A gabani, suna shiryar da mutane, kuma Ya saukar da littattafai masu rarrabewa. Lalle ne waɗanda suka kafirta da ayoyin Allah, suna da azaba mai tsanani. Kuma Allah Mabuwayi ne, Ma'abucin azabar ramuwa
Shi ne wanda ya saukar da Littafi a gare ka, daga cikinsa akwai ayoyi bayyanannu, su ne mafi yawan Littafin, da wasu masu kama da juna. To, amma waɗanda yake a cikin zukatansu akwai karkata sai suna bin abin da yake da kama da juna daga gare shi, domin neman yin fitina da tawilinsa. Kuma babu wanda ya san tawilinsaface Allah. Kuma matabbata a cikin ilmi suna cewa: "Mun yi imani da Shi; dukkansa daga wurin Ubangijinmu yake." Kuma babu mai tunani face ma'abuta hankula
Kamar ɗabi'ar mutanen Fir'auna da waɗanda ke a gabaninsu, sun ƙaryata ayoyinMu, sai Allah Ya kama su saboda zunubansu, kuma Allah Mai tsananin uƙuba ne
Lalle ne wata aya ta kasance a gare ku a cikin ƙungiyoyi biyu da suka haɗu; ƙungiya guda tana yaƙi a cikin hanyar Allah, da wata kafira, suna ganin su ninki biyu nasu, a ganin ido. Kuma Allah Yana ƙarfafa wanda Yake so da taimakonSa. Lalle ne a cikin wannan, hakiƙa, akwai abin kula ga maabuta basira
An ƙawata wa mutane son sha'awoyi daga mata da ɗiya da dukiyoyi abubuwan tarawa daga zinariya da azurfa, da dawaki kiwatattu da dabbobin ci da hatsi. Wannan shi ne daɗin rayuwar duniya. Kuma Allah a wurinsa kyakkyawar makoma take
Ka ce: Shin kuma, in gaya muku mafi alheri daga wannan? Akwai gidajen Aljanna a wurin Ubangiji saboda waɗanda suka bi Shi da taƙawa, koguna suna gudana daga ƙarƙashinsu, suna madawwama a cikinsu, da matan aure tsarkakakku, da yarda daga Allah. Kuma Allah Mai gani ne ga bayinSa
Allah Ya shaida cewa: Lalle ne babu abin bautawa face Shi kuma malaiku da ma'abuta ilmi sun shaida, yana tsaye da adalci, babu abin bautawa face Shi, Mabuwayi, Mai hikima
Lalle ne, addini a wurin Allah, Shi ne Musulunci. Kuma waɗanda aka bai wa Littafi ba su saɓa ba, face a bayan ilmi ya je musu, bisa zalunci a tsakaninsu. Kuma wanda ya kafirta da ayoyin Allah, to, lalle ne Allah Mai gaugawar sakamako ne
To, idan sun yi musu da kai, sai ka ce: "Na sallama fuskata ga Allah, kuma wanda ya bi ni (haka)." Kuma ka ce wa waɗanda aka bai wa littafi da Ummiyyai:* "Shin kun sallama?" To, idan sun sallama, haƙiƙa, sun shiryu kuma idan sun juya, to, kawai abinda ke kanka, shi ne iyarwa. Kuma Allah Mai gani ne ga bayinSa
Lalle ne waɗanda suke kafirta da ayoyin Allah, kuma suna kashe Annabawa ba da wani hakki ba, kuma suna kashe waɗanda ke umurni da yin adalci daga mutane, to, ka yi musu bushara da azaba mai raɗaɗi
Shin, ba ka ga waɗanda aka bai wa rabo daga littafi ba ana kiran su zuwa ga Littafin Allah domin ya yi hukunci a tsakaninsu sa'an nan wata ƙungiya daga cikinsu ta juya baya, kuma suna masu bijirewa
Wannan kuwa, domin lalle ne su sun ce: "Wuta ba za ta shafe mu ba, face a 'yan kwanaki ƙidayayyu." Kuma abin da suka kasance suna ƙirƙirawa na ƙarya ya ruɗe su a cikin Addinin su
To, yaya idan Mun tara su a yini wanda babu shakka a cikinsa, kuma aka cika wa kowane rai sakamakon abin da ya tsirfanta, alhali kuwa, su ba za a zalunce su ba
Ka ce:* "Ya Allah Mamallakin mulki, Kana bayar da mulki ga wanda Kake so, Kana zare mulki daga wanda Kake so, kuma Kana buwayar da wanda Kake so, kuma Kana ƙasƙantar da wanda Kake so, ga hannunKa alheri yake. Lalle ne Kai, a kan kowane abu, Mai ikon yi ne
Kana shigar da dare a cikin yini, kuma Kana shigar da yini a cikin dare, kuma Kana fitar da mai rai daga mamaci, kuma Kana fitar da mamaci daga mai rai, kuma Kana azurta wanda Kake so ba da lissafi ba
