Ya ku mutane! Ku bi Ubangijinku da taƙawa Wanda Ya halitta ku daga rai guda, kuma Ya halitta, daga gare shi, ma'auransa, kuma Ya watsa daga gare su maza masu yawa da mata. Kuma ku bi Allah da taƙawa Wanda kuke roƙon juna da (sunan), shi, da kuma zumunta.* Lalle ne Allah Ya kasance, a kanku, Mai tsaro ne
Kuma ku bai wa marayu dukiyoyinsu, kuma kada ku musanya mummuna da mai kyau. Kuma kada ku ci dukiyoyinsu zuwa ga dukiyoyinku. Lalle shi, ya kasance zunubi ne mai girma
Kuma idan kun ji tsoron ba za ku yi adalci ba a cikin marayu,* to, (akwai yadda za a yi) ku auri abin da ya yi muku daɗi daga mata; biyu-biyu, da uku-uku, da huɗu-huɗu. Sa'an nan idan kun ji tsoron ba za ku yi adalci ba, to, (ku auri) guda ko kuwa abin da hannayenku na dama suka mallaka. Wannan shi ne mafi kusantar zama ba ku wuce haddi ba
Kuma ku bai wa mata sadakokinsu da sauƙin bayarwa. Sa'an nan idan suka yafe muku wani abu daga gare shi, da daɗin rai, to, ku ci shi da jin daɗi da sauƙin haɗiya
Kada ku bai wa wawaye* dukiyarku, wadda Allah Ya sanya ta a gare ku, kuna masu tsayuwa (ga gyaranta). Kuma ku ciyar da su a cikinta, kuma ku tufatar da su, kuma ku gaya musu magana sananniya ta alheri
Kuma ku jarraba marayu, har a lokacin da suka isa aure. To, idan kun lura da shiriya daga gare su, to, ku miƙa musu dukiyoyinsu. Kada ku ci ta da ɓarna, kuma da gaggawa kafin su girma. Kuma wanda yake wadatacce, to, ya kama kansa, kuma wanda yake faƙiri, to, ya ci, gwargwadon yadda ya kamata. To, idan kun miƙa musu dukiyoyinsu, sai ku shaidar a kansu. Kuma Allah Ya isa Ya zama Mai bincike
Maza suna da rabo* daga abin da iyaye biyu da mafi kusantar dangi suka bari, kuma mata suna da rabo daga abin da iyaye biyu da mafi kusantar dangi suka bari, daga abin da ya ƙaranta daga gare shi ko kuwa ya yi yawa, rabo yankakke
Kuma waɗanda suke da sun bar* zuriyya masu rauni a bayansu, za su ji tsoro a kansu, su yi sauna, sa'an nan su bi Allah da taƙawa, kuma su faɗi magana madaidaiciya
Allah Yana yi muku wasiyya a cikin 'ya'yanku; namiji yana da rabon mata biyu. Idan sun kasance mata ne fiye da biyu kuwa, to, suna da biyu daga kashi uku ɗin abin da ya bari, kuma idan ta zama guda ce (kawai) to, tana da rabi. Kuma iyayensa biyu kowane ɗaya daga cikinsu yana da ɗaya daga kashi shida ɗin abin da ya bari idan wani reshe ya kasance gare shi, to, idan reshe bai kasance gare shi ba, kuma iyayensa ne (kawai) suka gaje shi, to, uwa tana da sulusi (ɗaya daga cikin kashi uku). Sa'an nan idan 'yan'uwa sun kasance gare shi, to, uwarsa tana da sudusi (ɗaya daga cikin kashi shida) daga bayan wasiyya wadda ya yi ko kuwa bashi. Ubanninku da 'ya'yan ku, ba ku sani ba, wannensu ne mafi kusantar amfani, a gare ku. Yankawa daga Allah. Lalle ne, Allah Ya kasance Masani Mai hikima
Kuma kuna da rabin abin da matanku na aure suka bari idan reshe bai kasance gare su ba. Sa'an nan idan reshe ya kasance gare su, to, kuna da rubu'i (ɗaya daga cikin kashi huɗu) daga abin da suka barin, daga bayan wasiyya wadda suka yi ko kuma bashi. (Su) kuma suna da rubu'i daga abin da kuka bari idan reshe bai kasance ba gare ku, idan kuwa reshe ya kasance gare ku, to, suna da sumuni (ɗaya daga cikin kashi takwas) daga abin da kuka bari, daga bayan wasiyya wadda kuka yi ko kuwa bashi. Idan wani namiji ya kasance ana gadon sa bisa kalala, ko kuwa wata mace alhali kuwa yana da ɗan'uwa ko 'yar'uwa* to, kowane ɗaya daga cikinsu yana da sudusi (ɗaya daga cikin kashi shida), sai idan sun kasance mafi yawa daga wannan, to, su abokan tarayya ne a cikinsulusi (ɗaya bisa uku), daga bayan wasiyya wadda aka yi ko kuma bashi. Ba da yana mai cutarwa ba, ga wasiyya, daga Allah. Kuma Allah Masani ne Mai haƙuri
Waɗancan iyakokin Allah ne. Wanda ya yi ɗa'a ga Allah da Manzon Sa, (Allah) zai shigar da shi gidajen Aljanna (waɗanda) ɗoramu suna gudana daga ƙarƙashinsu, suna madawwama a cikinsu, kuma wannan shi ne rabo babba
Kuma wanda ya saɓa wa Allah da Manzon Sa, kuma ya ƙetare iyakokin Sa, zai shigarda shi wuta, yana madawwami a cikinta, kuma yana da wata azaba mai walakantarwa
Kuma waɗanda suka je wa alfasha daga matanku, to, ku nemi Shaidar mutane huɗu daga gare ku a kansu. To, idan sun yi shaida, sai ku tsare su a cikin gidaje har mutuwa ta karɓi rayukansu, ko kuwa Allah Ya sanya wata hanya a gare su
