Back to LanguagesPrevious ChapterNext Chapter
Hausa - Chapter 37 - As-Saffat
Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink
Verse 1 — Surah As-Saffat 37:1
Ina rantsuwa da masu yin sahu-sahu (a cikin salla ko yaƙi)
Verse 2 — Surah As-Saffat 37:2
Sa'an nan masu yin tsawa* domin gargaɗi
Verse 3 — Surah As-Saffat 37:3
Sa'an nan da masu karatun abin tunatarwa
Verse 4 — Surah As-Saffat 37:4
Lalle Abin bautawarku haƙiƙa ¦aya ne
Verse 5 — Surah As-Saffat 37:5
Ubangijin sammai da ƙasa da abin da ke tsakaninsu, kuma Ubangijin wuraren fitar rana
Verse 6 — Surah As-Saffat 37:6
Lalle Mu, Mun ƙawatar da sama ta kusa da wata ƙawa, watau taurari
Verse 7 — Surah As-Saffat 37:7
Kuma suna tsari daga dukan Shaiɗan mai tsaurin kai
Verse 8 — Surah As-Saffat 37:8
Ba za su iya saurare zuwa ga jama'a mafi ɗaukaka (Mala'iku) ba, kuma ana jifar su daga kowane gefe
Verse 9 — Surah As-Saffat 37:9
Domin tunkuɗewa kuma suna da wata azaba tabbatacciya
Verse 10 — Surah As-Saffat 37:10
Face wanda ya fizgi wata kalma, sai yula mai haske ta bi shi
Verse 11 — Surah As-Saffat 37:11
Ka tambaye su: "Shin su ne mafi wuya ga halittawa, ko, kuwa waɗanda Muka halitta?" Lalle Mu, Mun halitta su daga laka mai ɗauri
Verse 12 — Surah As-Saffat 37:12
A'a, ka yi mamaki, alhali kuwa suna ta yin izgili
Verse 13 — Surah As-Saffat 37:13
Kuma idan aka tunatar da su, ba su tunawa
Verse 14 — Surah As-Saffat 37:14
Idan suka ga wata aya, sai su dinga yin izgili
Verse 15 — Surah As-Saffat 37:15
Kuma su ce, "Wannnan ba kome ba, face sihiri, ne bayyananne
Verse 16 — Surah As-Saffat 37:16
Shin, idan mun mutu, kuma muka kasance turɓaya da kasusuwa, ashe, lalle mu tabbas waɗandaake tayarwa ne
Verse 17 — Surah As-Saffat 37:17
Ashe ko da ubanninmu na farko
Verse 18 — Surah As-Saffat 37:18
Ka ce: "Na'am alhali kuwa kuna ƙasƙantattu
Verse 19 — Surah As-Saffat 37:19
Tsawa guda kawai ce, sai ga su, suna dubi
Verse 20 — Surah As-Saffat 37:20
Kuma su ce: "Ya bonenmu! Wannan ita ce ranar sakamako
Verse 21 — Surah As-Saffat 37:21
Wannan ita ce ranar rarrabewa wadda kuka kasance kuna ƙaryatawa
Verse 22 — Surah As-Saffat 37:22
Ku tara waɗanda suka yi zalunci, da abokan haɗinsu, da abin da suka kasance suna bautawa
Verse 23 — Surah As-Saffat 37:23
Wanin Allah, saboda haka ku shiryar da su zuwa ga hanyar Jahim
Verse 24 — Surah As-Saffat 37:24
Kuma ku tsayar da su, lalle su, waɗanda ake yi wa tambaya ne
Verse 25 — Surah As-Saffat 37:25
Me ya same ku, ba ku taimakon juna
Verse 26 — Surah As-Saffat 37:26
A'a, su a yau, masu sallamawa ne
Verse 27 — Surah As-Saffat 37:27
Kuma sashensu ya fuskanta ga sashe, suna tambayar juna
Verse 28 — Surah As-Saffat 37:28
Suka ce: "Lalle ku, kun kasance kuna je mana daga wajen dama (inda muka amince)
Verse 29 — Surah As-Saffat 37:29
Suka ce: "A'a, ba ku kasance muminai ba