Kada muminai su riƙi kafirai masoya, baicin muminai. Kuma wanda ya yi wannan, to, bai zama a cikin kome ba daga Allah, face fa domin ku yi tsaro daga gare su da 'yar kariya. Kuma Allah yana tsoratar da ku kanSa. Kuma zuwa ga Allah makoma take
Ka ce: "Idan kun ɓoye abin da ke a cikin ƙirazanku, ko kuwa kun bayyana shi, Allah Yana sanin sa. Kuma Yana sanin abin da ke a cikin sammai da ƙasa. Kuma Allah a kan kowane abu Mai ikon yi ne
A Ranar da kowane rai yake samun abin da ya aikata daga alheri, a halarce, da kuma abin da ya aikata daga sharri, alhali yana gurin, da dai lalle a ce akwai fage mai nisa a tsakaninsa da abin daya aikata na sharrin! Kuma Allah Yana tsoratar da ku kanSa. Kuma Allah Mai tausayi ne ga bayin Sa
A lokacin da matar Imrana* ta ce: "Ya Ubangijina! Lalle ni, na yi bakancen abin da ke cikin cikina gare Ka; ya zama 'yantacce, sai Ka karɓa daga gare ni. Lalle ne Kai, Kai ne Mai ji, Masani
To, a lokacin da ta haife ta sai ta ce: "Ya Ubangijina! Lalle ne ni, na haife ta mace!"KumaAllah ne Mafi sanin abin da ta haifa." Kuma namiji bai zama kamar mace ba. Kuma ni na yi mata suna Maryamu* kuma lalle ne ni, ina nema mata tsari gare Ka, ita da zuriyarta daga Shaiɗan jefaffe
Sai Ubangijinta Ya karɓe ta karɓa mai kyau. Kuma Ya yabanyartar da ita yabanyartarwa mai kyau, kuma Ya sanya renonta ga Zakariyya. Ko da yaushe Zakariyya ya shiga masallaci, a gare ta, sai ya sami abinci a wurinta. (Sai kuwa) ya ce: "Ya Maryamu! Daga ina wannan yake gare ki?" (Sai) ta ce: "Daga wurin Allah yake. Lalle ne Allah yana azurta wanda Ya so ba da lissafi ba
Sai mala'iku suka kiraye shi, alhali kuwa shi yana tsaye yana salla a cikin masallaci. (Suka ce), "Lalle ne Allah yana ba ka bushara da Yahaya, alhali yana mai gaskatawar wata kalma daga Allah, kuma shugaba, kuma tsarkakke kuma annabi daga salihai
Ya ce: "Ya Ubangijina! Yaya yaro zai samu a gare ni, alhali kuwa, lalle tsufa ya same ni, kuma matata bakarariya ce?" Allah ya ce, "Kamar hakan ne, Allah yana aikata abin da Yake so
Ya ce: "Ya Ubangijina! Ka sanya mini wata alama!" (Allah) Ya ce "Alamarka ita ce ba za ka iya yi wa mutane magana ba har yini uku face da ishara. Sai ka ambaci Ubangijinka da yawa. Kuma ka yi tasbihi da marece da safe
Wannan yana daga labarun* gaibi, Muna yin wahayinsa zuwa gare ka (Muhammadu). Ba ka kasance ba a wurinsu a lokacin da suke jefa alƙalumansu (domin ƙuri'a) wane ne zai yi renon Maryam. Kuma ba ka kasance a wurinsu ba a lokacin da suke ta yin husuma
A lokacin da mala'iku suka ce "Ya Maryamu! Lalle ne Allah Yana ba ki bushara da wata kalma daga gare Shi; sunansa Masihu isa ɗan Maryama, yana mai daraja a duniya da Lahira kuma daga Makusanta
Ta ce: "Ya Ubangijina! Yaya yaro zai kasance a gare ni, alhali kuwa wani mutum bai shafe ni ba?" (Allah) Ya ce: "Kamar wannan ne, Allah yana halittar abin da Yake so. Idan Ya hukunta wani al'amari, sai ya ce masa, "Ka kasance!, Sai yana kasancewa
Kuma (Ya sanya shi) manzo zuwa ga Bani Israila'ila (da sako, cewa), Lalle ne, ni haƙiƙa na zo muku, da wata aya daga Ubangijinku. Lalle ne ni ina halitta muku daga laka, kamar siffar tsuntsu sa'an nan in hura a cikinsa, sai ya kasance tsuntsu, da izinin Allah. Kuma ina warkar da wanda aka haifa makaho da kuturu, kuma ina rayar da matottu, da izibin Allah. Kuma ina gaya muku abin da kuke ci da abin da kuke ajiyewa acikin gidajenku. Lalle ne, a cikin wannan akwai aya a gare ku, idan kun kasance masu yin imani