Kuma waɗanda (maza biyu) suka je mata* daga ku, to, ku cutar da su, sa'an nan idan sun tuba kuma suka kyautata halayensu, sai ku kau da kai da ga barinsu. Lalle ne Allah Ya kasance Mai kaɓar tuba ne, Mai jin ƙai
Abar da take tuba kawai ga Allah, ita ce ga waɗanda suke aikatawar mugun aiki da jahilci sa'an nan su tuba nan kusa* to, waɗannan Allah Yana karɓar tu barsu kuma Allah Ya kasance Masani ne, Mai hikima
Ba tuba ba ce ga waɗanda suke aikatawar munanan ayyuka har idan mutuwa ta halarci ɗayansu ya ce: "Lalle ne ni, na tuba yanzu," kuma ba tuba ba ce ga waɗanda suke mutuwa alhali kuwa suna kafi rai Waɗannan mun yi musu tattalin wata azaba mai raɗaɗi
Ku waɗanda suka yi imani! Ba ya halatta a gare ku, ku gaji mata a kan tilas kuma kadaku hana su aure domin ku tafi da sashen abin da kuka ba su, face idan suka zo da wata alfasha* bayya nanniya kuma ku yi zamantakewa da su da alheri sa'an nan idan kun ƙi su, to akwai tsammanin ku ƙi wani abu alhali kuwa Allah Ya sanya wani alheri mai yawaa cikinsa
Kuma idan kun yi nufin musanya mata a matsayin wata mata, alhali kuwa kun bai wa ɗayarsu ƙinɗari* to kada ku karɓi kome daga gare, shi, shin, za ku karɓe shi da ƙarya da zunubi bayyananne
Kuma kada ku auri abin da ubanninku suka aura daga mata, face abin da ya shige. Lalle ne shi, ya kasance alfasha da abin ƙyama. Kuma ya munana ya zama hanya
An haramta muku uwayenku, da 'ya'yanku, da 'yan'uwanku mata, da goggonninku, da innoninku, da 'ya'yan ɗan'uwa, da 'ya'yan 'yar'uwa, da uwayenku waɗanan da suka shayar da ku mama, da 'yan'uwanku mata na shan mama, da uwayen matanku, da agololinku waɗanda suke cikin ɗakunanku daga matanku, waɗanda kuka yi duhuli da su, kuma idan ba ku yi duhuli da su ba, to, babu laifi* a kanku, da matan 'ya'yanku waɗanda, suke daga tsatsonku, kuma kada ku haɗa tsakanin 'yan'uwa biyu mata, face abin da ya shige. Lalle ne, Allah Ya kasance Mai gafara ne Mai jin ƙai
Da tsararrun auren* wasu maza, face dai abin da hannuwanku suka mallaka. (Ku tsare) Littafin Allah a kanku. Kuma an halatta muku abin da yake bayan wancan. Ku nema da dukiyoyinku, kuna masu yin aure, ba masu yin zina ba. sa'an nan abin da kuka ji daɗi da shi daga gare su, to, ku ba su ijarorinsu bisa farillar sadaki. Babu laifia gare ku ga abin da kuka yi yardatayya** da shi a bayan farillar sadaki. Lalle ne Allah Ya kasance Masani ne, Mai hikima
Kuma wanda* bai sami wadata ba daga cikinku bisa ga ya auri 'ya'ya muminai, to, (ya aura) daga abin da hannuwanku na dama suka mallaka, daga kuyanginku muminai. Kuma Allah ne Mafi sani ga imaninku, sashenku daga** sashe. Sai ku aure su da izinin mutanensu. Kuma ku ba su ijarorinsu bisa ga abin da aka sani, suna masu kamun kai ba masu zina ba, kuma ba masu riƙon abokai ba. To, idan aka aure su, sai kuma suka zo da wata alfasha, to, akwai a kansu rabin abin da ko a kan, 'ya'ya daga azaba. wancan (auren kuyanga) ga wanda ya ji tsoron wahala ne daga gare ku. Kuma ku yi haƙuri shi ne mafi alheri a gare ku. Kuma Allah Mai gafara ne Mai jin ƙai
Ya ku waɗanda suka yi imani! Kada ku ci dukiyoyinku a tsakaninku da yaudara*, face idan ya kasance, daga fatauci ne, bisa yardatayya daga gare ku. Kuma kada ku kashe kanku. Lalle ne Allah Ya kasance, game da ku, Mai jin ƙai ne
Kuma kada ku yi gurin abin da Allah Ya fifita sashenku da shi a kan sashe; maza suna da rabo daga abin da suka tsirfanta, kuma mata suna da rabo daga abin da suka tsirfanta. Ku roƙi Allah daga falalar Sa. Lalle ne Allah Ya kasance ga dukkan kome, Masani
Kuma ga kowa, Mun sanya magada daga abin da mahaifa da mafiya kusancin zumunta suka bari. Kuma waɗanda rantsuwoyinku suka ƙulla* ku ba su rabonsu. Lalle ne, Allah Ya kasance, a kan dukkan kome, Mahalarci
Maza masu tsayuwa ne* a kan mata, saboda abin da Allah Ya fifita sashensu da shi a kan sashe kuma saboda abin da suka ciyar daga dukiyoyinsu. To, salihanmata masu ɗa'a ne, masu tsarewa ga gaibi saboda abin da Allah Ya tsare. Kuma waɗanda kuke tsoron bijirewarsu, to, ku yi musu gargaɗi, kuma ku ƙaurace musu a cikin wuraren kwanciya, kuma ku doke su. Sa'an nan kuma, idan sun yi muku ɗa'a, to, kada ku nemiwata hanya a kansu. Lalle ne Allah Ya kasance Maɗaukaki, Mai girma
