Lalle ne Fir'auna ya ɗaukaka a cikin ƙasa, kuma ya sanya mutanenta ƙungiya-ƙungiya, yana raunanar da wata jama'a daga gare su; yana yanyanka ɗiyansu maza kuma yana rayar da matan. Lalle shi ya kasance daga masu ɓarna
Kuma Muka yi wahayi zuwa ga uwar Musa, cewa ki shayar da shi, sai idan kin ji tsoro game da shi, to, ki jefa shi a cikin kogi, kuma kada ki ji tsoro, kuma kada ki yi baƙin ciki. Lalle ne Mu, Masu mayar da shi ne zuwa gare ki, kuma Masu sanya shi ne a cikin Manzanni
Sai mutanen Fir'auna suka tsince shi, domin ya kasance maƙiyi da baƙin ciki a gare su. Lalle ne Fir'auna da Hamana da rundunoninsu, sun kasance masu aikin ganganci
Kuma matar* Fir'auna ta ce ("Ka bar shi yana) sanyin ido a gare ni da gare ka! Kada ka kashe shi, akwai fatan ya amfane mu, ko mu riƙe Shi ɗa," alhali kuwa su ba su sansance ba
Kuma zuciyar uwar Musa ta wayi gari yofintatta.* Lalle ne, haƙiƙa, ta yi kusa ta bayyanar da shi, ba domin Mun ɗaure zuciyarta ba, domin ta kasance daga muminai
Kuma Muka hana masa masu shayai da mama, a gabanin haka sai ta ce: "Ko in nunamuku mutanen wani gida, su yi muku renonsa alhali kuwa su masu nasiha ne a, gare shi
Sai Muka mayar da shi zuwa ga uwarsa domin idanunta su yi sanyi, kuma ba za ta yi baƙin ciki ba, kuma domin ta san cewa lalle wa'adin Allah gaskiya ne, amma kuma mafi yawansu ba su sani ba
Kuma sai ya shiga garin a lokacin da mutanen garin suka shagala, sai ya samu, a cikin garin, waɗansu maza biyu suna faɗa, wannan daga ƙungiyarsa, kuma ɗayan daga maƙiyansa, sai wannann da yake daga ƙungiyarsa ya nemi agajinsa, sai Musa ya yi masa ƙulli, ya kashe shi. Ya ce: "Wannan aikin Shaiɗan ne, domin shi maƙiyi ne mai ɓatarwa, bayyananne
Sai ya wayi gari a cikin birnin yana mai tsoro, yana sauna. Sai ga wanda ya nemi taimako daga gare shi a jiya, yana neman agajinsa. Musa ya ce masa, "Lalle kai ɓatacce ne, bayyananne
To, a lokacin da Musa ya yi nufin ya damƙi wanda yake maƙiyi ne a gare su, (mai neman agajin) ya ce,* "Ya Musa! Shin kananufin ka kashe ni ne kamar yadda ka kashe wani rai jiya? Ba ka son kome face ka kasance mai tanƙwasawa** a cikin ƙasa kuma ba ka nufin ka kasance daga masu kyautatawa
Kuma wani mutum ya zo daga mafi nisan birnin yana taliya da gaggawa, ya ce: "Ya Musa! Lalle mashawarta suna shawara game da kai domin su kashe ka saboda haka ka fita. Lalle ni, mai nasiha ne a gare ka
Kuma a lokacin da ya isa mashayar Madyana, ya sami wata jam'ar mutane suna shayarwa, kuma a bayansu ya sami waɗansu mata biyu suna korar (tumakinsu). Ya ce: "Mene ne sha'aninku?" Suka ce, "Ba za mu iya shayarwa ba sai makiyaya sun fita, kuma ubanmu tsoho* ne mai daraja
Sai ya shayar musu, sa'an nan kuma ya juya zuwa ga inuwa, sa'an nan ya ce: "Ya Ubangijina! Lalle ne, ga abin da Ka saukar zuwa gare ni na alheri ni mai bukata ne
Sai ɗayansu ta je masa, tana tafiya a kan jin kunya, ta ce, "Ubana yana kiran ka, domin ya saka maka ijarar abin da ka shayar saboda mu." To, a lokacin da ya je masa, ya gaya masa labarinsa, ya ce: "Kada ka ji tsoro, ka tsira daga mutane azzalumai