Verse 30 — Surah As-Saffat 37:30
Kuma wani dalili bai kasance ba gare mu a kanku. A'a, kun kasance mutane ne masu ketare iyaka
Verse 31 — Surah As-Saffat 37:31
Saboda haka maganar Ubangijinmu ta wajaba a kanmu. Lalle mu, masu ɗanɗanawa ne
Verse 32 — Surah As-Saffat 37:32
Saboda haka muka ɓatar da ku. Lalle mu, mun kasance ɓatattu
Verse 33 — Surah As-Saffat 37:33
To lalle su a ranar nan, masu tarayya ne a cikin azabar
Verse 34 — Surah As-Saffat 37:34
Lalle Mu, kamar haka Muke aikatawa game, da masu laifi
Verse 35 — Surah As-Saffat 37:35
Lalle su, sun kasance idan an ce musu: "Babu abin bautawa, face Allah," sai su dora girman kai
Verse 36 — Surah As-Saffat 37:36
Kuma suna cewa, "Shin, mu lalle masu barin gumakanmu ne, saboda maganar wani mawaƙi mahaukaci
Verse 37 — Surah As-Saffat 37:37
A'a, ya zo da gaskiya kuma ya gaskata Manzanni
Verse 38 — Surah As-Saffat 37:38
Lalle ku, haƙiƙa masu ɗanɗana azaba mai raɗaɗi ne
Verse 39 — Surah As-Saffat 37:39
Kuma ba za a saka muku ba face da abin da kuka kasance kuna aikatawa
Verse 40 — Surah As-Saffat 37:40
Face bayin Allah waɗanda aka tsarkake
Verse 41 — Surah As-Saffat 37:41
Waɗannan suna da abinci sananne
Verse 42 — Surah As-Saffat 37:42
Ya'yan itacen marmari, kuma suna waɗanda ake girmamawa
Verse 43 — Surah As-Saffat 37:43
A cikin gidajen Aljannar ni'ima
Verse 44 — Surah As-Saffat 37:44
A kan karagu, suna masu fuskantar juna
Verse 45 — Surah As-Saffat 37:45
Ana kewayawa a kansu da hinjalan giya, ta daga waɗansu maremari
Verse 46 — Surah As-Saffat 37:46
Fara mai daɗi ga mashayan
Verse 47 — Surah As-Saffat 37:47
A cikinta babu jiri kuma ba su zama masu maye daga gare ta ba
Verse 48 — Surah As-Saffat 37:48
Kuma a wurinsu, akwai matan aure masu taƙaita kallonsu, masu manyan idanu
Verse 49 — Surah As-Saffat 37:49
Kamar dai su ƙwai ne ɓoyayye
Verse 50 — Surah As-Saffat 37:50
Sai sashensu ya fuskanta a kan sashe, suna tambayar juna
Verse 51 — Surah As-Saffat 37:51
Wani mai magana daga cikinsu ya ce: "Lalle ni wani aboki ya kasance a gare ni (a duniya)
Verse 52 — Surah As-Saffat 37:52
Yana cewa, "Shin, kai lalle, kana daga masu gaskatawa ne
Verse 53 — Surah As-Saffat 37:53
Ashe, idan muka mutu, kuma muka, kasance turɓaya da kasusuwa, ashe, lalle, mu tabbas waɗanda ake saka wa ne
Verse 54 — Surah As-Saffat 37:54
(Mai maganar) ya ce: "Shin, ko ku, masu tsinkaya ne (mu gan shi)
Verse 55 — Surah As-Saffat 37:55
Sai ya tsinkaya, sai ya gan shi a cikin tsakar Jahim
Verse 56 — Surah As-Saffat 37:56
Ya ce (masa), "Wallahi, lalle, ka yi kusa, haƙiƙa, ka halakani
Verse 57 — Surah As-Saffat 37:57
Kuma ba domin ni'imar Ubangijina ba, lalle, da na kasance daga waɗanda ake halartarwa (tare da kai a cikin wuta)
Verse 58 — Surah As-Saffat 37:58
Shin fa, ba mu zama masu mutuwa ba
Verse 59 — Surah As-Saffat 37:59