Kuma idan kun ji tsoron saɓawar tsakaninsu to ku aika da wani mai sulhu daga mutanensa da wani mai sulhu daga mutanenta*. Idan sun yi nufin gyarawa, Allah zai daidaita tsakaninsu (ma'auran). Lalle ne Allah Ya kasance Masani Mai jarrabawa
Kuma ku bauta wa *Allah kuma kada ku haɗa wani da Shi, kuma ga mahaifa ku yi kyautatawa, kuma ga ma'abucin zumunta da marayu da matalauta, da maƙwabci ma'abucin kusanta, da maƙwabci manisanci, da aboki a gefe da ɗan hanya, da abin da hannuwanku na dama suka mallaka. Lalle ne Allah ba Ya son wanda ya kasance mai taƙama, mai yawan alfahari
Waɗanda suke yin rowa, kuma suna umurnin mutane da yin rowa, kuma suna ɓoyewar abin da Allah Ya ba su na falalarSa. Kuma Mun yi tattali, saboda kafirai, azaba mai walakantarwa
Kuma waɗanda suke ciyar da dukiyoyinsu domin nuna wa mutane, kuma ba su yin imani da Allah, kuma ba su yin imanida Ranar Lahira kuma wanda Shaiɗan ya kasance abokin haɗi a gare shi, to, ya munana ga abokinhaɗi
Kuma mene ne a kansu, idan sun yi imani da Allah, kumada Ranar Lahira, kuma sun ciyar da abin da Allah Ya azurta su, kuma Allah Ya kasance, gare su, Masani
Ya ku waɗanda suka yi imani! Kada ku kusanci salla alhali kuwa kuna masu maye*, sai kun san abin da kuke faɗa kuma haka idan kuna masu janaba, face mai ƙetare hanya, har ku yi wanka. Kuma idan kun kasance majinyata, ko kuwa a kan tafiya ko kuwa wani daga cikinku, idan ya zo daga kashi, ko kuwa kun shafi mata ba ku sami ruwa ba, to ku nufi, fuskar ƙasa mai kyau, ku yi shafa ga fuskokinku da hannuwanku.** Lalle ne Allah Ya kasance Mai yafewa Mai gafara
Daga waɗanda suka tuba (Yahudu), akwai wasu suna karkatar da magana daga wurarenta suna cewa: "Munjiya* kuma mun ƙiya, kuma ka jiya a wani wurin jiyawa, kuma ra'ina (da ma'anar 'ruɓaɓɓe'), ka tsare mu," domin karkatarwa da harsunansu, kuma domin suka a cikin addini. Kuma da lalle su, sun ce: "Mun jiya kuma mun yi ɗa'a, kuma ka saurara kuma ka dakata mana," haƙiƙa, da ya kasance mafi alheri a gare su, kuma mafi daidaita; amma Allah Ya la'ane su, saboda kafircinsu don haka ba za su yi imani ba, sai kaɗan
Ya ku waɗanda aka bai wa Littafi! Ku yi imani da abinda Muka saukar, yana mai gaskatawa ga abin da yake tare da ku, tun gabanin Mu shafe wasu fuskoki, sa'an nan Mu mayar da su a kan bayayyakinsu, ko Mu la'ane su kamar yadda Muka la'ani masu Asabar. Kuma umurnin Allah ya kasance abin aikatawa
Lalle ne, Allah ba Ya gafarta a yi shirki game da Shi, kuma Yana gafarta abin da yake bayan wannan ga wanda Yake so, kuma wanda ya yi shirki da Allah, to, lalle ne ya ƙirƙiri zunubi mai girma
Shin, ba ka gani ba, zuwa ga waɗanda suke tsarkake kansu? A'a, Allah ne Yake tsarkake wanda Yake so. Kuma ba za a zalunce su da zaren gurtsun dabino ba
Shin, ba ka gani ba zuwa ga waɗanda aka bai wa rabo da ga Littafi suna imani da gunki da Shaiɗan* kuma suna cewa ga waɗanda suka kafirta: "Waɗannan ne mafiya shiriya daga waɗanda suka yi imani ga hanya
Ko suna hasadar mutane* ne a kan abin da Allah Ya ba su daga falalar Sa? To, lalle ne, Mun bai wa gidan Ibrahim Littafida hikima kuma Mun ba su mulki mai girma
Lalle ne waɗanda suka kafirta da ayoyinMu za Mu ƙone su da wuta, ko da yaushe fatunsu suka nuna, sai Mu musanya musu wasu fatun, domin su ɗanɗani azaba. Lalle ne Allah Ya kasance Mabuwayi, Mai hikima
Kuma waɗanda suka imani, kuma suka aikata ayyuka na ƙwarai, za Mu shigar da su gidajen Aljanna, (waɗanda) ƙoramu suna gudana daga ƙarƙashinsu, suna dawwamammu a cikinsu har abada suna da, a cikinsu, matan aure masu tsarki, Kuma Muna shigar da su a wata inuwa matabbaciyar lumshi
Lalle ne Allah Yana umurnin ku ku bayar da amanoni zuwa ga masu su.* Kuma idan kun yi hukunci a tsakanin mutane, ku yi hukunci da adalci. Lalle ne Allah madalla da abin da Yake yi muku wa'azi da shi. Lalle ne Allah Ya kasance Mai ji ne, Mai gani
Ya ku waɗanda suka imani! Ku yi ɗa'a ga Allah, kuma ku yi ɗa'a ga ManzonSa, da ma'abuta al'amari daga cikinku.* Idan kun yi jayayya a cikin wani abu, to ku mayar da shi zuwa ga Allah da Manzon Sa idan kun kasance kuna imani da Allah da Ranar Lahira. wannan ne mafi alheri, kuma mafi kyau ga fassara