Ya ce: "Lalle ne ina nufin in aurar da kai ɗayan 'ya'yana biyu, waɗannan, a kan ka yi mini aikin ijara shekara takwas to, idan ka cika goma, to, daga, gare ka yake. Ba ni so in tsananta maka, za ka same ni, in Allah Ya so, daga salihai
Ya ce: "Wannan yana a tsakanina da tsakaninka kowane ɗayan adadin biyun na ƙare, to, babu wani zalunci a kaina. Kuma Allah ne Wakili ga abin da muke faɗa
To, a lokacin da Musa ya ƙare adadin kuma yana tafiya da iyalinsa, sai ya tsinkayi wata Wuta daga gefen dutse (¦ur). Ya cewa iyalinsa, "Ku dakata, lalle ne ni, na tsinkayi wata wuta, tsammanina ni, mai zo muku ne daga gare ta da wani labari, ko kuwa da guntun makamashi daga Wutar don ko ku ji ɗimi
To, a lokacin da ya je wurinta (Wutar) aka kira shi, daga gefen rafin na dama, a cikin wurin nan mai albarka, daga itaciyar (cewa) "Ya Musa! Lalle Ni ne Allah Ubangijin halittu
Kuma ka jefa sandarka." To, a lokacin da ya gan ta, tana girgiza kamar ƙaramar macijiya, ya juya yana mai bayar da baya, bai koma ba. "Ya Musa! Ka fuskanto, kuma kada ka ji tsoro lalle ne kana daga waɗanda ke amintattu
Ka shigar da hannunka a cikin wuyan rigarka, ya fita fari, ba da wata cuta ba, kuma ka haɗa hannuwanka ga kafaɗunka, domin tsoro (ya gushe daga gare ka). To, waɗannan abubuwa dalilai biyu ne daga Ubangijinka zuwa ga Fir'auna da 'yan Majalisarsa. Lalle sun kasance mutane ne fasiƙai
Kuma ɗan'uwana Haruna shi ne mafi fasaha daga gareni, ga harshe, saboda haka Ka aika shi tare da ni, yana mai taimako, yana gaskata ni, lalle ne ina tsoron su ƙaryata ni
Ya ce: "Za Mu ƙarfafa damtsenka game da ɗan'uwanka kuma Mu sanya muku wani dalili, saboda haka ba za su sadu zuwa gareku ba, tare da ayoyinMu, ku da waɗanda suka bi ku ne marinjaya
To, a lokacin da Musa ya je musu da ayoyinMu bayyanannu, suka ce: "Wannan ba kome ba sai sihiri, wanda aka ƙaga, kuma ba mu ji wannan ba daga wajen ubanninmu na farko
Kuma Musa ya ce: "Ubangijina ne Mafi sanin wanda ya zo da shiriya daga gare Shi, da wanda aƙibar gida take kasancewa agare shi. Lalle ne masu zalunci ba su cin nasara
Kuma Fir'auna ya ce: "Ya ku mashawarta! Ban san kuna da wani abin bautawa baicina ba, saboda haka ka hura mini wuta, ya Hamanu! a kan laka* (domin a yi tubali), sa'an nan ka sanya mini bene tsammanina zan ninƙaya zuwa ga Ubangijin Musa kuma lalle ne ni, haƙiƙa, ina zaton sa daga maƙaryata
Kuma lalle ne haƙiƙa, Mun bai wa Musa Littafi daga bayan Mun halakar da ƙarnonin farko, domin su zama abubuwan kula ga mutane, da shiriya da rahama, tsammaninsu suna tunawa
Kuma amma Mu, Mun ƙaga halittawar wasu ƙarnoni har lokatan rayuwa suka yi tsawo a kansu. Kuma ba ka kasance mazauni ba a cikin mutanen Madyana, kana karanta musu ayoyinMu, amma Mu Mun kasance masu aikawa (da kai game* da waɗancan labarai)
Kuma ba ka kasance ga gefen dutse ba a lokacin da Muka yi kira, kuma amma domin rahama daga Ubangijinka, domin ka yi gargaɗi ga mutane waɗanda suke wani mai gargaɗi a gabaninka bai je musu ba, tsammaninsu suna tunawa
