Ya san abin da yake shiga a cikin ƙasa da abin da yake fita daga gare ta, da abin da yake sauka daga sama da abin da yake hawa a cikinta, kuma Shi ne Mai jin ƙai, Mai gafara
Kuma waɗanda suka kafirta suka ce: "Sa'a ba za ta zo mana ba." Ka ce: "Kayya! Na rantse da Ubangijina, lalle, za ta zo muku." Masanin gaibi, gwargwadon zarra ba ta nisanta daga gare Shi a cikin sammai kuma ba ta nisanta a cikin ƙasa, kuma babu mafi ƙaranci daga wancan kuma babu mafi girma face yana a cikin Littafi bayyananne
Kuma waɗanda aka bai wa ilmi suna ganin abin nan da aka saukar zuwa gare ka daga Ubangijinka, shi ne gaskiya, kuma yana shiryarwa zuwa ga hanyar Mabuwayi, Godadde
Kuma waɗanda suka kafirta suka ce: "Shin za mu nuna muku wani namiji wanda yake gaya muku wai idan an tsattsage ku, kowace irin tsattsagewa, lalle ku, tabbas, kuna a cikin wata halitta sabuwa
Ashe fa, ba su yi dubi ba zuwa ga abin da ke a gaba gare su da abin da ke a bayansu daga sama da ƙasa? idan Mun so, sai Mu shafe ƙasa da su, ko kuma Mu kayar da wani ɓaɓɓake daga sama a kansu. Lalle, a cikin wancan akwai aya ga dukan bawa mai maida al'amarinsa ga Allah
Kuma lalle, haƙiƙa, Mun bai wa Dawuda wata falala dagagare Mu. Ya duwatsu, ku konkoma sautin tasbihi tare da shi kuma da tsuntsaye. Kuma Muka tausasa masa baƙin ƙarfe
Kuma ga Sulaiman, Mun hore masa iska, tafiyarta ta safiya daidai da wata, kuma ta maraice daidai da wata. Kuma Muka gudanar masa da marmaron gaci, kuma daga aljannu (Muka hore masa) waɗanda ke aiki a gaba gare shi, da iznin Ubangijinsa. Wanda ya karkata daga cikinsu, daga umurnin Mu, sai Mu ɗanɗana masa daga azabar sa'ir
Suna aikata masa abin da yake so, na masallatai da mutummutumai da akussa kamar kududdufai, da tukwane kafaffu. Ku aikata godiya, ya ɗiyan Dawuda, kuma kaɗan ne mai godiya daga bayi Na
Sa'an nan a lokacin da Muka hukunta mutuwa a kansa babu abin da ya ja hankalinsu, a kan mutuwarsa, face dabbar ƙasa (gara) wadda take cin sandarsa. To a lokacin da ya faɗi, sai aljannu suka bayyana (ga mutane) cewa da sun kasance sun san gaibi, da ba su zauna ba a cikin azaba mai wulakantarwa
Lalle, haƙiƙa, akwai aya ga saba'awa* a cikin mazauninsu: gonakin lambu biyu, dama da hagu. "Ku ci daga arzikin Ubangijinku, kuma ku yi godiya gare shi. Gari mai daɗin zama, da Ubangiji Mai gafara
Sai suka bijire saboda haka Muka saki Malalin Arimi (dam) a kansu, kuma Muka musanya musu gonakinsu biyu da waɗansu gonaki biyu masu 'ya'yan itace kaɗan: talakiya da goriba da wani abu na magarya kaɗan
Kuma Muka sanya, a tsakaninsu da tsakanin* garuruwan da Muka Sanya albarka a cikinsu, waɗansu garuruwa masuganin juna kuma Muka ƙaddara tafiya a cikinsu, "Ku yi tafiya a cikinsu, daruruwa da ranaiku, kuna amintattu
Sai suka ce: "Ya Ubangijinmu! Ka nisantar da tsakanin tafiyoyinmu," kuma suka zalunci kansu, saboda haka Muka sanya su labaran hira kuma Muka kekkece* su kowace, irin kekkecewa. Lalle a cikin wancan akwai ayoyi ga dukan mai yawan haƙuri, mai yawan godiya
Kuma ba ya da wani dalili a kansu face dai domin Mu san wanda yake yin imani da Lahira daga wanda yake a cikin shakka daga gare ta. Kuma Ubangijinka, a kan kome, Mai tsaro ne
