Back to Languages

Hausa - Chapter 38 - Sad

Translation by Abubakar Mahmood Jummi — Permalink

Verse 1 — Surah Sad 38:1

S, Ina rantsuwa da Al-ƙur'ani mai hukunce-hukunce

Verse 2 — Surah Sad 38:2

A'a, waɗanda suka kafirta suna cikin girman kai (ga rikon al'adunsu) da saɓani (tsakanin junansu)

Verse 3 — Surah Sad 38:3

Da yawa Muka halakar da wani ƙarni, a gabaninsu, suka yi kira (neman ceto), babu lokacin kuɓucewa

Verse 4 — Surah Sad 38:4

Kuma suka yi mamaki domin Mai gargaɗi, daga cikinsu, ya je musu. Kuma kafirai sukace, "Wannan mai sihiri ne, maƙaryaci

Verse 5 — Surah Sad 38:5

Shin, ya sanya gumaka duka su zama abin bautawa guda? Lalle wannan, haƙiƙa, abu ne mai ban mamaki

Verse 6 — Surah Sad 38:6

Shugabanni daga cikinsu, suka tafi (suka ce),"Ku yi tafiyarku, ku yi haƙuri a kan abubuwan bautawarku. Lalle wannan, haƙiƙa, wani abu ne ake nufi

Verse 7 — Surah Sad 38:7

Ba mu taɓa ji ba, game da wannan a cikin addinin ƙarshe. Wannan bai zama ba face ƙiren ƙarya

Verse 8 — Surah Sad 38:8

Shin, an saukar da Alƙur'ani ne a kansa, a tsakaninmu (mu kuma ba mu gani ba)?" A'a, su dai suna cikin shakka daga hukunciNa A'a, ba su i da ɗanɗanar azaba ba

Verse 9 — Surah Sad 38:9

Ko kuma a wurinsu ne ake ajiye taskokin rahamar Ubangijinka, Mabuwayi, Mai yawan kyauta

Verse 10 — Surah Sad 38:10

Ko kuma su ne da mallakar sammai da ƙasa da abin da ke a tsakaninsu? To sai su hau a cikin sammai (domin, su hana saukar Alƙur'ani ga Muhammadu)

Verse 11 — Surah Sad 38:11

Rundunoni ne abin da ke can, rusassu, na ƙungiyoyinsu

Verse 12 — Surah Sad 38:12

Mutanen Nuhu sun ƙaryata, a gabaninsu, da Adawa da Fir'auna mai turakun (da suka kafe mulkinsa)

Verse 13 — Surah Sad 38:13

Da Samudawa da mutanen Luɗu da ma'abuta ƙunci, *waɗancan ne ƙungiyoyin

Verse 14 — Surah Sad 38:14

Babu kowa a cikinsu face ya ƙaryata Manzanni, saboda haka azabaTa ta wajaba

Verse 15 — Surah Sad 38:15

Kuma waɗannan *ba su jiran kome face tsawa guda, wadda ba ta da hani

Verse 16 — Surah Sad 38:16

Kuma suka ce: "Ya Ubangijinmu! Ka gaggauta mana da rabonmu, a gabanin ranar bincike

Verse 17 — Surah Sad 38:17

Ka yi haƙuri bisa ga abin da suke faɗa (na izgili), kuma ka ambaci bawan Mu Dawuda ma'abucin ƙarfin ibada. Lalle, shi, mai mayar da al'amari ga Allah ne

Verse 18 — Surah Sad 38:18

Lalle Mu, Mun hore duwatsu tare da shi, suna yin tasbihi maraice da fitowar rana

Verse 19 — Surah Sad 38:19

Da tsuntsaye waɗanda ake tattarawa, kowannensu mai komawa ne a gare shi

Verse 20 — Surah Sad 38:20

Kuma Muka ƙarfafa mulkinsa, kuma Muka ba shi hikima* da rarrabewar magana

Verse 21 — Surah Sad 38:21

Kuma shin, labarin masu husuma ya zo maka, a lokacin da suka haura garun masallaci