Sai mutuwarmu ta farko, kuma ba mu zama waɗanda ake azabtarwa ba
Verse 60 — Surah As-Saffat 37:60
Lalle, wannan shi ne babban rabo mai girma
Verse 61 — Surah As-Saffat 37:61
Saboda irin wannan, sai masu aiki su yi ta aikatawa
Verse 62 — Surah As-Saffat 37:62
Shin wancan shi ne mafi zama alheri ga liyafa ko itaciyar zaƙƙum
Verse 63 — Surah As-Saffat 37:63
Lalle, Mu, Mun sanya ta fitina ga. azzalumai
Verse 64 — Surah As-Saffat 37:64
Lalle ita wata itaciya ce wadda take fita daga asalin Jahim
Verse 65 — Surah As-Saffat 37:65
Gundarta, kamar dai shi kanun Shaiɗan ne
Verse 66 — Surah As-Saffat 37:66
To, lalle su haƙiƙa masu ci ne daga gare ta. Sa'an nan masu cika cikuna ne daga gare ta
Verse 67 — Surah As-Saffat 37:67
Sa'an nan lalle suna da wani garwaye a kanta, daga ruwan zafi
Verse 68 — Surah As-Saffat 37:68
Sa'an nan lalle makomarsu, haƙiƙa, zuwa ga Jahim take
Verse 69 — Surah As-Saffat 37:69
Lalle su, sun iske ubanninsu batattu
Verse 70 — Surah As-Saffat 37:70
Saboda haka su, a kan gurabunsu, suke gaggawa
Verse 71 — Surah As-Saffat 37:71
Kuma tabbas haƙiƙa mafi yawan mutanen farko sun ɓace a gabaninsu
Verse 72 — Surah As-Saffat 37:72
Kuma tabbas haƙiƙa, Mun aika masu gargaɗi a cikinsu
Verse 73 — Surah As-Saffat 37:73
Sai ka duba yadda aƙibar waɗanda aka yi wa gargaɗi ta kasance
Verse 74 — Surah As-Saffat 37:74
Face bayin Allah waɗanda aka tsarkake
Verse 75 — Surah As-Saffat 37:75
Kuma lalle, haƙiƙa' Nuhu ya kira Mu. To, madalla da masu karɓawa, Mu
Verse 76 — Surah As-Saffat 37:76
Kuma Mun tsirar da shi da mutanensa daga bakin ciki babba
Verse 77 — Surah As-Saffat 37:77
Muka sanya zurriyarsa suna masu wanzuwa
Verse 78 — Surah As-Saffat 37:78
Kuma Muka bar masa (yabo) a cikin jama'ar ƙarshe
Verse 79 — Surah As-Saffat 37:79
Aminci ya tabbata ga Nuhu, a cikin halittu
Verse 80 — Surah As-Saffat 37:80
Lalle Mu kamar haka Muke saka wa masu kyautatawa
Verse 81 — Surah As-Saffat 37:81
Lalle shi, yana daga bayin Mu muminai
Verse 82 — Surah As-Saffat 37:82
Sa'an nan Muka nutsar da waɗansunsu
Verse 83 — Surah As-Saffat 37:83
Kuma lalle daga ƙungiyarsa, haƙiƙa, Ibrahim yake
Verse 84 — Surah As-Saffat 37:84
A lokacin da ya je wa ubangijinsa da zuciya kuɓutacciya
Verse 85 — Surah As-Saffat 37:85
A lokacin da ya ce wa ubansa da mutanensa, "Mene ne kuke bautawa
Verse 86 — Surah As-Saffat 37:86
Shin, ƙiren ƙarya (watau) gumaka, wanin Allah, kuke bautawa
Verse 87 — Surah As-Saffat 37:87
To, mene ne zatonku game da Ubangijin halittu
Verse 88 — Surah As-Saffat 37:88
Sai ya yi dubi, duba ta sosai, a cikin taurari
Verse 89 — Surah As-Saffat 37:89
Sa'an nan ya ce: "Ni mai rashin lafiya ne
Verse 90 — Surah As-Saffat 37:90
Sai suka juya ga barinsa, suna masu juyawa da baya
Verse 91 — Surah As-Saffat 37:91
Sai ya karkata zuwa ga gumakansu, sa'an nan ya ce: "Ashe ba za ku ci ba