Ka ce: "Ku kirayi waɗanda kuka riya (cewa abubuwan bautawa ne) baicin Allah, ba su Mallakar ma'aunin zarra a cikin sammai, kuma ba su Mallakarsa a cikin ƙasa kuma ba su da wani rabon tarewa a cikinsu (sammai da ƙasa), kuma ba Shi da wani mataimaki daga gare su
Kuma wani ceto ba ya amfani a wurin Sa face fa ga wanda Ya yi izni a gare shi. Har a lokacin da aka kuranye* tsoro daga zukatansu, sai su ce, 'Mene ne Ubangijinku Ya ce?' Suka ce: 'Gaskiya', kuma shi ne Maɗaukaki, Mai girma
Kuma waɗanda suka kafirta suka ce: "Ba za mu yi imanida wannan Alƙur'ani ba, kuma ba za mu yi imani da abin da yakea gabaninsa ba (na waɗansu littattafan sama)." Kuma da ka gani a lokacin da azzalumai suke abin tsayarwa wurin Ubangijinka, sashensu na mayar wa sashe maganar maraunana (mabiya) suke cewa makangara (shugabanni) "Ba dominku ba, lalle, da mun kasance muminai
Kuma maraunana suka ce wa makangara. "A'a, (ku tuna) makircin dare da na rana a lokacin da kuke umurnin mu da mu kafirta da Allah, kuma mu sanya Masa abokan tarayya." Kuma suka assirtar da nadama a lokacin da suka ga azaba. Kuma Muka sanya ƙuƙumma a cikin wuyoyin waɗanda suka kafirta. Lalle, ba za a yi musu sakamako ba face da abin da suka kasance suna aikatawa
Kuma ba mu aika wani mai gargaɗi ba a cikin wata alƙarya face mani'imtanta (shugabanni) sunce, "Lalle mu, masu kafirta ne da abin da aka aiko ku da shi
Kuma dukiyarku ba ta zamo ba, haka ɗiyanku ba su zamo abin da yake kusantar da ku ba a wurinMu, kusantarwar muƙami face wanda, ya yi imani kuma ya aikata aikin ƙwarai. To, waɗannan suna da sakamakon ninkawa saboda abin da suka aikata. Kuma su amintattu ne a cikin benaye
Ka ce: "Lalle, Ubangijina Yana shimfida arziki ga wanda Ya so daga bayinSa, kuma Yana ƙuntatawa a gare shi, kuma abin da kuka ciyar daga wani abu, to, Shi ne zai musanya shi, kuma Shi ne Mafi ficin masu azurtawa
Saboda haka, a yau sashenku ba ya mallakar wani amfani ga wani sashen, kuma ba ya mallakar wata cuta, kuma Muna cewa ga waɗanda suka yi zalunci, Ku ɗanɗani azabar wuta wadda "kuka kasance game da ita, kuna ƙaryatawa
Kuma idan an karanta ayoyin Mu bayyanannu a kansu, sai su ce: "Wannan bai zama ba face namiji ne yana son ya kange ku daga abin da ubanninku suka kasance suna bauta wa." Kuma su ce: "Wannan bai zama ba face ƙiren ƙarya da aka ƙaga." Kuma waɗanda suka kafirta suka ce: ga gaskiya a lokacin da ta je musu: "Wannan ba kome ba face sihiri ne bayyananne
Kuma waɗanda suke a gabaninsu, sun ƙaryata, alhali kuwa ba su kai ushurin-ushurin abin da Muka ba su ba, sai suka ƙaryata Manzanni Na! To, yaya musu Na (ga maƙaryata) ya kasance
Ka ce: "Ina yi muku wa'azi ne kawai da kalma guda! watau ku tsayu domin Allah, bibbiyu da ɗaiɗai, sa'an nan ku yi tunani, babu wata hauka ga ma'abucinku. Shi bai zama ba face mai gargaɗi ne a gare ku a gaba ga wata azaba mai tsanani
Ka ce: "Idan na ɓace, to, ina ɓacewa ne kawai a kan kaina. Kuma idan na shiryu, to, saboda abin da Ubangijina Yake yowar wahayi ne zuwa a gare ni. Lalle Shi Mai ji ne, Makusanci
Kuma an shamakance a tsakaninsu da tsakanin abin da suke marmari, kamar yadda aka aikata da irin ƙungiyoyinsu a gabaninsu. Lalle su sun kasance a cikin shakka mai sanya kokanto