Kuma ina mai gaskatawa ga abin da yake a gabanina daga Taurata. Kuma (nazo) domin in halatta muku sashen abin da aka haramta muku. Kuma na tafo muku da wata aya daga Ubangijinku. Sai ku bi Allah da taƙawa, kuma ku yi mini ɗa'a
To, a lokacin da Isa ya gane kafirci daga gare su, sai ya ce: "Su wane ne mataimakana zuwa ga Allah?" Hawariyawa suka ce: "Mu ne mataimakan Allah. Mun yi imani da Allah. Kuma ka shaida cewa lalle ne mu, masu sallamawa ne
A lokacin da Ubangiji Ya ce: "Ya Isa! Lalle NI Mai karɓar ranka ne, kuma Mai ɗauke ka ne zuwa gare Ni, kuma Mai tsarkake ka daga waɗanda suka kafirta, kuma Mai sanya waɗanda suka bi ka a bisa waɗanda suka kafirta har Ranar ¡iyama. Sa'an nan kuma zuwa gare Ni makomarku take, sa'an nan in yi hukunci a tsakaninku, a cikin abin da kuka kasance kuna saɓa wa juna
Lalle ne misalin Isa a wurin Allah kamar misalin Adama ne, (Allah) Ya halitta shi daga turɓaya, sa'an nan kuma Ya ce masa: "Ka kasance: "Sai yana kasancewa
To, wanda ya yi musu* da kai a cikinsa, a bayan abin da ya zo maka daga ilmi, to ka ce: "Ku zo mu kirayi, 'ya'yanmu da 'ya'yanku da matan mu da matanku da kanmu da kanku sa'an nan kuma mu ƙanƙantar da kai sa'an nan kuma mu sanya la'anar, Allah a kan maƙaryata
Ka ce: "Ya ku Mutanen Littafi!* Ku tafo zuwa ga kalma mai daidaitawa** a tsaka ninmu da ku; kada mu bauta wa kowa fa ce Allah. Kuma kada mu haɗa kome da Shi, kuma kada sashenmu ya riƙi sashe Ubangiji, baicin Allah." To, idan sun juya ba ya sai ku ce: "ku yi shaida cewa, lalle ne mu masu sallama wa ne
Ya Mutanen Littafi! Don me kuke hujjacewa a cikin sha'anin lbrahima, alhali kuwa ba a saukar da Attaura da injila ba face daga bayansa? Shin ba ku hankalta
Ga ku ya waɗannan! Kun yi hujjacewa a cikin abin da yake kuna da wani ilmi game da shi, to, don me kuma kuke yin hujjacewa a cikin abin da ba ku da wani ilmi game da shi? Allah yana sani, kuma ku, ba ku sani ba
Ibrahima bai kasance Bayahude ba, kuma bai kasance Banasare ba, amma ya kasance mai karkata zuwa ga gaskiya, mai sallamawa, kuma bai kasance daga masu shirki ba
Lalle ne mafi hakkin mutane da Ibrahima haƙiƙa, su ne waɗanda suka bi shi a (zamaninsa) da wannan Annabi (Muhammadu) da waɗanda suka yi imani. Kuma Allah ne Majiɓincin muminai
Kuma wata ƙungiya daga Mutanen Littafi ta ce: "Ku yi imani da abin da aka saukar a kan waɗanda suka yi imani (da Muhammadu) a farkon yini, kuma ku kafirta a ƙarshensa; tsammaninsu, za su komo
Kada ku yi imani face* da wanda ya bi addininku." Ka ce: "Lalle ne, shiriya ita ce shiriyar Allah. (Kuma kada ku yi imani) cewa an bai wa wani irin abin da aka ba ku, ko kuwa su yi musu da ku a wurin Ubangijinku." Ka ce: "Lalle ne falala ga hannun Allah take, yana bayar da ita ga wanda Yake so, kuma Allah Mawadaci ne, Masani
Kuma daga Mutanen Littafi akwai wanda yake idan ka ba shi amanar kinɗari,* zai bayar da shi gare ka, kuma daga gare su akwai wanda idan ka ba shi amanar dinari, ba zai bayar da shi gare ka ba, face idan ka dawwama a kansa kana tsaye. Wannan kuwa, domin lalle ne su sun ce, "Babu laifi a kanmu a cikin Ummiyyai.**" Suna faɗar ƙarya ga Allah, alhali kuwa suna sane
Lalle ne waɗanda suke sayen 'yan tamani kaɗan da alkawarin Allah da rantsuwoyinsu, waɗannan babu wani rabo a gare su a Lahira, Kuma Allah ba Ya yin magana da su, kuma ba Ya dubi zuwa gare su, a Ranar ¡iyama, kuma ba Ya tsarkake su, kuma suna da Azaba mai raɗaɗi
