Back to Languages

Hausa - Chapter 33 - Al-Ahzab

Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink

Verse 1 — Surah Al-Ahzab 33:1

Ya kai Annabi! Ka bi Allah da taƙawa, kuma kada ka yi ɗa'a ga kafirai da munafukai. Lalle, Allah Ya kasance Mai ilmi, Mai hikima

Verse 2 — Surah Al-Ahzab 33:2

Kuma ka bi abin da aka yi wahayi da shi zuwa gare ka daga Ubangijinka. Lalle, Allah Ya kasance Mai labartawa ga abin da kuke aikatawa

Verse 3 — Surah Al-Ahzab 33:3

Ka dogara ga Allah. Kuma Allah Ya isa Ya zama wakili

Verse 4 — Surah Al-Ahzab 33:4

Allah bai sanya zuciya biyu ba ga wani namiji a cikinsa, kuma bai sanya matanku waɗanda kuke yin zihari daga gare su, su zama uwayenku ba, kuma bai sanya ɗiyan hankakarku su zama ɗiyanku ba. wannan abu naku, maganarku ce da bakunanku alhali kuwa Allah na faɗar gaskiya, kuma Shi ne ke shiryarwa ga hanyar ƙwarai

Verse 5 — Surah Al-Ahzab 33:5

Ku kira su ga ubanninsu, shi ne mafi adalci a wurin Allah. To, idan ba ku san ubanninsu ba, to, 'yan uwanku ga addini da dimajojinku. Kuma babu laifi a gare ku ga abin da kuka yi kuskure da shi, kuma amma (akwai laifi) ga abin da zukatanku suka ganganta, kuma Allah Ya kasance Mai gafara, Mai jin ƙai

Verse 6 — Surah Al-Ahzab 33:6

Annabi ne mafi cancanta* ga muminai bisa ga su kansu, kuma matansa uwayensu ne. Kuma ma'abuta zumunta waɗansunsu sun fi waɗansu a cikin Littafin Allah bisa ga muminai da Muhajirai, face fa idan kun aikata wani alheri zuwa ga majiɓintanku. Wancan ya kasance a cikin Littafi, rubutacce

Verse 7 — Surah Al-Ahzab 33:7

Kuma a lokacin da Muka riƙi alkawarin Annabawa daga gare su, kuma daga gare ka, kuma daga Nuhu da Ibrahim da Musa da kuma Isa ɗan Maryama, kuma Muka riƙi wani alkawari mai kauri daga gare su

Verse 8 — Surah Al-Ahzab 33:8

Domin Ya tambayi masu gaskiya a kan gaskiyarsu, kuma Ya yi tattalin wata azaba mai raɗaɗi ga kafirai

Verse 9 — Surah Al-Ahzab 33:9

Ya ku waɗanda suka yi imani! Ku tuna ni'imar Allah a kanku a lokacin da waɗansu rundunoni suka zo muku, sai Muka aika wata iska a kansu da waɗansu rundunoni waɗanda ba ku gani ba, Kuma Allah Ya kasance Mai gani ga abin da kuke aikatawa

Verse 10 — Surah Al-Ahzab 33:10

A lokacin da suka zo muku daga samanku da kuma ƙasa daga gare ku, kuma a lokacin da gannai suka karkata kuma zukata suka kai ga maƙosai, kuma kuka yi zaton zace-zace, game da Allah

Verse 11 — Surah Al-Ahzab 33:11

A can aka jarrabi muminai, kuma aka yi girgiza da su, girgiza mai tsanani

Verse 12 — Surah Al-Ahzab 33:12

Kuma a lokacin da munafukai da waɗanda akwai cuta a cikin zukatansu ke cewa, Allah da Manzon Sa, "Ba su yi mana wa'adin kome ba, face ruɗi

