ƙidayawa

Verse 48 — Surah Al-Hajj 22:48

Kuma da yawa daga alƙarya, Na yi jinkirin azaba gare ta (da laifinta) sa'an nan Na kama ta, kuma zuwa gare Ni makoma take

Verse 49 — Surah Al-Hajj 22:49

Ka ce: "Ya ku mutane! Ni wani mai gargaɗi ne kawai zuwa gare ku, mai bayyanawa

Verse 50 — Surah Al-Hajj 22:50

To, waɗanda suka yi imani, kuma suka aikata ayyuka na ƙwarai, suna da gafara da arziki na karimci

Verse 51 — Surah Al-Hajj 22:51

Kuma waɗanda suka yi aikin ɓatawa a cikin ayoyinMu, suna masu gajiyarwa, waɗancan 'yan Jahim ne

Verse 52 — Surah Al-Hajj 22:52

Kuma ba Mu aika wani manzo ba a gabaninka, kuma ba Mu umurci wani Annabi ba face idan ya yi buri,* sai Shaiɗan ya jefa (wani abu) a cikin burinsa, sa'an nan Allah Ya shafe abin da Shaiɗan ke jefawa. Sa'an nan kuma Allah Ya kyautata ayoyin Sa. Kuma Allah Masani ne, Mai hikima

Verse 53 — Surah Al-Hajj 22:53

Domin Ya sanya abin da Shaiɗan ke jefawa ya zama fitina ga waɗanda a cikin zukatansu akwai cuta, da masu ƙeƙasassun zukatansu. Kuma lalle ne azzalumai haƙiƙa, suna a cikin saɓanimai nisa

Verse 54 — Surah Al-Hajj 22:54

Kuma domin waɗanda aka bai wa ilmi su sani lalle shi ne gaskiya daga Ubangijinka domin su yi imani da shi saboda zukatansu su natsu gare shi. Kuma lalle ne Allah, haƙiƙa, Mai shiryar da waɗanda suka yi imani ne zuwa ga hanya madaidaiciya

Verse 55 — Surah Al-Hajj 22:55

Kuma waɗanda suka kafirta ba za su gushe ba suna a cikin shakka daga gare shi, har Sa'a ta je musu bisa ga abke, ko kuwa azabar wani yini bakarare ta je musu

Verse 56 — Surah Al-Hajj 22:56

Mulki a ranar nan ga Allah yake, Yana hukunci a tsakaninsu. To, waɗanda suka yi imani, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, suna a cikin gidajen Aljannar ni'ima

Verse 57 — Surah Al-Hajj 22:57

Kuma waɗandra suka kafirta kuma suka ƙaryata, game da ayoyin Mu, to, waɗannan suna da azaba mai wulakantarwa

Verse 58 — Surah Al-Hajj 22:58

Kuma waɗanda suka yi hijira a cikin tafarkin Allah sa'an nan kuma aka kashe su, ko suka mutu, lalle ne Allah Yana azurta su da arziki mai kyau. Kuma lalle ne Allah, haƙiƙa, Shi ne Mafi alherin masu azurtawa

Verse 59 — Surah Al-Hajj 22:59

Lalle ne, Yana shigar da su a wata mashiga wadda za su yarda da ita. Kuma lalle ne Allah, haƙiƙa Masani ne, Mai haƙuri

Verse 60 — Surah Al-Hajj 22:60

Wancan! Kuma wanda ya rama azaba da misalin abin da aka yi masa, sa'an nan kuma aka zalunce shi, lalle ne Allah Yana taimakon sa. Lalle ne Allah haƙiƙa Mai yafewa ne, Mai gafara

Verse 61 — Surah Al-Hajj 22:61

Wancan! saboda Allah Yana shigar da dare a cikin yini, kuma Yana shigar da yini a cikin dare, kuma lalle, Allah Mai ji ne, Mai gani

Verse 62 — Surah Al-Hajj 22:62

Wancan! saboda lalle ne Allah, shi ne Gaskiya, kuma lalle ne, abin da suke kira waninSa shi ne ƙarya. Kuma lalle ne Allah, Shi ne Maɗaukaki, Mai girma

Verse 63 — Surah Al-Hajj 22:63

Ashe, ba ka gani ba, lalle ne, Allah Ya saukar da ruwa* daga sama, sai ƙasa ta wayi gari koriya? Lalle Allah Mai tausasawa ne, Mai ƙididdigewa

Verse 64 — Surah Al-Hajj 22:64

Abin da ke a cikin sammai, da abin da ke a cikin ƙasa, Nasa ne, kuma lalle ne Allah, haƙiƙa, Shi ne wadatacce, Godadde

