Back to Languages

Hausa - Chapter 35 - Fatir

Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink

Verse 1 — Surah Fatir 35:1

Godiya ta tabbata ga Allah, Mai fara halittar sammai da ƙasa, Mai sanya mala'iku manzanni masu fukafukai, bibbiyu, da uku-uku da hurhuɗu. Yana ƙarawar abin da Ya ke so a cikin halittar. Lalle Allah Mai ikon yi ne a kan kome

Verse 2 — Surah Fatir 35:2

Abin da Allah Ya buɗa wa mutane daga rahama, to, babu mai riƙewa a gare shi, kuma abin da Ya riƙe, to, babu mai saki a gare shi, wanin Sa, kuma Shi ne Mabuwayi, Mai hikima

Verse 3 — Surah Fatir 35:3

Ya ku mutane! Ku tuna ni'imar Allah a kanku. Shin, akwai wani mai halitta wanin Allah da zai azurta ku daga sama da, ƙasa? Babu wani abin bautawa, face Shi. To, yaya ake karkatar da ku

Verse 4 — Surah Fatir 35:4

Kuma idan sun ƙaryata ka, to, lalle, an ƙaryata waɗansu Manzanni a gabaninka, kuma zuwa ga Allah ake mayar da al'amura

Verse 5 — Surah Fatir 35:5

Ya ku mutane! Lalle wa'adin Allah gaskiya ne, saboda haka kada rayuwar duniya ta ruɗar da ku, kuma kada maruɗi ya ruɗe ku game da Allah

Verse 6 — Surah Fatir 35:6

Lalle Shaiɗan maƙiyi ne a gare ku, sai ku riƙe shi maƙiyi. Yana kiran ƙungiyarsa kawai ne, domin su kasance 'yan sa'ir

Verse 7 — Surah Fatir 35:7

Waɗanda suka kafirta suna da azaba mai tsanani kuma waɗanda suka yi imani, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, suna da wata gafara da sakamako mai girma

Verse 8 — Surah Fatir 35:8

Shin to, wanda aka ƙawata masa aikinsa, har ya gan shi mai kyau (yana daidai da waninsa)? Saboda haka, lalle, Allah Yana ɓatar da wanda Yake so, kuma Yana shiryar da wanda Yake so, saboda haka kada ranka ya halaka a kansu domin baƙin ciki. Lalle Allah Masani ne ga abin da suke sana'antawa

Verse 9 — Surah Fatir 35:9

Kuma Allah ne Ya aika da iskoki har su motsar da girgije, sa'an nan Mu kora shi zuwa ga gari matacce, sa'an nan Mu rayar da ƙasa game da shi a bayan mutuwarta. Kamar wancan ne Tashin ¡iyama yake

Verse 10 — Surah Fatir 35:10

Wanda ya kasance yana neman wata izza, to, Allah ne da izza gaba ɗaya. zuwa gare Shi magana mai daɗi ke hawa, kuma aiki na ƙwarai Yana ɗaukar ta Kuma waɗanda ke yin makircin munanan ayyuka, suna da wata azaba mai tsanani, kuma makircin waɗannan yana yin tasgaro

Verse 11 — Surah Fatir 35:11

Kuma Allah ne Ya halitta ku daga turɓaya, sa'an nan daga ɗigon maniyyi, sa'an nan Ya sanya ku surkin maza da mata. Kuma wata mace ba ta yin ciki, kuma ba ta haihuwa, face da saninSa, kuma ba za a rayar da wanda ake rayarwa ba, kuma ba za a rage tsawon ransa ba face yana a cikin Littafi. Lalle, wancan mai sauki ne ga Allah

Verse 12 — Surah Fatir 35:12

Kuma koguna biyu ba su daidaita: Wannan mai ruwan daɗi, mai zaƙi, mai sauƙin haɗiya kuma wannan mai ruwan gishiri mai zartsi, kuma daga kowane, kuna cin wani nama sabo, kuma kuna fitar da kawa wadda kuke tufantarta, kuma kana ganin jirage a cikinsa suna masu gudana, domin ku nemo daga falalar Sa, kuma tsammaninku za ku dinga godewa

Verse 13 — Surah Fatir 35:13

Yana shigar da dare a cikin rana, kuma Yana shigar da rana a cikin dare. Kuma Ya hore rana da wata kowannensu yana gudana zuwa ga ajali ambatacce Wannan Shi ne Allah, Ubangijinku, gare Shi mulki yake, kuma waɗanda kuke kira waninSa ba su mallakar ko fatar gurtsun dabino

