Back to Languages

Hausa - Chapter 25 - Al-Furqan

Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink

Verse 1 — Surah Al-Furqan 25:1

Albarka ta tabbata ga wanda Ya saukar da (Littafi) mai rarrabewa a kan bawanSa, domin ya kasance mai gargaɗi ga halitta

Verse 2 — Surah Al-Furqan 25:2

wanda Yake da mulkin sammai da ƙasa kuma bai riƙi abin haihuwa ba, kuma abokin tarayya bai kasance a gare Shi ba a cikin mulkin Sa kuma Ya halitta dukan kowane abu, sa'an nan Ya ƙaddara shi ƙaddarawa

Verse 3 — Surah Al-Furqan 25:3

Kuma suka riƙi abubuwan bautawa, baicin Shi, ba su yin halittar kome alhali su ne ake halittawa kuma ba su mallakar wa kansu wata cuta ko wani amfani, kuma ba su mallakar mutuwa kuma ba su mallakar rayarwa, kuma ba su mallakar tayarwa

Verse 4 — Surah Al-Furqan 25:4

Kuma waɗanda suka kafirta suka ce: "Wannan ba kome ba ne face ƙiron ƙarya da (Muhammadu) ya ƙirƙira shi, kuma waɗansu mutane na dabam suka taimake shi a kansa." To, lalle ne sun je wa zalunci da karkacewar magana

Verse 5 — Surah Al-Furqan 25:5

Kuma suka ce: "Tatsuniyoyi ne na farko ya rurrbuta, sai su ake shibtarsu a gare shi safe da yamma

Verse 6 — Surah Al-Furqan 25:6

Ka ce: "wanda Yake sanin asiri a cikin, sammai da ƙasane Ya saukar da shi. Lalle ne shi Ya kasance Mai gafara, Mai, jin ƙai

Verse 7 — Surah Al-Furqan 25:7

Kuma suka ce: "Mene ne ga wannan Manzo, yana cin abinci, kuma yana tafiya a cikin kasuwanni! Don me ba a saukar da mala'ika zuwa gare shi ba, domin ya kasance mai gargaɗi tare da shi

Verse 8 — Surah Al-Furqan 25:8

Ko kuwa a jefo wata taska zuwa gare shi, ko kuwa wata gona ta kasance a gare shi, yana ci daga gare ta?" Kuma azzalumai suka ce: "Ba ku bin kowa, face mutum sihirtacce

Verse 9 — Surah Al-Furqan 25:9

Ka duba yadda suka buga maka misalai sai suka ɓace, domin haka ba su iya bin tafarki

Verse 10 — Surah Al-Furqan 25:10

Albarka ta tabbata ga wanda idan Ya so, Ya sanya maka mafi alheri daga wannan (abu): gonaki, ƙoramu na gudana daga ƙarƙashinsu, kuma Ya sanya maka manyan gidaje

Verse 11 — Surah Al-Furqan 25:11

A'a, sun ƙaryata game da Sa'a, alhali kuwa Mun yi tattalin wuta mai tsanani ga wanda ya ƙaryata (manzanni) game da Sa'a

Verse 12 — Surah Al-Furqan 25:12

Idan ta gan su daga wani wuri mai nisa, sai su ji sautin fushi da wani ruri nata

Verse 13 — Surah Al-Furqan 25:13

Kuma idan an jefa su a wani wuri mai ƙunci daga gare ta, suna waɗanda aka ɗaure ciki daidai, sai su kirayi halaka a can

Verse 14 — Surah Al-Furqan 25:14

Kada ku kirayi halaka guda, kuma ku kirayi halaka mai yawa

Verse 15 — Surah Al-Furqan 25:15

Ka ce: "Shin, wancan ne mafi alheri, ko kuwa Aljannar dawwama wadda aka yi wa'adi ga masu taƙawa? Ta zama, a gare su, sakamako da makoma

Verse 16 — Surah Al-Furqan 25:16

Suna da abin da suke so, a cikinta suna madawwama. Wannan ya kasance wa'adi abin tambaya a kan Ubangijinka

Verse 17 — Surah Al-Furqan 25:17

Kuma ranar da Yake tara su da abin da suke bauta wa, baicin Allah sai Ya ce: "Shin ku nekuka ɓatar, da bayiNa, waɗannan, ko kuwa su ne suka ɓata daga hanya

Verse 18 — Surah Al-Furqan 25:18

suka ce: "Tsarki ya tabbata a gare Ka, ba ya kasancewa agare mu, mu riƙi waɗansu majiɓinta, baicin Kai, kuma amma Ka jiyar da su daɗi su da ubanninsu har suka manta da Tunatarwa, kuma sun kasance mutane ne halakakku

