Back to LanguagesPrevious ChapterNext Chapter
Hausa - Chapter 26 - Ash-Shuara
Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink
Verse 1 — Surah Ash-Shuara 26:1
Verse 2 — Surah Ash-Shuara 26:2
Waɗancan ayoyin Littafi ne bayyananne
Verse 3 — Surah Ash-Shuara 26:3
Tsammaninka kai mai zaka halakar da ranka ne, don ba su zamanto muminai ba
Verse 4 — Surah Ash-Shuara 26:4
Idan Mun so za Mu saukar, a kansu, da wata aya daga sama, sai wuyoyinsu su yini saboda ita suna masu ƙasƙantar da kai
Verse 5 — Surah Ash-Shuara 26:5
Kuma wata tunatarwa ba ta je musu ba, daga Mai rahama, sabuwa, face sun kasance daga barinta suna masu bijirewa
Verse 6 — Surah Ash-Shuara 26:6
To, lalle ne, sun ƙaryata, to, labaran abin da suka kasance suna yi na izgili da shi za ya je musu
Verse 7 — Surah Ash-Shuara 26:7
Shin, ba su duba ba zuwa ga ƙasa, da yawa Muka tsirar a cikinta, daga dukan nau'i mai kyau
Verse 8 — Surah Ash-Shuara 26:8
Lalle ne, a cikin wancan akwai aya, kuma mafi yawansu ba su kasance muminai ba
Verse 9 — Surah Ash-Shuara 26:9
Kuma lalle ne, Ubangijinka, haƙiƙa, Shi ne Mabuwayi, Mai rahama
Verse 10 — Surah Ash-Shuara 26:10
Kuma a lokacin da Ubangijinka Ya kirayi Musa, "Ka je wa mutanen nan azzalumai
Verse 11 — Surah Ash-Shuara 26:11
Mutanen Fir'auna ba za su yi taƙawa ba
Verse 12 — Surah Ash-Shuara 26:12
Ya ce: "Ya Ubangijina, ni ina tsoron su ƙaryata ni
Verse 13 — Surah Ash-Shuara 26:13
Kuma ƙirjina ya yi ƙunci* kuma harshena ba zai saku ba saboda haka ka aika zuwa ga Haruna
Verse 14 — Surah Ash-Shuara 26:14
Kuma suna da wani laifi a kaina, saboda haka ina tsoron kada su kashe ni
Verse 15 — Surah Ash-Shuara 26:15
Ya ce: "Kayya! Ku tafi, ku biyu, da AyoyinMu. Lalle ne, Muna tare da ku Muna Masu saurare
Verse 16 — Surah Ash-Shuara 26:16
Sai ku je wa Fir'auna, sa'an nan ku ce, Lalle ne, mu, Manzannin Ubangijin halitta ne
Verse 17 — Surah Ash-Shuara 26:17
Ka saki Bani Isra'ila tare da mu
Verse 18 — Surah Ash-Shuara 26:18
Ya ce: "Shin, ba mu yi renonka ba a cikinmu kana jariri, kuma ka zauna a cikinmu shekarudaga lokacin rayuwarka
Verse 19 — Surah Ash-Shuara 26:19
Kuma ka aikata aikinka wanda ka aikata alhali kai kana daga butulai
Verse 20 — Surah Ash-Shuara 26:20
Ya ce: "Na aikata shi a lokacin ina daga masu jahilcin fushi
Verse 21 — Surah Ash-Shuara 26:21
Saboda haka na gudu daga gare ku a lokacin da na ji tsoronku, sai Ubangijina Ya ba ni hukunci, kuma Ya sanya ni daga Manzanni
Verse 22 — Surah Ash-Shuara 26:22
Kuma waccan ni'ima ce, kana gorint a kaina, domin ka bautar da Bani Isra'ila
Verse 23 — Surah Ash-Shuara 26:23
Fir'auna ya ce: "Kuma mene ne Ubangijin halittu
Verse 24 — Surah Ash-Shuara 26:24
Ya ce: "Ubangijin sammai da ƙasa da abin da yake a tsakaninsu, idan kun kasance masu ƙarfin imani
Verse 25 — Surah Ash-Shuara 26:25
Ya ce wa waɗanda suke a gefensa, "Ba za ku saurara ba
Verse 26 — Surah Ash-Shuara 26:26