Verse 92 — Surah As-Saffat 37:92
Me ya same ku, ba ku magana
Verse 93 — Surah As-Saffat 37:93
Sai ya zuba duka a kansu da hannun dama
Verse 94 — Surah As-Saffat 37:94
Sai suka fuskanto zuwa gare shi, suna gaggawa
Verse 95 — Surah As-Saffat 37:95
Ya ce, "Kuna bauta wa abin da kuke sassaƙawa
Verse 96 — Surah As-Saffat 37:96
Alhali, Allah ne Ya halitta ku game da abin da kuke aikatawa
Verse 97 — Surah As-Saffat 37:97
Suka ce: "Ku gina wani gini saboda shi, sa'an nan ku jefa shi a cikin Jahim
Verse 98 — Surah As-Saffat 37:98
Saboda haka suka yi nufin makida game da shi. Sai Muka sanya su, su ne mafi ƙasƙanci
Verse 99 — Surah As-Saffat 37:99
Kuma (Ibrahim] ya ce: "Lalle, ni mai tafiya ne zuwa ga Ubangijina, zai shiryar da ni
Verse 100 — Surah As-Saffat 37:100
Ya Ubangijina! Ka ba ni (abokin zama) daga salihan mutane
Verse 101 — Surah As-Saffat 37:101
Sai Muka yi masa bushara da wani yaro *mai haƙuri
Verse 102 — Surah As-Saffat 37:102
To, a lokacin da ya isa aiki tare da shi, ya ce: "Ya ƙaramin ɗana! Lalle ne ina gani, a ciki barci, lalle ina yanka ka. To, ka duba me ka gani?" (Yaron) ya ce: "Ya, Babana! Ka aikata abin da aka umurce ka, za ka same ni, in Allah Ya so, daga masu haƙuri
Verse 103 — Surah As-Saffat 37:103
Yayin da suka mika wuya sai muka fansheshi da Rago
Verse 104 — Surah As-Saffat 37:104
Kuma Muka kira shi cewa "Ya Ibrahim
Verse 105 — Surah As-Saffat 37:105
Haƙiƙa ka gaskata mafarkin." Lalle kamar haka Muke saka wa masu kyautatawa
Verse 106 — Surah As-Saffat 37:106
Lalle wannan ita ce jarrabawa bayyananna
Verse 107 — Surah As-Saffat 37:107
Kuma Muka yi fansar yaron da wani abin yanka, mai girma
Verse 108 — Surah As-Saffat 37:108
Kuma Muka bar (yabo) a kansa a cikin mutanen ƙarshe
Verse 109 — Surah As-Saffat 37:109
Aminci ya tabbata ga Ibrahim
Verse 110 — Surah As-Saffat 37:110
Kamar haka Muke saka wa masu kyautatawa
Verse 111 — Surah As-Saffat 37:111
Lalle shi, yana daga bayinMu muminai
Verse 112 — Surah As-Saffat 37:112
Kuma Muka yi masa bushara* Da Is'haƙa ya zama Annabi daga salihan mutane
Verse 113 — Surah As-Saffat 37:113
Kuma Muka yi albarka a gare shi, kuma ga Is'haka. Kuma daga cikin zurriyarsu akwai mai kyautatawa da kuma maizalunci domin kansa, mai bayyanawa (ga zaluncin)
Verse 114 — Surah As-Saffat 37:114
Kuma lalle, Mun yi ni'ima ga Musa da Haruna
Verse 115 — Surah As-Saffat 37:115
Kuma Muka tsirar da su da mutanensu daga bakin ciki mai girma
Verse 116 — Surah As-Saffat 37:116
Kuma Muka taimake su, saboda haka suka kasance masu rinjaya
Verse 117 — Surah As-Saffat 37:117
Kuma Muka ba su Littafi mai iyakar bayani
Verse 118 — Surah As-Saffat 37:118
Kuma Muka shiryar da su ga hanya miƙaƙƙiya
Verse 119 — Surah As-Saffat 37:119
Kuma Muka bar (yabo) a gare su a cikin mutanen karshe
Verse 120 — Surah As-Saffat 37:120