Kuma lalle ne, daga gare su akwai wata ƙungiya suna karkatar da harsunansu da Littafi domin ku yi zaton sa daga Littafin, alhali kuwa ba shi daga Littafin. Kuma suna cewa: "Shi daga wurinAllah yake." Alhali kuwa shi, ba daga wurin Allah yake ba. Suna faɗar ƙarya ga Allah, alhali kuwa suna sane
Ba ya yiwuwa ga wani mutum, Allah Ya ba shi Littafi da hukunci da Annabci, sa'an nan kuma ya ce wa mutane: "Ku kasance bayi gare ni, baicin Allah." Amma (zai ce): "Ku kasance masu aikin ibada da abin da kuka kasance kuna karantar da Littafin, kuma da abin da kuka kasance kuna karantawa
Kuma a lokacin da Allah Ya riƙi alkawarin Annabawa: "Lalle ne ban ba ku wani abu ba daga Littafi da hikima, sa'an nan kuma wani manzo ya je muku, mai gaskatawa ga abin da yake tare da ku; lalle ne za ku gaskata Shi, kuma lalle ne za ku taimake shi." Ya ce: "Shin, kun tabbatar kuma kun riƙi alkawariNa a kan wannan a gare ku?" suka ce: "Mun tabbatar." Ya ce: "To, ku yi shaida, kuma Ni a tare da ku Ina daga masu shaida
Shin wanin Addinin Allah suke nema, alhali kuwa a gare Shi ne waɗanda ke cikin sama da ƙasa suka sallama wa, a kan so da ƙi, kuma zuwa gare Shi ake mayar da su
Ka ce: "Mun yi imani da Allah kuma da abin da aka saukar mana da abin da aka saukar wa Ibrahima da Isma'ila da Is'haƙa da Yaƙuba da jikoki, da abin da aka bai wa Musa da isa da annabawa daga Ubangijinsu, ba mu bambantawa a tsakanin kowa daga gare su. Kuma mu, zuwa gare Shi masu sallamawa ne
Yaya Allah zai shiryar da mutane waɗanda suka kafirta a bayan imaninsu, kuma sun yi shaidar cewa, lalle Manzo gaskiya ne, kuma hujjoji bayyanannu sun je musu? Allah ba Ya shiryar da mutane azzalumai
Lalle ne wanɗanda suka kafirta, kuma suka mutu alhali kuwa suna kafirai to ba za a karɓi cike da ƙasa na zinari daga ɗayansu ba, ko da ya yi fansa da shi, waɗannan suna da azaba mai raɗaɗi, kuma ba su da wasu mataimaka
Dukan abinci ya kasance halal ne ga Bani lsra'ila, face abinda Isra'ila ya haramta wa kansadaga gabanin saukar da Attaura. Ka ce: "To, ku zo da Attaura sa'an nan ku karanta ta, idan kun kasance masu gaskiya ne
A cikinsa akwai ayoyi bayyanannu; (ga misali) matsayin Ibrahima. Kuma wanda ya shige shi ya kasance amintacce. Kuma akwai hajjin ¦akin domin Allah a kan mutane, ga wanda ya sami ikon zuwa gare shi, kuma wanda ya kafirta to lalle Allah Mawadaci ne daga barin talikai
Ka ce: "Ya ku Mutanen Littafi! Don me kuke taushe wanda ya yi imani, daga hanyar Allah, kuma kuna neman ta zama karkatacciya, alhali kuwa kuna masu shaida? Kuma Allah bai gushe daga abin da kuke aikatawa ba yana Masani
Kuma yaya kuke kafircewa alhali kuwa ana karanta ayoyin Allah a gare ku, kuma a cikinku akwai manzonSa? Kuma wanda ya nemi tsari da Allah, to, an shiryar da shi zuwa ga hanya miƙaƙƙiya
Kuma ku yi daidami da igiyar Allah gaba ɗaya, kuma kada ku rarraba. Kuma ku tuna ni'imar Allah a kanku a lokacin da kuka kasance maƙiya sai Ya sanya soyayya a tsakanin zukatanku saboda haka kuka wayi gari, da ni'imarSa, 'yan'uwa. Kuma kun kasance a kan gaɓar rami na wuta sai Ya tsamar da ku daga gare ta, Kamar wannan ne Allah Yake bayyana muku ayoyinSa, tsammaninku, za ku shiryu
Kuma wata jama'a daga cikinku, su kasance suna kira zuwa ga alheri, kuma suna umurnida alheri, kuma suna hani dagaabin da ake ƙi. Kuma waɗannan, su ne masu cin nasara
A ranar da wasu fuskoki suke yin fari kuma wasu fuskoki suke yin baƙi (za a ce wa waɗanda fuskokinsu suke yin baƙin): "Shin kun kafirta a bayan imaninku? Don haka sai ku ɗanɗani azaba saboda abin da kuka kasance kuna yi na kafirci