Ya ce: "Ubangijinku, kuma Ubangijin ubanninku na farko
Verse 27 — Surah Ash-Shuara 26:27
Ya ce: "Lalle ne Manzonku, wanda aka aiko zuwa gare ku, haƙi ƙa, mahaukaci ne
Verse 28 — Surah Ash-Shuara 26:28
Ya ce: "Ubangijin mafitar rana da maɓuyarta da abin dayake a tsakaninsu, idan kun kasance kuna hankalta
Verse 29 — Surah Ash-Shuara 26:29
Ya ce: "Lalle ne idan ka riƙi wani abin bautawa wanina haƙiƙa, ina sanya ka daga ɗaurarru
Verse 30 — Surah Ash-Shuara 26:30
Ya ce: "Ashe, kuma ko da na zo maka da wani, abu mai bayyanawa
Verse 31 — Surah Ash-Shuara 26:31
Ya ce: "To, ka zo da shi idan ka kasance daga, masu gaskiya
Verse 32 — Surah Ash-Shuara 26:32
Sai ya jefa sandarsa, sai ga ta kumurci bayyananne
Verse 33 — Surah Ash-Shuara 26:33
Kuma ya fizge hannunsa, sai ga shi fari ga masu kallo
Verse 34 — Surah Ash-Shuara 26:34
(Fir'auna) ya ce ga mashawarta a gefensa, "Lalle ne, wannan haƙiƙa, masihirci ne, mai ilmi
Verse 35 — Surah Ash-Shuara 26:35
Yana son ya fitar da ku daga ƙasarku game da sihirinSa. To mene ne kuke shawartawa
Verse 36 — Surah Ash-Shuara 26:36
Suka ce: "Ka jinkirtar da shi, shi da ɗan'uwansa, kuma ka aika masu gayya a cikin birane
Verse 37 — Surah Ash-Shuara 26:37
Za su zo maka da dukkan mai yawan sihiri masani
Verse 38 — Surah Ash-Shuara 26:38
Sai aka tara masihirta domin ajalin yini sananne
Verse 39 — Surah Ash-Shuara 26:39
Kuma aka ce wa mutane "Ko ku masu taruwa ne
Verse 40 — Surah Ash-Shuara 26:40
Tsammaninmu mu bi masihirta, idan sun kasance su ne marinjaya
Verse 41 — Surah Ash-Shuara 26:41
To, a lokacin da masihirta suka je suka ce wa Fir'auna,"Shin, lalle ne, haƙiƙa muna da ijara idan mun kasance mu ne marinjaya
Verse 42 — Surah Ash-Shuara 26:42
Ya ce: "Na'am! Kuma lalle ne, ku ne a lokacin haƙiƙa muƙarrabai
Verse 43 — Surah Ash-Shuara 26:43
Musa ya ce musu, "Ku jefa abin da kuke masu jefawa
Verse 44 — Surah Ash-Shuara 26:44
Sai suka jefa igiyoyinsu, da sandunansu, kuma suka ce: "Da ƙarfin Fir'auna lalle ne mu, haƙiƙa, mu ne marinjaya
Verse 45 — Surah Ash-Shuara 26:45
Sai Musa ya jefa sandarsa, sai ga ta tana harhaɗe abin da suke yi na ƙarya
Verse 46 — Surah Ash-Shuara 26:46
Sai aka jefar da masihirta suna masu sujada
Verse 47 — Surah Ash-Shuara 26:47
Suka ce: "Mun yi imani da Ubangijin halitta
Verse 48 — Surah Ash-Shuara 26:48
Ubangijin Musa da Haruna
Verse 49 — Surah Ash-Shuara 26:49
Ya ce: "Ashe, kun yi imani saboda shi, a gabanin in yi muku izni? Lalle ne shi, haƙiƙa babbanku ne wanda ya koya muku sihirin, to, za ku sani. Lalle ne haƙiƙa, zan kakkatse hannuwanku da kafafunku a tarnaƙi, kuma haƙiƙa, zan tsire ku gaba ɗaya
Verse 50 — Surah Ash-Shuara 26:50
Suka ce: "Babu wata cuta! Lalle ne mu masu juyawa ne zuwa ga Ubangijinmu
Verse 51 — Surah Ash-Shuara 26:51
Lalle ne mu muna kwaɗayin Ubangijinmu, Ya gafarta mana kurakuranmu domin mun kasance farkon masu imani
Verse 52 — Surah Ash-Shuara 26:52
