Back to Languages

Hausa - Chapter 24 - An-Nur

Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink

Verse 1 — Surah An-Nur 24:1

(Wannan) sura ce. Mun saukar da ita, kuma Mun wajabta ta, kuma Mun saukar da ayoyi bayyanannu a cikinta, domin ku riƙa tunawa

Verse 2 — Surah An-Nur 24:2

Mazinaciya da mazinaci,* to, ku yi bulala ga kowane ɗaya daga gare su, bulala ɗari. Kuma kada tausayi ya kama ku game da su a cikin addinin Allah idan kun kasance kuna yin imani da Allah da Ranar Lahira. Kuma wani yankin jama, a daga muminai, su halarci azabarsu

Verse 3 — Surah An-Nur 24:3

Mazinaci ba ya aure* face da mazinaciya ko mushirika, kuma mazinaciya babu mai aurenta face mazinaci ko mushiriki. Kuma an haramta wannan a kan muminai

Verse 4 — Surah An-Nur 24:4

Kuma waɗanda ke jifar* mata masu kamun kai, sa'an nan kuma ba su je da shaidu huɗu ba to, ku yi musu bulala, bulala tamanin, kuma kada ku karɓi wata shaida tasu, har abada. Waɗancan su ne fasiƙai

Verse 5 — Surah An-Nur 24:5

Face waɗanda suka tubadaga bayan wannan, kuma suka gyaru, to lalle ne Allah Mai gafara ne, Mai jin ƙai

Verse 6 — Surah An-Nur 24:6

Kuma waɗanda ke jifar matan* aurensu kuma waɗansu shaidu ba su kasance a gare su ba, face dai kansu, to, shaidar ɗayansu, shaida huɗu ce da Allah, 'Lalle shi, haƙiƙa, yana daga magasganta

Verse 7 — Surah An-Nur 24:7

Kuma ta biyar cewa 'La'anar Allah ta tabbata a kansa, idan ya kasance daga maƙaryata

Verse 8 — Surah An-Nur 24:8

Kuma yana tunkuɗe mata azaba ta yi shaida, shaida huɗu da Allah, 'Lalle shi haƙiƙa, yana daga maƙaryata

Verse 9 — Surah An-Nur 24:9

Kuma ta biyar cewa 'Hushin Allah ya tabbata a kanta idan ya kasance daga magasganta

Verse 10 — Surah An-Nur 24:10

Kuma ba domin falalar Allah ba a kanku, da rahamar Sa, kuma cewa Allah Mai karɓar tuba ne, Mai hikima

Verse 11 — Surah An-Nur 24:11

Lalle ne waɗanda* suka zo da ƙiren ƙarya waɗansu jama'a ne daga gare ku, kada ku yi zatonsa sharri ne a gare ku. A'a, alheri ne gare ku. Kowane mutum daga gare su na da sakamakon abin da ya sana'anta na zunubi, kuma wanda ya jiɓinci girmansa, daga gare su, yana da azaba mai girma

Verse 12 — Surah An-Nur 24:12

Don me a lokacin da kuka ji shi muminai maza da muminai mata ba su yi zaton alheri game da kansu ba kuma su ce: "Wannan ƙiren ƙarya ne bayyananne

Verse 13 — Surah An-Nur 24:13

Don me ba su zo da shaidu huɗu a kansa ba? To idan ba su kawo shaidun nan ba to, waɗannan, a wurin Allah, su ne maƙaryata

Verse 14 — Surah An-Nur 24:14

Kuma ba domin falalar Allah ba a kanku da rahamarSa a cikin duniya da Lahira. Lalle ne, da azaba mai girma ta shafe ku a cikin abin da kuka kutsa da magana a cikinsa

Verse 15 — Surah An-Nur 24:15

A lokacin da kuke marabarsa da harsunanku kuma kuna cewa da bakunanku abin da ba ku da wani ilmi game da shi, kuma kuna zaton sa mai sauƙi alhali kuwa, shi a wurin Allah, babba ne

Verse 16 — Surah An-Nur 24:16

Kuma don me a lokacin da kuka ji shi, ba ku ce ba, "Ba ya yiwuwa a gare mu, mu yi magana a game da wannan. Tsarki ya tabbata a gare Ka, wannan ƙiren ƙarya ne mai girma

Verse 17 — Surah An-Nur 24:17

Allah Yana yi muku wa'azi, kada ku koma ga irinsa, har abada, idan kun kasance muminai