Verse 13 — Surah Al-Ahzab 33:13

Kuma a lokacin da wata ƙungiya daga gare su, ta ce, "Ya mutanen Yasriba!* Ba ku da wani matsayi, saboda haka ku koma." Kuma wata ƙungiya daga gare su na neman izni ga Annabi sunacewa, "Lalle gidajenmu kuranye suke," alhali kuwa ba kuranye suke ba, ba su da nufin kome face gudu

Verse 14 — Surah Al-Ahzab 33:14

Kuma da an shige ta (Madina) a kansu, daga sasanninta, sa'an nan aka tambaye su fitina (kafirci), lalle da sun je mata, kuma da ba su zauna a cikinta (Madina) ba face kaɗan

Verse 15 — Surah Al-Ahzab 33:15

Kuma lalle haƙiƙa, sun kasance suna yi wa Allah alkawari, a gabanin wannan; Ba za su juya domin gudu ba, kuma alkawarin Allah ya kasance abin tambaya

Verse 16 — Surah Al-Ahzab 33:16

Ka ce: "Gudun nan ba zai amfane ku ba daga mutuwa ko kisa. Kuma har in kun gudu, ba za a jishe ku daɗi ba face kaɗan

Verse 17 — Surah Al-Ahzab 33:17

Ka ce: "Wane ne wanda yake tsare ku daga Allah, idan Ya yi nufin wata cuta game da ku?" Kuma ba za su samar wa kansu wani majiɓinci ba, banda Allah, kuma ba za su samar wa kansu wani mataimaki ba

Verse 18 — Surah Al-Ahzab 33:18

Lalle Allah Ya san masu hana mutane fita daga cikinku, da masu cewa ga 'yan'uwansu,"Ku zo nan a wurinmu." Kuma ba za su shiga yaƙi ba face kaɗan

Verse 19 — Surah Al-Ahzab 33:19

Suna masu rowa gare ku, sa'an nan idan tsoro ya zo, sai ka gan su suna kallo zuwa gare ka, idanunsu suna kewaya, kamar wanda ake rufe hankalinsa saboda mutuwa. Sa'an nan idan tsoron ya tafi, sai su yi muku miyagun maganganu da harussa masu kaifi, suna masu rowa a kan dukiya. Waɗannan, ba su yi imani ba, saboda hakaAllah Ya ɓata ayyukansu. Kuma wannan ya kasance mai sauƙi ga Allah

Verse 20 — Surah Al-Ahzab 33:20

Suna zaton ƙungiyoyin kafirai ba su tafi ba. Kuma idan ƙungiyoyin kafirai sun zo, suna gurin da dai sun zama a karkara a cikin ƙauyawa, suna tambayar labaranku. Kuma ko da sun kasance a cikinku, ba za su yi yaƙi ba, face kaɗan

Verse 21 — Surah Al-Ahzab 33:21

Lalle, abin koyi mai kyau ya kasance gare ku daga Manzon Allah, ga wanda ya kasanee yana fatan rahamar Allah da Ranar Lahira, kuma ya ambaci Allah da yawa

Verse 22 — Surah Al-Ahzab 33:22

Kuma a lokacin da muminai suka ga ƙungiyoyin kafirai, sai suka ce, "Wannan ne abin da Allah da Manzon Sa suka yi mana wa'adi, Allah da Manzon Sa sunyi gaskiya." Kuma wannan bai ƙara musu kome ba face imani da sallamawa

Verse 23 — Surah Al-Ahzab 33:23

Daga muminai akwai waɗansu mazaje da suka gaskata abin da suka yi wa Allah alkwari a kansa, sa'an nan a cikinsu, akwai wanda ya biya bukatarsa,* kuma daga cikinsu akwai wanda ke jira. Kuma ba su musanya ba, musanyawa

Verse 24 — Surah Al-Ahzab 33:24

Domin Allah Ya saka wa masu gaskiya da gakiyarsu, kuma Ya azabtar da munafukai idan Ya so, ko Ya karɓi tuba a kansu. Lalle, Allah Ya kasance Mai gafara, Mai jin ƙai