Shin, ba ka gani ba, zuwa ga waɗanda suke riyawar cewa suna imani da abin da aka saukar zuwa gare ka da abin da aka saukar daga gabaninka, suna nufin su kai ƙara zuwa ga ¦agutu* alhali kuwa, lalle ne, an umurce su da su kafirta da shi, kuma Shaiɗan yana neman ya ɓatar da su, ɓatarwa mai nisa
To, yaya, idan wata masifa ta same su, saboda abin da hannuwansu suka gabatar sa'an nan kuma su je maka suna rantsuwa da Allah cewa, "Ba mu yi nufin kome ba sai kyautatawa da daidaitawa
Waɗannan ne waɗanda Allah Ya san abin da ke cikin zukatansu. Saboda haka ka kau da kai daga gare su, kuma ka yi musu gargaɗi, kuma ka gaya musu, a cikin sha'anin kansu, magana mai nauyi da fasaha
Kuma ba Mu aiki wani Manzo ba face domin a yi masa ɗa'a da izinin Allah. Kuma da dai lalle su a lokacin da suka zalunci kansu,* sun zo maka sa'an nan suka nemi gafarar Allah kuma Manzo ya nema musu gafara, haƙiƙa, da sun sami Allah Mai karɓar tuba Mai jin ƙai
To, a'aha! Ina rantsuwa da Ubangijinka, ba za su yi imani ba, sai sun yarda da hukuncinka ga abin da ya saɓa a tsakaninsu, sa'an nan kuma ba su sami wani ƙunci a cikin zukatansu ba, daga abin da ka hukunta, kuma su sallama sallamawa
Kuma da dai lalle Mu, Mun wajabta musu cewa, "Ku kashe kanku, ko kuwa ku, fita daga gidajenku," da ba su aikata shi ba, face kaɗan daga gare su. Kuma da dai lalle su sun aikata abin da ake yi musu gargaɗi da shi, haƙiƙa, da ya kasance mafi alheri dagagare su, kuma mafi tsanani ga tabbatarwa
Kuma waɗannan da suka yi ɗa'a ga Allah da Mazonsa, to, waɗannan suna tare da waɗanda Allah Ya yi ni'ima a kansu, daga annabawa da masu yawan gaskatawa, da masu shahada* da salihai. kuma waɗannan sun kyautatu ga zama abokan tafiya
Kuma lalle ne daga cikinku akwai mai fasarwa*. To idan wata masifa ta same ku, sai ya ce: "Lalle ne, Allah Ya yi mini ni'ima domin ban kasance mahalarci tare da su ba
Kuma lalle ne idan wata falala daga Allah ta same ku haƙiƙa, tabbas, yana cewa, kamar wata soyayya ba ta kasance a tsakaninku da shi ba: "Ya kaitona! Da na zama tare da su dai, domin in rabonta da rabo mai girma
Sai waɗanda suke sayar da rayuwar duniya su karɓi ta Lahira su yi yaƙi, a cikin hanyar Allah. Kuma wanda ya yi yaki a cikin hanyar Allah to a kashe shi ko kuwa ya rinjaya, sa'an nan za Mu ba shi ijara mai girma
Kuma mene ne ya same ku, ba ku yin yaƙi a cikin hanyar Allah, da waɗanda aka raunanar daga maza da mata da yara suna cewa: "Ya Ubangijinmu! Ka fitar da mu daga wannan alƙarya wadda mutanenta suke da zalunci, kuma Ka sanya mana majiɓinci daga gunKa, kuma Ka sanya mana mataimaki daga gunKa
Waɗanda suka yi imani, suna yaki a cikin hanyar Allah, kuma waɗanda suka kafirta suna yaƙi a cikin hanyar ¦agutu (Shaiɗan). To, ku yaƙi majiɓintan Shaiɗan. Lalle ne kaidin Shaiɗan ya kasance mai rauni
Shin, ba ka gani ba zuwa ga waɗanda aka ce musu: "Ku kange hannuwanku, kuma ku tsayar da salla, kuma ku bayar da zakka."? To a lokacin da aka wajabta musu yaƙi sai ga wani ɓangare daga cikinsu suna tsoron mutane kamar tsoron Allah ko kuwa mafi tsanani ga tsoron, kuma suka ce: "Ya Ubangijinmu! Don me Ka wajabta yaƙi a kanmu? Me ya hana Ka jinkirta mana zuwa ga wani ajali na kusa?"Ka ce: "Jin daɗin duniya kaɗan ne, kuma Lahira ce mafi alheri ga wanda ya yi taƙawa. Kuma ba a zaluntar ku da sililin hancin gurtsun dabino
Inda duk kuka kasance, mutuwa za ta riske ku, kuma ko da kun kasance ne a cikin ganuwoyi ingatattu!" Kuma idan wani alheri ya same su sai su ce: "Wannan daga wurin Allah ne," kuma idan wata cuta ta same su, sai su ce: "Wannan daga gare ka ne."Ka ce: "Dukkansu daga Allah ne." To, me ya sami waɗannan mutane, ba su kusantar fahimtar magana
Abin da ya same ka daga alheri, to, daga Allah yake, kuma abin da ya same ka daga sharri, to, daga kanka yake, kuma Mun aike ka zuwa ga mutane, (kana) Manzo, kuma Allah Ya isa ga zama shaida
Kuma suna cewa, "Da'a" sa'an nan idan sun fita daga wurinka, sai wata ƙungiya daga cikinsu ta kwana da niyyar wanin abin da take faɗa, alhali kuwa Allah na rubuta abin da suke kwana da niyyarsa. Saboda haka ka kau da kai daga gare su, kuma ka dogara ga Allah, kuma Allah Ya isa ya zama wakili
Kuma idan wani al'amari* daga aminci ko tsoro ya je musu, sai su watsa shi. Da sun mayar da shi zuwa ga Manzo da ma'abuta al'amari daga gare su, lalle ne, waɗanda suke yin bincikensa, daga gare su, za su san shi. Kuma ba domin falalar Allah ba a kanku da rahamar Sa, haƙiƙa, da kun bi Shaiɗan face kaɗan