Kun kasance mafi alherin al'umma wadda aka fitar ga mutane kuna umurni da alheri kuma kuna hani daga abin da ake ƙi, kuma kuna imani da Allah. Kuma da Mutanen Littafi sun yi imani, lalle ne, da (haka) ya kasance mafi alheri a gare su. Daga cikinsu akwai muminai, kuma mafi yawan su fasiƙai ne
An doka ƙasƙanci a kansu a inda duk aka same su face da wani alkawari daga Allah, da alkawari daga mutane. Kuma sun koma da fushi daga Allah, kuma aka doka talauci a kansu. Wannan kuwa domin su, lalle sun kasance suna kafirta da ayoyin Allah, kuma suna kashe annabawa, ba da wani haƙƙi ba. Wannan kuwa domin saɓawar da suka yi ne, kuma sun kasance suna yin ta'adi
Ba su zama daidai ba; daga Mutanen Littafi akwai wata al'umma wadda take tsaye, suna karatun ayoyin Allah a cikin sa'o'in dare, alhali kuwa suna yin sujada
Suna imani da Allah da Yinin Lahira, kuma suna umurui da abin da aka sani kuma suna hani daga abin da ba a sani ba, kuma suna gaugawa a cikin alherai. Kuma waɗannan suna cikin salihai
Lalle ne waɗanda suka kafirta, dukiyoyinsu ko ɗiyansu ba za su wadatar musu da kome ba daga Allah kuma waɗannan abokan wuta ne, su, acikinta, madawwama ne
Misalin abin da suke ciyarwa, a cikin wannan rayuwar duniya, kamar misalin iska ce (wadda) a cikinta akwai tsananin sanyi, ta sami shukar wasu mutane waɗanda suka zalunci kansu, sai ta halakar da ita. Allah bai zalunce su ba, amma kansu suka kasance suna zalunta
Ya ku waɗanda suka yi imani! Kada ku riƙi abokan asiri daga waninku, ba su taƙaita muku ɓarna. Kuma sun yi gurin abin da za ku cutu da shi. Haƙika, ƙiyayya ta bayyana daga bakunansu, kuma abin da zukatansu ke ɓoyewane mafi girma. Kuma lalle ne, Mun bayyana muku ayoyi, idan kun kasance kuna hankalta
Ga ku ya waɗannan! Kuna son su ba su son ku, kuma kuna imani da Littafi dukansa. Kuma idan sun haɗu da ku sukan ce "Mun yi imani". Kuma idan sun kaɗaita sai su ciji yatsu a kanku don takaici. Ka ce "Ku mutu da takaicinku. Lalle ne, Allah Masani ne ga abin da ke cikin ƙiraza
Idan wani alheri ya shafe ku sai ya baƙanta musu rai, kuma idan wata cutar ta shafe ku sai su yi farin ciki da ita. Kuma idan kun yi haƙuri kuma kuka yi taƙawa, ƙullinsu ba ya cutar ku da kome. Lalle ne, Allah ga abin da suke aikatawa Mai kewayewa ne
Na'am! Idan kuka yi haƙuri, kuma kuka yi taƙawa, kuma suka zo muku da gaugawarsu, irin wannan, Ubangijinku zai ƙare ku da dubu biyar daga malaiku masu alama
Kuma Allah bai sanya shi* ba, face domin bushara a gare ku, kuma domin zukatanku su natsu da shi. Taimako bai kasance ba face daga wurin Allah, Mabuwayi, Mai hikima
Babu kome a gare ka game da al'amarin (shiryar da su banda iyar da manzanci). Ko Allah Ya karɓi tubarsu, ko kuwa Ya yimusu azaba, to lalle ne su, masu zalunci ne
Allah ne da mulkin abin da yake a cikin sammai da abin da yake a cikin ƙasa, yana gafarta wa wanda Yake so, kuma yana azabta wanda Yake so, kuma Allah Mai gafara ne, Mai jin ƙai
Kuma ku yi gaugawa zuwa ga neman gafara daga Ubangijinku da wata Aljanna wadda faɗinta (dai dai da) sammai da ƙasa ne, an yi tattalinta domin masu taƙawa
Kuma waɗanda suke idan suka aikata wata alfasha ko suka zalunci kansu sai su tuna da Allah, saboda su nemi gafarar zunubansu ga Allah. Kuma wane ne ke gafara ga zunubai, face Allah? Kuma ba su doge a kan abin da suka aikata ba, alhali kuwa suna sane
Waɗannan sakamakonsu gafara ce daga Ubangijinsu, daga Gidajen Aljanna (waɗanda) ƙoramu na gudana daga ƙarƙashinsu, suna madawwama a cikinsu. Kuma madalla da ijarar masu aiki