Verse 25 — Surah Al-Ahzab 33:25

Kuma Allah Ya mayar *da waɗanda suka kafirta da fushinsu, ba su sami wani alheri ba. Allah Ya isar wa muminai daga barin yaƙi. Kuma Allah Ya kasance Mai ƙarfi, Mabuwayi

Verse 26 — Surah Al-Ahzab 33:26

Kuma Ya saukar *da waɗannan da suka taimake su daga mazowa Littafi, daga biranensu, kuma Ya jefa tsoro a cikin zukatansu; wata ƙungiya kuna kashewa, kuma kuna kama wata ƙungiyar

Verse 27 — Surah Al-Ahzab 33:27

Kuma Ya gadar da ku gonakinsu da gidajensu da dukiyoyinsu, da wata ƙasa wadda ba ku taɓa takarta ba. Kuma Allah ya kasance Mai ikon yi ne a kan kome

Verse 28 — Surah Al-Ahzab 33:28

Ya kai Annabi! Ka ce wa matanka, "Idan kun kasance kuna nufin rayuwar duniya da ƙawarta, to, ku zo in yi muku kyautar ban kwana kuma in sake ku, saki mai kyau

Verse 29 — Surah Al-Ahzab 33:29

Kuma idan kun kasance kuna nufin Allah da Manzonsa da gidan Lahria, to, lalle, Allah Ya yi tattalin wani sakamako mai girma ga masu kyautatawa daga gare ku

Verse 30 — Surah Al-Ahzab 33:30

Ya matan Annabi! Wadda ta zo da alfasha bayyananna daga cikinku za a ninka mata azaba ninki biyu. Kuma wancan ya kasance mai sauƙi ga Allah

Verse 31 — Surah Al-Ahzab 33:31

Kuma wadda ta yi tawali'u daga cikinku ga Allah da ManzonSa, kuma ta aikata aiki na ƙwarai, za Mu ba ta sakamakonta ninki biyu, kuma Mun yi mata tattalin arziki ma karamci

Verse 32 — Surah Al-Ahzab 33:32

Ya matan Annabi! Ba ku zama kamar kowa ba daga mata, idan kun yi taƙawa, saboda haka, kada ku sassautar da magana, har wanda ke da cuta a cikin zuciyarsa ya yi ɗammani, kuma ku faɗi magana ta alheri

Verse 33 — Surah Al-Ahzab 33:33

Kuma ku tabbata a cikin gidajenku,* kuma kada ku yi fitar gaye-gaye irin fitar gaye-gaye ta jahiliyyar farko. Kuma ku tsai da salla, kuma ku bayar da zakka, ku yi ɗa, a ga Allah da ManzonSa. Allah na nufin Ya tafiyar da ƙazamta kawai daga gare ku, ya mutanen Babban Gida! Kuma Ya tsarkake ku, tsarkakewa

Verse 34 — Surah Al-Ahzab 33:34

Kuma ku tuna abin da ake karantawa a cikin ɗakunanku daga ayoyin Allah da hukunci. Lalle Allah Ya kasance Mai tausasawa Mai labartawa

Verse 35 — Surah Al-Ahzab 33:35

Lalle, Musulmi maza da Musulmi mata da muminai maza da muminai mata, da masu tawali'u maza da masu tawaliu matada masu gaskiya maza da masu gaskiya mata, da masu haƙuri maza da masu haƙuri mata, da masu tsoron Allah maza da masu tsoron Allah mata, da masu sadaka maza da masu sadaka mata, da masu azumi maza da masu azumi mata da masu tsare farjojinsu maza da masu tsare farjojinsu mata, da masu ambaton Allah da yawa maza da masu ambatonsa mata, Allah Ya yi musu tattalin wata gafara da wani sakamako mai girma