Saboda haka, ka* yi yaƙi a cikin hanyar Allah, ba a kallafa maka ba, face a kanka, kuma ka kwaɗaitar da muminai. Akwai tsammanin Allah Ya kange gafin waɗanda suka kafirta, kuma Allah ne Mafi tsananin gafi, kuma Mafi tsananin azabtawa
Wanda ya yi* ceto, ceto mai kyau, zai sami rabo daga gare shi, kuma wanda ya yi ceto, ceto mummuna, zai sami ma'aunidaga gare shi, Kuma Allah Ya kasance, a kan dukkan kome, Mai ƙayyade lokaci
Kuma idan an gaishe* ku da wata gaisuwa, to, ku yi gaisuwa da abin da yake mafi kyau daga gare ta, ko kuwa ku mayar da ita. Kuma Allah Ya kasance a kan dukkan kome Mai lissafi
Allah babu abin bautawa face Shi. Lalle ne haƙiƙa Yana tara* ku har zuwa ga Yinin ¡iyama babu shakka a cikinsa. Kuma wane ne mafi gaskiya daga Allah ga abari
To, mene ne ya same* ku a cikin munafukai kun zama ƙungiya biyu, alhali kuwa Allah ne Ya mayar da su saboda abin da suka tsirfanta? Shin, kuna nufin ku shiryar da wanda Allah Ya ɓatar ne? Kuma wanda Allah Ya ɓatar to ba za ka sami wata hanya ba zuwa gare shi
Suna gurin ku kafirta kamar yadda suka kafirta, domin ku kasance daidai. Saboda haka kada ku riƙi wasu masoya daga cikinsu, sai sun yo hijira a cikin hanyar Allah. Sa'an nan idan sun juya, to, ku kama su kuma ku kashe su inda duk kuka same su. Kuma kada ku riƙi wani masoyi daga gare su ko wani mataimaki
Face dai waɗanda suke saduwa zuwa ga wasu mutane waɗanda a tsakaninku da su akwai alkawari, ko kuwa waɗanda suke sun je muku (domin) ƙirazansu sun yi ƙunci ga su yake ku, ko su yaƙi mutanensu. Kuma da Allah Ya so lalle ne, da Ya ba su iko a kanku, sa'an nan, haƙika, su yake ku. To, idan sun nisance ku sa'an nan ba su yaƙe ku ba, kuma suka jefa sulhu zuwa gare ku, to, Allah bai sanya wata hanya ba, a gare ku, a kansu
Za ku sami wasu* suna nufin su amintar da ku kuma su amintar da mutanensu, ko da yaushe aka mayar da su ga fitina, sai a dulmuya su a cikinta. To, idan ba su nisance ku ba, kuma sun jefa sulhu zuwa gare ku, kuma sun kange hannuwansu, to, ku kama su, kuma ku kashe su inda duk kuka kama su, kuma waɗannan, Mun sanya muku dalili bayyanannea kansu
Kuma ba ya kasancewa* ga mumini ya kashe wani mumini, face bisa ga kuskure. Kuma wanda ya kashe mumini bisa ga kuskure, sai ya 'yanta wuya mumina tare da miƙa diyya ga mutanensa, ace idan sun bari sadaka. Sa'an nan idan (wanda aka kashe) ya kasance daga wasu mutane maƙiya a gare ku, kuma shi muminine, sai ya 'yanta wuya mumina. Kuma idan ya kasance daga wasu mutane ne (waɗanda) a tsakaninku da tsakaninsu akwai alkawari, sai ya bayar da diyya ga mutanensa, tare da 'yanta wuya mumina. To, wanda bai sami (wuyan ba) sai azumin watanni biyu jere, domin tuba daga Allah. Kuma Allah Ya kasance Masani, Mai hikima
Kuma wanda ya kashe wani mumini da ganganci,* to, sakamakonsa Jahannama, yana madawwami a cikinta kuma Allah Ya yi fushi a kansa, kuma Ya la'ane shi, kuma Ya yi masa tattalin azaba mai girma
Ya ku waɗanda suka yi imani! Idan kun yi tafiya (a cikin ƙasa), domin jihadi, to, ku nemi bayani.* Kuma kada ku ce wa wanda ya jifa sallama zuwa gare ku: "Ba Musulmi kake ba." Kuna neman hajar rayuwar duniya, to, a wurin Allah akwai ganimomi masu yawa. Kamar wannan ne kuka kasance a gabanin ku musulunta, sa'an nan Allah Ya yi muku falala. Saboda haka ku zan neman bayani. Lalle ne Allah Ya kasance, ga abin da kuke aikatawa, Masani
Masu zama* daga barin yaƙi daga muminai, wasun ma'abuta larura da masu jihadi a cikin hanyar Allah da dukiyoyinsu da rayukansu, ba su zama daidai. Allah Ya fifita masu jihadi da dukiyoyinsu da rayukansu a kan masu zama, ga daraja. Kuma dukansu Allah Ya yi musu alkawari da abu mai kyau.** Kuma Allah ya fifita masu jihadi a kan masu zama da lada mai girma
Lalle ne, waɗanda mala'iku* suka karɓi rayukansu, (alhali) suna masu zaluntar kansu, sun ce (musu): "A cikin me kuka kasance?" (Su kuma) suka ce: "Mun kasance waɗanda aka raunana a cikin ƙasa." Suka ce: "Ashe ƙasar Allah ba ta kasance mayalwaciya ba, domin ku yi hijira a cikinta?" To, waɗannan makomarsu Jahannama ce. Kuma ta munana ta zama makoma