Verse 19 — Surah Al-Furqan 25:19

To, lalle ne, sun ƙaryata game da abin da kuke cewa, saboda haka ba ku iya karkatarwa ga (maganarsu), kuma ba ku iya taimako (ga hana azaba), kuma wanda ya yi zalunci a cikinku za Mu ɗanɗana masa azaba mai girma

Verse 20 — Surah Al-Furqan 25:20

Kuma ba Mu aika ba, a gabaninka daga Manzanni, face lalle su haƙiƙa suna cin abinci kuma suna tafiya a cikin kasuwoyi. Kuma Mun sanya sashen mutane fitina ga sashe. Shin kuna yin haƙuri? Kuma Ubangijia Ya kasance Mai gani

Verse 21 — Surah Al-Furqan 25:21

Kuma waɗanda ba su fatan haɗuwa da Mu suka ce: "Don me ba a saukar da mala'iku ba a kanmu, ko kuwa mu ga Ubangijinmu?" Lalle ne sun kangara a cikin rayukansu, kuma suka yi tsaurin kai, tsaurin kai mai girma

Verse 22 — Surah Al-Furqan 25:22

A ranar da suke ganin mala'iku babu bushara a yinin nan ga masu laifi kuma suna cewa,"Allah Ya kiyashe* mu

Verse 23 — Surah Al-Furqan 25:23

Kuma Muka gabata zuwa ga abin da suka aikata daga aiki, sai Muka sanya shi ƙura watsattsiya

Verse 24 — Surah Al-Furqan 25:24

Ma'abuta Aljanna a ranar nan su ne mafi alheri ga matabbata kuma mafi kyaun wurin ƙailula

Verse 25 — Surah Al-Furqan 25:25

Kuma a ranar da sama take tsattsagewa tare da gizagizai, kuma a saukar da mala'iku, saukarwa

Verse 26 — Surah Al-Furqan 25:26

Mulki a ranar nan, na gaskiya, yana ga Mai rahama, kuma ya zama yini, a kan kafirai, mai tsanani

Verse 27 — Surah Al-Furqan 25:27

Kuma ranar da azzalumi yake cizo a kan hannayensa, yana cewa "Ya kaitona! (A ce dai) na riƙi hanya tare da Manzo

Verse 28 — Surah Al-Furqan 25:28

Ya kaitona! (A ce dai) ban riƙi wane masoyi ba

Verse 29 — Surah Al-Furqan 25:29

Lalle ne, haƙiƙa ya ɓatar da ni daga Tunawa a bayan (Tunawar) ta je mini."Kuma Shaiɗan ya zama mai zumɓulewa ga mutum

Verse 30 — Surah Al-Furqan 25:30

Kuma Manzo ya ce: "Ya Ubangijina! Lalle mutanena sun riƙi wannan Alƙur'ani abin ƙauracewa

Verse 31 — Surah Al-Furqan 25:31

Kuma kamar haka ne, Muka sanya maƙiyi daga masu laifi ga kowane Annabi. Kuma Ubangijinka Ya isa ga zama Mai Shiryarwa, kuma Mai taimako

Verse 32 — Surah Al-Furqan 25:32

Kuma waɗanda suka kafirta suka ce: "Don me ba a saukar da Alƙur'ani a kansa ba, jimla guda?" kamar wancan! Domin Mu ƙarfafa zuciyarka game da shi, kuma Mun jeranta karanta shi da hankali jerantawa

Verse 33 — Surah Al-Furqan 25:33

Kuma ba za su zo maka da wani misali ba, face Mun je maka da gaskiya da mafi kyau ga fassara

Verse 34 — Surah Al-Furqan 25:34

Waɗanda ake tayarwa a kan fuskokinsu, zuwa ga Jahannama, waɗancan su ne mafi sharri ga wuri, kuma mafi ɓacewa ga hanya

Verse 35 — Surah Al-Furqan 25:35

Kuma lalle ne, Mun bai wa Musa Littafi, kuma Mun sanya ɗan'uwansa, Haruna, mataimaki tare da shi

Verse 36 — Surah Al-Furqan 25:36

Sai Muka ce: "Ku tafi, ku biyu, zuwa ga mutanen nan waɗanda suka ƙaryata game da ayo yin Mu." sai Muka darkake su, darkakewa

Verse 37 — Surah Al-Furqan 25:37

Kuma mutanen Nuhu, a lokacin da suka ƙaryata Manzanni, Muka nutsar da su, kuma Muka sanya su wata aya ga mutane, kuma Muka yi tattalin azaba mai raɗaɗi ga azzalumai