Verse 36 — Surah Al-Ahzab 33:36

Kuma ba ya halatta ga mumini kuma haka ga mumina, a lokacin da Allah da Manzonsa Ya hukunta wani umurni, wani zaɓi daga al'amarinsu ya kasance a gare su. Kuma wanda ya saɓa wa Allah da ManzonSa, to, ya ɓace, ɓacewa bayyananna

Verse 37 — Surah Al-Ahzab 33:37

Kuma a lokacin* da kake cewa ga wanda Allah Ya yi ni'ima a gare shi kai kuma ka yi ni'ima a gare shi, "Ka riƙe matarka, kuma ka bi Allah da taƙawa," kuma kana ɓoyewa a cikin ranka abin da Allah zai bayyana shi,** kana tsoron mutane, alhali kuwa Allah ne Mafi cancantar ka ji tsoronSa. to a lokacin da zaidu ya ƙare bukatarsa daga gare ta, Mun aurar da kai ita, domin kada wani ƙunci ya kasance a kan muminai a cikin (auren matan) ɗiyan hankakarsu, idan sun ƙare bukata daga gare su. Kuma umurnin Allah ya kasance abin aikatawa

Verse 38 — Surah Al-Ahzab 33:38

Wani ƙunci bai kasance a kan Annabi ba ga abin da Allah Ya faralta a kansa, a kan ƙa'idar, Allah a cikin (Annabawa) waɗanda suka shige daga gabaninsa. Kuma umurnin Allah ya kasance abin ƙaddarawa tabbatacce

Verse 39 — Surah Al-Ahzab 33:39

Waɗanda ke iyar da Manzancin Allah, kuma suna tsoronSa, kuma ba su tsoron kowa face Allah, Kuma Allah Ya isa Ya zama Mai hisabi

Verse 40 — Surah Al-Ahzab 33:40

Muhammadu bai kasance uban kowa ba daga mazanku, kuma amma shi ya kasance Manzon Allah kuma cikon Annabawa. Kuma Allah Ya kasance Masani ga kome

Verse 41 — Surah Al-Ahzab 33:41

Ya ku waɗanda suka yi imani! Ku ambaci Allah, ambata mai yawa

Verse 42 — Surah Al-Ahzab 33:42

Kuma ku tsarkake shi, a safiya da maraice

Verse 43 — Surah Al-Ahzab 33:43

(Allah) Shi ne Wanda ke tsarkake ku, da mala'ikun Sa (suna yi muku addu'a), domin Ya fitar da ku daga duffai zuwa ga haske. Kuma (Allah) Ya kasance Mai Jin ƙai ga muminai

Verse 44 — Surah Al-Ahzab 33:44

Gaisuwarsu a ranar da suke haɗuwa da shi "Salam", kuma Ya yi musu tattalin wani sakamako na karimci

Verse 45 — Surah Al-Ahzab 33:45

Ya kai Annabi! Lalle Mu Mun aike ka kana mai shaida, kuma mai bayar da bushara kuma mai gargaɗi

Verse 46 — Surah Al-Ahzab 33:46

Kuma mai kira zuwa ga Allah da izninSa, kuma fitila mai haskakawa

Verse 47 — Surah Al-Ahzab 33:47

Kuma ka yi bushara ga muminai cewa, suna da falalamai girma daga Allah

Verse 48 — Surah Al-Ahzab 33:48

Kuma kada ka yi ɗa'a ga kafirai da munafukai, kuma ka ƙyae cutarsu (gare ka), kuma ka dogara ga Allah. Allah Ya isa zama wakili

Verse 49 — Surah Al-Ahzab 33:49

Ya ku waɗanda suka yi imani! idan kun auri muminai mata, sa'an nan kuka sake su a gabanin ku shafe su, to, ba ku da wata idda da za ku lissafa a kansu, kuma ku yi musu kyautar jin daɗi* kuma ku sake su saki mai kyau

