To, addini tsarkakakke na Allah ne, kuma waɗanda suka riƙi waɗansu majibinta, ba Shi ba, (suna cewa) "Ba mu bauta musu ba face domin su kusantar da mu zuwa ga Allah, kusantar daraja." Lalle Allah na yin hukunci a tsakaninsu ga abin da suka zama suna saɓawa a cikinsa. Lalle Allah ba Ya shiryar da wanda yake mai ƙarya, mai kafirci
Da Allah Ya yi nufin Ya riƙi ɗa, to, lalle sai Ya zaɓa daga abin da Yake halittawa abin da Yake so. Tsarki ya tabbata a gare Shi. Shi ne Allah, Makaɗaici, Mai tilastawa
Ya halitta sammai da ƙasa da gaskiya. Yana shigar da dare a kan rana, kuma Yana shigar da rana a kan dare kuma Ya hore rana da wata, kowannensu yana gudana zuwa ga ajali ambatacce. To, Shi ne Mabuwayi, Mai gafara
Ya halitta ku daga rai guda, sa'an nan Ya sanya ma'auranta daga gare shi. Kuma ya saukar muku daga dabbobin gida nau'i takwas Yana halitta ku a cikin cikunnan uwayenku, halitta a bayan wata halitta, a cikin duffai uku. Wannan shi ne Allah Ubangijin ku. Mulki a gare shi yake. Babu abin bautawa face Shi. To, yaya ake karkatar da ku
Idan kun kafirta to, lalle Allah Wadatacce ne daga barinku, kuma ba Shi yarda da kafirci ga bayin Sa, kuma idan kun gode, Zai yarda da ita (godiyar) a gare ku, kuma wani rai mai ɗaukar nauyi, ba ya ɗaukar nauyin wani. Sa'an nan kuma makomarku zuwa ga Ubangijinku take, domin Ya ba ku labari game da abin da kuka kasance kuna aikatawa. Lalle Shi, Masani ne ga abin da yake a ainihin zukata
Kuma idan wata cuta ta shafi mutum, sai ya kira Ubangijinsa, yana mai mai da al'amari zuwa gare Shi, sa'an nan idan Ya juyar da cutar da ni'ima ta daga gare Shi, sai ya manta da abin da ya kasance yana kira zuwa gare shi a gabanin haka, kuma ya sanya wa Allah waɗansu abokan tarewa domin ya ɓatar (da su) daga hanyarSa. Ka ce (masa), "Ka ji daɗi da kafircinka, a ɗan lokaci, lalle kai daga 'yan wuta ne
Shin, wanda yake mai tawali'u sa'o'in dare, yana mai sujada kuma yana mai tsayi ga salla, yana tsoron Lahira, kuma yana fatan rahamar Ubangijinsa, (yana daidai da waninsa?) Ka ce: "Ashe, waɗanda suka sani, suna daidaita da waɗanda ba su sani ba?" Masu hankali kawai ke yin tunani
Ka ce: (Allah Ya ce): "Ya bayi Na waɗanda suka yi imani! Ku bi Ubangijinku da taƙawa. Waɗanda suka kyautata a cikin wannan duniya suna da sakamako mai kyau, kuma ƙasar Allah mai faɗi *ce. Masu haƙuri kawai ake cika wa ijararsu, ba da wani lissafi ba
To, ku bauta wa abin da kuke so, waninSa." Ka ce: "Lalle masu hasara, su ne waɗanda suka yi hasarar rayukansu da iyalansu, a Ranar ¡iyama. To, waccan fa, ita ce hasara bayyananna
Suna da waɗansu inuwowi na wuta daga samansu, kuma daga ƙasansu akwai waɗansu inuwowi. Wancan Shi ne Allah ke tsoratar da bayin Sa da shi. Ya bayiNa! To, ku bi Ni da taƙawa
Amma waɗanda suka bi Ubangijinsu da taƙawa, suna da benaye, daga samansu akwai waɗansu benaye ginannu, ƙoramu na gudana daga ƙarƙashinsu. Alkawarin Allah. Allah ba Ya saɓa wa alkawarinSa
