Back to Languages

Hausa - Chapter 30 - Ar-Rum

Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink

Verse 1 — Surah Ar-Rum 30:1

Verse 2 — Surah Ar-Rum 30:2

Verse 3 — Surah Ar-Rum 30:3

A cikin mafi kusantar ƙasarsu, kuma su, a bayan rinjayarsu, za sn rinjaya

Verse 4 — Surah Ar-Rum 30:4

A cikin'yan shekaru. Al'amari na Allah ne a gabanin kome da bayansa, kuma a ranar nan muminai za su yi farin ciki

Verse 5 — Surah Ar-Rum 30:5

Da taimakon Allah Yana taimakon wanda Yake so. Kuma Shi ne Mabuwayi, Mai jin ƙai

Verse 6 — Surah Ar-Rum 30:6

Wa'adin Allah, Allah ba ya saɓawa ga wa'adinsa, kuma amma mafi yawan mutane ba su sani ba

Verse 7 — Surah Ar-Rum 30:7

Suna sanin bayyanannar rayuwar duniya, alhali kuwa su shagalallu ne daga rayuwar Lahira

Verse 8 — Surah Ar-Rum 30:8

Shin, ba su yi tunani ba a cikin zukatansu cewa Allah bai halitta sammai da ƙasa ba da abin da ke tsakaninsu, face da gaskiya* da ajali ambatacce? Kuma lalle masu yawa daga mutane kafirai ne ga gamuwa da Ubangijinsu

Verse 9 — Surah Ar-Rum 30:9

Shin, kuma ba su yi tafiya ba, a cikin ƙasa domin su gani yadda aƙibar waɗanda ke a gabaninsu ta kasance? Sun kasance mafiya ƙarfi daga gare su kuma suka nomi ƙasa suka raya ta fiye da yadda suka raya ta, kuma manzanninsu suka je musu da hujjoji bayyanannu. Sabo da haka Allah ba Ya yiwuwa Ya zalunce su, amma kansu suka kasance suna zalunta

Verse 10 — Surah Ar-Rum 30:10

Sa'an nan aƙibar waɗannan da suka aikata mugun aiki ta kasance mafi muni, watau sun ƙaryata game da ayoyin Allah, kuma suka kasance suna izgili da su

Verse 11 — Surah Ar-Rum 30:11

Allah ne ke fara yin halitta, sa'an nan Ya sake ta sa'an nan zuwa gare Shi ake mayar da ku

Verse 12 — Surah Ar-Rum 30:12

Kuma a ranar da sa'a ke tsayuwa, masu laifi za su kasa magana

Verse 13 — Surah Ar-Rum 30:13

Kuma ba su da masu ceto daga abubuwan shirkinsu, kuma snn kasance masu kafircewa daga abubuwan shirkinsu

Verse 14 — Surah Ar-Rum 30:14

kuma a ranar tashin Alkiyama ranar ne suke rarrabuwa

Verse 15 — Surah Ar-Rum 30:15

To, amma waɗanda suka yi imani, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai to su ana faranta musu rayuka, a cikin wani lambu

Verse 16 — Surah Ar-Rum 30:16

Kuma waɗanda suka kafirta, kuma suka ƙaryata, game da ayoyinMu da kuma haɗuwa da Ranar Lahira, to, waɗancan ana halartar da su a cikin azaba

Verse 17 — Surah Ar-Rum 30:17

Saboda haka tsarkakewa ta tabbata ga Allah a lokacin da kuke shiga maraice, da lokacin da kuke shiga safiya

Verse 18 — Surah Ar-Rum 30:18

Kuma Shi ne da godiya, a cikin sammai da ƙasa kuma da lokacin yamma da lokacin zawali

Verse 19 — Surah Ar-Rum 30:19

Yana fitar da mai rai daga matacce kuma Yana fitar da matacce daga mai rai, kuma Yana rayar da ƙasa a bayan mutuwarta. Kuma haka ake fitar da ku

Verse 20 — Surah Ar-Rum 30:20

Kuma akwai daga ayoyin Sa, Ya halitta ku daga turɓaya, sai ga ku kun zama mutum, kuna watsuwa

Verse 21 — Surah Ar-Rum 30:21

Kuma akwai daga ayoyinsa, Ya halitta muku matan aure daga kanku, domin ku natsu zuwa gare ta, kuma Ya sanya soyayya da rahama a tsakaninku.* Lalle a cikin wancan akwai ayoyi ga mutane masu yin tunani

Verse 22 — Surah Ar-Rum 30:22

Kuma akwai daga ayoyin Sa halittar sammai da ƙasa da saɓa, war harsunanku, da launukanku. Lalle a cikin wannan akwai ayoyi ga masu ilmi

Verse 23 — Surah Ar-Rum 30:23

Kuma akwai daga cikin ayoyin Sa, barcinku a cikin dare da rana, da nemanku ga falalarsa. Lalle a cikin wannan akwai ayoyi ga mutane masu saurarawa