Aminci ya tabbata ga Musa da Haruna
Verse 121 — Surah As-Saffat 37:121
Lalle kamar haka Muke saka wa masu kyautatawa
Verse 122 — Surah As-Saffat 37:122
Lalle, suna daga bayin Mu muminai
Verse 123 — Surah As-Saffat 37:123
Kuma lalle Ilyas, haƙiƙa, yana daga Manzanni
Verse 124 — Surah As-Saffat 37:124
A lokacin da yake ce wa mutanensa, "Ashe, ba za ku yi taƙawa ba
Verse 125 — Surah As-Saffat 37:125
Shin, kuna bauta wa Ba'al ne, kuma kuna barin Mafi kyautatawar masu halitta
Verse 126 — Surah As-Saffat 37:126
Allah Ubangijinku, kuma Ubangijin ubanninku farko
Verse 127 — Surah As-Saffat 37:127
Sai suka ƙaryata shi. Saboda haka su lalle waɗanda za a halartawa ne (a wuta)
Verse 128 — Surah As-Saffat 37:128
Sai bayin Allah waɗanda aka tsarkake
Verse 129 — Surah As-Saffat 37:129
Kuma Muka bar (yabo) a gare shi, a cikin mutanen ƙarshe
Verse 130 — Surah As-Saffat 37:130
Aminci ya tabbata ga Ilyas
Verse 131 — Surah As-Saffat 37:131
Lalle Mu kamar haka Muke saka wa masu kyautatawa
Verse 132 — Surah As-Saffat 37:132
Lalle shi, yana daga bayin Mu muminai
Verse 133 — Surah As-Saffat 37:133
Kuma lalle Ludu, haƙiƙa, yana daga Manzanni
Verse 134 — Surah As-Saffat 37:134
A lokacin da Muka tsirar da shi, da mutanensa gaba ɗaya
Verse 135 — Surah As-Saffat 37:135
Sai wata tsohuwa tana a cikin masu wanzuwa (a cikin azaba)
Verse 136 — Surah As-Saffat 37:136
Sa'an nan Muka darkake waɗansu mutanen
Verse 137 — Surah As-Saffat 37:137
Kuma lalle ku, haƙiƙa, kuna shuɗewa a kansu, kuna masu asubanci
Verse 138 — Surah As-Saffat 37:138
Kuma da dare. Shin fa, ba za ku hankalta ba
Verse 139 — Surah As-Saffat 37:139
Kuma lalle Yunusa, haƙiƙa, yana daga Manzanni
Verse 140 — Surah As-Saffat 37:140
A lokacin da ya gudu zuwa ga jirgin ruwa wanda aka yi wa lodi
Verse 141 — Surah As-Saffat 37:141
Sa'an nan ya yi ƙuri'a, sai ya kasance a cikin waɗanda aka rinjaya
Verse 142 — Surah As-Saffat 37:142
Sai kifi ya yi loma da shi, alhali kuwa yana wanda ake zargi
Verse 143 — Surah As-Saffat 37:143
To, ba domin lalle shi ya kasance daga masu tasbihi ba
Verse 144 — Surah As-Saffat 37:144
Lalle da ya zauna a cikin cikinsa har ya zuwa ranar da za a tayar da su
Verse 145 — Surah As-Saffat 37:145
Sai Muka jefa shi ga wani fili alhali kuwa yana mai raunin rashin lafiya
Verse 146 — Surah As-Saffat 37:146
Kuma Muka tsirar da wata itaciya ta kankana a kusa da shi
Verse 147 — Surah As-Saffat 37:147
Kuma Muka aika shi zuwa ga waɗansu mutane dubuɗari, ko suna ƙaruwa (a kan haka)
Verse 148 — Surah As-Saffat 37:148
Sai suka yi imani saboda haka Muka jiyar da su dadi har wani lokaci
Verse 149 — Surah As-Saffat 37:149
Saboda haka, ka tambaye su, "Shin, Ubangijinka ne da 'ya'ya mata, kuma su da ɗiya maza
Verse 150 — Surah As-Saffat 37:150
Ko kuma Mun halitta mala'iku mata ne, alhali kuwa su sunahalarce
