Back to Languages

Hausa - Chapter 29 - Al-Ankabut

Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink

Verse 1 — Surah Al-Ankabut 29:1

Verse 2 — Surah Al-Ankabut 29:2

Ashe, mutane sun yi zaton a bar su su ce: "Mun yi imani," alhali kuwa ba za a Jarrabe su ba

Verse 3 — Surah Al-Ankabut 29:3

Kuma lalle Mun fitini waɗanda ke a gabaninsu, domin lalle Allah Ya san waɗanda suka yi gaskiya, kuma lalle Ya san maƙaryata

Verse 4 — Surah Al-Ankabut 29:4

Ko waɗanda ke aikata miyagun ayyuka sun yi zaton su tsere Mana? Abin da suke hukuntawa ya munana

Verse 5 — Surah Al-Ankabut 29:5

Wanda ya kasance yana fatan gamuwa da Alah to lalle ajalin Allah mai zuwa ne, kuma (Allah) Shi ne Mai ji, Masani

Verse 6 — Surah Al-Ankabut 29:6

Kuma wanda ya yi jihadi, to, yana yin jihadin ne domin kansa. lalle Allah haƙiƙa waɗatacce ne daga barin talikai

Verse 7 — Surah Al-Ankabut 29:7

Kuma waɗanda suka yi imani, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, lalle Muna kankare musu miyagun ayyukansu, kuma lalle Muna saka musu da mafi kyaun abin da suka kasance suna aikatawa

Verse 8 — Surah Al-Ankabut 29:8

Kuma Mun yi wa mutum wasiyyar kyautatawa ga uwayensa, kuma idan sun tsananta maka domin ka yi shirki da Ni game da abin da ba ka da ilmi gare shi, to, kada ka yi musu ɗa'a. Zuwa gare Ni makomarku take sa'an nan In ba ku labari ga abin da kuka kasance kuna aikatawa

Verse 9 — Surah Al-Ankabut 29:9

Kuma waɗanda suka yi imani, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, lalle Muna shigar da su a cikin mutanen kirki

Verse 10 — Surah Al-Ankabut 29:10

Kuma daga cikin mutane akwai mai cewa, 'Mun yi imani da Allah" sa'an nan idan aka cuce shi wajen aikin Allah, sai ya sanya fitinar mutane kamar azabar Allah kuma lalle idan taimakon Ubangijinka ya zo, haƙiƙa, ya kan ce: "Lalle mu mun kasance tare da ku." shin, Allah bai zama Mafi sani ba ga abin da ke a cikin ƙirazan halittun Sa

Verse 11 — Surah Al-Ankabut 29:11

Kuma lalle Allah na sanin waɗanda suka yi imani kuma lalle Yana sanin munafukai

Verse 12 — Surah Al-Ankabut 29:12

Kuma waɗanda suka kafirta suka ce wa waɗanda suka yi imani, "Ku bi hanyarmu, kuma Mu ɗauki laifuffukanku," alhali kowa ba su zamo masu ɗauka da a kome ba daga laifuffukansu. Lalle su maƙaryata ne

Verse 13 — Surah Al-Ankabut 29:13

Kuma lalle suna ɗaukar kayan nauyinsu da waɗansu nauyayan kaya tare da kayan nauyinsu, kuma lalle za a tambaye su a Ranar ¡iyama game da abin da suka kasance suna ƙirƙirawa na ƙarya

Verse 14 — Surah Al-Ankabut 29:14

Kuma lalle Mun aika Nuhu zuwa ga mutanensa, sai ya zauna a cikinsu shekara dubu face shekara hamsin, sa'an nan cikowar (¦ufana) ta kama su, alhali kuwa su ne masu zalunci

Verse 15 — Surah Al-Ankabut 29:15

Sa'an nan Muka tsirar da shi da mutanen jirgin, kuma Muka sanya jirgin ya zama wata aya ga talikai

Verse 16 — Surah Al-Ankabut 29:16

Da Ibrahim a lokacin da ya ce wa mutanensa, "Ku bauta wa Allah ku bi Shi da taƙawa. Wannan Shi ne alheri a gare ku idan kun kasance kuna sani

Verse 17 — Surah Al-Ankabut 29:17

Abin da dai kuke bautawa, baiein Allah, gumaka ne, kuma kun ƙirƙira ƙarya. Lalle waɗannan da kuke bauta wa baicin Allah, ba su mallaka muku arziki. Saboda haka ku nemi arziki a wurin Allah kawai, kuma ku bauta Masa, kuma ku yi godiya zuwa gare Shi. Zuwa gare Shi ake mayar da ku

Verse 18 — Surah Al-Ankabut 29:18

Kuma idan kun ƙaryata, to, lalle waɗansu al'ummomi a gabaninku sun ƙaryata, kuma babu abin da ke kan Manzo, face ayar da manzanci, iyarwa bayyananna

