Back to LanguagesPrevious ChapterNext Chapter
Hausa - Chapter 36 - Ya-Sin
Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink
Verse 1 — Surah Ya-Sin 36:1
Verse 2 — Surah Ya-Sin 36:2
Ina rantsuwa da Al-ƙur'ani* Mai hikima
Verse 3 — Surah Ya-Sin 36:3
Lalle kai, haƙiƙa kana cikin Manzanni
Verse 4 — Surah Ya-Sin 36:4
A kan hanya madaidaiciya
Verse 5 — Surah Ya-Sin 36:5
(Allah Ya saukar da Al-kur'ani) saukarwar Mabuwayi, Mai jin ƙai
Verse 6 — Surah Ya-Sin 36:6
Domin ka yi gargaɗi ga waɗansu mutane da ba a yi gargaɗi ga ubanninsu ba, saboda haka sumasu rafkana ne
Verse 7 — Surah Ya-Sin 36:7
Lalle, haƙiƙa, kalma* ta wajaba a kan mafi yawansu, domin su, ba za su yi imani ba
Verse 8 — Surah Ya-Sin 36:8
Lalle Mu, Mun sanya ƙuƙumma a cikin wuyoyinsu, sa'an nan su (ƙuƙumman sun kai) har zuwa ga haɓoɓinsu, saboda haka, su banƙararru ne
Verse 9 — Surah Ya-Sin 36:9
Kuma Muka sanya wata toshiya a gaba gare su, da wata toshiya a bayansu, saboda haka Muka rufe su, sai suka zama ba su gani
Verse 10 — Surah Ya-Sin 36:10
Kuma daidai yake a gare su, shin, ka yi musu gargaɗi ko ba ka yi musu gargaɗi ba, su ba za su yi imani ba
Verse 11 — Surah Ya-Sin 36:11
Kana yin gargaɗi kawai ga wanda ya bi Alƙur'ani ne, kuma ya ji tsoron mai rahama a fake. To, ka yi masa bushara da gafara da wani sakamako na karimci
Verse 12 — Surah Ya-Sin 36:12
Lalle Mu, Mu ne ke rayar da matattu kuma Mu rubuta abin da suka gabatar, da gurabunsu, kuma kowane abu Mun ƙididdige shi, a cikin babban Littafi Mabayyani
Verse 13 — Surah Ya-Sin 36:13
Kuma ka buga musu misali: Waɗansu ma'abuta alƙarya, a lokacin da Manzanni* suka je mata
Verse 14 — Surah Ya-Sin 36:14
A lokacin da Muka aika (Manzannin) biyu zuwa gare su, sai suka ƙaryata su, sa'an nan Muka ƙarfafa (su) da na uku, sai suka ce: "Lalle mu, Manzanni ne zuwa gare ku
Verse 15 — Surah Ya-Sin 36:15
Suka ce: "Ku ba ku zamo baface mutane ne kamarmu kuma Mai rahama bai saukar da kome ba, ba ku zamo ba face ƙarya kuke yi
Verse 16 — Surah Ya-Sin 36:16
Suka ce: "Ubangijinmu Ya sani, lalle mu, haƙiƙa Manzanni nezuwa gare ku
Verse 17 — Surah Ya-Sin 36:17
Kuma babu abin da ke kanmu, face iyar da manzanci bayyananne
Verse 18 — Surah Ya-Sin 36:18
Suka ce: "Lalle mu muna shu'umci da ku! Haƙiƙa idan ba ku, hanu ba, haƙiƙa, za mu jefe ku, kuma haƙiƙa wata azaba mai raɗaɗi daga gare mu za ta shafe ku
Verse 19 — Surah Ya-Sin 36:19
Suka ce: "Shu'umcinku, yana tare da ku. Ashe, domin an tunatar da ku? A'a, ku dai mutane ne masu ƙetare haddi
Verse 20 — Surah Ya-Sin 36:20
Kuma wani mutum daga mafi nisan birnin ya je, yana tafiya da gaggawa, ya ce: "Ya mutanena! Ku bi Manzannin nan
Verse 21 — Surah Ya-Sin 36:21
Ku bi waɗanda ba su tambayar ku wata ijara kuma su shiryayyu ne