Idan wani miki ya shafe ku, to, lalle ne, wani miki kamarsa ya shafi mutanen, kuma waɗancan kwanaki Muna sarrafa su a tsakanin mutane domin Allah Ya san waɗanda suka yi imani kuma Ya sami masu shahada daga gare ku. Kuma Allah ba Ya son azzalumai
Kuma Muhammadu bai zama ba face manzo lalle ne manzanni sun shuɗe a gabaninsa. Ashe idan ya mutu ko kuwa aka kashe shi, za kujuya a kan dugaduganku? To, wanda ya juya a kan dugadugansa, ba zai cuci Allah da kome ba. Kuma Allah zai saka wa masu godiya
Kuma ba ya yiwuwa ga wani rai ya mutu face da iznin Allah, wa'adi ne mai ƙayyadadden ajali. Kuma wanda yake nufin sakamakon duniya Muna ba shi daga gare ta. Kuma wanda ke nufin samakon Lahira Muna ba shi daga gare ta. Kuma za Mu saka wa masu godiya
Kuma da yawa wani Annabi wanda ya yi yaƙi, akwai jama'a masu yawa tare da shi, sa'an nan ba su yi laushi ba ga abin da ya same su a cikin hanyar Allah, kuma ba su yi rauni ba kuma ba su sad da kai ba. Kuma Allah yana son masu haƙuri
Kuma babu abin da ya kasance maganarsu face faɗarsu cewa: "Ya Ubangijinmu! Ka gafarta mana zunubanmu da ɓarnarmu a cikin al'amarinmu, kuma Ka tabbatar da dugaduganmu, kuma Ka taimake mu a kan mutanen nan kafirai
Za Mu jefa tsoro a cikin zukatan waɗanda suka kafirta saboda shirkin da suka yi da Allah game da abin da bai saukar da wani dalili ba game da shi. Kuma makomarsu wuta ce, kuma tir da mazaunin azzalumai
Kuma lalle ne haƙiƙa Allah Ya yi muku gaskiya ga wa'adinSa, a lokacin da kuke kashe su da izninSa har zuwa lokacin da kuka kasa,* kuma kuka yi jayayya a cikin al'amarin, kuma kuka saɓa a bayan (Allah) Ya nuna muku abin da kuke so. Daga cikinku akwai wanda yake nufin duniya kuma daga cikinku akwai wanda ke nufin Lahira. Sa'an nan kuma Ya juyar da ku daga gare su, domin Ya jarrabe ku. Kuma lalle ne, haƙiƙa, Ya yafe muku laifinku. Kuma Allah Ma'abucin falala ne ga muminai
A lokacin da kuke hawan dutse, gudane. Kuma ba ku karkata a kan kowa ba, alhali kuwa Manzon Allah na kiran ku a cikin na ƙarshenku.* Sa'an nan (Allah) Ya saka muku da baƙin ciki a tare da wani baƙin ciki. Domin kada ku yi baƙin ciki a kan abin da ya kuɓuce muku, kuma kada ku yi baƙin cikin a kan abin da ya same ku. Kuma Allah Masani ne ga abin da kuke aikatawa
Sa'an nan kuma (Allah) Ya saukar da wani aminci a gare ku daga bayan baƙin cikin; gyangyaɗi yana rufe wata ƙungiya daga gare ku, kuma wata ƙungiya, lalle ne, rayukansu sun shagaltar da su, suna zaton abin da ba shi ne gaskiya ba, a game da Allah, irin zaton jahiliyya, suna cewa: "Ko akwai waniabu a gare mu dai daga al'amarin?" Ka ce, "Lalle ne al'amari dukansa na Allah ne." Suna ɓoyewa a cikin zukatansu, abin da ba su bayyana shi a gare ka. Suna cewa: "Da muna da wani abu daga al'amarin da ba a kashe mu ba a nan."Ka ce: "Ko da kun kasance a cikin gidajenku, da waɗanda aka rubuta musu kisa sun fita zuwa ga wuraren kwanciyarsu;" kuma (wannan abu ya auku ne) domin Allah Ya jarrabi abin da ke cikin ƙirazanku. Kuma domin Ya tsarkake abin da ke cikin zukatanku. Allah Masani ne ga abin da ke cikin ƙiraza
Lalle ne waɗanda suka juya daga gare ku a ranar haɗuwar jama'a biyu, shaiɗan kawai ne ya talalaɓantar da su, saboda sashen abin da suka tsirfanta. Kuma lalle ne haƙiƙa, Allah Ya yafe laifidaga gare su. Lalle Allah ne Mai gafara Mai haƙuri
Ya ku waɗanda suka yi imani! Kada ku kasance kamar waɗanda suka kafirta kuma suka ce wa'yan'uwansu idan, sun yi tafiya a cikin ƙasa ko kuwa suka kasance a wurin yaƙi: "Da sun kasance a wurinmu da ba su mutun ba, kuma da ba a, kashe su ba." (Wannan kuwa) Domin Allah Ya sanya waccan magana ta zama nadama a cikin zukatansu. Kuma Allah ne Yake rayarwa kuma Yake matarwa. Kuma Allah, ga abin da kuke aikatawa, Mai gani ne