Kuma wanda ya yi hijira a cikin hanyar* Allah, zai samu, a cikin ƙasa, wuraren juyawa masu yawa da yalwa. Kuma wanda ya fita daga gidansa yana mai hijira zuwa ga Allah da ManzonSa, sa'an nan kuma mutuwa ta riske shi, to, lalle ne, ladarsa ta auku ga Allah, Kuma Allah Ya kasance, a gare ku, Mai gafara, Mai jin ƙai
Kuma idan kun yi tafiya a cikin ƙasa to, babu laifi a kanku ku rage* daga salla idan kun ji tsoron waɗanda suka kafirta su fitine ku. Lalle ne kafirai sun kasance, a gare ku, maƙiyi bayyananne
Kuma idan ka kasance a cikinsu, sai ka tsayar musu da salla, to, wata ƙungiya daga gare su ta tsaya tare da kai, kuma sai su riƙe makamansu. Sa'an nan idan sun yi salla, to, sai su kasance daga bayanku. Kuma wata ƙungiya ta dabam (ta) waɗanda ba su yi sallar ba, ta zo, sa'an nan su yi sallar tare da kai. Kuma su riƙi shirinsu da makamansu. Waɗanda suka kafirta sun yi gurin da dai kuna shagala daga makamanku da kayanku domin su karkata a kanku, karkata guda. Kuma babu laifi, a kanku idan wata cuta daga ruwan sama ta kasance a gare ku, ko kuwa kun kasance masu jinya ga ku ajiye makamanku kuma dai ku riƙi shirinku. Lalle ne, Allah Ya yi tattali, ga kafirai, azaba mai walakantarwa
Sa'an nan idan kun ƙare salla, to ku ambaci Allah tsaye da zaune da a kan sasanninku. Sa'an nan idan kun natsu, to, ku tsayar da Salla. Lalle ne salla ta kasance a kan muminai, farilla mai ƙayyadaddun lokuta
Kuma kada ku sassauta a cikin neman mutanen idankun kasance kuna jin zogi, to, lalle su ma, suna jin zogi kamar yadda kuke jin zogi. Kuma kuna tsammani, daga Allah, abin da ba su tsammani. Kuma Allah Ya kasance Masani Mai hikima
Lalle ne, Mu, Mun saukar,* zuwa gare ka, Littafi da gaskiya, domin ka yi hukunci a tsakanin mutane da abin da Allah Ya nuna maka, kuma kada ka kasance mai husuma domin masu yaudara
Suna neman ɓoyewa daga mutane kuma ba su nemanɓoyewa daga Allah, alhali kuwa Shi Yana tare da su a lokacin da suke kwana da niyyar yin abin da ba Ya yarda da shi daga maganar. Kuma Allah Ya kasance ga abin da suke aikatawa Mai kewayewa
Ga ku, ya waɗannan*! Kun yi jidali, domin tunkuɗe musu (kunya) a cikin rayuwar duniya, to, wane ne zai yi jidali domin tunkuɗe musu a Ranar ¡iyama? Ko kuwa wane ne zai kasance wakili a kansu
Kuma wanda ya yi tsiwirwirin kuskure ko kuwa zunubi sa'an nan kuma ya jefi wani barrantacce da shi, to, lalle ne ya tattali ƙirƙiren ƙarya da zunubi bayyananne
Kuma ba domin falalar Allah ba, a kanka, da rahamarSa, haƙiƙa, da wata ƙungiya daga gare su ta himmatu ga su ɓatar da kai. Kuma ba su ɓatarwa face kansu, kuma ba su cutar ka daga kome, Kuma Allah Ya saukar da Littafi da hikima gare ka, kuma Ya sanar da kai abin da ba ka kasance ka sani ba. Kuma falalar Allah ta kasance mai girma a gare ka
Babu wani alheri a cikin masu yawa daga ganawarsu* face wanda ya yi umurni da wata sadaka ko kuwa wani alheri ko kuwa gyara a tsakanin mutane. Wanda ya aikata haka domin neman yardodin Allah to za Mu ba shi lada mai girma
Kuma wanda ya saɓa wa* Manzo daga bayan shiriya ta bayyana a gare shi, kuma ya bi wanin hanyar muminai, za Mu jiɓintar masa abin da ya jiɓinta, kuma Mu ƙone shi da Jahannama. Kuma ta munana ta zama makoma
Lalle ne, Allah ba Ya gafarta a yi shirki da Shi, kuma Yana gafarta abin da yake bayan wannan, ga wanda Yake so. Kuma wanda ya yi shirki da Allah, to, lalle ne ya ɓace ɓata mai nisa
Kuma lalle ne, ina ɓatar da su, kuma lalle ne ina sanya musu guri, kuma lalle ne ina umurnin su domin su katse* kunnuwan dabbobi, kuma lalle ne ina umurnin su domin su canza halittar Allah." Kuma wanda ya riƙi Shaiɗan majiɓinci, baicin Allah, to, haƙiƙa ya yi hasara, hasara bayyananniya
Kuma waɗanda suka yi imani, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, za mu shigar da su gidajen Aljanna (waɗanda) ƙoramu suna gudana a ƙarƙashinsu, suna masu dawwama a cikinsu har abada bisa ga wa'adin Allah tabbatacce. Wane ne mafi gaskiya daga Allah ga magana
(Al'amari) bai zama gurace- guracenku ba, kuma* ba gurace- guracen Mutanen Littafi ba ne. Wanda ya aikata mummunan aiki za a saka masa da shi kuma ba zai sami wani masoyi ba, baicin Allah, kuma ba zai sami mataimaki ba
Kuma wanda ya yi aiki daga ayyukan ƙwarai, namiji ne ko kuwa mace, alhali kuwa Yana mumini, to, waɗannan suna shiga Aljanna kuma ba za a zalunce su da gwargwadon hancin gurtsun dabi no ba