Verse 22 — Surah Ya-Sin 36:22
Kuma mene ne a gare ni, ba zan bauta wa Wanda Ya ƙaga halittata ba, kuma zuwa gare Shi ake mayar da ku
Verse 23 — Surah Ya-Sin 36:23
Shin, zan riƙi waninSa abubuwan bautawa? Idan Mai rahama Ya nufe ni da wata cuta, to cetonsu ba ya amfanina da kome, kuma ba za su iya tsamar da ni ba
Verse 24 — Surah Ya-Sin 36:24
Lalle ni, a lokacin nan, tabbas, ina a cikin ɓata bayyananna
Verse 25 — Surah Ya-Sin 36:25
Lalle ni, na yi imani da Ubangijinku, saboda haka ku saurare ni
Verse 26 — Surah Ya-Sin 36:26
Aka ce *(masa), "Ka shiga Aljanna." Ya ce, "Da dai a ce mutanena suna iya sani
Verse 27 — Surah Ya-Sin 36:27
Game da gafarar da Ubangijjina ya yi mini, kuma Ya sanya ni a cikin waɗanda aka girmama
Verse 28 — Surah Ya-Sin 36:28
Kuma ba Mu saukar da waɗansu runduna ba daga sama* a kan (halaka) mutanensa, daga bayansa, kuma ba za Mu kasance. Masu saukarwa ba
Verse 29 — Surah Ya-Sin 36:29
Ba ta kasance ba face tsawa guda, sa'an nan sai ga su somammu
Verse 30 — Surah Ya-Sin 36:30
Ya nadama a kan bayi Na! Wani Manzo ba ya zuwa gare su face sun kasance suna masu yi masa izgili
Verse 31 — Surah Ya-Sin 36:31
Ba su gani ba, da yawa Muka halakar da (mutanen) ƙarnoni a gabaninsu kuma cewa su ba za su komo ba
Verse 32 — Surah Ya-Sin 36:32
Kuma lalle babu kowa face waɗanda ake halartarwa ne a wurin Mu
Verse 33 — Surah Ya-Sin 36:33
Kuma aya ce a gare su: ¡asa matacciya, Mu rayar da ita, Mu fitar da ƙwaya daga gare ta, sai ga shi daga gare ta suke ci
Verse 34 — Surah Ya-Sin 36:34
Kuma Muka sanya, a cikinta (ƙasa), waɗansu gonaki na dabino da inabobi, kuma Muka ɓuɓɓugar da ruwa daga maremari a cikinta
Verse 35 — Surah Ya-Sin 36:35
Domin su ci 'ya'yan itacensa, alhali kuwa hannayensu ba su aikata shi ba. Shin, to, ba za su gode ba
Verse 36 — Surah Ya-Sin 36:36
Tsarki ya tabbata ga Wanda Ya halitta nau'uka, namiji da mace, dukansu, daga abin da ƙasa ke tsirarwa, kuma daga kansu, kuma daga abin da ba su sani ba
Verse 37 — Surah Ya-Sin 36:37
Kuma aya ce a gare su: Dare Muna feɗe rana daga gare shi, sai ga su suna masu shiga duhu
Verse 38 — Surah Ya-Sin 36:38
Kuma rana tana gudana zuwa ga wani matabbaci nata. Wannan ƙaddarawar Mabuwayi ne, Masani
Verse 39 — Surah Ya-Sin 36:39
Kuma da wata Mun ƙaddara masa manziloli, har ya koma kamar tsumagiyar murlin dabino wadda ta tsufa
Verse 40 — Surah Ya-Sin 36:40
Rana ba ya kamata a gare ta, ta riski wata. Kuma dare ba ya kamata a gare shi ya zama mai tsere wa yini, kuma dukansua cikin sarari guda suke yin iyo
Verse 41 — Surah Ya-Sin 36:41
Kuma aya ce a gare su. Lalle Mu, Mun ɗauki zuriyarsu a cikin jirgin, wanda aka yi wa lodi
Verse 42 — Surah Ya-Sin 36:42
Kuma Muka halitta musu, daga irinsa, abin da suke hawa