Verse 18 — Surah An-Nur 24:18

Kuma Allah Yana bayyana muku ayoyin Sa, kuma Allah Masani ne, Mai hikima

Verse 19 — Surah An-Nur 24:19

Lalle ne waɗanda ke son alfasha ta watsu ga waɗanda suka yi imani suna da azaba mai raɗaɗi a cikin duniya da Lahira. KumaAllah, Shi ne Ya sani, alhali kuwa, ku ba ku sani ba

Verse 20 — Surah An-Nur 24:20

Kuma ba domin falalar Allah ba a kanku da rahamar Sa. Kuma lalle ne Allah Mai tausayi ne, Mai jin ƙai

Verse 21 — Surah An-Nur 24:21

Ya ku waɗanda suka yi imani, kada ku bi hanyoyin Shaiɗan. Kuma wanda ke bin hanyoyin Shaiɗan, to, lalle ne shi, yana umurni da yin alfasha da abin da ba a sani ba, kuma ba domin falalar Allah ba a kanku da rahamarSa, babu wani mutum daga gare ku da zai tsarkaka har abada, kuma amma Allah Yana tsarkake wanda Yake so kuma Allah Mai ji ne, Masani

Verse 22 — Surah An-Nur 24:22

Kuma kada* ma'abuta falala daga gare ku da mawadata su rantse ga rashin su bayar da alheri ga ma'abuta zumunta da miskinai da muhajirai, a cikin hanyar Allah. Kuma su yafe, kuma su kau da kai. shin, ba ku son Allah Ya gafarta muku, alhali Allah Mai gafara ne, Mai jin ƙai

Verse 23 — Surah An-Nur 24:23

Lalle ne waɗannan da suke jifar mata masu kamun kai gafilai* muminai, an la'ane su, a cikin duniya da Lahira, kuma sunada azaba mai girma

Verse 24 — Surah An-Nur 24:24

A ranar da harsunansu da hannayensu, da ƙafafunsu suke bayar da shaida a kansu, game da abin da suka kasance suna aikatawa

Verse 25 — Surah An-Nur 24:25

a ranar dl Allah Yake cika musu sakamakonsu tabbatacce kuma suna sanin (cewa) lalle Allah, Shi ne Gaskiya bayyananna

Verse 26 — Surah An-Nur 24:26

Miyagun mata domin miyagun maza suke, kuma miyagun* maza domin miyagun mata suke kuma tsarkakan mata domin tsarkakan maza suke kuma tsarkakan maza domin tsarkakan mata suke. waɗancan su ne waɗanda ake barrantawa daga abin da (masu ƙazafi) suke faɗa kuma suna da gafara da arziki na karimci

Verse 27 — Surah An-Nur 24:27

Ya ku waɗanda suka yi imani! Kada ku shiga gidaje waɗanda ba gidajenku ba sai kun sami izni, kuma kun yi sallama* a kan ma'abutansu. Wannan ne mafi alheri gare ku, tsammaninku, za ku tuna

Verse 28 — Surah An-Nur 24:28

To, idan ba ku sami kowa a cikinsu ba, to, kada ku shige su, sai an yi muku izni. Kuma idan an ce muku, "Ku koma." Sai ku koma, shi ne mafi tsarkaka a gare ku. Kuma Allah game da abin da kuke aikatawa, Masani ne

Verse 29 — Surah An-Nur 24:29

Babu laifi a kanku, ga ku shiga gidaje waɗanda ba zaunannu ba, a cikinsu akwai waɗansu kaya naku. Kuma Allah Yana sanin abin da kuke nunawa, da abin dakuke ɓayewa

Verse 30 — Surah An-Nur 24:30

Ka ce wa muminai maza su runtse daga ganinsu, kuma su tsare farjojinsu.* wannan shi ne mafi tsarki a gare su. Lalle ne, Allah, Mai ƙididdigewa ne ga abin da suke sana'antawa