Verse 22 — Surah Sad 38:22

A lokacin da suka shiga ga Dawuda, sai ya firgita daga gare su. Suka ce: "Kada kaji tsoro, masu husuma biyu ne; sashenmu ya zalunci sashe. Saboda haka, ka yi hakunci a tsakaninmu da gaskiya. Kada ka ƙetare haddi kuma ka shiryar da mu zuwa, ga tsakar hanya

Verse 23 — Surah Sad 38:23

Lalle wannan dan'uwana ne, yana da tunkiya casa'in da tara, kuma ina da tunkiya guda, sai ya ce: 'Ka lamunce mini ita. Kuma ya buwaye ni ga magana

Verse 24 — Surah Sad 38:24

(Dawuda) ya ce: "Lalle, haƙiƙa ya zalunce* ka game da tambayar tunkiyarka zuwa ga tumakinsa. Kuma lalle ne masu yawa daga abokan tarayya, haƙiƙa, sashensu na zambatar sashe face waɗanda suka yi imani, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai." Kuma Dawuda ya tabbata cewa Mun fitine shi ne, saboda haka, ya nemi Ubangijinsa gafara, kuma ya faɗi yana mai sujada, kuma ya mayar da al'amari ga Allah

Verse 25 — Surah Sad 38:25

Saboda haka Muka gafarta masa wancan, kuma lalle yana da wata kusantar daraja a wurin Mu, da kyaun makoma

Verse 26 — Surah Sad 38:26

Ya Dawuda! Lalle Mu Mun sanya ka Halifa a cikin ƙasa. To, ka yi hukunci tsakanin mutane da gaskiya, kuma kada ka biye wa son zuciyar, har ya ɓatar dakai daga hanyar Allah. Lalle waɗanda ke ɓacewa daga hanyar Allah suna da wata azaba mai tsanani domin abin da suka manta, a ranar hisabi

Verse 27 — Surah Sad 38:27

Kuma ba Mu halitta sama da ƙasa da abin da ke a tsakaninsu ba a kan ƙarya. Wannan shi ne zaton waɗanda suka kafirta. To, bone ya tabbata ga waɗanda suka kafirta daga wuta

Verse 28 — Surah Sad 38:28

Ko za Mu sanya waɗanda suka yi imani, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai kamar waɗanda suke masu barna ne a cikin ƙasa? Ko kuma za Mu sanya masu bin Allah da taƙawa kamar fajirai makarkata

Verse 29 — Surah Sad 38:29

(Wannan) Littafi ne, Mun saukar da shi zuwa gare ka, yana, mai albarka, domin su lura da ayoyinsa, kuma don masu hankali su riƙa yin tunani

Verse 30 — Surah Sad 38:30

Kuma Muka bai wa Dawuda Sulaiman. Madalla da bawanMu, shi. Lalle shi (Sulaiman) mai mayar da al'amari ne ga Allah

Verse 31 — Surah Sad 38:31

A lokacin da aka gitta masa dawaki masu asali, *a lokacin maraice

Verse 32 — Surah Sad 38:32

Sai ya ce: "Lalle ni, na fifita son dukiya daga tunawar Ubangijina, har (rana) ta faku da shamaki

Verse 33 — Surah Sad 38:33

Ku mayar da su a gare ni." Sai ya shiga yankansu* da takobi ga ƙwabrukansu da wuyoyinsu

Verse 34 — Surah Sad 38:34

Kuma lalle haƙiƙa, Mun fitini* Sulaiman kuma Muka jefa wani jikin mutum a kan karagarsa. Sa'an nan ya mayar da al'amari zuwa gare Mu

Verse 35 — Surah Sad 38:35

Ya ce: "Ya Ubangijina! Ka gafarta mini, kuma Ka ba ni mulki wanda ba ya kamata da kowa daga bayana.* Lalle Kai, Kai ne Mai yawan kyauta

Verse 36 — Surah Sad 38:36

Saboda haka Muka hore masa iska* tana gudu da umurninsa, tana tashi da sauƙi, inda ya nufa

Verse 37 — Surah Sad 38:37

Da shaiɗanu dukan mai gini, da mai nutsa (a cikin koguna)