Verse 43 — Surah Ya-Sin 36:43
Kuma idan Mun so, za Mu nutsar da su, har babu kururuwar neman agaji, a gare su, kuma ba su zama ana tsirar da su ba
Verse 44 — Surah Ya-Sin 36:44
Sai fa bisa ga wata rahama daga gare Mu, da jiyarwa daɗi zuwa ga wani ɗan lokaci
Verse 45 — Surah Ya-Sin 36:45
Kuma idan aka ce musu, "Ku kare abin da ke a gaba gare ku da abin da yake a bayanku, domin tsammaninku a ji tausayinku
Verse 46 — Surah Ya-Sin 36:46
Kuma wata aya daga ayoyin Ubangijinsu ba ta zuwa a gare su, sai sun kasance suna masu bijirewa daga gare ta
Verse 47 — Surah Ya-Sin 36:47
Kuma idan aka ce musu, "Ku ciyar daga abin da Allah Ya azurta ku," sai waɗanda suka kafirta su ce ga waɗanda suka yi imani, "Ashe, za mu ciyar da wanda idan Allah Ya so Yana ciyar da shi? Ba ku zama ba face a cikin ɓata bayyananniya
Verse 48 — Surah Ya-Sin 36:48
Kuma suna cewa, "A yaushe wannan wa'adi yake (aukuwa) idan kun kasance masu gaskiya
Verse 49 — Surah Ya-Sin 36:49
Ba su jiran (kome) face wata tsawa guda, za ta kama su, alhali kuwa suna yin husuma
Verse 50 — Surah Ya-Sin 36:50
Ba za su iya yin wasiyya* ba, kuma ba za su iya komawa zuwa ga iyalansu ba
Verse 51 — Surah Ya-Sin 36:51
Kuma aka yi busa a cikin ƙaho, to, sai ga su, daga kaburbura zuwa ga Ubangijinsu, suna ta gudu
Verse 52 — Surah Ya-Sin 36:52
Suka ce: "Ya bonenmu! Wane ne ya tayar da mu daga barcinmu?" "Wannan shi ne abin da Mai rahama ya yi wa'adi da shi, kuma Manzanni sun yi gaskiya
Verse 53 — Surah Ya-Sin 36:53
Ba ta kasance ba face wata tsawa ce guda, sai ga su duka, suna abin halartarwa a gare Mu
Verse 54 — Surah Ya-Sin 36:54
To, a yau, ba za a zalunci wani rai da kome ba. Kuma ba za a saka muku ba face da abin da kuka kasance kuna aikatawa
Verse 55 — Surah Ya-Sin 36:55
Lalle, 'yan Aljanna, a yau, suna cikin shagali, suna masu nishaɗi
Verse 56 — Surah Ya-Sin 36:56
Su da matan aurensu suna cikin inuwowi, a kan karagai, suna masu gincira
Verse 57 — Surah Ya-Sin 36:57
Suna da, 'ya'yan itacen marmari a cikinta kuma suna samun abin da suke kiran a kawo
Verse 58 — Surah Ya-Sin 36:58
Aminci," da magana,* daga Ubangiji Mai jin ƙai
Verse 59 — Surah Ya-Sin 36:59
Ku rarrabe dabam, a yau, ya ku masu laifi
Verse 60 — Surah Ya-Sin 36:60
Ashe, ban yi muku umurni na alkawari ba, ya ɗiyan Adamu? Cewa kada ku bauta wa Shaiɗan, lalle shi, maƙiyi ne a gareku bayyananne
Verse 61 — Surah Ya-Sin 36:61
Kuma ku bauta Mini. Wannan ita ce hanya madaidaciya
Verse 62 — Surah Ya-Sin 36:62
Kuma lalle haƙiƙa, (Shaiɗan) ya ɓatar da jama'a masu yawa daga gare ku. Ashe to ba ku kasance kuna yin hankali ba
Verse 63 — Surah Ya-Sin 36:63
Wannan ita ce Jahannama wadda kuka kasance ana yi muku wa'adi da ita
Verse 64 — Surah Ya-Sin 36:64