Verse 19 — Surah Al-Ankabut 29:19

Shin, ba su* ga yadda Allah ke fara yin halitta ba, sa'an nan kuma Ya mayar da ita? Lalle wannan abu ne mai sauƙi ga Allah

Verse 20 — Surah Al-Ankabut 29:20

Ka ce: "Ku yi tafiya cikin ƙasa, sa'an nan ku duba yadda (Allah) Ya fara yin halitta, sa'an nan kuma Allah Yana ƙaga wata halittar mayarwa. Lalle Allah Mai ikon yi ne a kan kome

Verse 21 — Surah Al-Ankabut 29:21

Yana azabta wanda Ya so, kuma Yana jin ƙan wanda Ya so. Kuma zuwa gare shi ake juyaku

Verse 22 — Surah Al-Ankabut 29:22

Kuma ba ku zamo masu buwaya ba a cikin ƙasa, kuma haka a cikin sama kuma ba ku da wani majiɓinci wanda ba Allah ba, kuma ha ku da wani mataimaki

Verse 23 — Surah Al-Ankabut 29:23

Kuma waɗanda suka kafirta da ayoyin Allah da gamuwa da shi, waɗannan sun yanke ƙauna daga rahamaTa kuma waɗannan suna da wata azaba mai raɗaɗi

Verse 24 — Surah Al-Ankabut 29:24

Sa'an nan babu abin da ya kasance jawabin mutanensa (Ibrahim) face dai suka ce: "Ku kashe shi ko, ku ƙona shi," Sai Allah Ya tsirar da shi daga wuta. Lallea cikin wannan akwai ayoyi ga mutanen da ke yin imani

Verse 25 — Surah Al-Ankabut 29:25

Kuma Ibrahim ya ce "Babu abin da kuka yi sai dai kub bar Allah kun riƙi gumaka saboda soyayyar tsakaninku a cikin rayuwar duniya, a'an nan a Ranar ¡iyama sashinku zai kafirce wa sashi, kuma makomarku ita ce wuta kuma ba ku da waɗansu mataimaka

Verse 26 — Surah Al-Ankabut 29:26

Sai Luɗu ya yi imani da shi. Kuma Ibrahim ya ce: "Lalleni mai ƙaura ne zuwa ga Ubangijina. Lalle Shi Shi ne Mabuwayi, Mai hikima

Verse 27 — Surah Al-Ankabut 29:27

Kuma Muka ba shi Ishaƙa da Ya'aƙuba, kuma Muka sanya Annabci da littafi a cikin zuriyarsa. Kuma Mun ba shi sakamakonsa a duniya, kuma lalle shi a Lahira, tabbas, yana a cikin salihai

Verse 28 — Surah Al-Ankabut 29:28

Da Luɗu, a lokacin daya ce wa mutanensa, "Lalle ku, haƙiƙa kuna je wa alfasha wadda wani mahaluƙi daga cikin duniya bai riga ku gare ta ba

Verse 29 — Surah Al-Ankabut 29:29

Ashe, lalle ku kuna je wa maza, kuma ku yi fashin hanya kuma ku je, a cikin majalisarku da abin da ba shi da kyau? To, jawabin mutanensa bai kasance ba face dai sun ce: 'Ka zo mana da azabar Allah, idan ka kasance daga masu gaskiya

Verse 30 — Surah Al-Ankabut 29:30

Ya ce: "Ya Ubangijina! Ka taimake ni a kan mutanen nan maɓarnata

Verse 31 — Surah Al-Ankabut 29:31

Kuma a lokacin da Manzannin Mu suka je wa Ibrahim da bushara suka ce: "Lalle mu masu halaka mutanen, wannan alƙarya ne. Lalle mutanenta sun kasance masu zalunci

Verse 32 — Surah Al-Ankabut 29:32

Ya ce: "Lalle akwai Luɗu a cikinta!" Suka ce: "Mu ne mafiya sani ga waɗanda suke a cikinta, lalle muna tsirar da shi da mutanensa, face fa matarsa ta kasance a cikin masu wanzuwa

Verse 33 — Surah Al-Ankabut 29:33

Kuma a lokacin da Manzannin Mu suka je wa Luɗu ya ɓata rai saboda su, kuma ya ƙuntata ga kirji saboda su. Kuma suka ce: "Kada ka ji tsoro kuma kada ka yi baƙin ciki lalle mu masu tsirar da kai ne da iyalanka, face dai matarka ta kasance daga masu wanzuwa

Verse 34 — Surah Al-Ankabut 29:34

Lalle mu, masu saukar da azaba ne daga sama a kan mutanen wannan alƙarya saboda abin da suka kasance suna yi na fasiƙanci

