Back to Languages
Hausa - Chapter 23
Translation by Abubakar Mahmood Jummi
Verse 1
Lalle ne, Muminai* sun sami babban rabo
Verse 2
Waɗanda suke a cikin sallarsu masu tawali'u ne
Verse 3
Kuma waɗanda suke, sudaga barin yasassar magana, masu kau da kai ne
Verse 4
Kuma waɗanda suke ga zakka masu aikatawa ne
Verse 5
Kuma waɗanda suke ga farjojinsu masu tsarewa ne
Verse 6
Face a kan matan aurensu, ko kuwa abin da hannayen damansu suka mallaka to lalle su ba waɗanda ake zargi, ba, ne
Verse 7
Saboda haka wanda ya nemi abin da ke bayan wancan, to, waɗancan su ne masu ƙetarewar haddi
Verse 8
Kuma waɗanda suke, suga amanoninsu da alkawarinsu masu tsarewa ne
Verse 9
Kuma da waɗanda suke, su a kan sallolinsu suna tsarewa
Verse 10
Waɗannan, su ne magada
Verse 11
Waɗanda suke gadon (Aljannar) Firdausi,* su a cikinta madawwama ne
Verse 12
Kuma lalle ne, haƙiƙa, Mun halitta mutum daga wani tsantsa daga laka
Verse 13
Sa'an nan kuma Muka sanya shi, ɗigon maniyyi a cikin matabbata natsattsiya
Verse 14
Sa'an nan kuma Muka halitta shi gudan jini, sa'an nan Muka halitta gudan jinin tsoka, sa'an nan Muka halitta tsokar ta zama ƙasusuwa, sa'an nan Muka tufatar da ƙasusuwan da wani nama sa'an nan kuma Muka ƙaga shi wata halitta dabam. Saboda haka albarkun Allah sun bayyana, Shi ne Mafi kyawun masu halittawa
Verse 15
Sa'an nan kuma ku, bayan wannan, lalle ne masu mutuwa ne
Verse 16
Sa'an nan kuma lalle ne ku a Ranar alkiyama, za a iayar da ku
Verse 17
Kuma lalle ne haƙiƙa Mun halitta, a samanku, hanyoyi bakwai, kuma ba Mu kasance, daga barin halittar, Masu shagala ba
Verse 18
Muka saukar da ruwa daga sama bisa gwargwado, sa'an nan Muka zaunar da shi a cikin ƙasa alhali, lalle ne Mu, a kan tafiyar da shi, Masu iyawa ne
Verse 19
Sai Muka ƙaga muku, game da shi (ruwan), gonaki daga dainai da inabobi, kuna da, a cikinsu, 'ya'yan itacen marmari masu yawa, kuma daga gare su kuke ci
Verse 20
Da wata itaciya,* tana fita daga dutsin Saina'a, tana tsira da man shafawa, da man miya domin masu ci
Verse 21
Kuma lalle ne kuna da abin lura a cikin dabbobin ni'imomi Muna shayar da ku daga abin da yake a cikinsu, kuma kuna da a cikinsu abubuwan amfani* masu yawa, kuma daga gare su kuke ci
Verse 22
Kuma a kansu da a kan jirgin ruwa ake ɗaukar ku
Verse 23
Kuma lalle ne haƙiƙa Mun aika Nuhu zuwa ga mutanensa, sai ya ce: "Ya mutanena! Ku bauta wa Allah. Ba ku da wani abin bautawa waninsa. Shin, to, ba za ku yi taƙawa ba
Verse 24
Sai mashawarta waɗanda suka kafirta daga mutanensa, suka ce: "Wannan ba kowa ba ne, face mutum misalinku, yana nufin ya ɗaukaka a kanku. Da Allah Ya so, lalle ne da Ya saukar da Mala'iku, Ba muji (kome) ba, game da wannan, a cikin ubanninmu na farko
Verse 25
Shi bai zamo kowa ba face wani namiji ne, a gare shi akwai hauka, sai ku yi jinkiri da shi har wani lokaci
Verse 26
Ya ce: "Ya Ubangijina! Ka taimakeni Saboda mutanena sun ƙaryata ni
Verse 27
Sai Muka yi wahayi zuwa gare shi. "Ka sana'anta jirgin bisa ga idon Mu, da wahayinMu. To, idan umuminMu ya je, kuma tanda ta ɓuɓɓuga da ruwa, to, ka shigar a cikinta daga kome, ma'aura biyu, da iyalanka, sai wanda Magana ta gabata a kansa, daga gare su, kuma kada ka roƙe Ni (saboda wani) a cikin waɗanda suka yi zalunci, lalle ne su waɗanda ake nutsarwa ne
Verse 28