Verse 38 — Surah Al-Furqan 25:38

Da Adawa da Samudawa, da mutanen Rassi, da waɗansu al'ummomi, a tsakanin wannan, masu yawa

Verse 39 — Surah Al-Furqan 25:39

Kuma kowannensu Mun buga masa misalai, kuma kowanne Mun halakar da (shi), halakarwa

Verse 40 — Surah Al-Furqan 25:40

Kuma lalle ne, haƙiƙa, (¡uraishi) sun je a kan alƙaryar nan wadda aka yi wa ruwa, ruwan azaba. Shin, ba su kasance sun gan ta ba? A'a, sun kasance ba su ƙaunar tayarwa (a ¡iyama)

Verse 41 — Surah Al-Furqan 25:41

Kuma idan sun gan ka, ba su rikon ka face da izgili, (suna cewa) "Shin, wannan ne wanda Allah Ya aiko, Manzo

Verse 42 — Surah Al-Furqan 25:42

Lalle ne, ya yi kusa ya ɓatar da mu daga Ubangijinmu, in ba domin da muka yi haƙuri a kansu ba."Kuma za su sani a lokacin da suke ganin azaba, wane ne mafi ɓacewa ga hanya

Verse 43 — Surah Al-Furqan 25:43

Shin, ka ga wanda ya riƙi UbangiJinsa son zuciyarsa? shin, to, kai ne ke kasancewa mai tsaro a kansa

Verse 44 — Surah Al-Furqan 25:44

Ko kana zaton cewa mafi yawansu suna ji, ko kuwa suna hankali? su ba su zama ba face dabbobin gida* suke. A'a, su ne mafi ɓacewa ga hanya

Verse 45 — Surah Al-Furqan 25:45

Ashe, ba ka duba ba zuwa ga Ubangijinka, yadda Ya miƙe inuwa? Kuma da Ya so da Ya bar ta tsaye cif, sa'an nan Muka sanya rana mai nuni a kanta

Verse 46 — Surah Al-Furqan 25:46

Sa'an nan Muka karɓe ta (inuwa) zuwa gare Mu, karɓa mai sauƙi

Verse 47 — Surah Al-Furqan 25:47

Kuma shi ne wanda Ya sanya muku dare ya zama tufa da barci ya zama hutawa, da yini ya zama lokacin tashi (kamar Tashin ¡iyama)

Verse 48 — Surah Al-Furqan 25:48

Kuma Shi ne Ya aika iskokin bushara gaba ga rahamar Sa, kuma Muka saukar da ruwa mai tsarkakewa daga sama

Verse 49 — Surah Al-Furqan 25:49

Domin Mu rayar, game da shi, gari matacce, kuma Mu shayar da shi dabbobi da mutane masu yawa daga abin da Muka halitta

Verse 50 — Surah Al-Furqan 25:50

Kuma lalle ne haƙiƙa Mun sarrafa* shi (Alƙur'ani) a tsakaninsu, domin su yi tunani, sai dai mafi yawan mutanen sun ƙi face kafirci

Verse 51 — Surah Al-Furqan 25:51

Kuma da Mun so, haƙiƙa da Mun aika da mai gargaɗi* a ciƙin kowace alƙarya

Verse 52 — Surah Al-Furqan 25:52

Saboda haka kada ka yi ɗa'a ga kafirai, ka yake su, da shi, yaƙi mai girma

Verse 53 — Surah Al-Furqan 25:53

Kuma shi ne Ya gauwaya tekuna biyu, wannan mai dadi, mai sauƙin haɗiya, kuma wannan gishiri gurbatacce, kuma Ya sanya wani shamaki a tsakaninsu da kariya mai shamakacewa

Verse 54 — Surah Al-Furqan 25:54

Kuma Shi ne Ya halitta mutum daga ruwa, sai Ya sanya shi nasaba da surukuta, kuma Ubangijinka Ya kasance Mai ikon yi

Verse 55 — Surah Al-Furqan 25:55

Kuma suna bauta wa, baicin Allah, abin da ba ya amfanin su, kuma ba ya cutar su, kuma kafiri ya kasance mai taimakon (Shaiɗan) a kan Ubangijinsa

Verse 56 — Surah Al-Furqan 25:56

Ba Mu aika ka ba sai kana mai bayar da bushara, kuma mai gargaɗi

Verse 57 — Surah Al-Furqan 25:57

Ka ce: "Ba ni tambayar ku wata ijara a kansa face wanda ya so ya riƙi wata hanya* zuwa ga Ubangijinsa