Verse 35 — Surah Al-Ankabut 29:35

Kuma lalle Mun bar wata aya bayyananna daga gare ta ga mutane masu hankalta

Verse 36 — Surah Al-Ankabut 29:36

Kuma zuwa ga Madyana, Mun aika ɗan'uwansu shu'aibu, sai ya ce: "Ya mutanena! Ku bauta wa Allah kuma ku yi fatan (rahamar) Ranar Lahira, kuma kada ku yi ɓarna a cikin ƙasa, alhali kuwa kuna masu lalatarwa

Verse 37 — Surah Al-Ankabut 29:37

Sai suka ƙaryata shi, saboda haka tsawa ta kama su, domin haka suka wayi gari suna guggurfane

Verse 38 — Surah Al-Ankabut 29:38

Da Adawa da Samudawa alhali kuwa lalle alamun azaba sun bayyana a gare su daga gidajensu kuma Shaiɗan ya ƙawata musu ayyukansu, saboda haka ya kange su daga hanyar Allah, kuma sun kasance masu basira

Verse 39 — Surah Al-Ankabut 29:39

Kuma ¡aruna da Fir'auna da Hamana, kuma lalle Musaya je musu da hujjoji, sai suka yi girman kai a cikin ƙasa kuma ba su kasance masu tserewa ba

Verse 40 — Surah Al-Ankabut 29:40

Saboda haka kowanensu Mun kama shi da laifinsa. Watau daga cikinsu akwai wanda Muka aika iskar tsakuwa a kansa kuma daga cikinsu akwai wanda tsawa ta kama, kuma daga cikinsu akwai wanda Muka birkice ƙasa da shi kuma daga cikinsu akwai wanda Muka nutsar. Ba ya yiwuwa ga Allah Ya zalunce su, amma sun kasance kansu suke zalunta

Verse 41 — Surah Al-Ankabut 29:41

Misalin waɗanda suka riƙi waɗansu masoya waɗanda ba Allah ba, kamar misalin gizogizo ne wanda ya riƙi wani ɗan gida, alhali kuwa lalle mafi raunin gidaje, shi ne gidan gizogizo, da sun kasance suna sane

Verse 42 — Surah Al-Ankabut 29:42

Lalle Allah Yana sane da abin da suke kira wanda ba Shi ba na wani abu duka kuma shi ne Mabuwayi, Mai hikima

Verse 43 — Surah Al-Ankabut 29:43

Kuma waɗancan misalan Muna bayyana su ga mutane kuma babu mai hankalta da su sai masu ilmi

Verse 44 — Surah Al-Ankabut 29:44

Allah Ya halitta sammai da ƙasa da gaskiya. Lalle cikin wancan akwai aya ga muminai

Verse 45 — Surah Al-Ankabut 29:45

Ka karanta abin da ake yin wahayi zuwa gare ka daga Littafi, kuma ka tsayar da salla. Lalle salla tana hanawa daga alfasha da abni ƙyama, kuma lalle ambaton Allah yafi girma, kuma Allah Yana sane da abin da kuke aikatawa

Verse 46 — Surah Al-Ankabut 29:46

Kada ku yi jayayya da mazowa Littafi sai fa da magana wadda ta fi kyau, sai fa waɗanda suka yi zalunci daga gare su, kuma ku ce, "Mun yi imani da abin da aka saukar a gare mu kuma aka saukar a gare ku, kuma Abin bautawarmu da Abin bautawarku Guda ne, kama mu masu sallamawa ne a gare shi

Verse 47 — Surah Al-Ankabut 29:47

Kuma kamar haka Muka saukar da Littafi a gare ka, to, waɗannan da Muka bai wa Littafi sana imani da shi, daga cikin waɗannan akwai mai imani da shi, kuma babu mai musun ayoyin Mu, face kafirai

Verse 48 — Surah Al-Ankabut 29:48

Kuma ba ka kasance kana karatun wani littafi ba a gabaninsa, kuma ba ka rubutunsa da damanka da haka ya auku, da masu ɓarna sun yi shakka

Verse 49 — Surah Al-Ankabut 29:49

A'a, shi ayoyi ne bayyanannu a cikin ƙirazan waɗanda aka bai wa ilmi. Kuma babu mai musun ayoyin Mu face azzalumai

Verse 50 — Surah Al-Ankabut 29:50

Kuma suka ce: "Don me ba a saukar masa da ayoi ba daga Ubangijinsa? "Ka ce: "Su ayoyi a wurin Allah kawai suke, kuma lalle ni mai gargaɗi kawai ne, mai bayyanawa

Verse 51 — Surah Al-Ankabut 29:51

Shin bai ishe su ba cewa lalle Mu, Mun saukar da Littafin akanka, ana karanta shi a kansu? Lalle a cikin wancan haƙiƙa akwai rahama da tunatawa ga mutanen da ke yin imani