Verse 50 — Surah Al-Ahzab 33:50

Ya kai Annabi! Lalle Mu, Mun halatta maka matanka waɗanda ka bai wa sadakokinsu da abin da hannun damanka ya mallaka daga abin da Allah Ya ba ka na ganima, da 'ya'yan baffanka, da 'ya'yan goggonninka da 'ya'yan kawunka da 'ya'yan innoninka waɗanda suka yi hijira tare da kai, da wata mace mumina idan ta bayar da kanta ga Annabi, idan shi Annabi yana nufin ya aure ta (halin wannan hukunci) keɓe yake gare ka, banda gamuminai. Lalle Mun san abin da Muka faralta a kansu (smuminai) game da matansuda abin da hannayensu suka mallaka. Do min kada wani ƙunci ya kasance a kanka, kuma Allah Ya kasance Mai gafara, Mai jin ƙai

Verse 51 — Surah Al-Ahzab 33:51

Kana iya jinkirtar da* wadda ka ga dama daga gare su, kuma kana taro wadda kake so zuwa gare ka. Kuma wadda ka nema daga waɗanda ka nisantar, to, babu laifi agare ka. Wannan ya fi kusantar da sanyaya idanunsu, kuma ba za su yi baƙin ciki ba, kuma su yarda da abin da ka ba su, su duka. Kuma Allah Yana sane da abin da yake a cikin zukatanku. Kuma Allah Ya kasance Masani, Mai haƙuri

Verse 52 — Surah Al-Ahzab 33:52

Waɗansu mata ba su halatta a gare ka a bayan haka, kuma ba za ka musanya su da matan aure ba, kuma ko kyaunsu ya ba ka sha'awa, face dai abin da hannun damanka ya mallaka. Kuma Allah Ya kasance Mai tsaro ga dukan kome

Verse 53 — Surah Al-Ahzab 33:53

Ya ku waɗanda suka yi imani! Kada ku shiga gidajen Annabi, face fa idan an yi izni a gare ku zuwa ga wani abinci, ba da kun tsaya jiran nunarsa ba, kuma amma idan an kira ku, to, ku shiga, sa'an nan idan kun ci, to ku watse, kuma ba da kun tsaya kuna masu hira da wani Iabari ba. Lalle wannan yana cutar da Annabi, to, yana jin kunyarku, alhali kuwa Allah ba Ya jin kunya daga gaskiya. Kuma idan za ku tambaye su waɗansu kaya, to, ku tambaye su daga bayan shamaki. Wannan ya fi muku tsarki ga zukatanku da zukatansu. Kuma ba ya halatta a gare ku, ku cuci Manzon Allah, kuma ba ya halatta ku auri matansa a bayansa har abada. lalle wannan a gare ku ya kasance babban abu a wurin Allah

Verse 54 — Surah Al-Ahzab 33:54

Idan kun bayyana wani abu, ko kuma kuka ɓoye shi, to, lalle Allah Ya kasance Masani ga kome

Verse 55 — Surah Al-Ahzab 33:55

Babu laifi a kansu game da ubanninsu, kuma babu game da ɗiyansu, kuma babu game da 'yan'uwansu maza, kuma babu game da ɗiyan 'yan'uwansu maza, kuma babu game da ɗiyan 'yan'uwansu mata, kuma babu game da matan muminai, kuma babu game da abin da hannayensu suka mallaka, kuma ku bi Allah da taƙawa. Lalle Allah Ya kasance Mahalarci a kan kome

Verse 56 — Surah Al-Ahzab 33:56

Lalle, Allah da mala'ikun Sa suna salati* ga Annabi. Ya ku waɗanda suka yi imani! Ku yi salati a gare shi, kuma ku yi sallama domin amintarwa a gare shi

Verse 57 — Surah Al-Ahzab 33:57

Lalle waɗanda ke cutar Allah da Mauzon Sa Allah Ya la'ane su, a cikin duniya da Lahira, kuma Ya yi musu tattalin azaba mai wulakantarwa