Verse 38 — Surah Sad 38:38

Waɗansu, ɗaɗɗaure a cikin maruruwa

Verse 39 — Surah Sad 38:39

Wannan kyautar Mu ce. Sai ka yi kyauta ga wanda kake so, ko kuma ka riƙe, babu wani bincike

Verse 40 — Surah Sad 38:40

Kuma lalle, haƙiƙa yana da kusantar daraja a wurin Mu da kyaun makoma

Verse 41 — Surah Sad 38:41

Kuma ka ambaci bawan Mu Ayyuba* a lokacin da ya kirayi Ubangijinsa, ya ce: "Lalle ni, Shaiɗan ya shafe ni da wahala da kuma wata azaba

Verse 42 — Surah Sad 38:42

Ka shura da ƙafarka. Wannan abin wanka ne mai sanyi da abin sha

Verse 43 — Surah Sad 38:43

Kuma Muka ba shi iyalansa da kwatankwacinsu tare da su saboda rahama daga gare Mu, da tunatarwa ga masu hankali

Verse 44 — Surah Sad 38:44

Kuma ka riƙi wata ƙulla da hannunka, ka yi duka da ita kuma kada ka karya rantsuwarka. Lalle Mu, Mun same shi mai haƙuri. Madalla da bawa, shi Lalle shi mai mayar da al'amari ga Allah ne

Verse 45 — Surah Sad 38:45

Kuma ka ambaci bayin Mu: Ibrahim da ls'haƙa da Ya'aƙuba, ma'abuta ƙarfin (ɗaukar umurnin Mu) da basira

Verse 46 — Surah Sad 38:46

Lalle Mu, Mun keɓance su game da wata, tsattsarkar aba: Hukunce-hukuncen gidan duniya (mai tunatar da su Lahira)

Verse 47 — Surah Sad 38:47

Kuma lalle su a wurin Mu, tabbas, suna daga zaɓaɓɓu, mafifita

Verse 48 — Surah Sad 38:48

Kuma ka ambaci Isma'ila da llyas da Zulkifli, kuma dukansu suna daga zaɓaɓɓu

Verse 49 — Surah Sad 38:49

Wannan tunatarwa ce, kuma lalle masu bin Allah da taƙawa, suna da kyakkyawar makoma

Verse 50 — Surah Sad 38:50

Gidajen Aljannar zama, alhali kuwa tana abar buɗe wa kofofi saboda su

Verse 51 — Surah Sad 38:51

Suna gingincire a cikinsu, suna kira a cikinsu, ga 'ya'yan itacen marmari masu yawa, da abin sha

Verse 52 — Surah Sad 38:52

Kuma a wurinsu akwai matan aure masu gajarta ganinsu ga mazansu, tsarar juna

Verse 53 — Surah Sad 38:53

Wannan shi ne abin da ake yi muku wa'adi ga ranar hisabi

Verse 54 — Surah Sad 38:54

Lalle wannan, haƙiƙa, azurtarwar Mu ce, ba ta ƙarewa

Verse 55 — Surah Sad 38:55

Wannan shi ne kuma lalle makangara, haƙiƙa, suna da mafi sharrin makoma

Verse 56 — Surah Sad 38:56

Jahannama, suna shigarta. To, shimfiɗar ta munana, ita

Verse 57 — Surah Sad 38:57

Wannan shi ne! To, su ɗanɗane shi: ruwan zafi ne da ruɓaɓɓen jini

Verse 58 — Surah Sad 38:58

Da wani daga siffarsa nau'i-nau'i

Verse 59 — Surah Sad 38:59

Wannan wani yanki ne mai kutsawa tare da ku, babu maraba a gare su, lalle su, masu shiga Wuta ne

Verse 60 — Surah Sad 38:60

Suka ce: "A'a, ku ne babu maraba a gare ku, ku ne kuka gabatar da shi a gare mu." To, matabbatar ta munana (ita wutar)

Verse 61 — Surah Sad 38:61

Suka ce: "Ya Ubangijinmu! Wanda ya gabatar da wannan a gare mu, to, Ka ƙara masa azaba, ninki, a cikin wuta