Kuma wane ne ya fi kyau ga addini daga wanda ya sallama fuskarsa ga Allah, alhali kuwa yana mai kyautatawa kuma ya bi aƙidar Ibrahim, Yana mai karkata zuwa ga gaskiya? Allah Ya riƙi Ibrahim badaɗayi
Suna yi maka fatawa a cikin sha'anin mata. Ka ce: "Allah Yana bayyana fatawarku a cikin sha'aninsu, da abin da ake karantawa a kanku a cikin Littafi, a cikin sha'anin marayun mata waɗanda ba ku ba su abin da aka rubuta musu* (na gado) ba, kuma kuna kwaɗayin ku aure su, da sha'anin waɗanda aka raunana daga yara, da sha'anin tsayuwarku ga marayu da adalci. Kuma abin da kuka aikata daga alheri, to, lalle ne, Allah Ya kasance Masani a gare shi
Kuma idan wata mace ta ji tsoron ƙiyo daga mijinta ko kuwa bijirewa to, babu laifi a kansu su yi sulhu a tsakaninsu, sulhu (mai kyau) Kuma yin sulhu ne mafi alheri. Kuma an halartar wa rayuka yin rowa. Kuma idan kun kyautata, kuma kuka yi taƙawa, to, lalle ne, Allah Ya kasance, ga abin da kuke aikatawa, Masani
Kuma ba za ku iya yin adalci ba a tsakanin* mata ko da kun yi kwaɗayin yi. Saboda haka kada ku karkata, dukan karkata, har ku bar ta kamar wadda aka rataye. Kuma idan kun yi sulhu, kuma kuka yi taƙawa, to, lalle ne Allah Ya kasance Mai gafara, Mai jin ƙai
Kuma Allah ne da mulkin abin da ke cikin sammai da abin da ke cikin ƙasa. Kuma lalle ne, haƙiƙa, Mun yi wasiyya ga waɗanda aka bai wa Littafi a gabaninku, da ku, cewa ku bi Allah da taƙawa, kuma idan kun kafirta, to, lalle ne, Allah Yana da abin da yake cikin sammai da abin da yake cikin ƙasa. Kuma Allah Ya kasance wadatacce, Godadde
Ya ku waɗanda suka yi imani! Ku kasance masu tsayuwa da adalci, masu shaida* saboda Allah, kuma ko da a kanku ne ko kuwa, mahaifa da mafi kusantar zumunta, ko (wanda ake yi wa shaida ko a kansa) ya kasance mawadaci ko matalauci, to, Allah ne Mafi cancanta da al'amarinsu. Saboda haka, kada ku bibiyi son zuciya, har ku karkata. Kuma idan kuka karkatar da magana, ko kuwa kuka kau da kai, to lalle ne Allah Ya kasance Masani ga abin da kuke aikatawa
Ya ku waɗanda suka yi imani! Ku yi imani* da Allah da Manzonsa, da Littafin da Ya sassaukar ga ManzonSa da Littafin nan wanda Ya saukar daga gabani. To, wanda ya kafirta da Allah da mala'ikunSa, da LittattafanSa, da ManzanninSa, da Ranar Lahira, to, lalle ne ya ɓace, ɓata mai nisa
Lalle ne waɗanda suka yi imani, sa'an nan kuma suka kafirta, sa'an nan kuma suka yi imani, sa'an nan kuma suka kafirta sa'an nan kuma suka ƙara kafirci, Allah bai kasance Yana gafarta musu ba, kuma ba zai shiryar da su ga Hanya ba
Kuma lalle ne Ya sassaukar* muku a cikin Littafi cewa idan kun ji ayoyin Allah, ana kafirta da su, kuma ana izgili da su, to, kada ku zauna tare da su, sai sun shiga cikin wani labari. Lalle ne ku, a lokacin nan misalinsu kuke. Lalle ne, Allah Mai tara munafukai da kafirai ne a cikin Jahannama gaba ɗaya
Waɗanda suke jiran dako game da ku; har idan wata nasara daga Allah ta kasance a gare ku, sai su ce: "Ashe, ba mu kasance tare da ku ba?" Kuma idan wani rabo ya samu ga kafirai sai su ce: "Ashe ba mu rinjaye ku ba, kuma muka tsare ku daga muminai?" To, Allah ne Yake yin hukunci tsakaninku a Ranar ¡iyama, kuma Allah ba zai sanya hanya ba ga kafirai a kan muminai
Lalle ne munafukai suna yaudarewa da Allah, alhali kuwa Shi ne mai yaudarasu; kuma idan sun tashi zuwa ga salla, sai su tashi suna masu kasala. Suna nunawa mutane, kuma ba su ambatar Allah sai kaɗan
Masu kai-kawo ne a tsakanin wancan; ba zuwa ga waɗannan ba, kuma ba zuwa ga waɗannan ba. Kuma wanda Allah Ya ɓatar, to, ba za ka samar masa wata Hanya ba
Sai waɗanda suka tuba, kuma suka gyara, kuma suka nemi fakuwa ga Allah, kuma suka tsarkake addininsu domin Allah, to, waɗannan suna tare da muminai, kuma Allah zai bai wa muminai lada mai girma
Lalle ne, waɗanda uke kafirta da Allah da ManzonSa kuma suna nufin su rarrabe* a tsakanin Allah da manzanninSa, kuma suna cewa: "Muna imani da sashe, kuma muna kafirta da sashe." Kuma suna nufin su riƙi hanya a tsakanin wannan
Kuma waɗanda suka yi imani da Allah da manzanninSa, kuma ba su rarrabe a tsakanin kowa ba daga gare su, waɗannan za Mu ba su ijarorinsu, kuma Allah Ya kasance Mai gafara, Mai jin ƙai