Verse 14 — Surah Fatir 35:14

Idan kun kira su, ba za su ji kiranku ba, kuma ko sun jiya, ba za su karɓa muku ba, kuma a Ranar ¡iyama za su kafirce wa shirkinku, kuma babu mai ba ka labari, kamar wanda ya sani

Verse 15 — Surah Fatir 35:15

Ya ku mutane! Ku ne masu bukata zuwa ga Allah, kuma Allah, Shi ne Mawadaci, Godadde

Verse 16 — Surah Fatir 35:16

Idan Ya so, zai tafi da ku, kuma Ya zo da wata halitta sabuwa

Verse 17 — Surah Fatir 35:17

Kuma wancan bai zama mabuwayi ba ga Allah

Verse 18 — Surah Fatir 35:18

Kuma wani rai mai ɗaukar nauyi, bai ɗaukar nauyin wani rai. Kuma idan ran da aka nauyaya wa kaya ya yi kira (ga wani mataimaki) zuwa ga kayansa, ba za a dauki kome ba daga gare shi, kuma ko da (wanda ake kiran) ya kasance makusancin zumunta ne. Kana gargaɗi kawai ne ga waɗanda ke tsoron Ubangijinsu a fake, kuma suka tsayar da salla. Kuma wanda ya tsarkake, to, yana tsarkaka ne domin kansa. Kuma zuwa ga Allah kawai makoma take

Verse 19 — Surah Fatir 35:19

Kuma makaho ba ya daidaita da mai gani

Verse 20 — Surah Fatir 35:20

Kuma duffai ba su daidaita, kuma haske ba ya daidaita

Verse 21 — Surah Fatir 35:21

Kuma inuwa ba ta daidaita, kuma iskar zafi ba ta daidaita

Verse 22 — Surah Fatir 35:22

Kuma rayayyu ba su daidaita kuma matattu ba su daidaita. Lalle Allah Yana jiyar da wa'azi ga wanda Ya so, kuma ba ka jiyar da waɗanda suke a cikin kaburbura

Verse 23 — Surah Fatir 35:23

Ba ka zama ba face mai gargaɗi kawai

Verse 24 — Surah Fatir 35:24

Lalle Mu Mun aike ka da gaskiya, kana mai bayar da bushara kuma mai gargaɗi. Kuma babu wata al'umma face wani mai gargaɗi ya shuɗe a cikinta

Verse 25 — Surah Fatir 35:25

Kuma idan suna ƙaryata ka, to, haƙiƙa, waɗanda suke a gabaninsu sun ƙaryata. Manzanninsu sun je musu da hujjoji, kuma da takardu, kuma da Littafi mai haske

Verse 26 — Surah Fatir 35:26

Sa'an nan Na kama waɗanda suka kafirta. To, yaya musu Na yake

Verse 27 — Surah Fatir 35:27

Ba ka gani ba, lalle Allah Ya saukar da ruwa daga sama? Sai Muka fitar, game da shi,'ya'yan itace masu saɓanin launuka kuma daga duwatsu akwai zane-zane, farfaru da jajaye, masu saɓanin launin, da masu launin baƙin ƙarfe, baƙaƙe

Verse 28 — Surah Fatir 35:28

Kuma daga mutane da dabbobi da bisashen gida, masu saɓanin launinsu kamar wancan. Malamai kawai ke tsoron Allah daga cikin bayin Sa. Lalle, Allah, Mabuwayi ne, Mai gafara

Verse 29 — Surah Fatir 35:29

Lalle waɗanda ke karatun Littafin Allah* kuma suka tsayar da salla, kuma suka ciyar daga abin da Muka azurta su da shi, a asirce da bayyane, suna fatan (samun) wani fatauci ne wanda ba ya yin tasgaro

Verse 30 — Surah Fatir 35:30

Domin (Allah) zai cika musu sakamakonsu, kuma Ya ƙara musu daga falalarSa. Lalle Shi Mai gafara ne, Mai godiya

Verse 31 — Surah Fatir 35:31

Kuma abin da Muka yi wahayi zuwa gare ka, daga Littafi

Verse 32 — Surah Fatir 35:32

Sa'an nan Mun gadar da Littafin, ga waɗanda Muka zaɓa daga bayinMu, sa'an nan daga cikinsu, akwai mai zalunci ga kansa, kuma daga cikinsu akwai mai tsakaitawa, kuma daga cikinsu akwai mai tserewa da ayyukan alheri da iznin Allah. Waccan ita ce falalar (Allah) mai girma