Verse 31 — Surah An-Nur 24:31

Kuma ka ce wa muminai mata su runtse daga gannansu, kuma su tsare farjojinsu kuma kada su bayyana ƙawarsu face abin da ya bayyana daga gare ta, kuma su doka da mayafansu a kan wuyan rigunansu, kuma kada su nuna ƙawarsu face ga mazansu ko ubanninsu ko ubannin mazansu, ko ɗiyansu, ko ɗiyan mazansu, ko 'yan'uwansu, ko ɗiyan 'yan'uwansu mata, ko matan* ƙungiyarsu, ko abin da hannayensu na dama suka mallaka, ko mabiya wasun masu bukatar mata daga maza, ko jarirai waɗanda. ba su tsinkaya a kan al'aurar mata. Kuma kada su yi duka da ƙafafunsu domin a san abin da suke ɓoyewa daga ƙawarsu. Kuma ku tuba zuwa ga Allah gaba ɗaya, ya ku muminai! Tsammaninku, ku sami babban rabo

Verse 32 — Surah An-Nur 24:32

Kuma ku aurar da gwauraye daga gare ku, da salihai daga bayinku, da kuyanginku. Idan sun kasance matalauta Allah zai wadatar da su daga falalarSa. Kuma Allah Mawadaci ne, Masani

Verse 33 — Surah An-Nur 24:33

Kuma waɗannan da ba su sami aure ba su kame kansu har Allah Ya wadatar da su daga, falalarsa. Kuma waɗanda ke neman fansa daga abin da hannuwanku na dama suka mallaka, to, ku ɗaura musu fansa idan kun san akwai wani alheri a cikinsu kuma ku ba su wani abu daga dukiyar Allah wannan da Ya ba ku. Kuma kada ku tilasta kuyanginku a kan yin zina, idan sun yi nufin tsaron kansu,* domin ku nemi rayuwar duniya, kuma wanda ya tilasta su to, lalle Allah, a bayan tilasta su, Mai gafara ne, Mai jin ƙai

Verse 34 — Surah An-Nur 24:34

Kuma lalle ne Mun saukar zuwa gare ku, ayoyi masu bayyanawa, da misali daga waɗanda suka shige daga gabaninku, da wa'azi ga masu taƙawa

Verse 35 — Surah An-Nur 24:35

Allah ne Hasken sammai da ƙasa, misalin HaskenSa, kamar taga, a cikinta akwai fitila, fitilar a cikin ƙarau, ƙarau ɗin kamar shi tauraro ne mai tsananin haske, ana kunna shi daga wata itaciya mai albarka, ta zaituni, ba bagabashiya ba kuma ba bayammaciya ba, manta na kusa ya yi haske, kuma ko wuta ba ta shafe shi ba, haske a kan haske, Allah na shiryar da wanda Yake so zuwa ga HaskenSa. Kuma Allah na buga misalai ga mutane, kuma Allah game da dukan kome, Masani ne

Verse 36 — Surah An-Nur 24:36

A cikin waɗansu gidaje waɗanda Allah Ya yi umurnin a ɗaukaka kuma a ambaci sunansa a cikinsu, suna yin tasbihi a gare Shi a cikinsu, safe da maraice

Verse 37 — Surah An-Nur 24:37

Waɗansu maza, waɗanda wani fatauci ba ya shagaltar da su, kuma sayarwa ba ta shagaltar da su daga ambaton Allah, da tsai da salla da bayar da zakka, suna tsoron wani yini wanda zukata suna bibbirkita a cikinsa, da gannai

Verse 38 — Surah An-Nur 24:38

Domin Allah Ya saka musu da mafi kyaun abin da suka aikata, kuma Ya ƙara musu daga falalarsa. Kuma Allah Yana azurta wanda Yake so, ba da lissafi ba

Verse 39 — Surah An-Nur 24:39

Kuma waɗanda suka ƙafirta ayyukansu suna kamar ƙawalwalniya ga faƙo, mai ƙishirwa yana zaton sa ruwa, har idan ya je masa bai iske shi kome ba, kuma ya sami* Allah a wurinsa, sai Ya cika masa hisabinsa. Kuma Allah Mai gaggawar sakamako ne

Verse 40 — Surah An-Nur 24:40

Ko kuwa kamar* duffai a cikin teku mai zurfi, taguwar ruwa tana rufe da shi, daga bisansa akwai wata taguwa, daga bisansa akwai wani girgije, duffai sashensu a bisa sashe, idan ya fitar da tafinsa ba ya kusa ya gan shi. Kuma wanda Allah bai sanya masa haske ba, to, ba ya da wani haske

Verse 41 — Surah An-Nur 24:41

Shin, ba ka gani ba (cewa) lalle ne Allah, Wanda yake a cikin sammai da ƙasa suna yi Masa tasbihi, kuma tsuntsaye suna masu sanwa, kowane lalle ya san sallarsa da tasbihinsa kuma Allah Masani ne ga abin da suke aikatawa