Verse 151 — Surah As-Saffat 37:151
To! Lalle su, daga ƙiren ƙaryarsu suna cewa
Verse 152 — Surah As-Saffat 37:152
Allah Ya haihu," alhali kuwa lalle su, haƙiƙa maƙaryata ne
Verse 153 — Surah As-Saffat 37:153
Shin, Ya zaɓi 'ya'ya mata ne a kan ɗiya maza
Verse 154 — Surah As-Saffat 37:154
Me ya same ku? Yaya kuke hukuntawa (wannan hukunci)
Verse 155 — Surah As-Saffat 37:155
Shin, ba ku tunani
Verse 156 — Surah As-Saffat 37:156
Ko kuma kuna da wani dalili bayyananne ne
Verse 157 — Surah As-Saffat 37:157
To, ku zo da littafinku idan kun kasance masu gaskiya
Verse 158 — Surah As-Saffat 37:158
Kuma suka sanya nasaba a tsakanin Sa da tsakanin aljannu. Alhali kuwa Lalle aljannu sun sani, "Lalle su, haƙiƙa waɗanda ake halartarwa ne (a cikin wuta)
Verse 159 — Surah As-Saffat 37:159
Tsarki ya tabbata ga Allah daga abin da suke siffantawa
Verse 160 — Surah As-Saffat 37:160
Sai bayin Allah waɗanda aka tsarkake
Verse 161 — Surah As-Saffat 37:161
To, lalle, ku da abin da kuke bautawa
Verse 162 — Surah As-Saffat 37:162
Ba ku zama masu buwaya ba a gare Shi
Verse 163 — Surah As-Saffat 37:163
Sai wanda yake mai shiga babbar wuta Jahim
Verse 164 — Surah As-Saffat 37:164
Kuma babu kowa daga cikinmu,* face yana da matsayi sananne
Verse 165 — Surah As-Saffat 37:165
Kuma lalle mu, haƙiƙa, mu ne masu yin sahu-sahu (domin ibada)
Verse 166 — Surah As-Saffat 37:166
Kuma lalle mu haƙiƙa, mu ne masu yin tasbihi
Verse 167 — Surah As-Saffat 37:167
Kuma lalle su, sun kasance suna cewa
Verse 168 — Surah As-Saffat 37:168
Da lalle muna da wani littafi irin na mutanen farko
Verse 169 — Surah As-Saffat 37:169
Lalle da mun kasance bayin Allah waɗanda aka tsarkake
Verse 170 — Surah As-Saffat 37:170
Sai suka kafirta da shi. Saboda haka za su sani
Verse 171 — Surah As-Saffat 37:171
Kuma lalle, haƙiƙa kalmar Mu ta gabata ga bayinMu, Manzanni
Verse 172 — Surah As-Saffat 37:172
Lalle su, haƙiƙa, su ne waɗanda ake taimako
Verse 173 — Surah As-Saffat 37:173
Kuma lalle rundunarMu, haƙiƙa, su ne marinjaya
Verse 174 — Surah As-Saffat 37:174
Saboda haka juya daga barinsu, har a wani lokaci
Verse 175 — Surah As-Saffat 37:175
Ka nuna musu (gaskiya), da haka za su dinga gani
Verse 176 — Surah As-Saffat 37:176
Shin fa, da azabarMu suke neman gaggawa
Verse 177 — Surah As-Saffat 37:177
To, idan ta sauka ga farfajiyarsu, to, safiyar wadanda ake yi wa gargaɗi ta munana
Verse 178 — Surah As-Saffat 37:178
Kuma ka juya daga barinsu har a wani lokaci
Verse 179 — Surah As-Saffat 37:179
Ka nuna (musu gaskiya), da haka za su dinga nunawa
Verse 180 — Surah As-Saffat 37:180
Tsarki ya tabbata ga Ubangijinka, Ubangijin rinjaye, daga barin abin da suke siffantawa
Verse 181 — Surah As-Saffat 37:181
Kuma aminci ya tabbata ga Manzanni
Verse 182 — Surah As-Saffat 37:182
Kuma godiya ta tabbata ga Allah Ubangijin halittu