Sa'an nan idan ka daidaitu kai da waɗanda ke tare da kai a kan jirgin, sai ka ce: "Godiya ta tabbata ga Allah wanda Ya tsirar damu daga mutane azzalumai
Verse 29
Kuma ka ce: 'Ya Ubangijina! Ka saukar da ni, saukarwa mai albarka. Kuma Kai ne Mafi alherin masu saukarwa
Verse 30
Lalle ne a cikin wancan akwai ayoyi, ko da yake Mun kasance, haƙiƙa' Masu jarrabawa
Verse 31
Sa'an nan kuma Muka ƙaga wani ƙarni na waɗansu dabam daga bayansu
Verse 32
Sai Muka aika a cikinsu Manzo daga gare su. "Ku bauta wa Allah. Ba ku da wani abin bautawa, sai Shi. Shin to, ba za ku yi taƙawa ba
Verse 33
Mashawarta daga mutanensa, waɗanda suka kafirta kuma suka ƙaryata game da haɗuwa da Lahira, kuma Muka ni'imtar da su a cikin rayuwar duniya, suka ce: "Wannan ba kowa ba face wani mutum ne kamarku, yana ci daga abin da kuke ci daga gare shi, kuma yana sha daga abin da kuke sha
Verse 34
Kuma lalle ne idan kun yi ɗa' a ga mutum misalinku, lalle ne, a lokacin nan, haƙiƙa, ku masu hasara ne
Verse 35
Shin, yana yi muku wa'adin (cewa) lalle ku, idan kun mutu kuma kuka kasance turɓaya da kasusuwa lalle ne ku waɗanda ake fitarwa ne
Verse 36
Faufau faufau ga abin da ake yi muku wa'adi da shi
Verse 37
Rayuwa ba ta zama ba face rayuwarmu ta duniya, muna mutuwa kuma muna rayuwa,* kuma ba mu zama waɗanda ake tayarwa ba
Verse 38
Bai zama kowa ba face namiji, ya ƙirƙira ƙarya ga Allah, kuma ba mu zama, saboda shi, masu imani ba
Verse 39
Ya ce: "Ya Ubangijina! Ka taimake ni saboda sun ƙaryata ni
Verse 40
Ya ce: "Daga abu kaɗan, lalle ne za su wayi gari suna masu nadama
Verse 41
Sai tsawa ta kama su da gaskiya, sai Muka sanya su tunkuɓa. Saboda haka nisa ya tabbataga mutane azzalumai
Verse 42
Sa'an kuma Muka ƙaga halittar wasu ƙarnoni dabam daga bayansu
Verse 43
Wata al'umma ba ta gabatar ajalinta, kuma ba za su jinkirta ba
Verse 44
Sa'an nan kuma Muka aika da ManzanninMu jere a koda yaushe Manzon wata al'umma ya je mata, sai su ƙaryata shi, saboda haka Muka biyar da sashensu ga sashe, kuma Muka sanya su labarun hira. To, nisa ya tabbata ga mutane (waɗanda) ba su yin imani
Verse 45
Sa'an nan kuma Muka aika Musa da ɗan'uwansa Haruna, game da ayoyin Mu da, dalili bayyananne
Verse 46
Zuwa ga Fir'auna da majalisarsa, sai suka kangara, alhali sun kasance mutane ne marinjaya
Verse 47
Sai suka ce: "Shin, za Mu yi imani saboda wasu mutane biyu misalinmu, alhali kuwa mutanensu a gare mu, masu bauta ne
Verse 48
Sai suka ƙaryata su saboda haka suka kasance halakakku
Verse 49
Kuma lalle ne, haƙiƙa, Mun bai wa Musa littafi tsammaninsu* za su shiryu
Verse 50
Kuma Mun sanya ¦an Maryama, shi da uwarsa wata aya* Kuma Muka tattara su zuwa ga wani tsauni ma'abucin natsuwa da maremari
Verse 51
Ya ku Manzanni! Ku ci daga abubuwa masu daɗi* kuma ku aikata aikin ƙwarai. Lalle Niga abin da kuke aikatawa, Masani ne
Verse 52
Kuma lalle ne, wannan al'ummarku ce, al'umma guda, kuma Ni, Ubangijinku ne, sai ku bi Ni da taƙawa
Verse 53
Sai (al'ummar) suka yanyanke al'amarinsu a tsakaninsu guntu-guntu,* kowace ƙungiya suna masu farin ciki da abin da yake a gare su
Verse 54
To, ka bar su a cikin ɓatarsu har a wani lokaci
Verse 55
Shin, suna zaton cewa abin da Muke taimakon su da shi daga dukiya da ɗiya
Verse 56
Muna yi musu gaggawa ne a cikin alherori
Verse 57
Lalle ne waɗanda suke masu sauna sabo da tsoron Ubangijinsu
Verse 58
Da waɗanda suke, game da ayoyin Ubangijinsu suna imani
Verse 59