Verse 42 — Surah An-Nur 24:42

Mulkin sammai da ƙasa ga Allah kawai yake, kuma zuwa ga Allah makoma take

Verse 43 — Surah An-Nur 24:43

Ashe, ba ka gani ba, lalle ne Allah Yana kora girgije, sa'an nan kuma Ya haɗa a tsakaninsa sa'an nan kuma Ya sanya shi mai hauhawar juna? Sai ka ga ruwa yana fita daga tsattsakinsa, kuma Ya saukar daga waɗansu duwatsu a cikinsa na ƙanƙara daga sama, sai ya samu wanda Yake so da shi, kuma Ya karkatar da shi daga barin wanda Yake so. Hasken walƙiyarsa Yana kusa ya tafi da gannai

Verse 44 — Surah An-Nur 24:44

Allah Yana juyar da dare da yini. Lalle ne a cikin wannan akwai abin kula ga ma'abuta gannai

Verse 45 — Surah An-Nur 24:45

Kuma Allah ne Ya halitta kowace dabba daga ruwa. To, daga cikinsu akwai waɗanda ke tafiya a kan cikinsu, kuma daga cikinsu akwai waɗanda ke tafiya a kan ƙafafu biyu, kuma daga cikinsu akwai waɗanda ke tafiya akan huɗu. Allah Yana halitta abin da Yake so, lalle Allah, a kan kowane abu, Mai ikon yi ne

Verse 46 — Surah An-Nur 24:46

Lalle ne haƙiƙa Mun saukar da ayoyi, masu bayyanawa. Kuma Allah Yana shiryar da wanda Yake so zuwa ga hanya madaidaiciya

Verse 47 — Surah An-Nur 24:47

Kuma suna cewa, "Mun yi imani da Allah da kuma Manzo, kuma mun yi ɗa'a." Sa'an nan kuma wata ƙungiya daga gare su, su juya daga bayan wancan. Kuma waɗancan ba muminai ba ne

Verse 48 — Surah An-Nur 24:48

Kuma idan aka kira su zuwa ga Allah da ManzonSa, domin Ya yi hukunci* a tsakaninsu, sai ga wata ƙnngiya daga gare su suna masu bijirewa

Verse 49 — Surah An-Nur 24:49

Kuma idan hakki ya kasance a gare su, za su je zuwa gare shi, snna masu miƙa wuya

Verse 50 — Surah An-Nur 24:50

Shin, a cikin zukatansu akwai cuta ne, ko kuwa suna tsoron Allah Ya yi zalunci a kansu da ManzonSa? A'a, waɗancan su ne azzalumai

Verse 51 — Surah An-Nur 24:51

Maganar muminai, idan aka kira su zuwa ga Allah da Manzon Sa domin Ya yi hukunci a tsakaninsu takan kasance kawai su ce "Mun ji, kuma mun yi ɗa'a, Kuma waɗannan su ne masu cin nasara

Verse 52 — Surah An-Nur 24:52

Kuma wanda ya yi ɗa'a ga Allah da ManzonSa, kuma ya ji tsoron Allah, ya kuma bi Shi da taƙawa to waɗannan su ne masu babban rabo

Verse 53 — Surah An-Nur 24:53

Kuma suka rantse da Allah iyakar rantsuwarsu, 'Lalle ne idan ka umurce su haƙiƙa suna fita.' Ka ce, "Kada ku rantse, ɗa'a sananna ce! Lalle ne, Allah Mai ƙididdigewa ne ga abin da kuke aikatawa

Verse 54 — Surah An-Nur 24:54

Ka ce: "Ku yi ɗa'a ga Allah kuma ku yi ɗa'a ga Manzo. To, idan kun juya, to, a kansa akwai abin da aka aza masa kawai, kuma a kanku akwai abin da aka aza muku kawai, Kuma idan kun yi masa ɗa'a za ku shiryu. Kuma babu abin da yake a kan Manzo face iyarwa bayyananna

Verse 55 — Surah An-Nur 24:55

Allah Ya yi wa'adi ga waɗanda suka yi imani daga gare. Ku, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, lalle zai shugabantar da su a cikin ƙasa kamar yadda Ya shugabantar da waɗanda suke daga gabaninsu, kuma lalle ne zai tabbatar musu da addininsu wanda Ya yardar musu, kuma lalle ne Yana musanya musu daga bayan tsoronsu da aminci, suna bauta Mini ba su haɗa kome da Ni. Kuma wanda ya kafirta a bayan wannan, to, waɗancan, su ne fasiƙai