Mutanen Littafi suna tambayar ka ka saukar da wani littafi daga sama, a kansu, to, lalle ne sun tambayi Musa mufa girma daga wannan, suka ce: "Ka nuna mana Allah bayyane." Sai tsawa ta kama su saboda zaluncinsu, sa'an nan kuma suka riƙi maraƙi (abin bautawa) bayan hujjoji bayyanannu sun je musu. Sa'an nan Muka yafe laifi daga wancan. Kuma Mun bai wa Musa dalili bayyananne
Kuma Muka ɗaukaka dutse sama da su, saboda alkawarinsu, kuma Muka ce musu: "Ku shiga ƙofar kuna masu tawali'u," Kuma Muka ce musu: "Kada ku ƙetare haddi a cikin Asabat," kuma Muka riƙi alkawari mai kauri daga gare su
To, saboda warwarewarsu ga alkawarinsu, da kafirtarsu da ayoyin Allah, da kisansu ga Annabawa, ba da hakki ba, da maganarsu: "Zukatanmu suna cikin rufi." A'a, Allah ne Ya yunƙe a kansu saboda kafircinsu, saboda haka ba za su yi imani ba face kaɗan
Da faɗarsu:* "Lalle ne mu, mun kashe Masihu isa ɗan Maryama Manzon Allah," alhali kuwa ba su kashe shi ba, kuma ba su kere shi ba, kuma ammaan kamanta shi ne a gare su. Lalle ne waɗanda sauka saɓa wa juna a cikin sha'aninsa lalle ne, suna shakka daga gare, shi, ba da wani ilmi face bin zato kuma ba su kashe shi ba bisa ga yaƙini
To, saboda zalunci daga waɗanda suka tuba (Yahudu) Muka haramta musu abubuwa masu daɗi waɗanda aka halatta su a gare su, kuma saboda taushewarsu daga hanyar Allah da yawa
Amma tabbatattu* a cikin ilmi daga gare su, da muminai, suna imani da abin da aka saukar zuwa gare ka, da abin da aka saukar daga gabaninka, madalla da masu tsai da salla, da masu bayar da zakka, da masu imani daAllah da Ranar Lahira. Waɗannan za Mu ba su lada mai girma
Lalle ne Mu, Mun* yi wahayi zuwa gare ka, kamar yadda Muka yi wahayi zuwa ga Nuhu da annabawa daga bayansa. Kuma Mun yi wahayi zuwa ga Ibrahima da Isma'ila da Is'haƙa da Yaƙubu da jikoki da isa da Ayuba da Yunusa da Haruna da Sulaiman. Kuma Mun bai wa Dawuda zabura
Da wasu Manzanni, haƙi ƙa, Mun ba da labarinsu a gare ka daga gabani, da wasu manzanni waɗanda ba Mu ba da labarinsu ba a gare ka, kuma Allah Ya yi magana da Musa, magana sosai
Manzanni masu bayar da bushara kuma masu gargaɗi domin kada wata hujja ta kasance ga mutane a kan Allah bayan Manzannin. Kuma Allah ya kasance Mabuwayi, Mai hikima
Ya ku mutane! Haƙiƙa, Manzo ya je muku da gaskiya daga Ubangijinku. Saboda haka ku yi imani ya fi zama alheri a gare ku. Kuma idan kun kafirta, to, Allah Yana da abin da ke cikin sammai da ƙasa. Kuma Allah Ya kasance Masani, Mai hikima
Ya Mutanen Littafi! Kada ku zurfafa a cikin addininku. Kuma kada ku faɗa, ga Allah, face gaskiya. Abin da aka sani kawai, Masi hu isa ɗan Maryama Manzon Allah ne, kuma kalmarSa, ya jefa ta zuwa ga Maryama, kuma ruhi ne daga gare Shi. Saboda haka, ku yi imani da Allah da manzanninSa, kuma kada ku ce, "Uku". Ku hanu (daga faɗin haka) ya fi zama alheri a gare ku. Abin da aka sani kawai, Allah Ubangiji ne Guda. TsarkinSa ya tabbata daga wani abin haifuwa ya kasance a gare Shi! Shi ne da abin da ke cikin sammai da abin da ke cikin ƙasa kuma Allah Ya isa Ya zama wakili
Masihu ba ya ƙyamar ya kasance bawa ga Allah, kuma haka mala'ikun nan makusanta. Kuma wanda ya yi ƙyamar bautarSa kuma yi yi girman kai, to, zai tara su zuwa gare shi gaba ɗaya
To, amma waɗanda suka yi imani, kuma suka aikata ayyukan ƙwaiai, to za Ya cika musu ijarorinsu, kuma Yana ƙara musu daga falalarSa. Kuma amma waɗanda suka yi ƙyama, kuma suka yi girman kai, to, za Ya yi musu azaba, azaba mai raɗɗi kuma ba su samun wani masoyi domin kansu, baicin Allah, kuma ba su samun mataimaki
To, amma waɗanda suka yi imani da Allah kuma suka faku a gare Shi, to, zai shigar da su cikin wata rahama daga gare Shi da wata falala, kuma Ya shiryar da su zuwa gare Shi ga tafarki madaidaici
Suna yi maka fatawa.* Ka ce: "Allah Yana bayyana muku fatawa a cikin 'Kalala."' Idan mutum ya halaka, ba shi da, reshe kuma yana da 'yar'uwa, to, tana da rabin abin da ya bari, kuma shi yana gadon ta, idan wani reshe bai kasance ba a gare ta. Sa'an nan idan ('yan'uwa mata) suka kasance biyu, to suna da kashi biyu daga kashi uku ɗin abin da ya bari. Kuma idan sun kasance, 'yan'uwa, maza da mata to namiji yana da misalin rabon mata biyu. Allah Yana bayyanawa a gare ku, domin kada ku ɓace. Kuma Allah ne, Masani ga dukan kome