Verse 65 — Surah Al-Hajj 22:65

Shin ba ka gani ba, lalle ne Allah Ya hore muku abin da yake a cikin ƙasa, kuma jirage suna gudana a cikin teku, da umurninSa kuma Yana riƙe sama domin kada ta faɗi a kan ƙasa face da izninsa? Lalle ne Allah ga mutane haƙiƙa, Mai tausayi ne, Mai jin ƙai

Verse 66 — Surah Al-Hajj 22:66

Kuma shi ne wanda Ya raya ku, sa'an nan kuma Yana matar da ku, sa'an nan kuma Yana rayar da ku. Lalle mutum, haƙiƙa, mai kafirci ne

Verse 67 — Surah Al-Hajj 22:67

Ga kowace al'umma Mun sanya wurin yanka, su ne masu yin baiko gare Shi, saboda haka, kada su yi maka jayayya a cikin al'amarin (hadaya). Kuma ka yi kira zuwa ga Ubangijinka lalle kai kana a kan shiriya madaidaiciya

Verse 68 — Surah Al-Hajj 22:68

Kuma idan sun yi maka jidali, sai ka ce: "Allah ne Mafi sani game da abin da kuke aikatawa

Verse 69 — Surah Al-Hajj 22:69

Allah ne zai yi hukunci a tsakaninku, a Ranar ¡iyama a cikin abin da kuka kasance a cikinsa kuna saɓawa juna

Verse 70 — Surah Al-Hajj 22:70

Ashe, ba ka sani ba, lalle ne Allah Yana sanin abin da yake a cikin sama da ƙasa? Lalle ne wancan yana cikin Littafi lalle wancan ga Allah mai sauƙi ne

Verse 71 — Surah Al-Hajj 22:71

Kuma suna bautawa baicin Allah, abin da (Allah) bai saukar da wani dalili ba game da shi, kuma abin da ba su da wani ilmi game da shi, kuma babu wani mai taimako ga azzalumai

Verse 72 — Surah Al-Hajj 22:72

Kuma idan ana karanta ayoyin Mu bayyanannu a kansu kana sanin abin ƙyama a cikin fuskokin waɗanda suka kafirta suna kusa su yi danƙa ga waɗanda ke karatun ayoyinMu a kansu. Ka ce: "Shin to in gaya muku abin da yake mafi sharri daga wannan? (Ita ce) Wuta." Allah Ya yi alkawarinta ga waɗanda suka kafirta. Kuma makomarsu ta munana

Verse 73 — Surah Al-Hajj 22:73

Ya ku mutane! An buga wani misali, sai ku saurara zuwa gare shi. Lalle ne waɗanda kuke kira baicin Allah, ba za su halitta ƙuda ba, ko da sun taru gare shi, kuma idan ƙudan ya ƙwace musu wani abu, ba za su kuɓutar da shi ba daga gare shi. Mai nema da wanda ake neman gare shi sun raunana

Verse 74 — Surah Al-Hajj 22:74

Ba su ƙaddara wa Allah hakkin girmanSa ba. Lalle ne Allah, haƙiƙa, Mai ƙarfi ne, Mabuwayi

Verse 75 — Surah Al-Hajj 22:75

Allah na zaɓen Manzanni daga mala'iku kuma daga mutane.* Lalle Allah, Mai ji ne, Mai gani

Verse 76 — Surah Al-Hajj 22:76

Yana sanin abin da ke gaba gare su da abin da ke bayansu, kuma zuwa ga Allah ake mayar da al'amura

Verse 77 — Surah Al-Hajj 22:77

Ya ku waɗanda suka yi imani! Ku yi ruku'i, kuma ku yi sujada, kuma ku bauta wa Ubangijinku, kuma ku aikata alheri, tsammaninku, ku sami babban rabo

Verse 78 — Surah Al-Hajj 22:78

Kuma ku yi jihadi a cikin (al'amarin) Allah, hakkin JihadinSa. shi ne Ya zaɓe ku alhali kuwa bai sanya wani ƙunci* ba a kanku a cikin addini. Bisa ƙudurcewar ubanku Ibrahim, shi ne ya yi muku suna Musulmi** daga gabanin haka. Kuma a cikin wannan (Littafi ya yi muku suna Musulmi), domin Manzo ya kasance mai shaida a kanku, ku kuma ku kasancemasu shaida a kan mutane. Saboda haka ku tsayar da salla kuma ku bayar da zakka kuma ku amince da Allah, Shi ne Majiɓincinku. Saboda haka madalla da Shi Ya zama Majiɓinci, madalla da Shi ya zama Mai taimako