Verse 52 — Surah Al-Ankabut 29:52

Ka ce: "Allah Ya isa shaida a tsakanina da tsakaninku Yana sane da abin da ke a cikin sammai da ƙasa, kuma waɗanda suka yi imani da ɗarya kuma suka kafirta da Allah, waɗannan su nemasu hasara

Verse 53 — Surah Al-Ankabut 29:53

Kuma suna neman ka da gaggauta azaba, to, ba domin ajali ƙayyadadde ba, da azaba ta je musu kuma lalle da tana iske su bisa ia abke, alhali kuwa su ba su sani ba

Verse 54 — Surah Al-Ankabut 29:54

Suna neman ka da gaggauta azaba, kuma lalle Jahannama, tabbas, mai kewayewa ce gakafirai

Verse 55 — Surah Al-Ankabut 29:55

Ranar da azaba ke rufe su daga samansu da kuma ƙasan ƙafafunsu kuma Ya* ce: "Ku ɗanɗani abin da kuka kasance kuna aikatawa

Verse 56 — Surah Al-Ankabut 29:56

Ya bayiNa, waɗanda suka yi imani! Lalle fa ƙasaTa mai yalwa* ce, sabada haka ku bauta Mini

Verse 57 — Surah Al-Ankabut 29:57

Kowane rai mai ɗanɗanar mutuwa ne, sa'an nan zuwa gare Mu ake mayar da ku

Verse 58 — Surah Al-Ankabut 29:58

Kuma waɗanda suka yi imani kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, lalle za Mu zaunar da su daga cikin Aljanna a gidajen bene, ƙoramu na gudana daga ƙarƙashinsu, suna madawwama a cikinsu. To, madalla da sakamakon masu aikin ƙwarai

Verse 59 — Surah Al-Ankabut 29:59

Waɗanda suka yi haƙuri, kuma suna dogara ga Ubangijinsu kawai

Verse 60 — Surah Al-Ankabut 29:60

Kuma da yawa* dabba wadda ba ta ɗaukar abincinta Allah Yana ciyar da ita tare da ku, kuma Shi ne Mai ji, Mai ilmi

Verse 61 — Surah Al-Ankabut 29:61

Lalle idan ka tambaye su: "Wane ne ya halitta sammai da ƙasa kuma ya hore rana da wata?" Lalle suna cewa Allah ne. TO, yaya ake karkatar da su

Verse 62 — Surah Al-Ankabut 29:62

Alah ne ke shimfiɗa arziki ga wanda Yake so daga cikin bayinsa kuma Yana ƙuntatawa ga (wanda, Yake so). Lalle Allah, Masani ne ga dukan kome

Verse 63 — Surah Al-Ankabut 29:63

Kuma lalle idan ka tambaye su. "Wane ne ya saukar da ruwa daga sama, har ya rayar da ƙasa game da shi a bayan mutuwarta?" Lalle suna cewa, "Allah ne." Ka ce: "Godiya ta tabbata ga Allah." A'a, mafi yawansu ba su hankalta

Verse 64 — Surah Al-Ankabut 29:64

Kuma wannan rayuwa ta duniya ba ta zamo ba, face abar shagala da wasa kuma lalle Lahira tabbas, ita ce rayuwa, da sun kasance suna sani

Verse 65 — Surah Al-Ankabut 29:65

To, a lokacin da suka shiga cikin jirgin ruwa, sun kirayi Allah suna masu tsarkake addini a gare shi, to, a lokacin da Ya tsirar da su zuwa ga tudun ƙasa, sai ga su suna shirki

Verse 66 — Surah Al-Ankabut 29:66

Domin su kafirce wa abin da Muka ba su kuma domin su ji daɗi sa'an nan kuma za su sani

Verse 67 — Surah Al-Ankabut 29:67

Shin, ba su ga cewa, lalle Mun sanya Hurumi amintacce ba alhali kuwa ana fisge mutane a gefensu? Shin, da ɓataccen abu suke imani kuma da ni'imarAllah suka kafirta

Verse 68 — Surah Al-Ankabut 29:68

Kuma wane ne ya fi zalunci bisa ga wanda ya ƙirƙira ƙarya ya jingina ta ga Allah, ko kuma ya ƙaryata gaskiya a lokacin da ta je masa? Ashe a cikin Jahannama babu mazauna ga kafirai

Verse 69 — Surah Al-Ankabut 29:69

Kuma wadannan da suka yi ƙoƙari ga neman yardarMu, lalle Muna shiryar da su ga hanyoyinMu, kuma lalle Allah, tabbas, Yana tare da masu kyautatawa (ga addininsu)