Kuma Muka aika zuwa ga Musa cewa ka yi tafiyar dare da bayiNa, lalle ne ku waɗanda ake biya* ne
Verse 53 — Surah Ash-Shuara 26:53
Sai Fir'auna ya aika masu gayya a cikin birane
Verse 54 — Surah Ash-Shuara 26:54
Lalle ne, waɗannan, haƙiƙa, ƙungiya ce kaɗan
Verse 55 — Surah Ash-Shuara 26:55
Kuma lalle ne su, a gare Mu, Masu fusatarwa ne
Verse 56 — Surah Ash-Shuara 26:56
Kuma lalle ne mu haƙiƙa gaba ɗaya masu sauna ne
Verse 57 — Surah Ash-Shuara 26:57
Sai Muka fitar da su daga gonaki da maremari
Verse 58 — Surah Ash-Shuara 26:58
Da taskoki da mazauni mai kyau
Verse 59 — Surah Ash-Shuara 26:59
Kamar haka! Kuma Muka gadar da su ga Bani Israila
Verse 60 — Surah Ash-Shuara 26:60
Sai suka bi su suna masu fita a lokacin hudowar rana
Verse 61 — Surah Ash-Shuara 26:61
Sa'an nan a lokacin da jama'a biyu suka ga juna, sai abokan Musa suka ce: "Lalle ne mu haƙi ƙa, waɗanda ake riska ne
Verse 62 — Surah Ash-Shuara 26:62
Ya ce: "Kayya! Lalle ne Ubangijina Yana tare da ni, zai shiryar da ni
Verse 63 — Surah Ash-Shuara 26:63
Sai Muka yi wahayi zuwa ga Musa cewa "Ka doki teku da sandarka." Sai teku ta tsage,* kowane tsagi ya kasance kamar falalen dutse mai girma
Verse 64 — Surah Ash-Shuara 26:64
Kuma Muka kusantar da waɗansu mutane a can
Verse 65 — Surah Ash-Shuara 26:65
Kuma Muka tsirar da Musa da waɗanda suke tare da shi gaba ɗaya
Verse 66 — Surah Ash-Shuara 26:66
Sa'an nan kuma Muka nutsar da waɗansu mutanen
Verse 67 — Surah Ash-Shuara 26:67
Lalle ne a cikin wannan akwai aya, kuma mafi yawansu ba su kasance masu imani ba
Verse 68 — Surah Ash-Shuara 26:68
Kuma lalle ne Ubangijinka, kaƙiƙa, Shi ne Mabuwayi, Mai jin ƙai
Verse 69 — Surah Ash-Shuara 26:69
Kuma ka karanta, a kansu, labarin Ibrahim
Verse 70 — Surah Ash-Shuara 26:70
A sa'ilin da ya ce wa ubansa da mutanensa, "Mene ne kuke bauta wa
Verse 71 — Surah Ash-Shuara 26:71
Suka ce: "Muna bauta wa gumaka, saboda haka muna yini masu lazimta a gare su
Verse 72 — Surah Ash-Shuara 26:72
Ya ce: "Shin, suna jin ku, a lokacin da kuke kira
Verse 73 — Surah Ash-Shuara 26:73
Ko kuwa suna amfanin ku, ko suna cutar ku
Verse 74 — Surah Ash-Shuara 26:74
Suka ce: "A'a mun sami ubanninmu, kamar haka ne suke aikatawa
Verse 75 — Surah Ash-Shuara 26:75
Ya ce: "Shin to, kun ga abin da kuka kasance kuna bauta wa
Verse 76 — Surah Ash-Shuara 26:76
Ku da ubanninku mafi daɗewa
Verse 77 — Surah Ash-Shuara 26:77
To lalle ne, su maƙiya ne a gare ni, face Ubangijin halittu
Verse 78 — Surah Ash-Shuara 26:78
Wanda Ya halitta ni, sa'an nan Yana shiryar da ni
Verse 79 — Surah Ash-Shuara 26:79
Kuma Wanda Yake Shi ne Yake ciyar da ni, kuma Yana shayar da ni
Verse 80 — Surah Ash-Shuara 26:80
Kuma idan na yi jiyya, to, Shi ne Yake warkar da ni
Verse 81 — Surah Ash-Shuara 26:81
Kuma wanda Yake matar da ni, sa'an nan Ya rayar da ni
Verse 82 — Surah Ash-Shuara 26:82
Kuma wanda Yake ina kwaɗayin Ya gafarta mini kurakuraina, a ranar sakamako