Da waɗanda suke game da Ubangijinsu ba su yin shirki
Verse 60
Da waɗanda ke bayar da abin da suka bayar, alhali kuwa zukatansu suna tsorace domin suna komawa zuwa ga Ubangijinsu
Verse 61
Waɗancan suna gaggawar tsere a cikin ayyukan alheri, alhali kuwa suna masu tserewa zuwa gare su (ayyukan alheri)
Verse 62
Kuma ba Mu kallafa wa rai face abin iyawarsa, kuma a wurinMu akwai wani Littafi wanda yake magana da gakiya, kuma su ba a zaluntar su
Verse 63
A'a, zukatansu suna cikin jahilci daga wannan (magana), kuma suna da waɗansu ayyuka, baicin wancan, su a gare su, masu aikatawa ne
Verse 64
Har idan Mun kama mani'imtansu da azaba, sai ga su suna hargowa
Verse 65
Kada ku yi hargowa a yau, lalle ne ku, daga gare Mu ba a taimakon ku
Verse 66
Lalle ne, ayoyiNa sun kasance ana karatun su a kanku, sai kuka kasance, a kan dugaduganku, kuna komawa baya
Verse 67
Kuna masu girman kai gare shi (Annabi), da hira kuna alfasha
Verse 68
Shin fa, ba su yi ta'ammalin maganar (Alƙur'ani) ba, ko abin da bai je wa ubanninsu na farko ba ne ya je musu
Verse 69
Ko ba su san Manzonsu ba ne domin haka suke masu musu a gare shi
Verse 70
Ko suna cewa, "Akwai hauka gare shi?" A'a, ya zo musu da gaskiya, alhali kuwa mafi yawansu, ga gaskiya, masu ƙi ne
Verse 71
Kuma da gaskiya (Alƙur'ani) ya bi son zuciyoyinsu, haƙiƙa da sammai da ƙasa da wanda yake a cikinsu sun ɓaci. A'a, Mun tafo musu da ambaton* (darajar) su, sa'an nan su daga barin ambaton su masu bijirewa ne, bijirewa
Verse 72
Ko kana tambayar su wani haraji ne (a kan iyar da Manzanci a gare su)? To, harajin Ubangijinka ne mafi alheri kuma Shi ne Mafi alherin masu ciyarwa
Verse 73
Kuma lalle ne kai haƙiƙa kana kiran su zuwa ga hanya madaidaiciya
Verse 74
Kuma lalle waɗanda ba su yi imani da Lahira ba masu karkacewa daga hanya ne
Verse 75
Kuma da Mun ji tausayinsu, kuma Muka kuranye musu abin da yake tare da su na cuta, lalle ne da sun yi zurfi a cikin ɓatarsu, suna ɗimuwa
Verse 76
Kuma lalle ne haƙiƙa Muna kama su da azaba* sai dai ba su saukar da kai ba, ga Ubangijinsu, kama ba su yin tawali'u
Verse 77
Har idan Mun buɗe, akansu, wata ƙofa mai azaba mai tsanani sai ga su a cikinta suna masu mugi
Verse 78
Kuma Shi ne Wanda Ya ƙaga halittar ji da gani da zukata dominku. Kaɗan ƙwarai kuke godewa
Verse 79
Kuma Shi ne Ya halitta ku a cikin ƙasa, kuma zuwa gare Shi ake tayar da ku
Verse 80
Kuma Shi ne Wanda Yake rayarwa, kuma Yana matarwa, kuma a gare Shi ne saɓawar dare da yini take. Shin, to, ba za ku hankalta ba
Verse 81
A'a, sun faɗi misalin abin da na farko suka faɗa
Verse 82
Suka ce: "Shin idan mun mutu kuma muka kasance turɓaya da ƙasusuwa shin lale ne mu haƙiƙa waɗanda ake tayarwa ne
Verse 83
Lalle ne, haƙiƙa, an yi mana wa'adi, mu da ubanninmu ga wannan a gabani, wannan abu bai zama kome ba, face tatsuniyoyin na farko
Verse 84
Ka ce: "Wane ne da mulkin ƙasa da wanda ke a cikinta, idan kun kasance kuna sani
Verse 85
Za su ce: "Ta Allah ne." Ka ce, "Shin, to, ba za ku yi tunani ba
Verse 86
Ka ce: "Wane ne Ubangijin sammai bakwai kuma Ubangijin Al'arshi mai girma
Verse 87
Za su ce: "Na Allah ne." Ka ce, "Shin, to, ba za ku bi Shi da taƙawa ba
Verse 88
Ka ce: "Wane ne ga hannunsa mallakar kowane abu take alhali kuwa shi yana tsarewar wani, kuma ba a tsare kowa daga gare shi, idan kun kasance kuna sani
Verse 89
Za su ce: "Ga Allah yake." Ka ce: "To, yaya ake sihirce ku