Ku shige ta a yau, saboda abin da kuka kasance kuna yi na kafirci
Verse 65 — Surah Ya-Sin 36:65
A yau, Muna sanya hatimin rufi a kan bakunansu, kuma hannayensu su yi Mana magana, kuma ƙafafunsu su yi shaidu da abin da suka kasance suna aikatawa
Verse 66 — Surah Ya-Sin 36:66
Da Mun so, da Mun shafe gani *daga idanunsu, sai su yi tsere ga hanya, to, yaya za su yi gani
Verse 67 — Surah Ya-Sin 36:67
Kuma da Mun so, da Mun juyar da halittarsu a kan halinsu, saboda haka ba za su iya shuɗewa ba, kuma ba za su komo ba
Verse 68 — Surah Ya-Sin 36:68
Kuma wanda Muka raya shi, Mana sunkuyar da shi ga halittarsa. Ashe, ba su hankalta
Verse 69 — Surah Ya-Sin 36:69
Ba Mu sanar da shi (Annabi) waka ba, kuma waka ba ta kamata da shi (Annabi) ba. Shi (Al-ƙur'ani) bai zama ba face tunatarwa ce, da abin karatu bayyananne
Verse 70 — Surah Ya-Sin 36:70
Domin ya yi gargaɗi ga wanda ya kasance mai rai, kuma magana ta wajaba a kan kafirai
Verse 71 — Surah Ya-Sin 36:71
Shin, ba su gani ba (cewa) lalle Mun halitta musu dabbobi daga abin da HannayenMu suka aikata, sai suna mallakar su
Verse 72 — Surah Ya-Sin 36:72
Kuma Muka hore su, saboda su, saboda haka daga gare su abin hawansu yake, kuma daga gare su suke ci
Verse 73 — Surah Ya-Sin 36:73
Kuma suna da waɗansu amfanoni a cikinsu, da abubuwan sha. Ashe fa, ba za; su gode ba
Verse 74 — Surah Ya-Sin 36:74
Kuma suka riƙi waɗansu abubuwan bautawa wanin Allah, ɗammaninsu za su taimake su
Verse 75 — Surah Ya-Sin 36:75
Ba za su iya taimakonsu ba, alhali kuwa su runduna ce wadda ake halartarwa (a cikin wuta)
Verse 76 — Surah Ya-Sin 36:76
Saboda haka, kada maganarsu ta ɓata maka rai. Lalle Mu, Muna sanin abin da suke asirtawa da abin da suke bayyanawa
Verse 77 — Surah Ya-Sin 36:77
Ashe, kuma mutum bai ga (cewa) lalle Mu, Mun halitta shi daga maniyyi ba, sai ga shi mai yawan husuma, mai bayyanawar husumar
Verse 78 — Surah Ya-Sin 36:78
Kuma ya buga Mana wani misali, kuma ya manta da halittarsa, ya ce: "Wane ne ke rayar da ƙasusuwa alhali kuwa suna rududdugaggu
Verse 79 — Surah Ya-Sin 36:79
Ka ce: "Wanda ya ƙaga halittarsu a farkon lokaci Shi ke rayar da su, kuma Shi, game da kowace halitta, Mai ilmi ne
Verse 80 — Surah Ya-Sin 36:80
Wanda ya sanya muku wuta daga itace kore, sai ga ku kuna kunnawa daga gare shi
Verse 81 — Surah Ya-Sin 36:81
Shin, kuma Wanda Ya halitta sammai da ƙasa bai zama Mai ikon yi ba ga Ya halitta kwatankwacinsu? Na'am, zai iya! Kuma Shi Mai yawan halittawa ne, Mai ilmi
Verse 82 — Surah Ya-Sin 36:82
UmurninSa idan Ya yi nufin wani abu sai Ya ce masa kawai, "Ka kasance," sai yana kasancewa (kamar yadda Yake nufi)
Verse 83 — Surah Ya-Sin 36:83
Saboda haka, tsarki ya tabbata ga Wanda mallakar kowane abu take ga HannayenSa, kuma zuwa gare Shi ake mayar da ku