Saboda wata rahama ce daga Allah ka yi sanyin hali a gare su. Kuma da ka kasance mai hushi mai kaurin zuciya, da sun watse daga gefenka. Sai ka yafe musu laifinsu, kuma ka nema musu gafara, kuma ka yi shawara* da su a cikin al'amarin. Sa'an nan kuma idan ka yi niyyar zartarwa, to, ka dogara ga Allah, lalle ne, Allah Yana son masu tawakkali
Idan Allah Ya taimake ku, to, babu marinjayi a gare ku. Kuma idan Ya yarɓe ku, to, wane ne wanda yake taimakon ku bayanSa? Kuma ga Allah sai muminai su dogara
Kuma ba ya yiwuwa ga wani annabi ya ci gululu.* Wanda ya ci gululu zai je da abin da ya ci na gululun, a Ranar ¡iyama. Sa'an nan a cika wa kowane rai sakamakon abin da ya tsirfanta. Kuma su, ba za a zalunce su ba
Lalle ne haƙiƙa Allah Ya yi babbar falala* a kan muminai, domin Ya aika a cikinsu, Manzo daga ainihinsu yana karanta ayoyinSa a gare su, kuma yana tsar kake su, kuma yana karantar da su Littafi da hikima kuma lalle, sun kasance daga gabani, haƙiƙa suna cikin ɓata bayyananniya
Shin kuma a lokacin* da wata masifa, haƙiƙa, ta same ku alhali kuwa kun samar da biyunta, kun ce: "Daga ina wannan yake?" Ka ce: "Daga wurin rayukanku** yake." Lalle ne, Allah, a kan dukan kome, Mai ikon yi ne
Kuma domin Ya san waɗanda suka yi munafunci, kuma an ce musu: "Ku zo ku yi yaƙi a cikin hanyar Allah, ko kuwa ku tunkuɗe.*" Suka ce: "Da mun san (yadda ake) yaƙi da mun bi ku." Su zuwa ga kafirci a ranar nan, sun fi kusa daga gare su zuwa ga imani. Suna cewa da bakunansu abin da ba shi ne a cikin zukatansu ba. Allah ne Mafi sani ga abin da suke ɓoyewa
Waɗanda suka ce wa 'yan'uwansu kuma suka zauna abinsu: "Da sun yi mana ɗa'a, da ba a kashe su ba." Ka ce: "To, ku tunkuɗe mutuwa daga rayukanku, idan kun kasance masu gaskiya
Suna masu farin ciki saboda abin da Allah Ya ba su daga falalarSa, kuma suna yin bushara ga waɗanda ba su risku da su ba, daga bayansu; "Babu tsoro a kansu kuma ba su zama suna yin baƙin ciki ba
Waɗanda suka karɓa* kira zuwa ga Allah da ManzonSa, daga bayan miki ya same su. Akwai wata lada mai girma ga waɗanda suka kyautata** yi daga gare su, kuma suka yi taƙawa
Waɗanda mutane* suka ce musu: "Lalle ne, mutane sun tara (rundunoni) saboda ku, don haka ku ji tsornsu. Sai (wannan magana) ta ƙara musu imani, kuma suka ce: "Mai isarmu Allah ne kuma madalla da wakili Shi
Sa'an nan sukajuya da wata ni'ima daga Allah da wata falala, wata cuta ba ta shafe su ba, kuma suka bi yardar Allah. Kuma Allah ne Ma'abucin falala Mai girma
Kuma waɗannan da suke gaugawa a cikin kafirci kada su ɓata maka rai. Lalle ne su, ba za su cuci Allah da kome ba. Allah yana nufin cewa, ba zai sanya musu wani rabo ba a cikin Lahira kuma suna da wata azaba mai girma
Kuma kada waɗanda suka kafirta su yi zaton cewa, lalle ne jinkirin da Muke yi musu alheri ne ga rayukansu. Muna yi musu jinkirin ne domin su ƙara laifi kawai kuma suna da azaba mai wulaƙantarwa
Allah bai kasance yana barin muminai a kan abin da kuke kansa ba, sai* Ya rarrabe mummuna daga mai kyau. Kuma Al lah bai kasance Yana sanar da ku gaibi ba.** Kuma amma Allah Yana zaɓen wanda Ya so daga manzanninSa.*** Saboda haka ku yi imani da Allah da manzanninSa Kuma idan kun yi imani kuma kuka yi taƙawa, to, kuna da lada mai girma