Verse 58 — Surah Al-Ahzab 33:58

Kuma waɗanda suke cutar muminai maza da muminai mata, ba da wani abu da suka aikata ba to, lalle sun ɗauki ƙiren ƙarya da zunubi bayyananne

Verse 59 — Surah Al-Ahzab 33:59

Ya kai Annabi! Ka* ce wa matan aurenka da 'ya'yanka da matan muminai su kusantar da ƙasa daga manyan tufafin da ke a kansu. Wancan ya fi sauƙi ga a gane su domin kada a cuce su. Kuma Allah Ya kasance Mai gafara, Mai Jin ƙai

Verse 60 — Surah Al-Ahzab 33:60

Lalle, idan munafukai da waɗanda yake akwai wata cuta a cikin zukatansu, da masu tsegumi a cikin Madina, ba su hanu ba (daga halayensu),* lalle, za Mu shushuta ka a gare su, sa'an nan ba za su yi maƙwabtaka da kai ba, a cikinta, face kaɗan

Verse 61 — Surah Al-Ahzab 33:61

Tsinannu ne duk inda suka shi za'a kame su kuma akarkashe su kashe

Verse 62 — Surah Al-Ahzab 33:62

A kan hanyar Allah (ta gyaran jama'a) a cikin waɗanda suka shuɗe gabaninka, kuma ba za ka sami musanyawa ba ga hanyar Allah

Verse 63 — Surah Al-Ahzab 33:63

Suna tambayar ka* ga Sa'a. Ka ce: "Saninta yana wurin Allah kawai." Kuma me ya sanar da kai cewa ana tsammanin sa'a ta kasance kusa

Verse 64 — Surah Al-Ahzab 33:64

Lalle Allah Ya la'ani kafirai, kuma Ya yi musu tattalin wata wuta mai ƙuna

Verse 65 — Surah Al-Ahzab 33:65

Suna madawwama a cikinta har abada, ba su samun majiɓinci, kuma ba su samun mataimaki

Verse 66 — Surah Al-Ahzab 33:66

Ranar da ake juya fuskokinsu a cikin wuta suna cewa, "Kaitonmu, saboda, rashin biyarmu ga Allah da rashin biyarmu ga Manzo

Verse 67 — Surah Al-Ahzab 33:67

Kuma suka ce: "Ya Ubangijinmu! Lalle mu mun* bi shugabanninmu da manyanmu! Sai suka ɓatar da mu daga hanya

Verse 68 — Surah Al-Ahzab 33:68

Ya Ubangijinmu! Ka ba su ninki biyu na azaba, kuma ka la'ane su, la'ana mai girma

Verse 69 — Surah Al-Ahzab 33:69

Ya ku waɗanda suka yi imani! Kada ku kasance kamar waɗanda suka cuci* Musa sa'an nan Allah Ya barrantar da shi daga abin da suka ce. Kuma ya kasance mai daraja a wurin Allah

Verse 70 — Surah Al-Ahzab 33:70

Ya ku waɗanda suka yi imani! Ku bi Allah da taƙawa kuma ku faɗi magana madaidaiciya

Verse 71 — Surah Al-Ahzab 33:71

Ya kyautata muku ayyukanku, kuma Ya gafarta zunubanku. Kuma wanda ya yi ɗa'a ga Allah da Manzon Sa, to, lalle, ya rabbanta, babban rabo mai girma

Verse 72 — Surah Al-Ahzab 33:72

Lalle Mu, Mun gitta amana ga sammai da ƙasa da duwatsu, sai suka ƙi ɗaukarta kuma sukaji tsoro daga gare ta, kuma mutum ya ɗauke ta, lalle shi (mutum) ya kasance mai yawan zalunci, mai yawan jahilci

Verse 73 — Surah Al-Ahzab 33:73

Domin Allah Ya azabta munafukai maza da munafukai mata, da mushirikai maza da mushirikai mata, kuma Allah Ya karɓi tuba ga muminai maza da muminai mata. Kuma Allah Ya kasance Mai gafara, Mai jin ƙai