Shin, ba ka gani ba cewa lalle Allah Ya saukar da ruwa daga sama, sa'an nan Ya gudanar da shi yana maremari a cikin ƙasa sa'an nan Ya fitar da shuka game da shi, launukan shukar masu saɓanin juna sa'annan shukar ta ƙeƙashe har ka gan ta fatsifatsi, sa'an nan Allah Ya sanya ta dandaƙaƙƙiya? Lalle ne ga wancan akwai tunatarwa ga masu hankali (ga iyawar gudanar da ruwa a cikin gidajen Aljanna)
Shin fa, wanda Allah Ya buɗa ƙirjinsa, domin Musulunci sa'an nan shi yana a kan haske daga Ubangijinsa, (zai zama kamar waninsa)? To, bone ya tabbata ga maƙeƙasa zukatansu daga ambaton Allah. Waɗancan suna a cikin wata ɓata bayyananna
Allah Ya sassaukar da mafi kyaun labari, Littafi mai kama da juna, wanda ake konkoma karatunsa fatun waɗanda ke tsoron Ubangijinsu, suna taƙura saboda Shi, sa'an nan fatunsu da zukatansu su yi laushi zuwa ga ambaton Allah. Waccan ita ce shiryarwar Allah, Yana shiryar da wanda Ya so game da ita. Kuma wanda Allah Ya ɓatar, to, ba shi da wani mai shiryarwa
Shin fa, wanda ke kare muguwar azaba da fuskarsa (yana zama kamar waninsa) a Ranar ƙiyama? Kuma a ce wa azzalumai, "Ku ɗanɗani abin da kuka kasance kuna aikatawa
Allah Ya buga misali; wani mutum (bawa) a cikinsa akwai masu tarayya, masu mugun halin jayayya, da wani mutum (bawa) dukansa ga wani mutum. Shin, za su daidaita ga misali? Godiya ta tabbata ga Allah (a kan bayani). A'a, mafi yawan mutane ba su sani ba
To, wane ne mafi zalunci daga wanda ya yi ƙarya ga Allah, kuma ya ƙaryata gaskiya a lokacin da ta je masa? Shin babu mazauni a cikin Jahannama ga kafirai
Kuma lalle idan ka tambaye su: "Wane ne ya halitta sammai da ƙasa?" Haƙiƙa, za su ce, "Allah ne." Ka ce: "Ashe, to, kun gani abin da kuke kira, waɗanda suke wanin Allah ne, idan Allah Ya nufe ni da wata cuta, shin su abubuwan nan masu kuranye, cutarsa ne? Ko kuma Ya nufe ni da wata rahama, shin, su abubuwan nan masu kame rahamarSa ne?" Ka ce: "Mai isata Allah ne, gare Shi masu tawakkali ke dogara
Lalle Mu Mun saukar da littafi a gare ka domin mutane da gaskiya. Sa'an nan wanda ya nemi shiriya, to, domin kansa, kuma wanda ya ɓace, to, yana ɓacewa ne a kanta. Kuma ba ka zama wakili a kansu ba
Allah ne ke karɓar rayuka a lokacin mutuwarsu, da waɗannan da ba su mutu ba, a cikin barcinsu. Sa'an nan Ya riƙe wanda Ya hukunta mutuwa a kansa kuma Ya saki gudar, har zuwa ga ajali ambatacce. Lalle a cikin wancan, haƙiƙa, akwai ayoyi ga mutane waɗanda ke yin tunani
Kuma idan aka ambaci Allah Shi kaɗai zukatan waɗanda ba su yi imani ba da Lahira, su yi ƙiyama, kuma idan an ambaci waɗanda suke kiran, wasun Sa, sai gasu suna yin busharar farin ciki
Ka ce: "Ya Allah, Mai ƙaga halittar sammai da ƙasa, Masanin gaibi da bayyane! Kai ne ke yin hukunci a tsakanin bayinKa a cikin abin da suka kasance suna saɓa wa juna a cikinsa