Verse 33 — Surah Fatir 35:33

Gidajen Aljannar zama suna shigar su. Ana ƙawace su a cikinsu, da ƙawa ta mundaye daga zinariya da lu'ulu'u, kuma tufafinsu, a cikinsu alharini ne

Verse 34 — Surah Fatir 35:34

Kuma suka ce: "Godiya ta tabbata ga Allah Wanda Ya tafiyar da baƙin ciki daga gare mu. Lalle Ubangijinmu, haƙiƙa Mai gafarane, Mai godiya

Verse 35 — Surah Fatir 35:35

Wanda Ya saukar da mu a gidan zama, daga falalarSa, wata wahala ba ta shafar mu a cikinsa, kuma wata kasawa ba ta shafar mu a cikinsa

Verse 36 — Surah Fatir 35:36

Kuma waɗanda suka kafirta suna da wutar Jahannama, ba a yin hukunci a kansu balle su mutu kuma ba a sauƙaƙa musu daga azabarta. Kamar haka Muke saka wa kowane mai yawan kafirci

Verse 37 — Surah Fatir 35:37

Kuma su, suna hargowar neman agaji a cikinta. (Suna cewa) "Ya Ubangijinmu! Ka fitar da mu, mu aikata aiki mai kyau, wanin wanda muka kasance muna aikatawa." Ashe, kuma, ba Mu rayar da ku ba, abin da mai tunani zai iya yin tunani a ciki, kuma mai gargaɗi ya je muku? To, ku ɗanɗana, saboda haka babu wani mataimaki, ga azzalumai

Verse 38 — Surah Fatir 35:38

Lalle Allah ne Masanin gaibin sammai da ƙasa. Lalle Shi ne Masani ga abin da yake ainihin zukata

Verse 39 — Surah Fatir 35:39

Shi ne Wanda Ya sanya ku masu maye wa juna, a cikin ƙasa. To, wanda ya kafirta, to, kafircinsa yana a kansa. Kuma kafircin kafirai ba ya kara musu kome face baƙin jini, kuma kafircin kafirai ba ya kara musu kome face hasara

Verse 40 — Surah Fatir 35:40

Ka ce: "Shin, kun ga abubuwan shirkinku, waɗanda kuke kira, wasun Allah? Ku nuna mini, mene ne suka halitta daga ƙasa? Ko suna da tarayya ne a cikin sammai? Ko kuma Mun ba su wani littafi ne saboda haka suna a kan wata hujja ce daga gare shi? A'a, azzalumai ba su yin wani wa'adi, sashensu zuwa ga sashe, face ruɗi

Verse 41 — Surah Fatir 35:41

Lalle Allah Yana riƙe sammai da ƙasa domin kada su gushe. Kuma haƙiƙa, idan sun gushe, babu wani baicin Sa da zai riƙe su. Lalle Shi Ya kasance Mai haƙuri, Mai gafara

Verse 42 — Surah Fatir 35:42

Kuma suka* yi rantsuwa da Allah, mafi nauyin rantsuwarsu, "Lalle, idan wani mai gargaɗi ya zo musu tabbas za su kasance mafi shiryuwa, daga ɗayan al'ummomi." To, a lokacin da mai gargaɗi ya je musu, bai ƙara su da kome ba face gudu

Verse 43 — Surah Fatir 35:43

Domin nuna girman kai a cikin ƙasa da makircin cuta. Kuma makirci na cuta ba ya fadawa face a kan mutanensa. To shin suna jiran (wani abu ne) face dai hanyar (kafiran) farko. To, ba za ka sami musanya ba ga hanyar Allah. Kuma ba za ka sami juyarwa ba ga hanyar Allah

Verse 44 — Surah Fatir 35:44

Ashe, kuma ba su yi tafiya ba, a cikin ƙasa, domin su duba yadda aƙibar waɗannan da suke a gabaninsu ta kasance? Alhali kuwa sun kasance mafifita ƙarfi daga gare su? Kuma Allah bai kasance wani abu na iya rinjayar Sa ba, a cikin sammai, kuma haka a cikin kaƙa. Lalle Shi ne Ya kasance Masani, Mai ikon yi

Verse 45 — Surah Fatir 35:45

Kuma da Allah Yana kama mutane saboda abin da suka aikata, da bai bar wata dabba ba a kanta (kasa). Amma Yana jinkirta musu zuwa ga ajalin da aka ambata. Sa'an nan idan ajalinsu ya zo, to, lalle Allah ya kasance Mai gani ga bayin Sa