Verse 56 — Surah An-Nur 24:56

Kuma ku tsayar da salla, kuma ku bayar da zakka, kuma ku yi ɗa'a ga Manzo, tsammaninku a yi muku rahama

Verse 57 — Surah An-Nur 24:57

Kada lalle ka yi zaton waɗanda suka kafirta za su buwaya a cikin ƙasa, kuma makomarsu wuta ce, kuma lalle ne makomar ta munana

Verse 58 — Surah An-Nur 24:58

Ya ku waɗanda suka yi imani! Waɗannan da hannuwanku na dama suka mallaka da waɗanda ba su isa mafarki ba daga cikinku, su nemi izni* sau uku; daga gabanin sallar alfijir da lokacin da kuke ajiye tufafinku saboda zafin rana, kuma daga bayan sallar isha'i. Su ne al'aurori uku a gare ku. Babu laifi a kanku kuma babu a kansu a bayansu. Su masu kewaya ne a kanku sashenku a kan sashe. Kamar wannan ne Allah Yake bayyana ayoyin Sa a gare ku. Kuma Allah Masani ne, Mai hikima

Verse 59 — Surah An-Nur 24:59

Kuma idan yara daga cikinku suka isa mafarki to su nemi izni, kamar yadda waɗanda suke a gabaninsu suka nemi iznin. Kamar wannan ne Allah Yake bayyana ayoyin Sa a gare ku, kuma Allah Masani ne, Mai hikima

Verse 60 — Surah An-Nur 24:60

Kuma tsofaffi daga mata, waɗanda ba su fatan wani aure to, babu laifi a kansu su ajiye tufafinsu, ba suna masu fitar da ƙawa ba, kuma su tsare mutuncinsu shi ne mafi alheri a gare su. Kuma Allah Mai ji ne, Masani

Verse 61 — Surah An-Nur 24:61

Babu laifi a kan makaho, kuma babu laifi a kan gurgu, kuma babu laifi a kan majiyyaci, kuma babu laifi a kan kowanenku, ga ku ci (abinci) daga gidajenku, ko daga gidajen ubanninku, ko daga gidajen uwayenku, ko daga gidajen 'yan'uwanku maza, ko daga gidajen 'yan'uwanku mata, ko daga gidajen baffanninku, ko daga gidajen gwaggwanninku, ko daga gidajen kawunnanku, ko daga gidajen innoninku ko abin da kuka mallaki mabuɗansa ko abokinku babu laifi a gare ku ku ci gaba ɗaya, ko dabam- dabam. To, idan kun shiga wasu gidaje, ku yi sallama a kan kawunanku,* gaisuwa ta daga wurin Allah mai albarka, mai daɗi. Kamar wancan ne Allah Yake bayyana muku ayoyinSa, tsammaninku ku yi hankali

Verse 62 — Surah An-Nur 24:62

Waɗanda ke muminai sosai, su ne waɗanda suka yi imani da Allah da ManzonSa, kuma idan sun kasance tare da shi, a kan wani al'amari na aikin gayya, ba su tafiya sai sun neme shi izni. Lalle ne, waɗanda suke biɗar ka izni waɗancan su ne suke yin imani da Allah da ManzonSa. To, idan sun neme ka izni saboda wani sha'aninsu, to, ka yi izni ga wanda ka so daga gare su, kuma ka nema musu gafara daga Allah. Lalle Allah Mai gafara ne, Mai jin ƙai

Verse 63 — Surah An-Nur 24:63

Kada ku sanya kiran Manzo* a tsakaninku kamar kiran sashenku ga sashe. Lalle ne Allah Yana sanin waɗanda ke sancewa daga cikinku da saɗaɗe. To, waɗanda suke saɓawa daga umurnin Sa, su yi saunar wata fitina ta same su, ko kuwa wata azaba mai raɗaɗi ta same su

Verse 64 — Surah An-Nur 24:64

To! Lalle Allah ne Yake da mulkin abin da ke a cikin sammai da ƙasa, haƙiƙa, Yana sanin abin da kuke a kansa kuma a ranar da ake mayar da su zuwa gare shi, sai Yana ba su labari game da abin da suka aikata. Kuma Allah, ga dukkan kome, Masani ne