Kuma da waɗanda suka yi zalunci suna da abin da ke cikin ƙasa gaba ɗaya, da misalinsa a tare da shi lalle da sun yi fansa da shi daga mummunar azaba, a Ranar ¡iyama. Kuma abin da ba su kasance suna zato ba, daga Allah, ya bayyana a gare su
To, idan wata cuta ta shafi mutum, sai ya kiraye Mu, sa'an nan idan Muka canza masa ita, ya sami ni'ima daga gare Mu, sai ya ce: "An ba ni ita ne a kan wani ilmi nawa kawai." A'a ita wannan (magana) fitina ce, kuma amma mafi yawansu ba su sani ba
Sai (sakamakon) munanan abin da suka aikata ya same su. Kuma waɗanda suka yi zalunci daga waɗannan, (sakamakon) munanan abin da suka aikata zai same su, kuma ba su zama mabuwaya ba
Ashe kuma ba su sani ba cewa Allah, na shimfiɗa arziƙi ga wanda Yake so, kuma Yana ƙuƙuntawa? Lalle a cikin wancan akwai ayoyi ga mutane waɗanda ke yin imani
Ka ce: (Allah Ya ce): "Ya bayi Na waɗanda suka yi barna a kan rayukansu! Kada ku yanke ƙauna daga rahamar Allah. Lalle Allah na gafarta zunubai gaba ɗaya. Lalle Shi, Shi ne Mai gafara, Mai jin ƙai
Kuma an yi wahayi zuwa gare ka da kuma zuwa ga waɗanda suke a gabaninka, "Lalle idan ka yi shirki haƙiƙa aikinka zai ɓaci, kuma lalle za ka kasance daga masu hasara
Kuma ba su ƙaddara Allah a kan haƙiƙanin* ikon yinsa ba: ¡asa duka damƙarSa ce, a Ranar ¡iyama, kuma sammai abubuwan naɗewa ne ga damanSa. Tsarki ya tabbata a gare Shi, kuma Ya ɗaukaka daga barin abin da suke shirki da shi
Kuma aka busa a cikin ƙaho, sai waɗanda ke a cikin sammai da ƙasa suka suma sai wanda Allah Ya so (rashin sumansa) sa'an nan aka hura a cikinsa, wata hurawa, sai ga su tsaitsaye, suna kallo
Kuma ƙasa ta yi haske da hasken Ubangijinta, kuma aka aza littafi, kuma aka zo da Annabawa da masu shaida, kuma aka yi hukunci a tsakaninsu, da gaskiya, alhali kuwa, su, ba za a zalunce su ba
Kuma aka kora waɗanda suka kafirta zuwa Jahannama, jama'a-jama'a har a lokacin da suka je mata, sai aka buɗe ƙofofinta, kuma matsaranta suka ce musu, "Ashe, waɗansu Manzanni, daga cikinku ba su je muku ba, suna karanta ayoyin Ubangijinku a kanku, kuma suna yi muku gargaɗin gamuwa da yininku wannan?" Suka ce, "Na'am, "kuma amma kalmar azaba ita ce ta wajaba a kan kafirai
Kuma aka kora waɗanda suka bi Ubangijinsu da taƙawa zuwa Aljanna jama'a-jama'a har a lokacin da suka je mata, alhali kuwa an buɗe kofofinta, kuma matsaranta suka ce musu, "Aminci ya tabbata a gare ku, kun ji daɗi, saboda haka ku shige ta, kuna madawwama (a cikinta)
Kuma suka ce: "Godiya ta tabbata ga Allah Wanda Ya yi mana gaskiya ga wa'adinSa, kuma Ya gadar da mu ƙasa, muna zama a cikin Aljanna a inda muke so." To, madalla da ijarar ma'aikata
Kuma kana ganin mala'iku suna masu tsayawa da haƙƙoƙin da aka ɗora musu daga kewayen Al'arshi, suna tasbihi game da gode wa Ubangijinsu. Kuma aka yi hukunci a tsakaninsu da gaskiya. Kuma aka ce, "Godiya ta tabbata ga Allah, Ubangijin halittu