Verse 62 — Surah Sad 38:62

Kuma suka ce: "Me ya same mu, ba mu ganin waɗansu mazaje, mun kasance muna ƙidaya su daga ashararai

Verse 63 — Surah Sad 38:63

Shin, mun riƙe su abin izgili ne ko idanunmu sun karkata daga gare su ne

Verse 64 — Surah Sad 38:64

Lalle wannan, haƙiƙa, gaskiya ne, husumar mutanen wuta

Verse 65 — Surah Sad 38:65

Ka ce: "Ni mai gargaɗikawai ne, kuma babu wani abin bautawa sai Allah, Makaɗaici, Mai tilastawa

Verse 66 — Surah Sad 38:66

Ubangijin sammai da ƙasa da abin da ke a tsakaninsu Mabuwayi, Mai gafara

Verse 67 — Surah Sad 38:67

Ka ce: "Shi (Alkur'ani) babban labari ne mai girma

Verse 68 — Surah Sad 38:68

Ku, masu bijirewa ne daga gare shi

Verse 69 — Surah Sad 38:69

Wani ilmi bai kasance a gare ni ba game da jama'a (mala'iku) mafi ɗaukaka a lokacin da suke yin husuma

Verse 70 — Surah Sad 38:70

Ba a yi mini wahayin kome ba face cewa ni mai gargaɗi kawai ne, mai bayyanawa

Verse 71 — Surah Sad 38:71

A lokacin da Ubangijinka Ya ce wa mala'iku, "Lalle Ni Mai halitta mutum ne daga laka

Verse 72 — Surah Sad 38:72

Sa'an nan idan Na daidaita shi, kuma Na hura (wani abu) daga Ruhi Na a cikinsa to ku faɗi kuna masu sujada a gare; shi

Verse 73 — Surah Sad 38:73

Sai mala'ikun suka yi sujada dukansu, gaba ɗaya

Verse 74 — Surah Sad 38:74

Face Iblis, ya yi girman kai, kuma ya kasance daga kafirai

Verse 75 — Surah Sad 38:75

(Allah) Ya ce, "Ya Ibilis! Me ya hana ka, ka yi sujada ga abin da Na halitta da HannayeNa biyu? Shin, ka yi girman kai ne, ko kuwa ka kasance daga maɗaukaka ne

Verse 76 — Surah Sad 38:76

Ya ce, "Ni, mafifici ne daga gare shi: Ka halitta ni daga wuta, kuma Ka halitta shi daga laka

Verse 77 — Surah Sad 38:77

Ya ce, "To, ka fita daga gare ta, domin lalle kai la'ananne ne

Verse 78 — Surah Sad 38:78

Kuma lalle a kanka akwai la'anaTa har zuwa ranar sakamako

Verse 79 — Surah Sad 38:79

Ya ce, "Ya Ubangijina! To, Ka yi mini jinkiri zuwa ga ranar da ake tayar da su

Verse 80 — Surah Sad 38:80

Ya ce, "To, lalle kana daga waɗanda aka yi wa jinkiri

Verse 81 — Surah Sad 38:81

Zuwa ga yinin lokaci sananne

Verse 82 — Surah Sad 38:82

Ya ce, "To, ina rantsuwa da buwayar Ka, lalle, ina ɓatar da su gaba ɗaya

Verse 83 — Surah Sad 38:83

Face bayin Ka tsarkakakku daga gare su

Verse 84 — Surah Sad 38:84

(Allah) Ya ce, "To, (wannan magana ita ce) gaskiya. Kuma gaskiya Nake faɗa

Verse 85 — Surah Sad 38:85

Lalle za Ni cika Jahannama daga gare ka, kuma daga wanda ya bi ka daga gare su, gaba ɗaya

Verse 86 — Surah Sad 38:86

Ka ce: "Ba ni tambayar ku wata ijara, a kansa kuma ba ni daga masu ƙaƙalen faɗarsa

Verse 87 — Surah Sad 38:87

Shi (Alkur'an) bai zama ba face ambato ne ga dukan halitta

Verse 88 — Surah Sad 38:88

Kuma lalle za ku san babban labarinsa* a bayan ɗan lokaci