Back to Languages

Hausa - Chapter 32 - As-Sajdah

Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink

Verse 1 — Surah As-Sajdah 32:1

Verse 2 — Surah As-Sajdah 32:2

Saukar da Littafin babu shakka a gare shi, daga Ubangijin talikai yake

Verse 3 — Surah As-Sajdah 32:3

Ko suna cewa (Muhammadu ne) ya ƙirƙira shi? A'a, shi ne gaskiya daga Ubangijinka, domin ka yi gargaɗi ga mutane waɗanda wani mai gargaɗi bai je musu ba a gabaninka, fatan za su shiryu

Verse 4 — Surah As-Sajdah 32:4

Allah ne wanda Ya halitta sammai da ƙassai da abin da yake a tsakaninsu a cikin kwanuka shida, sa'an nan Ya daidaita a kan Al'arshi. Ba ku da, baicin Shi, wani majiɓinci kuma babu wani maceci. Shin, ba za ku yi tunani ba

Verse 5 — Surah As-Sajdah 32:5

Yana shirya al'amari daga sama zuwa ga ƙasa, sa'an nan ya taka zuwa gare Shi a cikin yini, wanda gwargwadonsa shekaru dubu ne ga abin da kuke lissafawa

Verse 6 — Surah As-Sajdah 32:6

Wannan shi ne Masanin fake da bayyane, Mabuwayi, Mai jinƙai

Verse 7 — Surah As-Sajdah 32:7

Wanda Ya kyautata kome, Wanda Ya halitta shi. Shi ne kuma Ya fara halittar mutum daga laka

Verse 8 — Surah As-Sajdah 32:8

Sa'an nan Ya sanya ɗiyansa daga wani asali na wani ruwa wulakantacce

Verse 9 — Surah As-Sajdah 32:9

Sa'an nan Ya daidaita shi, kuma Ya hura a cikinsa, daga ruhinSa kuma Ya sanya muku ji, da ganunuwa da zukata. Godiyarku kaɗan ce ƙwarai

Verse 10 — Surah As-Sajdah 32:10

Kuma suka ce: "Shin, idan mun ɓace a cikin ƙasa, shin, lalle mu, tabbas ne muna zama a cikin wata halitta sabuwa?" A'a, su game da gamuwa da Ubangijinsu kafirai

Verse 11 — Surah As-Sajdah 32:11

Ka ce: "Mala, ikin mutuwa ne. wanda aka wakkala a gare ku, shi ne ke karɓar rayukanku.* Sa'an nan zuwa ga Ubangijinku ake mayar da ku

Verse 12 — Surah As-Sajdah 32:12

Kuma da ka gani a lokacin da masu laifi suke masu sunkuyar da kawunansu a wurin Ubangijinsu, "Ya Ubangijinmu! Mun gani, kuma mun ji, to, Ka mayar da mu mu aikata aiki na ƙwarai. Lalle mu masu yaƙini ne

Verse 13 — Surah As-Sajdah 32:13

Kuma da Mun so da Mun bai wa kowane rai shiriyarsa to, amma magana ta tabbata daga gare Ni! Lalle ne Ina cika Jahannama daga aljannu da mutane gaba ɗaya

Verse 14 — Surah As-Sajdah 32:14

To, ku ɗanɗana saboda abin da kuka manta na haɗuwa da ranarku wannan. Lalle Mu ma Mun manta da ku, kuma ku danɗani azabar dawwama saboda abin da kuka kasance kuna aikatawa

Verse 15 — Surah As-Sajdah 32:15

Waɗanda ke imani da ayoyin Mu kawai, su ne waɗanda idan aka karanta musu ayoyinMu sai su faɗi suna masu sujada kuma su yi tasbihi game da gode wa Ubangijinsu, alhali kuwa su ba su yin girman kai

Verse 16 — Surah As-Sajdah 32:16

Sasanninsu na nisanta daga wuraren kwanciya, suna kiran Ubangijinsu bisa ga tsoro da ɗammani, kuma suna ciryawa daga abin da Muka azurta su

Verse 17 — Surah As-Sajdah 32:17

Saboda haka wani rai bai san abin da aka ɓoye musu ba, na sanyin idanu, domin sakamako ga abin da suka kasance suna aikatawa

Verse 18 — Surah As-Sajdah 32:18

Shin, wanda ya zama mumini yana kamar wanda ya zama fasiƙi? Ba za su yi daidai ba

Verse 19 — Surah As-Sajdah 32:19

Amma waɗanda suka yi imani, kuma suka aikata ayyukan ƙwafai, to, suna da gidajen Aljannar makoma, a kan liyafa saboda abin da suka kasance suna aikatawa

Verse 20 — Surah As-Sajdah 32:20

Kuma waɗanda suka yi fasiƙanci to makomarsu ita ce wuta, ko da yaushe suka yi nufin su fita daga gare ta, sai a mayar da su a cikinta, kuma a ce musu: "Ku ɗanɗana azabai wuta, wadda kuka kasance kuna ƙaryatawa game da ita

Verse 21 — Surah As-Sajdah 32:21

Kuma lalle Muna ɗanɗana musu daga azaba, mafi ƙasƙanci, kafin a kai ga azaba mafi girma, domin fatan za su komo

Verse 22 — Surah As-Sajdah 32:22

Kuma wane ne ya fi zalunci bisa ga wanda aka tunatar da ayoyin Ubangijinsa, sa'an na ya bijire daga barinsu? Lalle Mu, Masu yin azabar ramuwa ne ga masu laifi

Verse 23 — Surah As-Sajdah 32:23

Kuma lalle haƙiƙa, Mun bai wa Musa Littafi,* saboda haka kada ka kasance a cikin shakka daga haɗuwa da shi. Kuma Mun sanya shi ya zama shiriya ga Bani Isra'ila

Verse 24 — Surah As-Sajdah 32:24

Kuma Mun sanya shugabanni daga cikinsu, suna shiryarwa da umurnin Mu, a lokacin da suka yi haƙuri, kuma sun kasance suna yin yaƙini da ayoyin Mu

Verse 25 — Surah As-Sajdah 32:25

Lalle Ubangijinka shi ne zai rarrabe a tsakaninsu a Ranar ¡iyama a cikin abin da suka kasance suna saɓa wa juna a cikinsa

Verse 26 — Surah As-Sajdah 32:26

Shin, ba ya shiryar da su cewa da yawa Muka halakara gabaninsu, daga al'ummomi suna tafiya a cikin masaukansu?* Lalle a cikin wancan akwai ayoyi. Shin, ba su ji ne

Verse 27 — Surah As-Sajdah 32:27

Shin, kuma ba su gani ba cewa lalle Mu, Muna kora ruwa zuwa ga ƙasa ƙeƙasasshiya, sa'an nan Mu fitar, game da shi, wata shuka wadda dabbobinsu, da su kansu ke ci daga gare ta? Ashe fa ba su gani ba

Verse 28 — Surah As-Sajdah 32:28

Kuma suna cewa, "Yaushe wannan hukunci yake, aukuwa idan kun kasance masu gaskiya

Verse 29 — Surah As-Sajdah 32:29

Ka ce: "Ranar hukuncin nan, imanin waɗanda suka kafirta ba zai amfane su ba (a cikinta) kuma ba za a yi musu jinkiri ba

Verse 30 — Surah As-Sajdah 32:30

Saboda haka ka kau da kai daga barinsu, kuma, ka yi jira lalle, su ma masu jira ne