Kuma kada waɗannan da suke yin rowa da abin da Allah Ya ba su daga falalarSa su yi zaton shi ne mafi alheri a gare su A'a, shi mafi sharri ne a gare su. Za a yi musu saƙandami da abin da suka yi rowa da Shi a Ranar ¡iyama Kuma ga Allah gadon sammai da ƙasa yake, kuma Allah, ga abin da kuke aikatawa, Masani ne
Lalle ne, haƙiƙa Allah Ya ji maganar waɗanda suka ce: "Lalle ne, Allah faƙiri ne, mu ne wadatattu." za mu rubuta abin da suka faɗa, da kisan da suka yi wa Annabawa ba da wani haƙƙi ba kuma Mu ce: "Ku ɗanɗani azabar gobara
Waɗanda suka ce: "Lalle ne Allah Ya yi alkawari zuwa gare mu, kada mu yi imani saboda wani Manzo sai ya zo mana da Baiko wadda wuta za ta ci." Ka ce: "Lalle ne wasu manzanni sun je muku, a gabanina, da hujjoji bayyanannu, kuma da abin da kuka faɗa, to, don me kuka kashe su, idan kun kasance masu gaskiya
To, idan sun ƙaryata ka, to lalle ne, an ƙaryata wasu manzanni a gabaninka, sun je musu da hujjoji bayyanannu da littattafai, da kuma Littafi mai haske
Kowane rai mai ɗanɗanar mutuwa ne. Kuma ana cika muku ijarorinku kawai ne a Ranar ¡iyama. To, wanda aka nisantar daga barin wuta, kuma aka shigar da shi Aljanna, to, lalle ne ya tsira. Kuma rayuwar duniya ba ta zama ba face jin daɗin ruɗi
Lalle ne za a jarraba* ku a cikin dukiyarku da rayukanku, kuma lalle ne kuna jin cutarwa mai yawa daga waɗanda aka bai wa Littafi a gabaninku da kuma waɗanda suka yi shirki. Kuma idan kun yi haƙuri, kuma kuka yi taƙawa, to lalle ne, wannan yana daga manyan al'amurra
Kuma a lokacin da Allah Ya riƙi alkawarin waɗanda aka bai wa* Littafi, "Lalle ne kuna bayyana shi ga mutane, kuma ba za ku ɓoye shi ba." Sai suka jefarda shi a bayan bayansu, kuma suka sayi 'yan kuɗi kaɗan da shi. To, tir da abin da suke saye
Kada lalle ka yi zaton waɗanda suke yin farin ciki da abin da suka bayar, kuma suna son a yabe su da abin da ba su aikata ba. To, kada lalle ka yi zaton su da tsira daga azaba. Kuma suna da azaba mai raɗadi
Waɗanda suke ambatar Allah a tsaye da zaune da a kan sasanninsu, kuma suna tunani a kan halittar sammai da ƙasa: "Ya Ubangijinmu! Ba Ka halitta wannan a kan banza ba. TsarkinKa! Saboda haka Ka tsare mu daga azabar wuta
Ya Ubangijinmu! Lalle ne mu mun ji Mai kira yana kira zuwa ga imani cewa, 'Ku yi imani da Ubangijinku.' Sai muka yi imani. Ya Ubangijinmu! Saboda haka Ka gafarta mana zunubanmu, kuma Ka kankare miyagun ayyukanmu daga gare mu. Kuma Ka karɓi rayukanmu tare da mutanen kirki
Ya Ubangijinmu! Ka ba mu abin da Ka yi mana wa'adi (alkawari) a kan manzanninKa, kuma kada Ka tozarta mu a Ranar ¡iyama. Lalle ne Kai, ba Ka saɓawar Alkawari
Saboda haka Ubangijinsu Ya karɓa musu cewa, "Lallene Ni ba zan tozartar da aikin wani mai aiki ba daga gare ku, namiji ne ko kuwa mace, sashenku daga sashe. To, waɗanda suka yi hijira kuma aka fitar da su daga gidajensu, kuma aka cutar da su a cikin hanyaTa, kuma suka yi yaƙi, kuma aka kashe su, lalle ne zan kankare musumiyagun ayyukansu, kuma lalle ne zan shigar da su gidajen Aljanna (waɗanda) ƙoramu ke gudana daga ƙarƙashinsu, a kan sakamako daga wurin Allah. Kuma a wurinSa akwai kyakkyawan sakamako
Amma waɗanda suka bi Ubangijinsu da taƙawa suna da Gidajen Aljanna (waɗabda) ƙoramu ke gudana a ƙarƙashinsu suna madawwama a cikinsu, a kan, liyafa daga wurin Allah, kuma abin da ke wurin Allah ne mafi alheri ga barrantattu
Kuma lalle ne daga Mutanen Littafi* haƙiƙa akwai wanda yake yin imani da Allah da abin da aka saukar zuwa gare ka, da abin da aka saukar zuwa gare su, suna masu tawalu'i ga Allah, ba su sayen tamani kaɗan da ayoyin Allah. Waɗannan suna da ijararsu a wurin Ubangijinsu. Lalle ne Allah Mai gaugawar sakamako da yawa ne