Verse 90
A'a, Mun zo musu da gaskiya, kuma lalle ne su, haƙiƙa, maƙaryata ne
Verse 91
Allah bai riƙi wani abin haihuwa ba, kuma babu wani abin bautawa tare da Shi. Idan haka ne (akwai abin bautawa tare da Shi), lalle ne da kowane abin bautawar ya tafi da abin da ya halitta, kuma lalle ne, da waɗansu sun rinjaya a kan waɗansu, tsarki ya tabbata ga Allah, daga abin da suke siffantawa
Verse 92
Masanin ɓoye da bayyane. sa'an nan Ya ɗaukaka daga barin abin da suke yi na shirka
Verse 93
Ka ce: "Ya Ubangijina! Ko dai Ka nuna mini abin da ake yi musu wa'adi da shi
Verse 94
Ya Ubangijina, to, kada Ka sanya ni a cikin mutane azzalumai
Verse 95
Kuma lalle ne Mu haƙiƙa Masu iyawa ne a kan Mu nuna maka abin da Muke yi musu wa'adi da shi
Verse 96
Ka tunkuɗe cuta da wadda take ita ce mafi kyau. Mu ne Mafi sani game da abin da suke siffantawa
Verse 97
Ka ce: "Ya Ubangijina, ina neman tsari da Kai daga fizge-fizgen Shaiɗanu
Verse 98
Kuma ina neman tsari da Kai, ya Ubangijina! Domin kada su halarto ni
Verse 99
Har idan mutuwa ta je wa ɗayansu, sai ya ce: "Ya Ubangijina, Ku mayar da ni (duniya)
Verse 100
Tsammanina in aikata aiki na ƙwarai cikin abin da na bari." Kayya! Lalle ne ita kalma ce, shi ne mafaɗinta, alhali kuwa a baya gare su akwai wani shamaki har ranar da za a tayar da su
Verse 101
Sa'an nan idan an yi busa a cikin ƙaho, to, babu dangantakoki a tsakaninsu a ranar nan kuma ba za su tambayi junansu ba
Verse 102
To, wadanda sikelinsu ya yi nauyi, to, waɗannan su ne masu babban rabo
Verse 103
Kuma waɗanda sikelinsu ya yi sauƙi, to, waɗannan ne waɗanda suka yi hasarar rayukansu suna madawwama a cikin Jahannama
Verse 104
Fuskokinsu suna balbalar wuta, kuma su a cikinta masu yagaggun leɓɓa daga haƙora ne
Verse 105
Shin, ayoyiNa ba su kasance ana karanta su a kanku ba sai kuka kasance game da su kuna ƙaryatawa
Verse 106
Suka ce: "Ya Ubangijinmu, shaƙawace ta rinjaya a kanmu, kuma mun kasance mutane ɓatattu
Verse 107
Ya Ubangjinmu! Ka fitar da mu daga gare ta, sa'an nan idan mun koma, to, lalle ne, mu ne masu zalunci
Verse 108
Ya ce: "Ku tafi (da wulakanci) a cikinta. Kada ku yi Mini magana
Verse 109
Lalle ne waɗansu ƙungiyoyi daga bayiNa sun kasance suna cewa, "Ya Ubangijinmu! Mun yi imani, sai Ka gafarta mana, kuma Ka yi mana rahama, kuma Kai ne Mafi alherin masu tausayi
Verse 110
Sai kuka riƙe su leburori har suka mantar da ku ambato Na kuma kun kasance, daga gare su kuke yin dariya
Verse 111
Lalle ne Ni Ina saka musu a yau, saboda abin da suka yi wa haƙuri. Domin lalle ne su su ne masu samun babban rabo
Verse 112
Ya ce: "Nawa kuka zauna a cikin ƙasa na ƙidayar shekaru
Verse 113
Suka ce: "Mun zauna a yini ɗaya ko rabin yini, sai ka tambayi masu ƙidayawa
Verse 114
Ya ce: "Ba ku zauna ba face kaɗan, da dai kun kasance kuna sani
Verse 115
Shin, to, kun yi zaton cewa Mun halitta ku ne da wasa kuma lalle ku, zuwa gare Mu, ba za ku komo ba
Verse 116
Allah Mamallaki gaskiya, Ya ɗaukaka. Babu abin bautawa, face Shi. Shi ne Ubangijin Al'arshi, mai daraja
Verse 117
Kuma wanda ya kira, tare da Allah, waɗansu abubuwan bautawa na dabam, ba yana da wani dalili game da shi (kiran) ba, to hisabinsa yana wurin Ubangijinsa kawai. Lalle ne, kafirai ba su cin nasara
Verse 118
Kuma ka ce: "Ya Ubangijina! Ka yi gafara, Ka yi rahama, kuma Kai ne Mafi alherin masu rahama