Kuma ba domin wata masifa ta same su ba saboda abin da hannayensu suka gabatar, su ce: "Ya Ubangijinmu! Don me ba Ka aiko wani Manzo zuwa gare mu ba, har mu dinga bin ayoyinKa, kuma mu kasance daga muminai
Sa'an nan a lokacin da gaskiya ta je musu daga wurin Mu, suka ce: "Don me ba a ba shi kamar abin da aka bai wa Musa ba?" Shin kuma ba su kafirta ba da abin da aka bai wa Musa a gabanin (wannan)? suka ce: "Sihirori biyu ne suka taimaki juna," kuma suka ce: "Lalle ne mu, masu kafirta ne ga dukansu
To, idan ba su karɓa maka ba to sai ka sani suna bin son zuciyarsu ne kawai, kuma wane ne mafi ɓata daga wanda ya bi son zuciyarsa, ba tare da wata shiriya daga Allah ba? Lalle ne, Allah ba ya shiryar da mutane azzalumai
Kuma idan ana karanta shi a kansu, sai su ce: "Mun yi imani da shi, lalle shi ne gaskiya daga Ubangijinmu. Lalle mu, mun kasance a gabaninsa masu sallamawa
Waɗancan ana ba su ladansu sau biyu, saboda haƙurin da suka yi, kuma da kyautatawa suna tunkuɗewar munanawa kuma daga abin da Muka azurta susuna ciyarwa
Kuma idan sun ji yasassar magana sukan kau da kai daga barinta, kuma sukan ce, "Ayyukanmu suna a gare mu, kuma ayyukanku suna a gare ku, aminci ya tabbata a kanmu ba mu neman jahilai (da husuma)
Kuma suka ce: "Idan mun bi shiriya tare da kai ana fizge mu* daga ƙasamiu." Shin, ba Mu tabbatar musu da mallakar Hurumi ba, ya zama amintacce, ana jawowa zuwa gare shi, 'ya'yan itacen kowane iri, bisa ga azurtawa daga gare Mu? Amma kuma mafi yawansu ba su sani ba
Kuma da yawa Muka halakar da wata alƙarya wadda ta yi butulci ga rayuwarta. To, waɗancan gidajensu ne, ba a zaune su ba, a bayansu, face kaɗan. Kuma mun kasance Mu ne Magada
Kuma Ubangijinka bai kasance Mai halaka alƙaryu ba, sai Ya aika a cikin hedkwatarsu da wani Manzo yana karanta ayoyinMu a kansu. Kuma ba Mu kasance Masu halaka alƙaryu ba, face mutanensu sun kasance masu zalunci
Kuma abin da aka ba su daga kome, to, jin daɗin rayuwar duniya ne da ƙawarta. Kuma abin da ke wurin Allah, shi ne mafi alheri, knma mafi wanzuwa. Shin ba ku hankalta
Shin fa, wanda Muka yi wa wa'adi, wa'adi mai kyau, sa'an nan shi mai haɗuwa da shi ne, yana zama kamar wanda Muka jiyar da shi ɗan daɗi, daɗin rayuwar duniya, sa'an nan shi a Ranar ¡iyama yana daga masu shiga wuta
Waɗanda magana ta wajaba a kansu, su ce: "Ya Ubangijinmu! Waɗannan su ne waɗanda muka halakar mun halakar da su kamar yadda muka halaka. Mun barranta zuwa gare Ka, ba su kasance mu suke bauta wa ba
Kuma Ubangijinka Yana halitta abin da Yake so kuma Yake zaɓi. Zaɓi bai kasance a gare su ba. Tsarki ya tabbata ga Allah, kuma (Allah) Ya ɗaukaka daga barin abin da suke yi na shirka
Kuma Shi ne Allah, babu abin bautawa face Shi. Kuma Shi ne abin godiya a cikin ta farko (duniya), da ta ƙarshe (Lahira). Kuma Shi ne da hukunci, kuma zuwa gare Shi ake mayar da ku