Verse 83 — Surah Ash-Shuara 26:83
Ya Ubangijina! Ka ba ni hukunci, kuma Ka riskar da ni ga salihai
Verse 84 — Surah Ash-Shuara 26:84
Kuma Ka sanya mini harshen gaskiya* a cikin mutanen ƙarshe
Verse 85 — Surah Ash-Shuara 26:85
Kuma Ka sanya ni daga magadan Aljannar ni'ima
Verse 86 — Surah Ash-Shuara 26:86
Kuma Ka gafarta wa ubana, lalle ne shi, ya kasance daga ɓatattu
Verse 87 — Surah Ash-Shuara 26:87
Kuma kada Ka kunyata ni a ranar da ake tayar da su
Verse 88 — Surah Ash-Shuara 26:88
A ranar da dukiya ba ta amfani, kuma ɗiya ba su yi
Verse 89 — Surah Ash-Shuara 26:89
Face wanda ya je wa Allah da zuciya mai tsarki
Verse 90 — Surah Ash-Shuara 26:90
Kuma aka kusantar da Aljanna ga masu taƙawa
Verse 91 — Surah Ash-Shuara 26:91
Kuma aka fitar da wuta babba domin halakakku
Verse 92 — Surah Ash-Shuara 26:92
Kuma aka ce musu, "Ina abin da kuka kasance kuna bautawa
Verse 93 — Surah Ash-Shuara 26:93
Baicin Allah? Shin suna tamakon ku ko kuwa suna tsare kansu
Verse 94 — Surah Ash-Shuara 26:94
Sai aka kikkife su* a cikinta, su da halakakkun
Verse 95 — Surah Ash-Shuara 26:95
Da rundunar Ibilisa gaba ɗaya
Verse 96 — Surah Ash-Shuara 26:96
Suka ce: alhali suna a cikinta suna yin husuma
Verse 97 — Surah Ash-Shuara 26:97
Rantsuwa da Allah! Lalle ne mun kasance, haƙiƙa, a cikin ɓata bayyananna
Verse 98 — Surah Ash-Shuara 26:98
A lokacin da muke daidaita ku da Ubangijin halittu
Verse 99 — Surah Ash-Shuara 26:99
Kuma babu abin da ya ɓatar da mu face masu laifi
Verse 100 — Surah Ash-Shuara 26:100
Saboda haka ba mu da waɗansu maceta
Verse 101 — Surah Ash-Shuara 26:101
Kuma ba mu da aboki, masoyi
Verse 102 — Surah Ash-Shuara 26:102
Saboda haka da lalle muna da (damar) komawa, domin mu kasance daga muminai
Verse 103 — Surah Ash-Shuara 26:103
Lalle ne, a cikin wancan akwai aya, kuma mafi yawansu, ba su kasance muminai ba
Verse 104 — Surah Ash-Shuara 26:104
Kuma lalle ne, Ubangijinka, Shi ne Mabuwayi, Mai jin ƙai
Verse 105 — Surah Ash-Shuara 26:105
Mutanen Nuhu sun ƙaryata Manzanni
Verse 106 — Surah Ash-Shuara 26:106
A lokacin da Dan uwansu Nuhu ya ce musu, "Ba za ku ji tsoron Allah ba
Verse 107 — Surah Ash-Shuara 26:107
Lalle ne, zuwa gare ku, ni Manzo ne amintacce
Verse 108 — Surah Ash-Shuara 26:108
To, ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗa'a
Verse 109 — Surah Ash-Shuara 26:109
Kuma ba ni tambayar ku wata ijara a kansa. Ijarata ba ta zama ba face daga Ubangijin halittu
Verse 110 — Surah Ash-Shuara 26:110
Saboda haka, ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗa'a
Verse 111 — Surah Ash-Shuara 26:111
Suka ce: "Ashe, za mu yi imani saboda kai alhali kuwa mafiya ƙasƙanci sun bi ka
Verse 112 — Surah Ash-Shuara 26:112
Ya ce: "Kuma ba ni da sani ga abin da suka kasance sana aikatawa
Verse 113 — Surah Ash-Shuara 26:113
Hisabinsu bai zama ba face ga Ubangijina, da kuna sansancewa