Verse 24 — Surah Ar-Rum 30:24

Kuma akwai daga cikin ayoyin Sa, Ya nuna muku walƙiya a kan tsoro da ɗammani kuma Ya dinga saukar da ruwa daga sama Sa'an nan Ya rayar da ƙasa game da shi a bayan mutuwarta. Lalle a cikin wannan akwai ayoyi ga mutane masu hankaltawa

Verse 25 — Surah Ar-Rum 30:25

Kuma akwai daga ayoyinsa, tsayuwar sama da asƙa bisa umurninsa, sa'an nan idan Ya kira ku, kira ɗaya, daga ƙasa, sai ga ku kuna fita

Verse 26 — Surah Ar-Rum 30:26

Kuma wanda ke cikin sammai da ƙasa Nasa ne shi kaɗai. Dukansu masu tawali'u ne a gare Shi

Verse 27 — Surah Ar-Rum 30:27

Kuma Shi ne Wanda Ya fara halitta, sa'an nan Ya sake ta kuma sakewarta ta fi sauƙi a gare shi. Kuma Yana da misali wanda ya fi ɗaukaka a cikin sammai da ƙasa kuma Shi ne Mabuwayi, Mai jin ƙai

Verse 28 — Surah Ar-Rum 30:28

Ya buga muku wani misali daga kanku. Ko kuna da abokan tarewa, daga cikin bayin da hannayenku na dama suka mallaka, a cikin arzikinku, watau ku zama daidai a ciki kuna tsoron su kamar tSoronku ga kanku? Haka dai Muke bayyana ayoyi, daki-daki, ga mutane masu hankaltuwa

Verse 29 — Surah Ar-Rum 30:29

A'aha! waɗanda suka yi zaunci sun bi son zuciyoyinsu, ba tare da wani ilmi ba. To wane ne zai shiryar da wanda Allah Ya ɓatar, kuma ba su da waɗansu mataimaka

Verse 30 — Surah Ar-Rum 30:30

Saboda haka, ka tsayar da fuskarka ga addini,* kana mai karkata zuwa ga gaskiya, halittar Allah da Ya halitta mutane a kanta. Babu musanyawa ga halittar Allah, wannan shi ne addini madaidaici kuma amma mafi yawan mutane ba su sani ba

Verse 31 — Surah Ar-Rum 30:31

Kuna masu mai da al'amari gare Shi, kuma ku bi Shi dataƙawa, kuma ku tsayar da salla, kuma kada ku kasance daga mushirikai

Verse 32 — Surah Ar-Rum 30:32

Watau waɗanda suka rarrabe addininsu kuma suka kasance ƙungiya-ƙungiya, kowace ƙungiya tana mai farin ciki da abin da ke a gare ta kawai

Verse 33 — Surah Ar-Rum 30:33

Kuma idan cuta ta shafi mutane, sai su kirayi Ubangijinsu, suna masu mai da al'amari gare Shi, sa'an nan idan Ya ɗanɗana musu wata rahama daga gare Shi, sai ga wani ɓangare daga gare su suna shirki da Ubangijinsu

Verse 34 — Surah Ar-Rum 30:34

Domin su kafirta dl abin da Muka ba su. To ku ji daɗi kaɗan Sa'an nan za ku, sani

Verse 35 — Surah Ar-Rum 30:35

Ko Mun saukar da wani dali li a gare su? Shi kuwa yana magana da abin da suka kasance suna shirkin da shi

Verse 36 — Surah Ar-Rum 30:36

Kuma idan Muka ɗanɗana wa mutane wata rahama, sai su yi farin ciki da ita kuma idan cuta ta same su, saboda abin da hannayensu suka gabatar, sai ga su suna yanke ƙauna

Verse 37 — Surah Ar-Rum 30:37

Shin, kuma ba su gani ba cewa Allah na shimfida arziki ga wanda Yake so kuma Yana ƙuntatawa? Lalle a cikin wancan akwai ayoyi ga mutane masu yin imani

Verse 38 — Surah Ar-Rum 30:38

Saboda haka ka bai wa zumu hakkinsa da miskinai da ɗan hanya, wannan shi ne alheri ga waɗanda ke nufin yardar Allah kuma waɗancan su ne masu samun babban rabo

Verse 39 — Surah Ar-Rum 30:39

Kuma abin da kuka bayar na riba domin ya ƙaru a cikin dukiyar mutane to, ba zai ƙaru ba, a wurin Allah. Kuma abin da kuka bayar na zakka, kana nufin yardar Allah to (masu yin haka) waɗancan su ne masu ninkawa (ga dukiyarsu)

Verse 40 — Surah Ar-Rum 30:40

Allah ne Wanda Ya halicce ku, sa'an nan Ya azurta ku, sa'an nan Ya matar da ku, sa'an nan Ya rayar da ku. Ashe, daga cikin abubuwan shirkinku akwai wanda ke aikata wani abu daga waɗannan ahubuwa? Tsarki ya tabbata ga Allah, kuma Ya ɗaukaka bisa ga abin da suke yi na shirki

Verse 41 — Surah Ar-Rum 30:41

¥arna ta bayyana a cikin ƙasa da teku, saboda abin da hannayen mutane suka aikata. Domin Allah Ya ɗanɗana musu sashin abin da suka aikata, ɗammaninsu za su komo