Ka ce: "Shin, kun gani, idan Allah Ya sanya dare tutur a kanku har zuwa Ranar ¡iyama, wane abin bautawa wanin Allah zai zo muku da haske? Shin, ba ku ji
Ka ce: "Shin, kun gani, idan Allah Ya sanya yini a kanku tutur zuwa Ranar ¡iyama, wane abin bautawa, wanin Allah, zai zo muku da dare wanda kuna natsuwa a cikinsa? Shin fa, ba ku gani
Kuma Muka zare mai shaida daga kowace al'umma, sa'an nan Muka ce: "Ku kawo dalilinku." Sai suka san cewa lalle gaskiya ga Allah take. Kuma abin da suka kasance suna ƙirƙirawa na ƙarya ya ɓace daga barinsu
Lalle ne ¡aruna ya kasance daga mutanen Musa, sai ya fita* daga tsarinsu alhali Mun ba shi taskokin abin da yake mabuɗansa suna nauyi ga jama'a** ma'abuta ƙarfi a lokacin da mutanensa suka ce masa, "Kada ka yi annashuwa, lalle ne Allah ba Ya son masu annashuwa
Kuma ka biɗa a cikin abin da Allah Ya ba ka, gidan Lahira, kuma kada ka manta da rabonka daga duniya. Kuma ka kyautata, kamar yadda Allah Ya kyautata zuwa gare ka, kuma kada ka nemi ɓarna a cikin ƙasa,* lalle ne Allah ba Ya son masu barna
Ya ce: "An ba ni shi a kan wani ilmi wanda yake gare ni ne kawai." Shin, kuma bai sani ba cewa lalle Allah haƙiƙa Ya halakar a gabaninsa, daga ƙarnoni, wanda yake Shi ne mafi tsananin ƙarfi daga gare shi, kuma mafi yawan tarawar dukiya, kuma ba za a tambayi masu laifi daga zunubansu ba
Sai (¡aruna) ya fita a kan mutanensa a cikin adonsa. Waɗanda suke nufin rayuwar duniya suka ce: "Ina dai muna da kwatancin abin da aka bai wa ¡aruna! Lalle shi haƙiƙa ma'abucin rabo babba ne
Kuma waɗanda aka bai wa ilmi suka ce: "Kaitonku! sakamakon Allah ne mafi alheri a wanda ya yi tunani, kuma ya aikata aikin ƙwarai,* kuma babu wanda ake haɗawa da ita face mai haƙuri
Sai Muka shafe ƙasa* da shi da kuma gidansa. To, waɗansu jama'a ba su kasance gare shi ba, waɗanda suke taimakon sa, baicin Allah, kuma shi bai kasance daga masu taimakon kansu ba
Kuma waɗanda suka yi burin matsayinsa a jiya suka wayi gari suna cewa, "Wai! Allah Yana shimfiɗa arziki, ga wanda Yake so daga bayinsa, kuma Yana ƙuntatawa. Ba domin Allah Ya yi mana falala ba da Ya shafe ƙasa da mu. Wai! lalle ne shi, kafirai ba su cin nasara
Wanda ya zo da abu mai kyau, to, yana da mafi alheri daga gare shi, kuma wanda ya zo da mugun abu, to, ba za a sakawa waɗanda suka aikata miyagun ayyuka ba, face da abin da suka kasance suna aikatawa
Lalle ne wanda Ya faralta Alƙur'ani a kanka, haƙiƙa, Mai Mayar da kai ne zuwa ga makoma. ka ce: "Ubangijina ne Mafi sani ga wanda ya zo da shiriya, da kuma wanda yake a cikin ɓata bayyananne
Kuma ba ka kasance kana fatan a jefa Littafin nan zuwa gare ka ba, face dai domin rahama daga Ubangijinka. Saboda haka kada ka zama mai taimako* ga kafirai
Kuma kada lalle su karkatar da kai daga barin ayoyin Allah, a bayan har an saukar da su uwa gare ka. Ka yi kira zuwa ga Ubangijinka, kuma kada lalle ka kasance daga masu shirka
Kada ka kira wani abin bautawa na dabam tare da Allah. Babu abin bautawa face Shi. Kowane abu mai halaka ne face fuskar Sa. Shi ne da hukunci kuma zuwa gare Shi ake mayar da ku