Verse 114 — Surah Ash-Shuara 26:114
Ban zama mai kore muminai ba
Verse 115 — Surah Ash-Shuara 26:115
Ni ba kowa ba ne sai mai gargaɗi mai bayyanawa
Verse 116 — Surah Ash-Shuara 26:116
Suka ce: "Lalle ne, idan ba ka hanu ba, ya Nuhu, (daga maganarka,) haƙiƙa, kana kasancewa daga waɗanda ake jefewa
Verse 117 — Surah Ash-Shuara 26:117
Ya ce: "Ya Ubangijina! Lalle ne mutanena sun ƙaryata ni
Verse 118 — Surah Ash-Shuara 26:118
Sai ka yi hukunci, a tsakanina da tsakaninsu tabbataccen hukanci, kuma ka tsirar da ni, da waɗanda suke tare da ni daga muminai
Verse 119 — Surah Ash-Shuara 26:119
Sai Muka tsirar da shi, shi da waɗanda suke tare da shi, a cikin jirgi wanda aka yi wa lodi
Verse 120 — Surah Ash-Shuara 26:120
Sa'an nan Muka nutsar a bayan haka, da sauran
Verse 121 — Surah Ash-Shuara 26:121
Lalle ne a cikin wannan akwai aya, kuma mafi yawansu, ba su kasance masu imani ba
Verse 122 — Surah Ash-Shuara 26:122
Kuma Lalle ne, Ubangijinka, haƙiƙa, Shi ne Mabuwayi, Mai Rahama
Verse 123 — Surah Ash-Shuara 26:123
Adawa sun ƙaryata Manzanni
Verse 124 — Surah Ash-Shuara 26:124
A lokacin da ɗan'uwansu, Hudu ya ce musu, "Ba za ku yi taƙawa ba
Verse 125 — Surah Ash-Shuara 26:125
Lalle ne ni, zuwa gare ku, haƙiƙa, Manzo ne, amintacce
Verse 126 — Surah Ash-Shuara 26:126
Saboda haka ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗa'a
Verse 127 — Surah Ash-Shuara 26:127
Kuma ba ni tambayar wata ijara a kansa. Ijarata ba ta zama ba, face daga Ubangijin halittu
Verse 128 — Surah Ash-Shuara 26:128
Shin, kuna yin ginin sitadiyo* a kowane tsauni ne, kuna yin wasa
Verse 129 — Surah Ash-Shuara 26:129
Kuma kuna riƙon matsarar ruwa, tsammaninku, ku dawwama
Verse 130 — Surah Ash-Shuara 26:130
Kuma idan kun yi damƙa, sai ku yi damƙar kuna masu tanƙwasawa
Verse 131 — Surah Ash-Shuara 26:131
To ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗa'a
Verse 132 — Surah Ash-Shuara 26:132
Ku ji tsoron wanda Ya taimake ku da abin da kuka sani
Verse 133 — Surah Ash-Shuara 26:133
Ya taimake ku da dabbobin ni'ima da ɗiya
Verse 134 — Surah Ash-Shuara 26:134
Da gonaki da maremari
Verse 135 — Surah Ash-Shuara 26:135
Lalle ne ni, ina ji muku tsoron azabar wani yini mai girma
Verse 136 — Surah Ash-Shuara 26:136
Suka ce: "Daidai ne a kanmu: Ka yi wa'azi ko ba ka kasance daga masu wa'azi ba
Verse 137 — Surah Ash-Shuara 26:137
Wannan abu bai zamo ba face halayen* mutanen farko
Verse 138 — Surah Ash-Shuara 26:138
Kuma mu ba mu zama waɗanda ake yi wa azaba ba
Verse 139 — Surah Ash-Shuara 26:139
Saboda haka suka ƙaryata shi, sai Muka halakar da su. Lalle ne a cikin wannan akwai aya, kuma mafi yawansu ba su kasance masu imani ba
Verse 140 — Surah Ash-Shuara 26:140
Kuma lalle ne, Ubangijinka, haƙiƙa, Shi ne Mabuwayi, Mai jin ƙai
Verse 141 — Surah Ash-Shuara 26:141
Samudawa sun ƙaryata Manzanni
Verse 142 — Surah Ash-Shuara 26:142
A lokacin da ɗan'uwansu Salihu ya ce: "Shin, ba za ku bi Allah da taƙawa ba