Verse 42 — Surah Ar-Rum 30:42

Ka ce: "Ku tafi a cikin ƙasa sa'an nan ku dubi yadda aƙibar waɗanda suka kasance a gabaninku ta kasance. Mafi yawansu sun kasance masu yin shirka

Verse 43 — Surah Ar-Rum 30:43

Saboda haka, ka tsayar da fuskarka ga addini madaidaici a gabanin wani yini ya zo, babu makawa gare Shi daga Allah, a ranar nan mutane suna tsagewa (su rabu biyu)

Verse 44 — Surah Ar-Rum 30:44

Wanda ya kafirta, to, kafircinsa na kansa, kuma wanda ya aikata aikin ƙwarai, to, saboda kansu suke yin shimfiɗa

Verse 45 — Surah Ar-Rum 30:45

Domin Ya saka wa waɗanda suka yi imani, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, daga falalarSa. Lalle Allah ba Ya son kafirai

Verse 46 — Surah Ar-Rum 30:46

Kuma akwai daga ayoyinSa, ya aika iskoki masu bayar da bushara kuma domin Ya ɗanɗana muku daga rahamarSa, kuma domin jiragen ruwa su gudana da umurninSa, kuma domin ku nema daga falalar Sa, fatanku za ku gode

Verse 47 — Surah Ar-Rum 30:47

Kuma lalle Mun aiki waɗansu Manzanni a gabaninka, zuwa ga mutanensu sai suka je musu da hujjoji, bayyanannu, sa'an nan Muka azabtar da waɗanda suka yi laifi, kuma ya kasance tabbatacce taimakon muminai wajibi ne a kan mu

Verse 48 — Surah Ar-Rum 30:48

Allah ne Wanda ke aika iskoki, sai su motsar da girgije, sa'an nan Ya shimfiɗa shi a cikin sama yadda Yake so, kuma Ya sanya shi wani ɓaɓɓake, sa'an nan ka ga ruwa na fita daga tsakaninsa. Sa'an nan idan Allah Ya sami waɗanda Ya so daga bayinsa, Sai ga su suna bushara da shi

Verse 49 — Surah Ar-Rum 30:49

Kuma ko da sun kasance a gabanin a saukar da shi a kansu, kusa-kusa, suna baƙin ciki hai ba su iya magana

Verse 50 — Surah Ar-Rum 30:50

Sai ka dubi alamomin rahamar Allah yadda Yake rayar da ƙasa a bayan mutuwarta. Lalle wannan (Mai wannan aiki), tabbas, Mai rayar da halitta ne, kuma Shi Mai ikon yi ne a kan kome

Verse 51 — Surah Ar-Rum 30:51

Kuma lalle idan Mun aika wata iska, suka ganta fatsifatsi, lalle za su yini a bayansa suna kafirta

Verse 52 — Surah Ar-Rum 30:52

Saboda haka, kai, ba ka jiyar da matattu kira, kuma ba ka jiyar da kurame kira idan sun juya baya suna gudu

Verse 53 — Surah Ar-Rum 30:53

Kuma ba ka zamo mai shiryar da makafi ba daga ɓatarsu, ba ka jiyarwa face wanda ke yin imani da ayoyin Mu, watau su ne masu miƙa wuya, su sallama

Verse 54 — Surah Ar-Rum 30:54

Allah ne Ya halitta ku daga rauni,* sa'an nan Ya sanya wani ƙarfi a bayan wani rauni, sa'an nan Ya sanya wani rauni da furfura a bayan wani ƙarfi, Allah na halitta abin da Ya so, kuma Shi ne Mai ilmi, Mai ikon yi

Verse 55 — Surah Ar-Rum 30:55

Kuma a ranar da Sa'a* ke tsayuwa, masu laifi na rantsuwa: Ba su zauna a cikin kabari ba face sa'a guda. Kamar haka suka kasance ana karkatar da su

Verse 56 — Surah Ar-Rum 30:56

Kuma waɗanda aka bai wa ilmi da imani suka ce: "Lalle, haƙiƙa kun zauna a cikin Littafin Allah, har zuwa ranar tayarwa, to, kuma wannan ita ce ranar tayarwar, kuma amma ku, kun kasance* ba ku sani ba

Verse 57 — Surah Ar-Rum 30:57

To, a ranar da uzurin waɗanda suka yi zalunci ba ya amfaninsu, kuma ba a neman yardarsu

Verse 58 — Surah Ar-Rum 30:58

Kuma lalle tabbas Mun buga kowane irin misali ga mutane a cikin wannan Alƙur'ani, kuma lalle idan ka je musu da kowace aya, lalle, waɗanda suka kafirta za su ce "Ku, ba kome kuke ba face masu barua

Verse 59 — Surah Ar-Rum 30:59

Kamar haka Allah Yake shafe haske a kan zukatan waɗanda ba su sani ba

Verse 60 — Surah Ar-Rum 30:60

Saboda haka ka yi haƙuri lalle wa'adin Allah gaskiya ne, kuma kada waɗanda ba su da yaƙini su sassance maka hankali