Verse 58 — Surah Al-Furqan 25:58

kuma ka dogara a kan Rayayye wanda ba Ya mutuwa, kuma ka yi tasbihi game da gode Masa. Kuma Ya isa zama Mai ƙididdigewa ga laifuffukan bayinSa

Verse 59 — Surah Al-Furqan 25:59

Wanda Ya halitta sammai da ƙasa da abin da yake a tsakaninsu, a cikin kwanuka shida sa'an nan Ya daidaitu a kan Al'arshi Mai rahama, sai ka tambayi mai bayar da labari game da Shi

Verse 60 — Surah Al-Furqan 25:60

Idan aka ce musu, "Ku yi sujada ga Mai rahama." Sai su ce: "Mene ne Mai rahama? Ashe za mu yi sujada ga abin da kuke umurnin mu?"Kuma wannan (magana* ta ƙara musu gudu)

Verse 61 — Surah Al-Furqan 25:61

Albarka ta tabbata ga Wanda Ya sanya masaukai* (na tafiyar wata) a cikin sama kuma Ya sanya fitila da wata mai haskakewa a cikinta

Verse 62 — Surah Al-Furqan 25:62

Kuma Shi ne wanda Ya sanya dare da yini a kan mayewa, ga wanda yake son ya yi tunani, ko kuwa ya yi nufin ya gode

Verse 63 — Surah Al-Furqan 25:63

Kuma bayin Mai rahama* su ne waɗanda ke yin tafiya a kan ƙasa da sauƙi, kuma idan jahilai sun yi musu magana, sai su ce: "Salama" (a zama lafiya)

Verse 64 — Surah Al-Furqan 25:64

Kuma waɗanda suke kwana suna masu sujada da tsayi a wurin Ubangijinsu

Verse 65 — Surah Al-Furqan 25:65

Kuma waɗanda suke cewa "Ya Ubangijinmu! Ka karkatar da azabar Jahannama daga gare mu. Lalle ne, azabarta ta zama tara

Verse 66 — Surah Al-Furqan 25:66

Lalle ne ita ta munana ta zama wurin tabbata da mazauni

Verse 67 — Surah Al-Furqan 25:67

Kuma waɗanda suke idan sun ciyar, ba su yin ɓarna, kuma ba su yin ƙwauro, kuma (ciyarwarsu) sai ta kasance a tsakanin wancan da tsakaitawa

Verse 68 — Surah Al-Furqan 25:68

Kuma waɗanda ba su kiran wani ubangiji tare da Allah, kuma ba su kashe rai wanda Allah Ya haramta face da hakki kuma ba su yin zina. Kuma wanda ya aikata wancan, zai gamu da laifuffuka

Verse 69 — Surah Al-Furqan 25:69

A riɓanya masa azaba a Ranar ¡iyama. Kuma ya tabbata a cikinta yana wulakantacce

Verse 70 — Surah Al-Furqan 25:70

Sai wanda ya tuba, kuma ya yi imani, kuma ya aikata aiki na ƙwarai to, waɗancan Allah Yana musanya miyagun ayyukansu da masu kyau. Allah Ya kasance Mai gafara Mai jin ƙai

Verse 71 — Surah Al-Furqan 25:71

Kuma wanda ya tuba,* kuma ya aikata aiki mai kyau, to, lalle ne sai ya tuba zuwa gaAllah

Verse 72 — Surah Al-Furqan 25:72

Kuma waɗanda suke ba su yin shaidar zur, kuma idan sun shuɗe ga yasassar magana sai su shuɗe suna masu mutumci

Verse 73 — Surah Al-Furqan 25:73

Kuma waɗanda suke idan an tunatar da su da ayoyin Allah, ba su saukar da kai, suna kurame* da makafi

Verse 74 — Surah Al-Furqan 25:74

Kuma waɗanda suke cewa "Ya Ubangijinmu! Ka ba mu sanyin idanu daga matanmu da zuriyarmu, kuma Ka sanya* mu shugabanni ga masu taƙawa

Verse 75 — Surah Al-Furqan 25:75

Waɗannan ana saka musu da bene, saboda haƙurin da suka yi, kuma a haɗa su, a cikinsa, da gaisuwa da aminci

Verse 76 — Surah Al-Furqan 25:76

Suna madawwama a cikinsa. Ya yi kyau ga zama matabbaci da mazauni

Verse 77 — Surah Al-Furqan 25:77

Ka ce: "Ubangijina ba Ya kula da ku in ba domin addu'arku* ba. To, lalle ne, kun ƙaryata, saboda haka al'amarin za ya zama malizimci