Verse 143 — Surah Ash-Shuara 26:143
Lalle ne ni zuwa gare ku, Manzo ne, amintacce
Verse 144 — Surah Ash-Shuara 26:144
Saboda haka ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗa'a
Verse 145 — Surah Ash-Shuara 26:145
Kuma ba ni tambayar ku wata ijara a kansa. Ijarata ba ta zama ba face da a Ubangijin halittu
Verse 146 — Surah Ash-Shuara 26:146
Shin, ana barin ku* a cikin abin da yake a nan, kuna amintattu
Verse 147 — Surah Ash-Shuara 26:147
A cikin gonaki da maremari
Verse 148 — Surah Ash-Shuara 26:148
Da shuke-shuke da dabi nai, 'ya'yan itacensu hirtsi* masu narkewa a ciki
Verse 149 — Surah Ash-Shuara 26:149
Kuma kuna sassaƙa gidaje daga duwatsu, kuna masu alfahari
Verse 150 — Surah Ash-Shuara 26:150
Saboda haka ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗa'a
Verse 151 — Surah Ash-Shuara 26:151
Kada ku yi ɗa'a ga umurnin maɓarnata
Verse 152 — Surah Ash-Shuara 26:152
Waɗanda suke yin ɓarna a cikin ƙasa, kuma ba su kyautatawa
Verse 153 — Surah Ash-Shuara 26:153
Suka ce: "Kai daga masu sihiri kurum kake
Verse 154 — Surah Ash-Shuara 26:154
Ba kowa kake ba, face mutum kamarmu. To, ka zo da wata aya idan ka kasance daga masu gaskiya
Verse 155 — Surah Ash-Shuara 26:155
Ya ce: "Wannan rakuma ce tana da shan* yini, kuma kuna da shan yini sasanne
Verse 156 — Surah Ash-Shuara 26:156
Kada ku shafe ta da cuta har azabar yini mai girma ta shafe ku
Verse 157 — Surah Ash-Shuara 26:157
Sai suka soke ta sa'an nan suka wayi gari suna masu nadama
Verse 158 — Surah Ash-Shuara 26:158
Saboda haka azaba ta kama su. Lalle ne a cikin wannan akwai aya, kuma mafi yawansu, ba su kasance masu imani ba
Verse 159 — Surah Ash-Shuara 26:159
Lalle ne Ubangijinka, haƙi ƙa, Shi ne Mabuwayi, Mai jin ƙai
Verse 160 — Surah Ash-Shuara 26:160
Mutanen Luɗu sun ƙaryata Manzanni
Verse 161 — Surah Ash-Shuara 26:161
A lokacin da ɗan'uwansu,* Luɗu ya ce musu, "Ba za ku yi taƙawa ba
Verse 162 — Surah Ash-Shuara 26:162
Lalle ne ni, zuwa gare ku, Manzo ne, amintacce
Verse 163 — Surah Ash-Shuara 26:163
Saboda haka ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗa'a
Verse 164 — Surah Ash-Shuara 26:164
Kuma ba ni tambayar ku wata ijara, Ijarata ba ta zama ba face daga Ubangijin halittu
Verse 165 — Surah Ash-Shuara 26:165
Shin kuna je wa maza daga cikin talikai
Verse 166 — Surah Ash-Shuara 26:166
Kuma kuna barin abin da Ubangijinku Ya halitta muku daga matanku? A'a, ku mutane ne masu ƙetarewa
Verse 167 — Surah Ash-Shuara 26:167
Suka ce: "Lalle ne haƙiƙa idan ba ka hanu ba, ya Luɗu! Tilas ne kana kasancewa daga waɗanda ake fitarwa (daga gari)
Verse 168 — Surah Ash-Shuara 26:168
Ya ce: "Lalle ne ga aikinku, haƙiƙa, ina daga masu ƙinsa
Verse 169 — Surah Ash-Shuara 26:169
Ya Ubangijina! Ka tsirar da ni da iyalina daga abin da suke aikatawa
Verse 170 — Surah Ash-Shuara 26:170
Saboda haka Muka tsirar da shi, Shi da mutanensa gaba ɗaya
Verse 171 — Surah Ash-Shuara 26:171
Face wata tsohuwa a cikin masu wanzuwa
Verse 172 — Surah Ash-Shuara 26:172
Sa'an nan kuma Muka hallaka wasu
Verse 173 — Surah Ash-Shuara 26:173
Kuma Muka yi ruwan sama a kansu ruwa, sai dai ruwan waɗanda ake yi wa gargaɗi ya munana
Verse 174 — Surah Ash-Shuara 26:174
Lalle ne ga wannan, akwai aya, kuma mafi yawansu ba su kasance masu imani ba
Verse 175 — Surah Ash-Shuara 26:175
Kuma lalle ne Ubangijinka, haƙiƙa, Shi ne Mabuwayi, Mai jin ƙai
Verse 176 — Surah Ash-Shuara 26:176
Ma'abuta ƙunci sun ƙaryata Manzanni
Verse 177 — Surah Ash-Shuara 26:177
A lokacin da Shu'aibu ya ce musu, "Ba za ku yi taƙawa ba
Verse 178 — Surah Ash-Shuara 26:178
Lalle ne ni, zuwa gare ku, Manzo ne, amintacce
Verse 179 — Surah Ash-Shuara 26:179
Saboda haka ku bi Allah da taƙawa kuma ku yi mini ɗa'a
Verse 180 — Surah Ash-Shuara 26:180
Kuma ba ni tambayar ku wata ijara a kansa. Ijarata ba ta zama ba face daga Ubangijin halittu
Verse 181 — Surah Ash-Shuara 26:181
Ku cika mudu, kuma kada ku kasance daga masu sanyawar hasara (ga mutane)
Verse 182 — Surah Ash-Shuara 26:182
Kuma ku yi awo da sikeli daidaitacce
Verse 183 — Surah Ash-Shuara 26:183
Kuma kada ku nakasa wa mutane abubuwansu kuma kada ku yi fasadi a cikin ƙasa kuna masu ɓarna
Verse 184 — Surah Ash-Shuara 26:184
Kuma ku ji tsoron Allah wanda Ya halitta ku, ku da jama'ar farko
Verse 185 — Surah Ash-Shuara 26:185
Suka ce: "Kai dai daga waɗanda suke sihirtattu kawai ne
Verse 186 — Surah Ash-Shuara 26:186
Kuma ba kowa kake ba, face mutum kamarmu kuma lalle ne muna zaton ka, haƙiƙa, daga maƙaryata
Verse 187 — Surah Ash-Shuara 26:187
To ka jefo wani ɓaɓɓake daga sama a kanmu, idan ka kasance daga masu gaskiya
Verse 188 — Surah Ash-Shuara 26:188
Ya ce: "Ubangijina ne Mafi sani ga abin da kuke aikatawa
Verse 189 — Surah Ash-Shuara 26:189
Sai suka ƙaiyata shi, saboda haka, azabar ranar girgije* ta kama su. Lalle ne ita, ta kasance azabar yini mai girma
Verse 190 — Surah Ash-Shuara 26:190
Lalle a cikin wancan haƙika akwai aya, amma mafi yawansu ba su kasance masu imani ba
Verse 191 — Surah Ash-Shuara 26:191
Kuma lalle Ubangijinka, haƙiƙa, Shi ne Mabuwayi, Mai jin ƙai
Verse 192 — Surah Ash-Shuara 26:192
Kuma lalle shi (Alƙur'ani), haƙiƙa, saukarwar Ubangijinhalittu ne
Verse 193 — Surah Ash-Shuara 26:193
Ruhi* amintacce ne ya sauka da shi
Verse 194 — Surah Ash-Shuara 26:194
A kan zuciyarka, domin ka kasance daga masu gargaɗi
Verse 195 — Surah Ash-Shuara 26:195
Da harshe na Larabci mai bayani
Verse 196 — Surah Ash-Shuara 26:196
Kuma lalle shin, haƙiƙa, yana a cikin litattafan (Manzannin) farko
Verse 197 — Surah Ash-Shuara 26:197
Ashe, bai kasance aya ba a gare su, ya zama Malaman Bani Isra'ila sun san shi
Verse 198 — Surah Ash-Shuara 26:198
Kuma da mun saukar da shi a kan sashen Ajamawa
Verse 199 — Surah Ash-Shuara 26:199
Ya karanta shi a kansu, ba su kasance saboda shi masu imani ba
Verse 200 — Surah Ash-Shuara 26:200
Kamar wancan ne! Muka shigar da shi a cikin zukatan masu laifi
Verse 201 — Surah Ash-Shuara 26:201
Ba za su yi imani da shi ba sai sun ga azabar nan mai raɗadi
Verse 202 — Surah Ash-Shuara 26:202
Sai ta taho musu kwatsam, alhali kuwa su, ba su sansance ba
Verse 203 — Surah Ash-Shuara 26:203
Sai su ce: "Shin, mu waɗanda ake yi wa jinkiri ne
Verse 204 — Surah Ash-Shuara 26:204
Ashe, to, da azabar Mu suke neman gaggawa
Verse 205 — Surah Ash-Shuara 26:205
Ashe, to, ka gani, idan Muka jishe su daɗi a shekaru
Verse 206 — Surah Ash-Shuara 26:206
Sa'an nan abin da suka kasance ana yi musu wa'adi (da shi) ya je musu
Verse 207 — Surah Ash-Shuara 26:207
Abin da suka kasance ana jishe su daɗin ba zai tunkuɗe azaba ba daga gare* su
Verse 208 — Surah Ash-Shuara 26:208
Kuma ba Mu halakar da wata alƙarya ba face tana da masu gargaɗi
Verse 209 — Surah Ash-Shuara 26:209
Domin tunatarwa, kuma ba Mu kasance Masu zalunci ba
Verse 210 — Surah Ash-Shuara 26:210
Kuma (Alƙur'ani) Shaiɗanu ba su ɗora sauka da shiba
Verse 211 — Surah Ash-Shuara 26:211
Kuma ba ya kamata a gare su (su Shaiɗanu su sauka da shi), kuma ba su iyawa
Verse 212 — Surah Ash-Shuara 26:212
Lalle ne su, daga saurare, haƙiƙa, waɗanda aka nisantar ne
Verse 213 — Surah Ash-Shuara 26:213
Saboda haka, kada ka kira wani abin bautawa na dabam tare da Allah, sai ka kasance daga waɗanda ake yi wa azaba
Verse 214 — Surah Ash-Shuara 26:214
Kuma ka yi gargaɗi ga danginka mafiya kusanci
Verse 215 — Surah Ash-Shuara 26:215
Kuma ka sassauta fikafikanka* ga wanda ya bi ka daga muminai
Verse 216 — Surah Ash-Shuara 26:216
Sa'an nan idan suka saɓa maka to ka ce: "Lalle ni, barrantacce ne daga abin da kuko aikatawa
Verse 217 — Surah Ash-Shuara 26:217
Kuma ka dogara ga Mabuwayi, Mai jin ƙai
Verse 218 — Surah Ash-Shuara 26:218
Wanda Yake ganin ka a lokacin da kake tashi tsaye
Verse 219 — Surah Ash-Shuara 26:219
Da jujjuyawarka a cikin masu yin sujada
Verse 220 — Surah Ash-Shuara 26:220
Lalle Shi, Shi* ne Mai ji, Masani
Verse 221 — Surah Ash-Shuara 26:221
Shin, (kuna so) in gaya* muku a kan wanda Shaiɗannu kan sauka
Verse 222 — Surah Ash-Shuara 26:222
Sukan sauka a kan dukkan maƙaryaci, mai zunubi
Verse 223 — Surah Ash-Shuara 26:223
Suna jefa (abin da suka) ji, alhali kuwa mafi yawansu maƙaryata ne
Verse 224 — Surah Ash-Shuara 26:224
Kuma mawaƙa* halakakku ne ke bin su
Verse 225 — Surah Ash-Shuara 26:225
Shin, ba ku cewa, lalle ne su, cikin kowane rango suna yin ɗimuwa (su ƙetare haddi) ba
Verse 226 — Surah Ash-Shuara 26:226
Kuma lalle ne, su, suna faɗin abin da ba su aikatawa
Verse 227 — Surah Ash-Shuara 26:227
Face waɗanda suka yi imani suka aikata ayyukan ƙwarai, kuma suka ambaci Allah da yawa, kuma suka rama zalunci, daga bayan an zalunce su. Kuma waɗanda suka yi zalunci, za su sani a wace majuya suke juyawa